GADAR TSAUTSAYI

GADAR TSAUTSAYI 34

by @nusybee143

Page 34



Shaheeda dai ko zata ganta a bakin wuta ba zata taɓa canjawa daga Shaheeda ba,don haka ta dube shi a zafafe ta ce"idan karuwanci zan yi ba zan wahalar da kaina na zo nan ina roƙonka aiki ba,na san hanyoyi da yawa da zan yi karuwanci ba sai na wahala wajen wani aikin dabam ba,idan karuwa kake so ba sai ka bada aiki ba,ka san inda za ka same su"ta ja tsaki ta miƙe ta fice daga office ɗin a fusace 

A ranar yini ta yi cikin ɓacin rai saboda abin da aka yi mata,amma hakan bai saka ta karaya ba, washe gari ma ta sake fita neman aikin 

Haka ta yi ta yawon neman aiki a kamfanoni,amma rashin takardu ne yake yi mata cikas,na ƙarshe ma ce mata ya yi"ki nuna min wata shaida na cewa kin taɓa yin karatu a matsayin software engineer,na yi miki alƙawarin zan ɗauke ki aiki a kamfanin nan"jikinta a sanyaye ta tashi ta fice daga office ɗin,don dai a yanzu bata da wata shaida,bata sake nadamar banzatar da karatunta akan soyayya ba sai yanzu 

Lokacin da take ba wa su Azeema labarin abin da yake faruwa idan ta je neman aiki daga ita har Azeema kuka suke yi, Rabi'u ne ya ja numfashi ya dubi Shaheeda ya ce"Fatima,akwai alamun cewa ba komai kika gaya mana game da kanki ba, lokaci ya yi da ya kamata ki faɗa mana komai,kin ga an zama ɗaya,kuma ba mu san ta inda zai yiwu mu taimaka miki ba

Na gane kamar ke ba irinmu ba ce, ƴar ƙauye ko yar talakawa, saboda yanayin mu'amalarki da mutane da kuma wayewarki,don Allah ki gaya mana gaskiyar abin da ya same ki idan har kin ɗauke mu kamar yadda muka ɗauke ki"

Babu musu ta goge hawayenta,a hankali ta fara ba su labarinta tun daga tafiyarta karatu zuwa ƙasar Belgium har zuwa lokacin da ta kama haya a gidan nasu,ta ƙarasa cikin matsanancin kuka, saboda ita kaɗai ta san irin ciwon da take ji a duk lokacin da ta tuna mahaifinta ya yi disowning ɗinta,ya bar wa duniya ita, duk da yadda yake tsananin sonta,kuma itama take tsananin sonshi 

Kafin ta kammala labarin Azeema ma ta yi kuka har da shiɗewa,shi kanshi Rabi'u sai da ya dake sosai ya hana kanshi zubar da hawaye, labarinta ya dake shi sosai, ya taɓa masa zuciya sosai,a haka ma ta yi juriya,da wata ce tsaf trauma zata jefa ta a cikin wani mawuyacin halin 

Cikin dakewa ya dube ta, cikin sanyin jiki ya ce"babu komai, Allah ya ji mana mai kyau, rayuwa ce sai da jarrabawa, Allah ya ba ki ikon hayewa,mu ma haka muke rayuwa ba mu da kowa,dama ita Azeema marainiya ce,ni kuma ni kaɗai uwata ta haife ni, waɗanda muke uba ɗaya suna da wadata sosai,amma sai mu wuni ba mu saka ko ruwa a bakinmu ba saboda talauci,a gabanmu za su ci abinci mai rai da lafiya amma amma babu wanda zai yi tunanin yi mana tayi,ganin wahala da wariya zata iya yi mana illa ya sa kan dole muka bar garin muka dawo birni,gashi nan kuma muna gurgura rayuwar, sai fatan Allah ya kawo mana ɗauki"

Daga lokacin sabo da kulawa ya sake shiga tsakanin Shaheeda da ma'auratan,ta ɗauke su a matsayin ƴan'uwan da ta rasa a rayuwarta, Rabi'u shine cin su,shan su,suturarsu da duk wani jigo nasu,hakan ya sake kwantarwa da Shaheeda hankali sosai 

Tsawon watanni uku suna tafiya a haka,ba su da wata bayyananniyar matsala,sai dai wadda ba'a rasawa,a lokacin kuma Allah ya kawo musu wata Sabuwar jarrabawa 

Tun Rabi'u yana jinya a tsaitsaye har ya kwanta sosai,gashi fama ake yi da kuɗin maganin Mubarak, wanda Shaheeda take kai shi ganin likita lokaci zuwa lokaci, kuma dama Rabi'u ne yake biyan kuɗin maganin 

Tun ciwo yana ƙarami har ya girma, dole aka kwashi Rabi'u zuwa asibiti 

Tashin hankali ba'a saka maka rana! tashin farko aka buƙaci kuɗi masu yawa don a yiwa Rabi'u gwaji, kuɗin da ko kwatankwacinsu ba su da shi, hankalinsu ya tashi, dole Shaheeda ta koma ta kwashi ƴan kunnanyenta na Gold ta shiga da su kasuwa ta siyar, duk da cewa ba'a siya da daraja sosai ba amma bata damu ba,biyan buƙata ta fi dogon buri 

Bayan ta biya kuɗin gwaje-gwajen aka zo aka ɗauki sample ɗin da ake buƙata ita kuma ta dawo kusa da Azeema ta zauna, suka cigaba da jimami da fargabar amsar da za'a ba su 

Sai ga sakamakon ciwon hanta,kuma ana buƙatar kuɗi mai yawa don a yi masa treatment,sannan kuma a ɗora shi akan magani, hankalinsu Shaheeda ya tashi,don ba su da kuɗin da aka buƙata ba su da dalilinsu,tuni Azeema ta fashe da kuka cikin tsananin tashin hankali,don ta san idan ya mutu sai ta fi kowa shiga wani hali 

Shaheeda ce ta kwantar mata da hankali, sannan ta ce "ki daina dansa, in sha Allah zuwa anjuma na ga wasu gidaje masu manyan gate,ba za'a rasa na Allah a cikinsu ba,sai mu nema masa taimako,zan tafi da katin maganin,ke kuma sai ki zauna a wajensa"Azeema tana murmushi ta ce "na gode Shaheeda,ki bar Mubarak a nan saboda rana, kuma kin ha yana ta fama da zazzaɓi"babu musu Shaheeda ta kwanto shi daga bayanta,ta miƙawa Azeema shi,dama bata son yawo da shi sai dole saboda larurarsa

Gidajen masu hali ta fara bi don neman taimako,tana nuna takardun asibiti na Rabi'u,sai dai babu abin da ta samo,sai ma a gidan ƙarshe da aka sakar mata karnuka ta fito a guje,ta yi kuka sosai, zuciyarta cike da ƙuna da baƙin ciki,daga nan ta fara bin masallatai,shima dai ba wani abu ta samo ba, kasancewar yau ɗin ba juma'a ba ce

Daka ƙarshe dai titi ta dawo tana bara tana roƙon a taimaka musu da kuɗin magani,ta yi matukar gajiya,ga yunwa,don tun safe ta fito, yanzu ana maganar ƙarfe biyar na yamma,bata karya ba,ko ruwa ma bata sakawa cikinta ba

Gaba ɗaya abin da ta samu Naira dubu shida da ɗari huɗu ne,ga shi abinci mai ba su da shi,kuma gobe take saka ran mayar da Mubarak asibiti, saboda jikinsa da ya fara dawowa,don tun wancan satin ya kamata a ce ta koma asibiti an sake duba shi 

Wujiga-wujiga ta shiga asibitin, Azeema da take zaune rungume da Mubarak da yake ta bacci ta taso da sauri tana faɗin "Fatima na ji ki shiru, Allah ya sa lafiya,ga jikin Mubarak yana ta tsananta,tun ɗazu yana ta kuka jikinsa yana zafi,ga numfashinsa dai ƙoƙarin ɗaukewa yake yi, likitoci kuma sai magana suke yin bar yaya ba'a biya kuɗin magani ba"hawaye suka zubo mata tana kallon Azeema ta ce "kuɗin ba su da yawa Azeema,ga abubuwa suna ta ƙara yi mana yawa,ina tsoron jikin Mubarak Azeema, zazzaɓi yake sosai,gobe kawai zan je kasuwa na siyar da laptop ɗina da wayata na biya Bill ɗin yaya na kai shi asibiti shima"

Azeema ta kwantar da murya ta ce"babu komai,mu zuba idanu kawai mu ga abin da Allah zai yi,amma kar ki siyar da kayan da kika ce da su za ki fara aiki, ba'a san abin da gobe zata haifar ba"

Shaheeda ta goge hawaye ta ce"biyan buƙata ya fi dogon buri Azeema,yaya fa yana kwance babu lafiya,shine mai kula da komai namu,ga Mubarak shima, yanzu idan muka rasa ko ɗaya a cikinsu ne ya kike tunani?

Gwara na siyar kawai,zuwa nan gaba Allah zai kawo wani"Azeema ta rungume ta suka cigaba da kuka tare, cikin damuwa da jin rashin gata

Ilai kuwa a ranar da zazzaɓi Mubarak ya kwana, numfashinsa yana sarƙafewa,ga Rabi'u wanda kuɗin da aka bayar ba su isa ba,amma an fara duba shi,ga damuwa,da ƙyar Shaheeda ta iya cin abinci kaɗan,duk da tarin yunwar da take ji 

Washe gari kuwa da wuri ta koma gida,ta ɗauko laptop ɗinta da wayarta don ta je ta siyar 

Wani darasi da Arnold ya taɓa koya mata ne ya faɗo kanta, don haka ta zauna ta gwada don ta gani 

Cikin Sa'a kuwa ya yi, lokaci guda Naira dubu ɗari biyar ta faɗo account ɗin ta

Ai kuwa wani ihun farin ciki ta yi har tana taka rawa,shikenan yanzu zata biya kuɗin maganin Rabi'u,ta mayar da Mubarak asibiti,su ci abinci mai kyau,ta kamawa Rabi'u ɗaki mai kyau ma,dama kullum sai tsangwama da hantararsu ake yi a ward ɗin su Rabi'u, saboda ɓangaren maza ne,ga su kuma mata,sam ba sa wani sakewa a wajen 

Ai kuwa nan da nan ta wuce banki,a can ta yi ATM card da bata da shi, sannan ta ciro dubu ɗari biyu ta wuce asibitin,tana zuwa ta biya kuɗin maganin Rabi'u,ta biya aka canja masa ɗaki zuwa VIP,sannan ta siyawa Azeema lafiyayyen abinci ta kai mata

Azeema ta saki baki tana kallon abincin,ga nama iya nama,sai haɗiyar yawu take yi,ta ce "Fati idan muka kashe kuɗin kuma fa?

Gashi ko Mubarak ɗin ba ki kai asibiti ba"tana murmushi ta ce"ke dai ci,babu abin da zai gagara in sha Allah,komai zai warware da ikon Allah"Azeema ta girgiza kai ta ce "ba zan iya ci ni kaɗai ba alhali na tabbatar ba ki ci ba,ki zauna mu ci tare to"

Shaheeda ta girgiza kai ta ce "ba zan iya cin abinci a wannan halin ba, dole sai na kai Mubarak asibiti tukunna,ke dai ci abinci kawai"daga haka ta yi waje ba tare da ta sake sauraren Azeema ba

Yau bata juma ba a asibitin ta dawo asibitin da aka kwantar da Rabi'u,ta yi mamakin ganin Azeema bata ci abincin ba,ta dube ta tana faɗin "meyasa kika ƙi cin abincin Azeema?ke ma fa akwai ki da taurin kai"

Azeema ta girgiza kai ta ce"ke ma kin san ba zan iya cin abinci ba alhali na san ba ki ci ba,ki zauna kawai mu ci"babu musu Shaheeda ta zauna suka fara cin abincin tare

Kwana uku suka ƙara a asibitin aka sallami Rabi'u,a lokacin Azeema ta fara tsorata da hidimar kuɗi da Shaheeda take yi musu, saboda komai na su ya canja,cima yanzu lafiyayyiya suke ci, ba'a maganar na Rabi'u ma,da Shaheeda ta tanadar masa duk abubuwan da likitoci suka ce su zai iya ci 

Sai da suka nutsu a gida,bayan sun gama cin abinci, Rabi'u yake tambayar Shaheeda ina ta samu wannan kuɗin da ko hanyar rabinsu ba su da shi?

Azeema ta dube shi da mamaki ta ce"yaya kwamfutarta fa ta siyar da wayarta,ka gansu ai masu kyau da tsada ne"Rabi'u ya kalle ta, Shaheeda ta girgiza kai ta ce"ba su bane,wata hanyar samu ce ta buɗe min"

Azeema da ɗoki ya kama ta ta ce"wacce hanyar samu ce haka?"

Kai tsaye Shaheeda ta ce"ka san na je neman taimako wajen ƴan siyasa da masu madafun iko na gwamnati,neman taimako da ba ka da lafiya,amma duka sun hana mu,ni kuma na ga ai kuɗinmu ne,don haka na yi amfani da ƙarfin ilmin computer da Allah ya ba ni na fasa account na bankin na ɗibi kuɗi, dama ai namu ne, don haka rabona na ɗiba"

Wani kallo suke yi mata a tsorace, Rabi'u ya ce"kina so ki janyo mana masifa dai ko Fati?

Shiga harkar gwamnati fa!kina gaya min za ki rinƙa ɗibar kuɗin gwamnati,ba kya tsoron kamu da hukunci?"

Kai tsaye Shaheeda ta ce"babu mai iya kama ni,idan kuka ba ni haɗin kai komai zai yiwu,ba saka ku zan yi a cikin wannan aikin ba,asalima dole zan ɗauke ku zuwa nesa,shima Mubarak zan yi nesa da shi,ko don jinyarsa,ba zan iya riƙe shi ba,gwara na kai wa wata ƙanwar mahaifiyata shi "

Yanzu kam sun fara yi mata kallon taɓaɓɓiya, Azeema ta ce"to tunda ba kya son Mubarak ɗin ki ba ni na riƙe shi"

Wani kallo Shaheeda ta yi mata ta ce"wa ya ce miki bana son shi?

Kawai hakan ya fi ne,za mu bar nan,za mu samu ingantacciyar rayuwar da muke muradi,na yi karatu mai kyau a jami'ar Ghent University ta ƙasar Belgium, mahaifina ya narkar da kuɗi mai yawa,kuma nima na takure kaina na koyi karatu sosai, mijina ya koya min abubuwa da yawa,sai kuma a ce bayan duk wannan saboda wasu common takardu a ce ba zan wasa basirata ba?

Ba zai yiwu ba kuwa! yadda na wahala na yi karatu ya kamata na ci moriyar karatun,na samu na rufawa kaina asiri haka nan

Yanzu dai ku shirya,nan da kwana uku za mu bar garin nan,don bayan kuɗin magani na sake hacking na samu kuɗi million biyu,sai mu san yadda za muyi ko?"







#Nusy_bee