KAIFI ƊAYA

12

by @ummishatu1111

12

To my old fans, the ones that reads me years ago❤️, it's been a while since I heard from you and honestly I miss you, i miss us, am back with KAIFI ƊAYA a story of love pain and hope to heal. If u still think of me, come meet Dr Mimi & Afeef their story will touch your hearts. I need ur opinions like before, i miss chatting with you in the comment, please come back let's start again together, thank you for being with me from the beginning, I love you all. 💙


Dear Rahama, thank you for the gift you sent me yesterday, the coffee was delicious..... Tnx alot! 


***Tsantsar tsanar da ta bayyana ƙarara akan fuskartace tasa ya dauke idanuwansa daga gareta ya kalli gefe, tamkar ta tashi taje ta rufe shi da duka haka take ji saboda irin bakin cikin da ya ƙunsa mata, wani irin nauyi take jin ƙirjinta da numfashinta sunyi mata,

"Naga miss calls dinki any problem?" ya fada idanuwansa na kallon wani wuri,

"kai wanne irin macuci ne mayaudari azzalumi maci amana? Mun shirya abu da kai rimi rimi amma daga karshe kana kokarin mayar damu kananan yara....... Soo listen and listen good, ko mazan duniya sun kare babu abinda zanyi da kai da sunan miji, tun wuri kaje ka warware abinda ka sarƙa domin wallahi tallahi bazai yi mana kyau ba gaba dayanmu.... Idan har baka warware wannan abun da ka kulla ba you will see the other side of me that even me never knew its existing...... "

" wallahi tallahi Anty Mimi banyi muku haka da niyyar in saka ku cikin matsala ko fushin iyaye ko wani abu mai kama da haka ba, ni kawai nayi hakane dan in tseratar daku daga faɗawa halaka da kuma fushin ubangiji........ Na san yanzu ba zaki fahimta ba amma wata rana ina yi muku fatan ku fahimci tsantsar soyayyata da kaunata gareku, banda mugun nufi akanku Allah shine shaida, maganar yaya Aliyu kiyi hakuri ki manta dashi ki cireshi daga cikin ranki ki dauka Allah gata yayi miki shiyasa ya canja miki dani wanda idan kin karɓa da kyakkyawar niyya zai zame miki mafi alkhairi fiye da auren Aliyu....... Insha Allah zamu rayu tare har gaban abada..... "

Gaba ɗaya wannan maganganun nasa jinsu take kamar yana watsa mata wuta shiyasa bata san lokacin da ta tashi daga inda take zaune ba ta nufe shi tana zuwa ta wanke shi da mari zuciyar ta kamar zata buga dan ɓacin rai,

" ƙarya kake yi ni bazan taɓa rayuwa dakai ba maci amana makaryaci mayaudari.... Wanne aure ne kake maganar zai yi albarka? Auren da aka gina shi da ƙarya da yaudara da cin amana da kuma zalunci? Idan har ka san ba zaka sake niba meyasa tun farko baka fito ka fada mana ba ka nuna mana zaka yi yanda muke so? Ba zan taɓa rayuwa dakai ba idan ma wannan shine plan dinka wallahi ni nafi karfin ka...... "

" Anty Mimi ki fahimceni...."

Kunnuwanta ta toshe ta kurma ƙara tamkar mai aljanu babu shiri ya fita daga cikin dakin yana jiyo ihunta kamar wata karamar yarinya, yana fita daga cikin part din hajiya yaci karo da suhana tana kokarin shiga, motar shi kawai ya shiga yabar gidan ya koma asibiti wurin Irfan,

Kayan kwalliyar ta dake jere reras gaban mirror taje ta fara watsi da su tana ƙara saboda tsabar bakin cikin da take ciki kenan ma bashi da niyyar rabuwa da ita ko sakinta? Shiga cikin bedroom din suhana tayi a kidime tana shiga ta rike ta,

"Anty Mimi me yake faruwa? Me kike yi haka?"

"suhana ba zan iya zama da wannan yaron ba..... Akan me? Saboda me?" ta karasa maganar cikin ƙara,

"ya isa anty Mimi, calm down...... Yi hakuri, zo ki zauna..... Yi hakuri..... Yi shuru.... Zauna" suhana ta fada cikin lallabawa, kama hannunta tayi suka je bakin gado ta zauna tana haki,

"Haba anty Mimi komai yayi zafi fa maganin sa Allah, wannan abun da kike yi kamar karamar yarinya bai dace dake ba..... Kiyi hakuri ki nutsu...."

Shuru Anty Mimi tayi tana mayar da numfashi idanuwanta a runtse, ta san duk yanda zata yiwa suhana bayani ba zata fahimceta ba tunda ba wai zata fito ne fili ta sanar da ita yanda abin ya faro ko kuma ya samo asali ba,

" Breakfast din da na kawo miki baki ci ba anty Mimi why?" suhana ta tambaya tana duba warmers din da ta ajiye mata tunda safe,

"bana jin yunwa..... Am no hungry"

"daurewa zaki yi anty please....."

"zanci idan ina jin yunwa"

Tashi suhana tayi ta gyara mata kan mirror dinta ta tattare wanda suka fashe ta fita.

Tun daga wannan ranar bata sake saka shi cikin idanuwanta ba ko taji motsin shi duk da cewa time to time yana zuwa gidan, kwanan yaya haidar biyar a asibiti ta tambayi hajiya tana son taje ta duba shi amma hajiya tace ba zata je ba tayi masa fatan samun sauki daga gida Allah zai amsa ba sai taje ba, duk da tana son zuwa dole tana ji tana gani haka ta hakura domin bayan hanatan da hajiya tayi harda sake fadawa Abba nan shima ya hana yace koda wasa kar yaji ta je duba Aliyu idan kuma ta matsu da dole sai taje to ta kira mijinta suje tare, ta rasa yaya zata yi da bakin cikin da take dawainiya dashi cikin zuciyarta. 

Yaya Aliyu tunda yake kwance gadon asibiti bai san wanda ke kansa ba sai yau da ya farfaɗo har ya samu bakin magana, Umma mahaifiyar shi dake tare dashi ya kalla sai janan kanwarshi cikin bakin cikin da yake jin har ya koma ga Allah bazai bar cikin zuciyarsa ba yace da umma,

"umma Mimi ta zo?"

"Mimi bata zo ba Haidar amma kowa yazo ya duba ka, ka koma ka kwanta ka daina magana...."

"umma Abban anty Mimi bai kyauta min ba, abinda yayi min ko bare ba zai yimin ba, ya zabi Afeef sama dani, he takes Afeefs side......."

Haushi, ɓacin rai da damuwa umma ta shiga bayan Aliyu ya gama rattaba mata duk abubuwan da suka faru wanda sune suka ja har yayi wannan accident din, umma cika tayi tai fam shiyasa da daddare bayan magriba kowa yana zuwa ganin haidar ana ta murnar ya fara magana yana gane kowa da Afeef yazo umma kicin kicin tayi da fuska ta hade rai kamar bata taɓa dariya ba haka kuma da kyar ta amsa gaisuwar shi ita kuwa janan ko gaishe shi bata yi ba dan gaba daya haushinsa suke ji bama shi kadai ba har da iyayen anty Mimi da ita Mimin, ita laifin ta wai bata zo ta duba shi ba, su kuma Abba da Ammi laifinsu sun fifita Afeef akan Haidar, shi dai Afeef bai kawo komai cikin ransa ba ya juya ya fita duk da cewa Aliyun bai amsa gaisuwar shi ba, yana fita Abba ƙarami ya shigo wato Abba baƙi mahifin su Aliyu, har lokacin umma a turɓune take,

"Ya mai jikin? Ya dan ci abincin kuwa?"

"Au dama ka damu dashi ne? Ai na zaci kai baka damu dashi ba yanda sauran mutane suka damu da ƴayan su...."

Kallonta Abba yayi cike da mamaki,

"ban fahimce ki ba.... Ban gane abinda kike fada ba.... Duk me ya kawo wannan maganar?"

"Ai bazaka fahimta ba dama, kowa ya nuna nasa yake so sai kaine baka son naka, kowa ya koma daga bayan ɗansa ya goyi bayansa amma kai banda kai, to idan kai baka son sa ni ina son sa saboda yanda kowanne ɗa ya tsaga jikin uwarsa ya fito nima haka ya tsaga jikina ya fito, wallahi bazan taɓa ƙin ɗana ba akan na wani.. " gaba ɗaya maganganun nan na umma ɗaurewa Abba kai suka yi saboda a iya saninsa abinda ya faru bai wani kai ya kawo ba, sannan hukuncin da ɗan uwansa ya yanke akan wannan saɓanin da su haidar suka samu yayi daidai dan ko shine irinsa zai yanke, ya san idan ya tsaya yi mata bayani ba lallai ta fahimta ba sannan nan asibiti ne bai kamata su zauna suna hayaniya ba akan marar lafiya da girman su da komai dan haka ya juya ya fita kawai ba tare da ya zauna ba, duk da ya fita din umma bata iya yin shuru ba haka ta cigaba da fadar duk abinda yazo bakinta. Washe gari kamar yadda Ammi ta saba da kanta ta shiga kitchen ta hada abinci wanda za a kai asibiti dan tunda ya kwanta kullum ita ke kai musu abinci safe rana dare sannan ana kaiwa daga bangaren hajiya kaka ma, yau harda kunun tsamiya ta yiwa Aliyu saboda shi masoyin kunun tsamiya ne, tare da suhana suka tafi Irfan ya kai su, tun shigar su cikin dakin da Aliyu yake Ammi taga kamar fuskar umma babu walwala sannan ta canja, zama tayi tana tambayar ya mai jikin umma ta amsa ciki ciki,

"Allah ya bashi lafiya, ga kunun tsamiya nan da na iyo masa idan ya tashi sai ya sha..."

"Ai da ma kin barshi kawai, wanda akayi a baya ma ya isa amma wannan yanzu ku koma dashi kawai mun gode...."

Shuru Ammi tayi tana nazarin maganar da umma ta fada amma sai taga bai dace tayi shuru ba gara koma menene su warware shi a yanzu,

"umman janan me yake faruwa? Yanzu dan na kawowa Aliyu abinci ai ba wani abu bane, ba duk ɗaya bane..."

"ba ɗaya bane, ada shine ake ɗaya amma yanzu kowa nasa yake so.... Banda haka me zai saka ku amince ku yarda ku aurar da Mimi ga Afeef bayan Aliyu ne ya aureta ai ana barin halal dan kunya, sannan kun fi kowa sanin so muke mu haɗa Afeef da janan aure tun suna ƙanana, tun janan tana jaririya da aka haife ta muka kuduri niyyar aurawa Afeef, amma saboda kowa kansa ya sani kuma nasa ya sani shine kuka murde magana kuka karkatar da ita kuka bawa Afeef Mimi, idan har akwai zumunci da kaunar juna ya dace Aliyu ya saki mata Afeef ya aura? Idan har akwai kara da kunya ya dace ku bawa Afeef yar ku bayan Aliyu ne ya taɓa auren ta? Idan ma zaton ku Aliyu ne baya haihuwa shiyasa kuka dage har sai da kuka raba su kuka kashe auren yanzu kuka aurawa Afeef to ɗana lafiyar sa ƙalau kuma bashi da matsalar haihuwa dama ai maza basu cika zama juya ba sai mata ne ke zama juya..... "

" Yanzu duk akan wannan umman janan kika kullace mu har kike irin wadannan maganganun a gaban yara? Ai da Aliyu da Mimi da Afeef ni duk daya ne awurina.... "

" wallahi karya kike yi ba ɗaya bane, daga ke har mijinki iya kanku kuke so.... Kuma anyi walkiya "

" Ammi tashi mu tafi... " suhana ta faɗa cikin dacin rai, wannan wacce irin masifa ce daga zuwan su shikenan kamar dama ana jira?

" A'a suhana bari tukunna ta gama fadar duk abinda take son ta fada, ni bani na hada auren Afeef da Mimi ba nima ina zaune aka kawo min goro haka bani naje na raba auren mimi da haidar ba shine dan radin kansa ya saketa to yayi mata saki ɗai ɗai ɗai har uku ya zamuyi da su? Ai dole a hakura ta auri wani tunda ba a garin mahaukata muke ba.... "

" ai shiyasa kuka aura mata kanin bayansa wanda suka fito tsatso daya saboda babu kunya bare kara.... "

Tashi suhana tayi ta fice daga cikin dakin bayan ta dauki basket din dake dauke da abincin da suka zo da shi, tana fita ta hango hajiya da Afeef da ya kawota sun nufo dakin Irfan yana gefen su.......