13
13
***Yanda umma ke magana a zafafe cikin zafin rai shine yafi komai bawa Ammi mamaki, to ko umma ta manta irin zazzafar soyayyar dake tsakanin Haidar da Ammi ne? Itace fa ta raineshi tun daga yaye ta hada su da Faruk ta raina har suka girma suka kai minzalin aure, shi Aliyun ma sai bayan da ya girma sannan ya gane ba sune iyayen sa ba su umma ne saboda a hannun Ammi ya taso,
"Wadannan maganganun da kike yi ummansu sai nake ji a raina kamar dama can akwai wani miki acikin zuciyarki ko kuma akwai wani kulli da kika ajiye...."
"babu abinda na kullata acikin raina, kawai dai gani nayi lokaci yayi wanda zamu fadawa kawunanmu gaskiya tunda kowa yanzu nasa shine nasa sannan iya nasa yake so...."
Suhana tana tsaye ranta idan yayi dubu a bace yake su hajiya suka ƙaraso, babu wanda ta iya buda baki ta yiwa magana tana ji suna tambayar ta har sun fito zasu tafi ne?
" ku kyale ƴar jakar uba, tana ji ana yi mata magana.... " inji Hajiya ita dai Suhana bata tanka ba tana ganin su suka shiga ɗakin da yaya Aliyu yake kuma suna shiga suka ji Ammi na cewa,
"maganar fa kowa Nasa yake so bata taso ba dan kece kika fahimci abin ahaka sannan kika juya shi izuwa hakan shiyasa kike kallon kamar yanzu kowa bayan nasa yake bi, ni har gobe Aliyu matsayin ɗa yake awurina, baida banbanci da yaran da na haifa dan duk ɗaya nake kallon su... "
" wallahi ƙarya kike wannan maganar ba har zuciyarki ba..... Da ɗaya kike kallonsu da yayanki kamar yadda kika fada ai da baki goyi bayan a rusa rayuwar sa ba.... Auren cin amana auren ɓata zumunci "
" wai me yake faruwa ne nake ta jin maganganu satata kamar saukar ruwan sama? " hajiya kaka ta bukata lokacin da ta kai tsakiyar cikin ɗakin,
" hajiya sannu da zuwa, babu komai dama magana ce akan abinci da na kawowa Aliyu umman sa tace baya bukata in koma dashi, duk dai maganar akan auren Mimi ne da Afeef...... "
" to me ya faru da auren Mimi da Afeef din? Aure nice nan na bada umarni aka daura shi sai akayi yaya? "
" to umman janan ta dauki laifin ta dora a kaina tana ganin kamar da saka hannuna ko hadin bakina..."
"ko da hadin bakinki ko babu, ko da saka hannunki ko babu aurene dai na cin amana aka yi da rashin kara...." umma ta fada cikin faɗa da matsanancin fushi,
"Au haka akayi? Amanar wa aka ci?" hajiya ta fada cike da mamaki,
"Hajiya..... Ammi.... Umma dan Allah abar maganar nan haka, a asibiti fa muke, muna tare da marar lafiya bai kamata a saka shi a gaba da hayaniya ba..." Irfan ya fada cike da damuwa,
"hakane Irfan, muje dama tafiya za muyi...."
"Dan Allah idan kun tafi ba sai kun sake dawowa ba mun gode iya haka ma"
Hajiya bata ce komai ta juya ta fita nan suma su Ammi suka bita daya bayan ɗaya suka fita haba sai yanzu suka gane dalilin shurun da suka ga Suhana tayi musu lokacin da suka zo ashe itama bakin ciki ne ya fito da ita kuma ya hana ta magana. Har suka koma gida babu wanda ya iya cewa uffan akan maganar, hajiya ɓacin rai kamar me, ganinta bai kamata umma ta farfadi irin maganganun da ta fada ba ko dan ganin idonta,
Suna isa gida hajiya tace da Ammi su wuce part dinta, anty Mimi tana zaune a falo tana kokarin haɗa coffee ko wai zata samu taji karfin jikinta saboda rabon ta da abinci 2 days kenan shiyasa gaba daya jikinta babu kwari, shigowarsu hajiya ya katse mata tunanin ta da take yi,
"wai me ma ya sakata duk ta yiwa mutane irin wannan dibar albarkar? Akan wanne dalili? Saboda me?" hajiya ta tambayi Ammi wadda ta samu wuri ta zauna suma su Afeef duk sun zazzauna,
"wallahi hajiya ban sani ba ko dama akwai wani abu acikin ranta sai Allah, nifa abinci kawai muka je mu kai musu nida suhana sannan mu duba Haidar, shikenan fa daga zuwanmu umman janan tace basa bukatar abinci mu koma dashi kuma kar a sake kai musu wai ai mun koma daga bayan ƴarmu mun ware Haidar maganganu dai iri iri ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba..... "
" Kina ji? Ranar da Aliyu yayi accident faɗa suka yi da shalele, Ya daddaki Afeef akan dai wai kawai Afeef yace kar ya sake ganin ya daukar masa mata a motar sa, shine fa nan Abbansu ya yiwa tufkar hanci yace bai yarda ba kar kuma a sake, shine Aliyu ya futa cikin fushi yaje yayi wannan hatsarin, to menene abin laifi anan?"
" ita tace wai ai bayan yayan mu muka koma su muke so kuma abayansu muke.... "
" ki rabu da ita, kar ku sake zuwa asibitin da sunan duba Aliyu, nima ba sake zuwa zanyi ba, tunda haka take so kuma ta zaba "
Anty Mimi duk tana jin abinda yake faruwa take ta sake shiga damuwa jin wata sabuwar matsalar tana kokarin kunno kai cikin family din, gaske dai Afeef ya zamar mata masifa inama tun farko Aliyu ya fahimce ta sannan ya gane hakan zata faru da duk ba akai ga haka ba da tuni hakan bata faru ba gashi nan yanzu abubuwa sai sake damalmalewa suke yi suna sake tsananta suna yin tssmari, ba za ta iya shan wannan coffee dinba duk da ta san tana da bukatar sa, barin falon tayi ba tare da ta ji karshen maganar ba, shi kansa Afeef abun ya bashi mamaki saboda bai taba zaton umma zata iya rufe ido tayi wani abu makamancin hakan ba duba da irin hadin kai da kuma kyakkyawar alakar dake tsakanin ahalin shekara da shekaru kai kusan ma tun daga tushe dan baka gane ɗan wannan da ɗan wannan saboda babu bambanci kuma kowanne ɗa yana iya zama a gidan duk wanda yake so babu mai takura masa ko karara bare nuna banbanci, ita dai Ammi tashi tayi ta koma ɓangarenta ranta duk babu dadi dan wannan shine Karon farko da irin hakan ta faru a tarihin zamansu kuma tun daga ranar bata sake komawa asibiti da sunan duba Aliyu ba kamar yadda hajiya ta bada umarni, duka iyayensu maza babu wanda ya san hakan ta faru sai Abba baƙi da yake dan zargi kan lamarin saboda shima umman ba wai kyale shi tayi ba.
Bayan faruwar lamarin da kwana biyu suhana ta fito daga side dinsu da safe zata shiga side din hajiya anty Mimi na nemanta ta hango janan itama tana fitowa daga side dinsu dauke da warmers da alama girki tazo daukar musu zata koma asibiti, duk da taga janan din ta dauke kai tayi kamar bata ganta ba amma hakan bai hana ta karasawa ba inda take,
"janan.... Ya jikin yaya Haidar?"
"yana nan kullum yana ƙara samun lafiya, ɗan bakin ciki sai dai ya mutu....."
"me kuma ya kawo maganar yan bakin ciki anan? Wa yake bakin ciki da samun lafiyar tasa?"
"oho, yo abu a duhu, ai ta yuyu ba haka aka so ba a ganshi ya cigaba da rayuwa shiyasa aka yi masa turin jeka ka mutu, amma da yake ranshi da lafiya awurin Allah yake ba mutum ba gashi nan a raye...... Aikin banza"
Janyo mayafinta suhana tayi saboda ganin ta juya zata tafi,
"ai komai aka yi da jaki sai yaci kara, ke yanzu banda jakanta ko wani ne kika ji yana fadin haka a kanmu ai sai inda karfin ki ya kare..... Dan yaya Afeef bai aureki ba sauran maza sun kare a duniya ne?"
"naji dadi da kika fahimci haka,kuma sai me dan bai aureni ba, auren da yayi auren cin amana, auren son zuciya, insha Allah wannan auren babu inda zai je....."
"ehh anji anyi cin amanar, ke me ya hana ya aureki, insha Allah idan ma wannan shine fatanki da burinki auren anty Mimi da yaya Afeef mutuwa ce zata raba...."
Faɗa ne ya kaure tsakanin suhana da janan a haka anty Mimi ta fito saboda ta gaji da jiranta ta same su suna cacar baki kamar zasu dambatu, ko kallonta janan bata yiba ta ja tsaki ta fice ganin ta karaso inda suke,
" suhana menene haka kuma?
"anty Mimi wallahi bance mata komai ba daga tambayar jikin yaya Aliyu shikenan ta hau farfada min maganganu....."
"ya isa koma gida kawai, bari naje office.... Dama abu zan saki kiyi min bari kawai sai na dawo" motarta taje ta shiga ta fita daga cikin gidan ita kuma suhana ta koma wurin Ammiey. Tamkar kazar da ƙwai ya fashewa acikin ciki haka ta samu kanta lokacin da take driving gaba daya hankalinta baya kan tuƙin da take yana can wata duniya daban ta tunani, ada family dinsu abin sha'awa ne sannan abin kwatance agari kuma awurin duk wani wanda ya san su amma yanzu akan wannan maganar gashi nan kawuna sun fara rarrabuwa gaba tana shirin shiga tsakani, bata san traffic lights ta tsayar da ita ba kawai sai ji tayi garammm ta bugi wata mota dake gabanta, cike da masifa da bala'i mai motar ya fito dan har danger dinshi ta baya ta fashe haka kuma wurin da ta bugeshi ya lotsa ya mokaɗe motarshi sabuwa mai kyau da tsada,
"innalillahi wa inna ilaihir....... Ya salam" ta faɗa gabanta yana faduwa kuma babu shiri ta cire sit belt dinta itama ta fita,
"ke makauniyar ina ce? Are you blind? Bakya gani ne ko yaya? Saboda kawai baku san zafin nema ba kuna kwance a gida an siyo muku motoci an baku shiyasa zaku fito kuna tuki na gadara da ganin dama ko?....."
"Dan Allah bawan Allah kayi hakuri, ina da emergency ne da yawa zanje hospital in duba su...... Kayi hakuri ka fada min amount din da zai yi fixing motar, please am very sorry....." ta fada tana ɗaga masa ID card dinta, gani yayi da gaske din ita medical doctor ce sannan ya gamsu da bayanin da tayi shiyasa kawai ya jijjiga kai yace,
" Babu komai kawai kije...."
"nagode madalla, kuma ina mai sake baka hakuri akan abun da ya faru...." Komawa cikin motar ta tayi ta nufi asibitin.
Days on
***
Rayuwa take cikin bakin ciki da ɓacin rai da kuma damuwa, rabon da ta ga Afeef tun ranar da suka dawo daga asibiti dasu hajiya da Ammi, ko aikin ta ma yanzu kam sai a hankali dan tamkar bata san aikin nata ba yanzu dan yadda take gudanar dashi akwai damuwa acikinsa, duk patients din da take dubawa da wadanda take yiwa theater matsaloli na biyo baya kawai sa'ar da ta samu kuma Allah ya taimaketa shine ba asamu asarar rai ta silar ta ba,
Yau dai da taje office kira ta samu daga sama wato hukumar dake kula da asibitin har da ƙarin baƙi da suka zo daga hukumar lafiya ta ƙasa wadanda keda alhakin kulawa da duk wani likita, lokacin da ta shiga conference hall din nasu taga dai MD na asibitin sai sauran manyan Doctors da consultants sai kuma baƙin da suka zo,
"Dr a gaskiya ba zamu cigaba da zuba ido kina kokarin salwantar da rayuwar al'umma ba, ranar kin bawa wata mai ciki injection wadda bai kamata abawa pregnant women ba, a dai wannan ranar kin bawa wata mata mai diabetes wata injection wadda ba ayiwa masu wannan ciwon, kinyi theater sama da guda goma duk matsala tana biyo baya, gaskiya ba za mu cigaba da taking wannan risk din ba...... Ina ganin lokaci yayi da ya kamata ki koma gida ki kwanta ki huta ki samu isasshen bacci...... Dr we are concerned your performance has declined, patients safety is at risk" wannan shine bayanin da Chairman yayi mata bayan sauran baƙin da manyan likitoci sun gama yi mata tambayoyi masu kama da na ƙurulla, sannan sun yi doguwar tattaunawa da ita, license dinta suka karɓa da identity card dinta da coat sannan ta tashi ta fita dan bata da wata hujja wacce zata kare kanta ko kuma wani abu mai kama da haka, office dinta ta shiga ta tattara nata yanata ta fita daga cikin asibitin idanuwanta jajur duk da bata yi kuka ba, gudu take shararawa har Allah ya kaita gida lafiya, Hajiya da jikokinta suna falo ta shiga ta zauna jikinta ba ƙwari, kallo ɗaya hajiyan tayi mata ta gane bata cikin nutsuwarta, sai da hajiyan ta matsa mata da tambayar me ya faru da ta dawo yanzu bayan lokacin dawowarta bai yi ba sannan ta fada mata anyi suspending dinta a asibiti kuma an karɓe license dinta, lokacin ne ta samu damar barin hawayen da suka jima cikin zuciyarta suna tafarfasa samun damar zubowa...........