BIYU A ƊAYA

Chapter 7

by @barista

BIYU A ƊAYA 

***
YOTA 13 
Team of FIVE INK LEGENDS 

Dedicated to princess Nimcyluv Sarauta 👸🏻

Page 7

GHANA 

Yamma nayi Bilqees ta bar restaurant kai tsaye ta dawo gida, ta wuce side nasu, Mamanta tana zaune bakin ƙofar ɗakin tana yanka ɗanyar kuɓewa, Bilqees tayi sallama, ta amsa tare da cewa 

"Kin dawo?"

"Eh Mama, barka da gida"

"Yawwa barka dai, ya kika baro cen?"

"As usual"

"Komai lafiya ko?"

"Eh Mama"

"To ya yi kyau, da fatan kin baiwa Alaja hakuri"

"Na bata ta kuma hakura"

"To sai ki kiyaye, ki san irin lafuzan da za ki dinga fitar wa in kina magana da Alaja, kai ko ma da wa kike magana"

"Zan kiyaye Mama"

Wuce ki cire uniform na aiki ki huta"

"To Mamata"

Da sauri ta shige ɗaki, ta cire uniform ɗin ta sanya riga da wando mara nawi ta fito ta karɓi aikin da Mama take yi ta soma yanka kuɓewar tare da cewa 

"Ina son miyar yauƙi"

"Ai nasan kina so shiyasa naje da kaina na sayo"

"Lah! Mama kin yi lafiya, har kika iya kika fita?"

Murmushi Maman Bilqees tayi tare da cewa 

"Jiki yayi sauƙi, ina zaune naji na samu ƙarfin jiki kawai na fita rattaki"

"Mun godewa Allah, Allah ya ƙara lafiya"

"Ameen, ki tashi ki tuƙa tuwon nayi talge"

"To Mama irin na Alaja restaurant zan yi miki"

Suna hira har ta kammala tuƙawa, ta bari zuwa wani lokacin ta kwashe, sannan ta haɗa miyar, a lokacin ana kiran sallah magrib don haka suka gabatar da sallah sannan ta zuba musu abinci suka ci.

"Mama"

"Na'am Bilqees"

"Alaja ta ce nasha nononta"

Ƙirjin Mama ya bada ras, a tsorace ta ce

"Kin sha nonon Alaja, Yaushe? A ina?"

"Haka ta ce a lokacin ina yarinya, wai in kun fita da Babana ku ka barni a gurinta take sanya ni a nono idan ina kuka"

Da ƙarfi Maman Bilqees ta sauke ajiyar zuciya, ta tattaro nutsuwar ta, tayi murmushi sosai da yasa Bilqees kura mata idanu na wani lokaci ta hasken kafi nepa dake maƙale jikin garu da ya haske fuskar mamanta, a hankali ta sauke numfashi tare da cewa 

"Alaja bata mantuwa"

"Kenan da gaske ne?"

"Eh da mun dawo take bamu labarin irin rigimar da kike mata har take sanyaki a busashen nononta"

Dariya Bilqees tayi sosai ta ce

"Babana me yake cewa?"

"Dariya kawai yake yi"

Suna hira har Alaja ta dawo ta bankaɗo labule tare da cewa 

"Mama Bilqees you didn't sleep?"

"Alaja kin dawo? Kin ganni yanzu nake shirin kwanciya"

"Yeah na dawo woo duk na gaji"

"To sannu Alaja a huta gajiya"

"Thank you woo"

Tayi ciki tana ta surutu, haka take yi da ta dawo babu ko sallama take shigo musu ɗaki kai tsaye ko ta tsaya daga bakin kofa ta ɗaga labule su gaisa da Maman Bilqees. Baccin gajiya ya sace Bilqees ganin haka yasa Mamanta ma kwanciyar nan da nan ita ma tayi bacci.


Washegari 

Tun da Bilqees ta idar da sallah asuba bata kwanta ba, kasancewar garin da sanyi ta ɗumama ruwan wanka bayan ta kammala ɗumama musu sauran abincin da ya rage ya kwana. Tana saka da shirya wa Alaja ta yaye labule tare da cewa 

"Mama Bilqees ba ki tashi bane?"

Maman Bilqees dake maƙale cikin bargo ta ce

"Alaja na tashi fah"

"Bilqees ki zo mu tafi"

"A'a Alaja bata yi breakfast ba"

"Za mu yi baƙi aiki za mu fara tun safe, zan bata abin karyawa"

"Alaja da kin yi hakuri"

"Ke Mama Bilqees ina ɗumame ne abin karyawan, sai wani cewa kike yi ta tsaya ta ci, mu je Bilqees indomie da kwai zan saka Laraba ta dafa miki"

Maman Bilqees bata sake cewa komai ba, haka Alaja ta sako ta gaba suka fito bakin gate anan suka tadda Majada suna tsaye suna jiran fitowar su. Duk sun cika kamar za su fashe don haushi, wai Alaja taje ta taho da Bilqees sai ka ce bata da ƙafar tafiya. Mashin suka hau biyu a ɗaya, uku a ɗaya haka suka iso Alaja special restaurant.....


*************************************

A daidai inda take sauƙa a mashin, anan ya sauke, ta sallame shi sannan ta tako zuwa inda nan yaran suke zaune, duk da cikin zuciyarta bata sa ran ganinsu ba a wannan ranar saboda lokaci yaja ba lallai ne ta same su ba. Sai take jin babu daɗi in har yau sun tafi ba tare da ta gansu ba, tana ko ƙarsa gurun ta hango su suna ta wasa, duk hankulansu ya yi nesa a wasan sai Nishaɗi suke yi. Ta sauke ajiyar zuciya tare da lumshe fararen idanun da suke cikin niqap ta buɗe su, ta soma takowa a hankali zuwa kusa da su.

Basu kula da ta iso ba sai wasa suke yi abin su suna dariya, tun da suka fito suka samu abin da suke nema su kayi shirin barin wajen amma sauran daga ciki suka ce su jira sai me rufaffiyar fuska ta iso ta basu biscuits da Alawa sannan za su tafi....

"Yeee ga tanan ta iso"

Cewar Aicha tana murna, nan sauran ma suka daina wasa suka zuba mata ido suna kallon ta har ta ƙaraso ta zauna a inda take zama su ma suka zauna suna kallon ta ba tare da sun yi mata magana ba, ta fuskance su ko gaisuwa basu iya yinta ba, a hankali tayi magana cikin siririyar muryarta 

"Sannun ku yara"

"Yauwa sannu me rufaffiyar fuska"

In ji ɗayan yaron, da mamaki ta dube shi kamar tayi magana kuma tayi shiru ta kalli Aicha tare da yi mata murmushi, duk da basa ganin fuskar amma kuma yanayin ta ya nuna murmushi take yi ta ce 

"Aicha babu gaisuwa?"

Nan duka suka haɗa baki wajen faɗin 

"Barka da safiya"

Bata amsa ba ta ce

"Yaran kirki suna gaida manya da safe, ku ma yaran kirki ne ku dinga gaisuwa"

"To za mu dinga yi"

Suka amsa baki ɗaya, nan ta fiddo da biscuit da Alawa ta raba musu suna murna suka karɓa, ta ce

"Ku tafi gida"

"Eh za mu tafi, ke fa ina ne gidan ku"

"Bani da gida"

Suka tsaya suna kallon ta, Aicha tayi magana irin ta yarinya ƙarama 

"To ina tite tana, ( ina kike kwana?"

Murmushi tayi a hankali ta ce

"Ni ban kai ku maraici ba don ni ban taɓa fita nayi roƙo ko maula ko bara ba"

"Mu ma sanya mu ake yi dole"

Cewar yarinya daga cikin su, cikin tausaya wa ta ce

"In sha Allahu wata rana za ku samu farin ciki"

"A wane gidan marayu kike?"

Inji yaron, ta sauke numfashi tare da cewa, 

"Na gefen makarantar sakandare"

"Lah mu muna na gefen makarantar firamare"

Cewar wacce ta fi Aicha kaɗan da tsawo. Ta sauke numfashi ta mik'e tayi musu sai anjima ganin basu da niyyar tafiya, ta soma takowa tana shirin barin wajen yaron ya ce 

"Ya sunan ki?"

"Uhm ku kirani da Aunty"

"To Aunty mun gode, gobe ma za ki dawo?"

"Eh"

ta faɗa zata juya iska ya ɗaga niqabin da ta rufe fuskar ta dashi, nan take fuskarta ta bayyana sabar tsoron da ganin fuskar yasa su kayi baya suka sake baki, Aicha ta ce

"Lah! Tettawa, ( kyakkyawa)"

Tayi saurin gyara niqabin ta yi sauri ta bar wajen.....


**********************************

Nigeria Maiduguri KIRAWA'S FAMILY

Fitowar sa kenan daga cikin office ɗauke da dukkanin abubuwan da yake amfani dasu ko da ya koma gida ne, ya sanya wa kofar office ɗin key yana ƙoƙarin barin gurin ya ji murya Dr Faisal yana cewa

"Special doctor an fito ne?"

A hankali ya juyo duk gajiya ya nuna a jikin shi, ya ɗan dawo da baya tare da cewa 

"Dr Faisal baka tafi bane?"

"Eh ina shirin tafiya aka ce akwai meeting nayi maka magana"

"Meeting! Yaushe?"

"Yanzun nan amma iya mu waɗan da za mu yi wannan tafiyar"

"Ok mu je"

Tare suka wuce meeting hall, sun tadda yawanci an halarta suka zauna nan aka gabatar da meeting, batu ne akan tafiyar su an yi kiran gaggawa gobe za su bar Maiduguri zuwa Abuja su kwana acen jibi akwai meeting sai gata kuma su tafi Ghana....

Sosai aka yi tayi musu bayanin yadda abin zai kasance, bayan an gama ne Dr Waahab yake tambayar zayyu waɗan da suke da mata su tafi da matan su? Nan aka amsa da eh amma iyaka masauki shine ƙarshen iyakan matan. Nan ko murna wajen Dr Faisal ba a magana.

Bayan sun fito ne Dr Waahab ya wuce parking space ya buɗe motar sa ya shiga ya tada ta kai tsaye ya dawo gida....


**********
Aiki suke yi suna hira yau kam kamar haɗin baki suka yi, duk sun tashi da son yin hira suna yi suna aiki, amma ban da Ashfat, tana fere arish potatoes a hankali tunanin ta baya jikinta ta faɗa a duniyar tunani, basu tanka mata ba, suka ci gaba da hirar su, jin tsayuwar mota yasa Ashfat dawowa daga tunanin da ta tafi ta tashi ta leƙa window kitchen ta hango motar Dr Waahab yayi parking tana gani ya fito har ya shige side nasa, ta sauke numfashi ta juyo taga dukkanin su sun zuba mata na mujiya.

Ta zauna tare da cewa 

"Mene ne kuma?"

"Ai ke za mu tambaya"

Cewar Hauwa, Ashfat ta sauke numfashi tare da cewa

"Ku yi abin gaban ku"

Sun fahimci kwana biyu bata daidai suka kyaleta ta ci gaba da aikinta, suna saka da aiki suka ji ƙamshin turare ya baɗe kitchen suka ɗago idanunsu ya sauƙa kan Dr Waahab dake tsaye sanye da kayan motsa jiki, suka gaida shi ya amsa, Ashfat idanunta kur akan sa, ya kalli Aunty Jamila tare da cewa 

"Har da ke a kitchen?"

"To ya za ayi na ce bari na taimaka"

"Da kin bari su yaran sun yi ai"

Wani ƙaton abu ya tokare wa Ashfat maƙoshi, wato har yanzu basu ma girma a idanunsa ba...

"Ai mun kusa kammalawa"

"Anyway shayi nake so"

"Akwai yanzu aka sauke"

"Ok bani a cup"

Ta zuba masa ya fice kai tsaye wajen motsa jiki, ya tadda Ya Sa'eed zaune suka gaisa ya zauna yana shan shayin, Sa'eed ne yayi magana

"Da alamu yau baka da ra'ayin motsa jiki"

Ya sauke numfashi a daidai lokacin da ya ajiye cup ɗin ya ce

"Me yasa kace haka?"

"Yau baka dawo da wuri ba"

"Eh mun yi meeting ne gobe za mu wuce Abuja"

"Don Allah! Da wuri haka?"

"Eh fah, ni ko shirya kayana banyi ba"

"Bros ya kamata kaje ka shirya"

"Eh amma mu ɗanyi wasan ko juggling ma sai na koma ciki"

"Ok no problem"

Suka tashi suka ɗan taɓa juggling sannan Dr Waahab ya ɗauki cup nashi ya wuce ya ajiye a kitchen a lokacin babu kowa a ciki har sun kammala aikinsu. Ɗakinsa ya wuce sai da ya watsa ruwa sannan ya sanya jallabiyansa ya watsa ruwa ya kwanta.


*********************************

GHANA 

Bilqees suna isowa Alaja special restaurant suka shigo kai tsaye a lokacin ɗaiɗaikun ma'aikatan ma sun fara shigowa, sun shigo Alaja ta ce 

"Laraba ke ko Jummai ku dafawa Bilqees indomie da kwai yanzun nan yunwa take ji"

Jin wannan maganar ta Alaja yasa ransu matuƙar ɓaci, zancen zuci Laraba tayi tana harar Bilqees ƙasa² "ke ba ki da ƙafa ne ko baki da hannun dafawa, don wulaƙanci ma ni zan dafa miki abin da za ki ce"

Haka ma Jummai da take ji kamar ta shaƙo Bilqees ta huce tayi zancen zuci "ai dole ki raina mu tun da kinga ana sanya mu muyi miki hidima, za ki gamu dani"

Ita dai Bilqees ta dubi wannan ta dubi wancen...

"Ba daku nake magana ba, kun yi min kunnen uwar shegu, ke Jummai je ki dafa mata, ke kuma Laraba haɗa min abin karyawa ki kai min ɗaki"

Tana faɗin haka ta wuce ciki, ta barsu nan tsaye Bilqees ta bar wajen sai hararar ta suke yi, ba abin su yi mata tas ba yanzu sai su yi laifi. Haka Jummai ta shige kitchen ba don ranta ya so ba, ta dafawa Bilqees indomie da kwai ta kawo mata.

A lokacin Bilqees tana tsaye tana kallon cleaners dake ta faman gyare-gyare suna ƙayata dining area, duk abin da zai burge customers sun yi decorating nasa tayi matukar ƙayatuwa.

Jummai tana isowa ta dangwarawa Bilqees plate ɗin da ta zuba mata indomie da kwai a hannunta, tayi saurin riƙe wa don kaɗan ya faɗo tayi tafiyar ta. Bilqees ta wuce ɗaki ta zauna ta soma  breakfast, a hankali take ci tana haɗawa da pure water guda ɗaya da ta gani a ɗakin, bata iya ta ci duka ba ta fito dashi ta baiwa cleaners da suke ƙoƙarin barin wajen akan su yi waje da plate ɗin ta dawo ta zauna a Corido tana sauke numfashi.....

Wannan shine rayuwar ta, a kullum gari ya waye, tana zuwa restaurant safe da yamma ta koma gida, saɓanin sauran ma'aikatan da suke kaiwa har dare. Ita ma da ƙyar Alaja ta amince da hakan, shima saboda rashin lafiya Mamanta ne. Customer sun fara isowa ta hango su daga reception tayi sauri ta wuce ciki ta tadda sauran ma'aikatan sun baza kayan girke-girke sai faman aiki su ke yi ta saka hannu ita ma tana yi ba tare da ta ce wa kowa ƙala ba.

Sun kammala aikinsu waiters suka shigo suka fitar da iya abincin da ake buƙata, sai a lokacin Bilqees ta samu ta huta, ta koma ta kishingiɗe tana sauke numfashi, a hankali ta lumshe idanunta...

"Special chef"

Taji muryar Majada ba tare da ta buɗe idanunta ba, ta sauke numfashi tare da cewa 

"Menene?"

"Haba friend, bai dace ki din ga min haka ba"

A hankali Bilqees ta sauke idanunta akan Majada ta numfasa tare da cewa 

"It's over between us Majada"

"Why?"

"Rayuwata da taki ta banbanta"

"Me yasa ki ka ce haka?"

"Please Majada, i can't clarify it"

"Uhm zan zamo kamar ki"

Ta ware fararen idanun kan Majada don tabbatar da abin da take faɗi har zuciyarta ne ko iya fatan baki...

"Da gaske nake"

"Uhm Allah yasa"

"Amin"

Duk da bata wani sake da Majada sosai ba, amma hakan ya yiwa Majada daɗi, ta mik'e ta bar wajen, babu shiri taga an janyo ta wani ɗaki, a tsorace ta ware idanuwa waje tana kallon su, bakinta na rawa ta furta sunayensu ɗaya bayan ɗaya 

"Aunty Jummai, Aunty Laraba" Aunty Zee....

"Sheeeet"

Shine abin da suka ce da ita, tayi shiru tana ci gaba da kallonsu, ta kasa yin shiru ta ce

"Menene haka?"

"Aiki za ki yi mana"

Cewar Jummai, da mamaki ta maida mata da 

"Aiki kuma?"

"Eh Majada, kuma akan ƙawarki Bilqees.....




Comments and share fisabilillah