Nadama page 18
by @mrsomar
NADAMAR DA NA YI🙆🏼
FATIMA ISAH
( MRS OMAR)
PAGE 18
********
"Ina zaki ai kya bari mu tafi tare ko? anya Fatima kin yi wa rayuwarmu adalci kuwa? Lokaci ɗaya duk kin ruguza komi yanzu ga abinda kika jawo mahaifinki ya yi fushi dake akan wannan makauniyar soyayyar dana tabbata yaron nan ba son gaskiya yake maki ba kece ke sonsa bashi ba."
Jajayen idanunta ta ɗago ta kalleshi dasu da suka koma kamar gauta ta yi murmushi takaici muryarta na rawa ta ce.
"Ya Faruok kenan you will never understand how much Musaddik loves me. Musaddik jinin jikina ne zan iya fuskantar komi dan ganin na chechi soyayyarsa. Musaddik namiji ɗaya tamkar da dubu, farin cikina ne shi, bani da farin ciki da ya wuce naga na auri Musaddik ba wanda zuciyata tafi tsana ba."
"Shikenan Fatima na yarda zuciyar ki bazata taɓa sona ba, duk abinda na yi mata ni kam nasan da sonki zan mutu, saboda duk lokacin danayi yunkurin cire soyayyarki a zuciyata to a ranar bazan taɓa barci da lafiya ba, Fatima na barki ki auri wanda kike so."
Muryarsa ta yi rauni sosai dan har sai da kwalla suka taru a gurbin idonsa, da sauri ya fito daga motar shi daidai lokacin Bilal na shirin parking itama jiki babu ƙwari ta buɗe ƙofar ta fito, ita take gaba suna binta a baya a babban parlourn kakar tasu suka yada zango, ganinta zaune ta kurawa TV ido tana kallon wani shiri daga tashar Arewa24 mai suna rayuwar matan ayau ana tattaunawane akan yawan sakin aure a arewa.
Ganninsu yasa ta maido hankalinta wajensu cike da mamaki.
"A'a umaru kune da safiyar nan inji dai lafiya?"
Murmushi sukayi suka samu waje suka zauna da sauri takai dubanta wajen Fatima ta ce.
"To fatsima har dake ake tafe anya tafiyar nan ta lafiya ce?"
Ido Faruok ya lumshe ya ɗan numfasa kafin ya ɗago kai ya dubi kakar tasu ya ce.
"Iya da sauki dai?"
"Kamar ya Umaru faɗa min meke faruwa."
"Iya akwai matsala babba na aikata abinda yasa nazo daga baya ina dana sani na saka yarinyar mutane a cikin matsala sanadin haka yasa Daddy ya yi ikirarin bazata zauna mashi a gida ba."
"Kaga Umaru ni fa ban gane inda wannan maganar taka ta dosa ba ka fito fili ka gaya min."
Kai ya girgiza ya shaƙi iska ya fitar sannan cikin murya can ƙasa ya ce.
"Na saketa Iya nayi mata sakin da ta haramta a wajen..."
Bai ida magana ba Iya ta buga yare tana faɗin
"Hande, hande en boni, yanzu Umaru irin sakayyar da zakayiwa iyayenta kenan? Anya Umaru."
"Iya kiyi hakuri banso nasa baki ba amma wallahi wannan matsala duk tana wajen Fatima.."
Hannu Faruok ya dagawa Bilal da sauri yana faɗin.
"Please, Bilal, just keep quite. You know I love Fatima please don't say anything about her."
"Taya zanyi shiru bayan ga gaskiya sai kaƙi faɗinta ka ɗaurawa kanka laifi."
Murmushi Faruok ya yi dan irin maganar da Bilal keyi da hausa yasan Iya zata iya yarda da abinda Bilal zai faɗa yasa ya ce
"Bilal wace gaskiya bayan wadda na faɗa ko kana so na ɗaurawa yar mutane laifin da bata aikata ba? No, Bilal. I beg you, just keep your mouth shut, please for my sake."
"Alright I'll do as you say."
"Thank you."
Dubanshi Faruok ya maida ga Iya ya ce.
"To Iya kinji abinda ya faru dan Allah Fatima ta zauna nan kafin Daddy ya sauko kuma nasan kece kawai zakiyi masa magana yaji."
"Umaru kenan ƙarya kake abinda ka faɗa min ga abokinka nan naso ya faɗi gaskiya ka hanasa anya Umaru."
"Iya kenan iya gaskiyar kenan na faɗa maki kuyi hakuri iya da irin kunyar dana baku ban cika alkawarin ba."
Shiru Iya tayi tana kallonshi saida ya gama magana ta ce.
"Naji Umaru amma ka sani zata zauna a nan na wani lokaci amma duk ranar da gaskiya ta yi halinta na gane ita ce keda laifi to tabbas nima sai ta bar min gida."
"Insha Allahu bama za'ayi haka ba."
Ita dai Fatima duk tana jinsu bata tanka ba, sun ɗan jima suna fira kafin suka tashi har zasu fita Faruok ya dawo ya cewa Iya yana son zaiyi magana da Fatima tashi Iya tayi ta basu waje, inda take zaune bata gusa ba yazo ya zauna ya kura mata manyan idonsa ya ɗan ɗauki lokaci yana kallon ta amma ita kam taki ɗago kai.
"Fatima yanzu cikin ƙwanakin da bazasu wuce wata biyu ba anyi komi an gama, Fatima ada duk son da nake maki na wasa ne ban gasgata haka ba sai jiya a darenmu na farko Fatima kina da wata baiwa da bako wane namiji bane ya kamata ya zama mijinki nagartacen namiji ne kawai ya kamata ya zama mijinki Fatima kina da baiwa."
Sai da ya numfasa kafin ya ci gaba da cewa.
"Fatima ki rufawa kanki asiri kada kiyi kuskure auren makahon nan."
"Dakata ya Faruok dama tunda naji ka fara magana nasan sai ka kushe abun kaunata, to kasani wallahi ban taɓa NADAMAR rabuwa dakai ba, ina farin cikin sosai dan yanzu zan mallaki abun kauna ta."
Tana rufe baki ta wani tashi zata wuce Faruok cikin zafin zuciya ya fincikota da karfinsa ta faɗa masa.
"Kina tunanin wannan makahon shine farin cikin ruhinki? alright naji kuma na yarda ke kina son sa amma shi ba son gaskiya yake maki ba."
"Naji a tunaninka kenan ka barni na shiga ciki kana taɓa ni ko ka manta ni ba matarka bace yanzu."
"Hahaha sai ki bari ki gama ida kafin ki fara ƙiran kanki a bazawara amma har yanzu ke matar aure ce."
Fuska ta yamutsa ta yi shiru dan tasa duk maganar da ta yi Faruok na dai-dai da ita.
"To ki ɗaga ni kinji jiki mai daɗi ba irin na makahonki ba kin kasa tashi."
Ido ya kashe mata ɗaya.
Cike da kunya Fatima ta tashi da sauri ta nufi dakin da suke sauka idan sunzo.
Faruok har ta shige yana kallonta.
Faruok na fita Bilal ya haushi da bala'i.
"Yanzu major abinda kayi ka kyauta wannan wace irin soyayya ce kuke daga kai har ita a rashin sani?"
"Hmm Bilal kenan wannan ita ce soyayya ta gaskiya anyway mubar wannan maganar ma ida a office."
Juyawa yayi ya shiga mota yabar Bilal a tsaye dan yasan halin Bilal da nacin magana.
*********
Su Fatima kenan tana shiga ɗaki ta maida ƙofa ta rufe ta ɗauko waya ta danna number Musaddik tamkar yana jirin kiranta ya ɗaga da sauri.
"Amincin Allah ya tabbata a gare ka yakai kyakkyawan mijina na har abada."
"Tare dake sarauniyar matayen duniya."
Murmushi ta yi cike da jin daɗi ta ce.
"Noor Hayat anya kana missing ɗina."
"Kamar ya mekika gani."
"Hahaha babu komi wasa nake maka, albishirinka."
"Goro amma idan ba albishir ɗin takardar sakinki zakiyi min ba to kiyi shiru da bakin ki."
"Oh my God me kakeci na baka na zuba, yau Faruok ya sake ni saki har uku."
"Oh my God are you sure."
"Yes dear mun kusan kasancewa tare har abada."
Knocking ɗin da ake ne yasa maganarta ta tsaya cak tana kallon ƙofa..