MARTANI BY RUKAYYA YUSUF IBRAHIM (A. Y. M Creatives)
Episode 2
MARTANI
A Story of Retribution
Rukayya Yusuf Ibrahim
(A. Y. M Creatives)
GMJ/26/49
Episode 02
"Yanzu Mama Hadiza kuma ki na ji ; kina gani suka ɗaurawa A'ishatu aure?".
Murmush tayi kafin ta ce" Rahana kenan, ko ina so ; ko ba na so dole ne suyi mata auran nan.
Kin san su waye dangin mahaifinta, bale kuma ga abunda ya sami Halima kinga ai auran shine maslaha".
Ajiyar zuciya Rahana tayi ta ce" Allah yasa haka shine mafi alkhairi. Yanzu me kike so ayi?".
" Yawwa daman in da hali so nake a dan yiwa A'ishatu gyara ko ya-ya ne. Don kinga ɗan Lami ya ce basa buƙatar komai sai A'isha har kayan daki da na kitchen duk sunce sun yafe.
San nan kuma ina so ki dawo gidan mu da zama, tunda kinga ina da larura rashin gani, nan kuma daman haya kuke, ko ba komai samu mai taimaka min".
Ajiyar zuciya Mama Rahana tayi ta ce" tabbas wannan auran basu daura shi ba , sai da suka mallake ki Mama Hadiza, amma ba komai in sun cuceki, su da Allah.
Zanyi duk abinda kika ce Allah yasa gidan zamanta ne".
Da " Amin " Umman A'isha ta amsa domin ta gane Rahana bazata fahimceta ba.
Haka suka dawo gida A'isha ta kasa ko da runtsawa saboda fargaban wannan aure da yazo mata a bazata.
Yadda ta ga rana haka ta ga dare . Washe gari da wuri ta shirya zuwa makaranta ko karyawa bata tsaya yi ba.
Duk abinda take Umma na kula da ita ,amma bata ce komai ba sai addu'a da take mata domin tasan babu wasu kalmomi da zasu sa ta tayi haƙuri a yadda ta lura da A'ishar.
Tafiyar mintuna biyar zuwa bakwai ce ta kawota Babban titin da zata hau mota. Cikin ikon Allah tana isa ta samu wani mai napep ta hau.
A ƙa'ida lacca sai 10:00am zata shiga, amma ji tayi zaman gidan duk ya ishe ta don haka ta fito.
Ko da suka isa cikin wani class ta shiga ta zauna babu kowa a cikinsa.
Ta saki kukan da take riƙewa saboda kar ta jefa Ummanta cikin damuwa.
Da ƙarfi take kukan, hawaye na zuba kamar famfo.
Sai da tayi mai isarta san nan ta yi shiru tana gogewa, san nan kuma ta faɗa duniyar tunani.
Bata san adadin mintinan da ta kwashe a haka ba , kawai sai jin muryar ƙawarta tayi tana cewa" A'ishatu Aliyu Usman " tayi firgit ta dawo daga duniyar tunaninta.
"Me kike yi a nan ? Wai daman kinzo ?" Ta jero mata tambayoyi ba tare da A'ishatu tayi yin ƙurin bata amsa ba.
Ganin haka yasa ta ce" kinga ki gyara zamanki Sir Ashraf ne ya ce mu dawo nan hall din can yayi masa zafi . Da ba dan haka ba inaga da baki samu lacture yau ba, kina nan kina tunani".
Miƙewa tayi suka koma sit din gaba, domin nan ne gurin zamansu a kowaca lacca balle kuma laccar Sir Ashraf da in bakayi da gaske ba, sai ya a kunyataka in kana zaman baya.
Sauran daliban ne kowa ya shigo suka samu guri suka zauna ana jiran malamin ya shigo .
Haɗaɗdan matashi ne mai jini a jika wanda ya haɗa duk wani qualities da ake nema a wajan namiji.
A hankali ya shigo hall din bakinsa dauke da sallama.
Miƙewa duka daliban sukai domin nuna girmawa ba tare since uffan ba, kamar yadda dokar makarantar take .
Bayan ya tsaya a gaban board ya kalle su yayi musu alamar su zauna.
Sir Ashraf Habeeb Farouk kenan, asali dabili ne a fannin MBBS wato medicine.
Nutsuwarsa da kwazo yasa bayan sun kammala karatu ya samu gurbin koyarwa a jami'ar duk da kasancewar ba burinsa ba kenan.
Yanzu haka babban likita ne kuma babban Malami.
Gyara tsatsuwarsa yayi ya fara musu bayani akan darasin da zasu yi cikin course din yake koyar da su na Biochemistry for Health Sciences.
Awa biyu suka dauka kafin ya sallame su ya kama gabansa, su ma kowa ya miƙe.
Nabila ce ta kalli A'isha ta ce" me yake damunki ne A'ishatu?".
Madadin ta bata amsa sai kawai ta fashe da kuka.
Cikin tashin hankali Nabila ta riƙeta tana fadin " sorry please don't cry my dear".
Cikin kuka ta ce" na rasa komai Nabila, plan din rayuwata duk sun ruguza min shi. Burina na kulawa da mahaifiyata ba zai cigaba ba".
Cikin tashin hankali bakinta na rawa Nabila ta ce" me..meya faru ne Shatu?".
Tsayawa tayi da kukan ta ce" an daura aurena jiya bayan sallar Jumma'a".
A firgice ta miƙe tana kallon A'isha cikin mamaki mai dauke da zallar tashin hankali.
Can kuma ta saitaa kanta ta ce" wa suka aura miki?".
"Ban sani ba Nabila , kuma ni bana son na sani ma. Wai kuma nan da Friday zan tare.
Babban tashin hankalina yanzu makomar karatuna, aikin da nake ana biyana kudi, ya-ya zaman auran zai kasance min?".
Ajiyar zuciya Nabila tayi , kana tasa hannunta kan kafadar A'isha ta ce" tabbas kina cikin damuwa , sai dai ba kuka ne mafita ba A'ishatu".
Ajiyar zuciya ta sauke tana duban Nabila idonta na zubar hawaye.
Nabila ta janyo ta zuwa wani loko dake bayan hall din da sukayi lacca ta na cewa" kina jina ki goge hawayanki A'ishatu , tabbas dangin Abbanku basu kyauta ba. Amma a gani na hakuri ya kamata kiyi, tunda sun riga sun daura auran. Saboda duk kukanki ko bujurewarki bazai yi amfani ba . Sai dai hakan ma ya ɗagawa Umma hankali ganin halin da kike ciki".
Goge hawayanta tayi ta ce" haka ne Nabila Nagode sosai da tunatar dani da ki kai.
Amma ina neman alfarma a gurinki don Allah, karki fadawa kowa wannan auran da aka yi min don Allah".
Murmushi Nabila tayi ta ce" kin san yadda muke ni dake A'ishatu ya wuce abota sai dai a kira ta da ƴan uwantaka, in sha Allah baza kiji wannan maganar tafita a bakina da sunan in fadawa wani ba".
Rungume juna sukayi sai kuma suka fito zuwa filin makarantar Nabila na cewa " ki saki jikinki karsu Summayya su gane halin da ake ciki".
Gurin siyan abinci suka je Nabila tayi musu order abinda zasu ci suka zauna suna taɓa hirar karatu.
Wani ihu suka ji wanda ya yi saurin dago kan su don ganin abunda ke faruwa.
Ƴan mata ne wanda suka amsa sunan su mata masu class suke faɗa a bainar nasi .
Nabila ta ce" ƴan level three ne, kai amma an zubar da aji, ko me ya haɗa su oho".
Wani dan Class din su ne da zuwansa kenan mai suna Ammar ya ce" akan Sir Ashraf ne kin san ku ƴan matan makarantar kun mace akansa".
A'ishatu ta watsa masa harara ta ce " sun dai mace akansa, Allah na tuba Ni banga abun so a jikin wannan mutumin ba wallahi".
Nabila ta sheƙe da dariya tana nunawa A'ishatu masu fadan tana cewa" ashe basu da gashi a cuci maza suke. Allah na tuba irin wannan ciko da badda kama da saukewa jikinsu ko ni mace bazan kalle su ba balle sir Ashraf".
Haka faɗa ya kace me daga ƙarshe kocce ƙawayanta suka zo kowa ta janye tasa, suka bar gurin kowacce taji jiki.
A'ishatu taja tsaki tana shirin miƙewa sai ga tawagar ƴan team din su da suke group discussion akan karatu.
Summayya Aminu Sadiq, Ahmad Bashir Ladan, Juwaira Khalid Musa , Fatima Nasir Nasir, Samir Ishaq .
Zama tayi Ammar na duban Samir yana cewa" kun bar show yanzu wasu ƴan mata sukai faɗa akan mafarkin Summy".
Summayya ta taɓe baki ta ce" mun gansu, ƴan wahala kuma nan gani nan bari dole a bar min kayana".
Dariya suka sa banda A'ishatu da ta tafi duniyar tubaninta.
"A'ishatu lafiyar ki kuwa?" Cewar Samir yana kallonta.
Dan murmushi tayi ta ce" nothing Samir ya kuke ya lacture din yau ?".
"Lafiya lau, ai Mafarkin Summy ya iya koyarwa" ya faɗa yana kallon Summayya.
Nan ma murmushi tayi kafin ta miƙe tana cewa " da wuri zan tafi gida , Umma zan raka unguwa. Abinda kuka yi Nabila sai ki min bayani Monday".
Gyada kai Nabila tayi ƙasan zuciyarta na tausayin ƙawarta ta.
Summy ta dubu A'ishatu da ta fara barin gurin da cewa" amma A'ishatu kamar baki da lafiya fa? Me ya same ki?".
Nabila ce tayi saurin cewa " ashe kin gane kema, wai jiya ne mage ta shigo gidan su , shine ko runtsawa batayi ba tsabar tsoro".
Summayya ta sheƙe da dariya har da riƙe ciki ta na fadin " Allah ki nutsu A'ishatu mene abun tsoro ne a mage?".
Fatima ta ce" gaskiya ni ma sonta nake ba, ki daina mata dariya ".
Samir ne ya miƙe ya ce" kinga A'ishatu zo na rakaki in dai Sumy da Teema suka fara musu sai su tsaida ki Umma ta zane ki".
Dariya tayi ta bishi suna ƴar hira , yayin da Juwaira ta bisu da kallo tana cewa" ban taɓa ganin ragwan namiji irin Samir ba. Yana son A'ishatu amma ya kasa sanar da ita sai hanya-hanya yake".
Fatima ta tafa hannu tana cewa " ki jiki Juwaira, shi ya faɗa Miki?".
Summy tayi dariya ta na fadin "ai ko makaho ya kalli Samir yadda yake rawar jiki a kanta ai yasan me yake nufi".
Ammar ya ce" ku kam Allah yaran nan kunfiya sa ido , ina ruwanku to ?".
Nabila ta matso tana cewa " don Allah mu duba aikin yau ina so na tafi gida da wuri ".
Daga nan hirar ta tsaya suka fara karatun su kamar yadda suka saba.
Shirye-shirye ya kankama sosai akan batun tariyar A'ishatu.
Ta sha gyaran jiki dai-dai ƙarfinsu wanda Mama Rahana ce da kanta tayi mata.
Kamar yadda ta ce baza ta bar karatuba, dangin mijin sun yarda da taimakon makocinsu, wanda daman shine ya tallafa mata ta fara karatun, amma batun koyarwa sunce basu san wannan zancan ba.
Hankalin A'ishatu ya ta shi sosai domin da koyarwar da take ne, take tallafawa Mahaifiyarta da dan uwanta.
Amma da yake Allah Mai Rahama ne A'ishatu tana cikin wannan damuwar.
Ranar Alhamis Adnan ya shigo yana murna ya samu ubangida a kasuwa mai kirki.
Zuwan farko ma da yaje yana rabon talliya yasa har da shi.
Farin ciki mara musaltuwa duk suka shiga domin Allah yaji riƙon su .
Sai dai duk da haka A'ishatu ta kudurce a ranta sana'ar hannun da take na turare baza ta bar shi ba.
Don a rayuwa babu abinda ta tsana kamar tambaye-tambaye ko tace roƙon ayi mata abu.
Washe gari ya kama Jumma'a tun ƙarfe hudu motocin daukar amarya ya suka zo .
Babu ƙawa ko guda daya aka tattara A'ishatu da mutane biyu Daga dangin mahaifinta da kuma biyu daga dangin Ummanta suka kaita gidan mijinta bayan dimbin nasihar da Umma tayi mata kan zaman aure.
____