Chapter 2
by @reeeyarh
TA SILAR KA 2
Ka cuce ni Ahmad ka cuce ni basan maina maka zaka saka mini da haka ba me ayra ta maka nayi dana sanin sanin ka Ahmad ka bata mini rayuwar diyata yarinyar da itace komai nawa inallilahi wa inna illaihi mai yasa sai yara na Ahmad na dauke ka kamar dan dana haifa ban taba koda maka kallan banza ba.
Ahmad kasan rayuwar danayi a baya kasan wahalar rainan yara kuwa me ayra ta maka she’s still young yarinyar da bata da uwa.
WACECE AYRA
A Shekarun baya a wani kauye dake jahar Jigawa mai suna yalleman wanda duk yan gari kudi gare su har ana cewa haka garin yake Allah ya azurta su sosai ta fanin kudi, alhaji Ahmad adam saffa mutun ne wanda yana daya daga cikin masu kudin garin Allah ya azurce shi da yara hudu wanda duk mata ne daya ne namiji kuma shene auta.
Sosai yaran sa sukai karatu duk ba a kasar ba sanda suka dawo babbar sunan ta sadiya wacce yanzu babbar lawyer ce sai mai bi mata da ta rasu sai kuma mai bi mata mai suna Asmau wanda sunan mahaifiyar ta aka sa mata sai na miji adam (papa).
Sanda papa ya gama degree farko a political science 2 a wannan lokacin yana da shekara 25 baban shi ya mishi aure da waya yar kanwar shi wacce sunan maman shi gare ta ba’a dade da mishi aure ba yace shi dai ya koma karo kararu a uk inda anan yake rayuwa a Oxford university da yawa daga cikin makarantar an sanshi har maganar shi ta fara fitowa gari.
Sanda ya gama degree na uku ne matar tashi ta haihu taci sunan kakar ta Asmau ana kiran ta da husna a wannan lokaci sosai ake maganar shi a kasar inda har takai shuwagabanin kasar sun bashi aiki koda ya fadawa baban shi yace kawai yayi aikin shi abin shi a kalla a wata yana samun 50 million.
Husna nada shekara shida aka haifi ayra mai suna halima, akoi abun da mahaifiyar ayra ta gane tun tana ciki papa ya dau soyayyar duniya ya daura mata har aka haifo a lokaci sosai samun kudi, haka ya shagoba ta sosai yayi mata gata.
Ayra tun tana karama ta shaku da baban ta hake suke rayuwa sosai ya daura mata soyayya duniya, wani lokaci sunje nigeria a garin su cikin dare yan fashi suka far musu inda anan suka kashe mom din ayra a lokacin bata fi three years ba.
Duk da sun harbe shi amma shi bai wani jinyata ba amma sanda akaiwa mom komai yana asibiti dan saida yayi kwana biyu ya farfado sosai yayi kukan rashin matar shi aiko ana 40 ya kawshe yaran shi ya koma inda ya fitoh damun a lokaci ayra was serious sick dan bata saba da kowa ba sai iyayen ta hakan yasa rashin mu ta shiga mumunan yanayi.
Sanda muka dawo na kaita asibiti nan aka ce zuciyar ta ta tabu because kullun tana kuka tana a kaita wurin mom bata da aiki ko cikin bacci badda kiran mom.
Saida yayi kusan ten years baije nigeria sai dai dangin shi suzo inda yake babu yadda ba,ayi dashi yayi aure ba amma yaki dan haka baban shi ya aura mishi wata yar uwar tashi shekarar su hudu da aure tazo haihuwa ta mutu abinda ta haifa shima ya mutu a lokacin ayra ta gama secondary school.
Husna kuma ta gama degree farko tana na biyu sosai sukaji mutuwar dan ayra saida tayi karamar jinya a lokaci mahaifin papa ya rasu dan haka babu mai takura masa akan ya sake aure, magaifiyar shi itama ta rasu bayan rasuwar baban shi da yan watanni.
Haka yaci gaba da kula da yaran shi inda anan husna ta gama degree ta na biyu Allah ya fitoh mata da miji wanda yayan friend dinta ne yan South Korea ne nan ta koma can da zama, papa mutun ne mai mutunci da karamawa sosai yake taimakon yanuwan shi duk da suma da nasu kudin.
Bayan husna tayi aure yarage daga papa sai ayra anan ma wata shakuwa ce ta shiga tsakanin su sanda ta gama degree ta na farko ne papa zaije nigeria tace zata bishi dan bata kuma zuwa ba tun bayan rasuwar mom.
A wannan lokaci ne daya je tace ita bata son zaman abuja dan Allah su koma yallema rigima sosai ayra ta mishi a nan ne suka hadu da shugaban Amy of nigeria shine ya hada su da GENERAL AHMAD MUHAMMAD KILA.
Saida aka zagaye gidan da sojoji sannan ya barta nan sukai two months sannan suka dawo abuja inda a lokaci wata shakuwa ta shiga tsakanin papa da gener inda yake jinshi kamar dan uwan shi na jini.
Sanda suka dawo abuja ne idan ayra tayi laifi har take gudun a hada ta da gener dan tana matukar tsoron shi shi papa har yake ganin is normal ya samu wanda yake controlling rashin jin ayra haka ya kuma yarda dashi sosai.
Ayra irin yaran nan ce da kudin baban ta sam bai dame ta ba amma bata ji ko kadan kuma bata damu da wani abuba wai shi media ba ko hoto bayi take ba kota kota.
A halin yanzu papa ya fitoh ta kara wandda abokin shi ne ya bashi shawarar hakan ya fitoh takarar shugaban kasa baki daya.
BACK TO STORY
A hankali papa ya sauko kasa yace gener dan girman Allah ka fada mini waya turo ka ka fada mini gener me ayra ta maka, cikin hawaye yace papa I’m sorry ka yafe mini amma wallahi babu wanda ya turo ni kaddara ce ta hau kaina.
Tashi ka tafi gener, kaje idan kayi hakan danka cutar dani ko ita Allah zai saka mana idan kuma kaddarar ce kamar yadda ka fada Allah ya maida muku ita alkairi, papa, just live gener.
Haka gener ya tashi ya fice bai tsaya ko ina ba saida airport dan bazai iya zama garin nan ba haka ya shiga jirgi, jirgin na tashi gener ya jingina da kujerar ya rufe idon shi.
SOME MONTHS AGO
gudu zugar gener keyi akan titi suna saurin zuwa gida domin magriba ta gaba toh nan sunzo daidai wata kwana wata budurwa na tsaye tana waya suka watsa mata ruwa aiko da sauri ta dauko dutse ta cilla a motar karshen wadda bata karasa hucewa ba.
Kittt motoh cin suka tsaya sojoji suka fara fitowa nan gener yace basu umarnin su dawo su huce kar’a kula koma waye, dan haka suka huce suka tafi a lokaci bai wani damu da ganin yarinyar ba.
Ita kuwa daga nan gidan wasu yan uwan su suka huce tace ita a raka ta gida haka aka raka ta amma da suka je sai aka hana su shiga gidan saboda sababib masu aiki ne gidan.
Wata number ta danna ta kira tace papa your gate mans sun hana ni shigowa gidan, a speaker tasa wayar dan suji aiko mutumin yace sorry baby new workers ne aka dauka duk da turanci suke maganar, tun kafin su gama magana aka kira su aka basu umarnin su bata hanya ta huce.
Sanda ta shiga a bakin kofa ta tsaya tace papa ni nayi fishi dakai kasa new workers sun wani tare ni dan haka good night bata shiga ba ta huce wani part din.
Gidan ba wani babban gida bane part biyu ne ciki sai wurin masu aiki, dan haka ta huce part dinta a lokacin papa bai kula taba dan yana da bako, wanka tayi tayi sallah sannan ta kunna tv tana kallo anan bacci yayi awan gaba da ita.
Sanda papa ya gama abinda yake sukai sallah tare da shugaban masu aikin yaje part din dan su sheda ta amma ya ganta kwance kan kujera tana bacci murmushi yayi yace ka ganta ko taje tayi abun da bata saba ba gashi yanzu tazo tana bacci kan kujera.
Karasawa yayi yana tashi ta dan yasan tabbas bata ci komai ba amma taki tashi zaunar da ita yayi yace baby ba kiyi dinner ba fa, cikin bacci ta turo baki tace papa nidai bazan yi ba I’m angry with you, ohhh baby idan kikai fishi dani ya zanyi I’m sorry babana please ko zaka hada mani tea.
Babu musu yaje ya hado tea yana tunanin wannan sangarta irin ta ayra sanda ya dawo ta fara bude idon ta kadan kadan a haka papa ya samu ya bata tea din sannan ya kaita daki ya kwantar ya kashe mata light.
Koda ya dawo palon yace babana kaga halin ta ko, murmushi kawai yayi yace gaskiyya ne papa wannan ayra yar gata ce sosai tunda nazo gidan nan maganar ta ake, ummm ai yarinyar ce saida lalla ba haka suka huce.
Koda suka koma papa yace ya zabi wurin kwana gida ai sunan baban shi gare shi dan haka ya dauka nan kamar gidan su ne yayi komai yake so, shidai baice komai ba nan papa yace toh kawai yaje dakin gefen ayra mana ya zauna tunda shima dan gida ne.
Haka suke rayuwa gidan saida suka cika kwana biyar amma ko so daya basu taba haduwa ba ranar yana zaune bakin gate papa ya kira shi yace ga ayra nan ta fitoh kar ya sake ya batta ta fitah aiko tana zuwa ya hade girar sama data kasa .
Data je taji gate din rufe shine tazo tace mishi hey kaga gate man din nan, bai kula ta ba tace I’m talking to you fa, nan ma shiru ya tashi zai bar wurin ta rike rigar shi juyowa yayi ya mata wani mugun kallo daya sata tayi saurin sakin shi ta fashe da kuka.
Baiko kulata ba ya huce abin shi aiko tasan hakan aikin papa ne dan haka ta huce dakin ta tasha kukan ta ana haka bayan one week papa yayi tafiya uk bada ita ba, haka suke rayuwa duk sanda zata fita gener ya hana ta ranar tazo fita babu kowa wurin aiko tayi sanda ta fice.
Allah ya taimaka gener yaga fitar ta yayi saurin binta aiko yasha gaban ta dai dai wata mota tazo inda take, cikin sanda da yake bai fitoh da komai ba kawai sai ya janyo ta jikin shi kokarin raba jikin ta da nashi tayi amma saiya sake rungumai ta cikin rada yace if you dare move again saina tsinka miki mari banza kawai.
Suna cikin haka ne sauran ma’aikatan suka karaso da sauri yace arrest them all yaja hannun ta suka huce ciki har cikin dakin ta ya kaita yace wallahi kika sake kokarin fita sai ranki ya baci.
Cikin tsiwa tace who the fuck are you to say this to me, aiko wani wawan mari ya zuba mata yace try me and see stupid yayi waje, ranar haka ta yini tana kuka amma ta kasa fadawa papa.
Saida yazo bacci ganin baiji motsin ta ba yasa a hankali ya bude dakin tana kwance tana bacci ta wani hade kai da guiwa wani tausayin ta yaji ganin ta haka dan yasan ba lalle an taba mata abinda ya mata yau ba shima zuciya ce ta dauke shi.
Karasawa yayi a hankali ya kira sunan ta aiko a zabure ta farka tana kiran sunan papa ganin shine yasa tayi saurin yin baya hanun ta ya kama ta fixge aiko ya kara daure fiska yace let’s go for dinner, kai ta girgiza mishi tace I’m not hungry, you have to ya kuma kamo hannun ta.
Tashi yayi ya tashe ta wata red sleeping dress ce jikin ta wacce rigar iya guiwa ta tsaya sai wani hannun dan karami da sauri ya dauke kanshi kan bedside yaga top din dan haka ya dako ya mika mata bata amsa ba harya juya ya kalle ta.
Have it, a hankali cikin yanayin mai jin bacci tace zafi, wani kallo ya mata yace you need more slap kenan da sauri ta girgiza mishi kai tace no I’m please don’t slap me again tana amsa.
Juyawa yayi harta gama saka rigar sannan ya juyo yace let’s go ya sata gaba yana bayan ta direct dinning area sukai da kanshi ya zuba mata abinci tace mishi please tasha tea because dare yayi bata cin abu mai nauhi, ya gamsu da hakan da haka ya hada mata.
Data gama saida ya tabbata ta kwanta sannan ya huce nashi dakin kiran sallar farko ne ya tashe shi saida yayi abinda zaiyi ya fitoh domin zuwa masallaci nan yace bari ya tashe ta bai karasa ba tun daga bakin kofa yaji muryar ta mai dadi tana raira karatun qur’ani mai girma.
Haka ya huce masallaci abin shi koda ya dawo baiji muryar ta ba dan ya dade acan din hakan ya bashi tabbacin bacci ta koma dan haka ya huce nashi dakin ya kwanta bai tashi ba sai around 10:00 wanda shima ihun tane ya tashe shi.
Babu shiri ya mike jallabiyar gefen gadon ya dauka ya zura sannan yayi dakin yana shiga daga ita sai towel da alama daga wanka ta fitoh ma kallo daya ya mata ta shiga hankali ta.
What about the shot, shagobe fuska tayi tace naji kukan kare and ina tsoron shi please kace a fita dashi wani takaici ne ya kama shi ko amsa mata baiba ya huce daga dakin, yana komawa wanka ya shige abin sa.
Sanda ya fitoh tana zaune palo tana video call da papa tana tambayar shi yaushe zai dawo, soon my girl badai kiyi musu rashin ji, yes papa, good girl zan shiga meeting see you later, kashe system din tayi tana kokari kuka bai ko kulata ba ya huce abin shi.
Around 12:00 ya dawo tana zaune inda ya barta cikin wata murya mai dadi yace have you eaten your breakfast, kasa tayi da kai tace good afternoon, bashi na tambaye ki ba i said kinyi breakfast, kai ta girgiza mishi yace why, ba’a kawo mini ba, ke baki iya ba, kai ta daga mishi.
Fita yayi bai jima ba ya dawo da daya daga cikin yan aikin gidan ta shiga ta hada mata saida ya tabbata taci dan a gaba yasa ta tana cikin ci aka kira shi a waya nan yayi picking a hankali yace Wslm, afternoon wifey ya kike, Masha Allah, ummmm, than, okay I will see you later, karki damu zan kira ki ina wani aiki ne.
Kallan ta yayi yaga shi take kallo wata harara ya watsa mata da tayi saurin kasa da kanta haka kullun yake kula da ita amma sosai take tsoron shi har papa ya dawo bayan two weeks nan take complain akan wannan sojan daya kawo kullun yana takura ta sai taci abinci waye waye har wani koikoyar yadda yake magana take.
Papa kallan bakin kofar yayi yace karaso mana babana dama ayra gulmar ka take, murmushi yayi duk da bai wani saki fuska ba ya karaso palon ya harare ta ta turo baki har kasa ya gaida papa nan papa yace ya tashi daga kasa ya dawo nan ya zauna yana nuna mishi gefen shi.
Ai ko da sauri ayra tace papa wurin zaman yaya kace wani ya zauna tab babu ruwa na kuma ni kar ace in tashi idan tazo ta karasa maganar tana karya da kai, toh yanzu tsakani da Allah yayar taki ba tayi aure ba ai space dinta sai asa wani.
Toh papa ai shima yana da auren, kallan shi papa yayi yace da gaske, murmushi kawai yayi yana mamakin surutu na ayra wanda tunda baban nata ya tafi a rana baifi ta fadi kalma goma ba ashe haka take.
A hankali yace ehhh papa harda baby girl, lalai ne Masha Allah Allah ya raya kace kaima auren wurin baban ka ya maka murmushi dayafi kuka ciwo yayi yace papa my father was not they when i get married i wish he’s.
Ayya sorry Allah ya mishi rahama, Ameen papa nagode, karka damu i wish i will be like a father to you, murmushi yayi yace thank you papa, a hankali ayra da idon ta ya ciko da kolla tace Allah ta mishi rahama, Ameen thank you.
Kallan su papa yayi yace let’s have dinner naga kamar bacci za kiyi ko baby, kai ta daga mishi tace papa please gobe naje gidan iyya Allah tunda ka tafi baya barina na fita ta nuna gener, murmushi papa yayi yace daidai kenan.
Papa ta fada a shagobe, daga yau he’s like a brother to kuma baki san sunan shi ba zaki na nuna shi, a hankali tace I’m sorry papa bansan sunan shi ba, what kuna tare kusan month kice baki san sunan shi ba ayra anya da gaske kike.
Papa da gaske i don’t know, ummm gaskiyya ne babana ka ciri tuta tunda har haka ta kasan ce, murmushi yayi yace ai ko magana bata fi yayi ba, ita ayra, ehhh, murmushi yayi yace da dalili gaskiyya dan ayra tana saurin saboda mutane.
Ni papa I’m hungry, ka bari ki san sunan yayan naki ko kuwa, baki ta turo papa yace his name is Ahmad ido ta zaro tace papa sunan grandpa ne fa tayi dariya tace sunan tsofafi yake da, gidan ku ayra.
Kunan ta ta kama tace sorry my love, dungure mata kai papa yayi yace da wana suna zaki na kiran shi tace grandpa wani kallo ya mata tayi kasa da kai papa yayi murmushi yace no change the name da alama brother ki baiso, tashi tayi zata bar palon tana turo baki.
Cikin wata murya mai sata ta shiga hankali ta yace come back here and sit, papa bai ce mishi komai ba duk da yaji wani iri saboda soyayyar da yake mata amma yana ganin mutunci shi sosai.
A hankali ta dawo ta zauna yace daga yau idan aka miki magana kika ce zaki bar wurin you will see yadda zanyi dake kin jini, kai ta daga tana kokarin fara kuka yace i don’t want to see those tears, aiko daf ta rike hawayen ta.
Sai yanzu papa ya gane dalilin da yasa ayra bata saba da shi ba amma ya birge shi tunda yana iya yiwa mutun abu gaban iyayen shi toh bazai taba cin amana ba dan haka yanzu zai daura kula da ayra a hanun shi dama tun tuni so yake tasan rayuwa dan iya gaskiyya yasan ya shagobata da yawa dan baya iya mata fada komai zatai.
Haka yace muje muci abinci babana, nan suka mike suna isa zata zauna yace ta zuba musu abinci, papa baice komai ba shidai kallan su yake kawai, kuka ta fashe dashi dan ita harga Allah bata san yadda zata zuba abinci ba.
Tashi yayi da kanshi ya zuba abinci sannan ya zauna murmushi papa yayi yace baby wai kuka bai miki wuya ne nikam, kai ta girgiza yace toh have your dinner and duk abinda ya miki ke yake taimako dan haka a yanzu baki da kamar shi tunda dama ku ba brother kuke dashi namiji ba.
Saida suka gama sannan yace kije ki kwanta za muyi magana da papa, papa ta kalla yace jeki idan na gama zan zo, no papa ta huce baza ka jeba dare yayi you have to rest a hankali ta huce tana tsoron tayi wani abu ya mare ta dan maganar shi ta zauna a brain dinta.
Tana fita ya kalli papa yace I’m sorry papa dan nasan you are not feeling good abinda nake mata but I have to papa kayi hakuri ba ina nufin yarka bata da tarbiya ba amma she have to know life soboda ayra shagabor ta tayi yawa kayi hakuri papa yadda ka dauke ni bazan iya ganin yarka haka na barta ba.
Murmushi yayi yace daidai kake ai babana karka damu i will always support you duk abinda kawa ayra na dauka kamar a yayan tane ya mata dama tun tini ina son hakan ya faru but bansan taya ba.
Murmushi yayi yace thank you papa, it’s my pleasure papa kaje ka kwanta dare yayi, tam kaima jeka kwanta maza, papa karka damu basai kaje wurin ayra ba i will check on her murmushi yayi yace tam shikenan babana,haka ya huce.
Koda yaje dakin ta yayi knocking a hankali tace papa come in, har zai juya sai kuma ya shiga tana zaune da towel da alama wanka tayi ganin haka yasa ya juya dakin shi ya huce shima ya shiga wanka sanda ya shirya cikin kayan bacci yana zaune yana waya da safeera yaji karar bude kofar ta dan haka ya fita domin ya duba.
Gani yayi tayi hanyar waje cikin kakausar murya yace ina zaki, da sauri ta juyo ta kalle shi sai tayi kasa da kanta, ba dake nake magana ba da sauri tace zanwa papa saida safe, get back to your room ya nuna mata hanyar dakin.
A hankali ta huce dakin tana shiga ta banko kofar ta sa key kallan kofar yayi kawai ya huce ya koma daki saida ya kira safeera sukai waya sosai kafin ya kwanta.
Washe gari bata tashi ba sai wajen 11:00 sanda ta gama komai 12:00 tayi direct wurin papa ta huce yana zaune yana waya zama tayi gefen shi harya gama sannan ta gaida shi ya amsa yayi kissing forehead din ta yace how was your night.
So boring, zaro ido yayi yace how, because of that man you call my brother, ayra i don’t want this, papa wallahi i hate him, reason, cause komai yayi baka mishi fada kuma fa kana gani yana mini fada.
Hannun ta ya rike yace ayra ki daina fadar haka you will always be my number one babu wanda ya fiki, amma papa, ayra kamar yadda kika san komai nawa yanzu ma zan fada miki Ahmad mutumin kirki ne I just feel like he’s one of my family.
Amma papa bai sona, injiwa shiko yake sonki tunda yake san koya miki rayuwa kika san me gobe zata haifar just ki dane mishi kallan makiyi kinji, amma papa, ya isa ayra huce kici abinci, kolla ce ta cika idon ta ta huce ganin babu kowa yasa ta dawo palon tace papa nifa azimi nake.
◦