Chapter 24
A parlour duk suka zauna dad ya wuce ɗakin hajiya mama.
Bayan yan mintuna sai gasu sun dawo tare.
Kujera me zaman mutum ɗaya ta zauna tana murmushi ta ce " har sun tafi kenan?"
Bayan sun amsa mata suka ɗan zamo daga kujerun da suke kai suka gaishe da ita.
Amsa masu ta yi da murmushi a fuskarta.
Bayan sun gaisa abokanan dad suka ce " toh hajiya mu zamu koma, Allah ya sanya mana alkhairi."
" Ameen" ta amsa masu sannan ta ce " toh mun gode Allah ya yi albarka."
Ameen suka amsa sannan suka ta shi dad ma ya miƙe zai yi musu rakiya.
Bayan sun fita uncle Haroon ya ce " hajiya ashe kina abuja."
Harara ta ɓalla mashi ta ce " da da nake kanon yaushe rabon da ka ɗakko ƙafarka da sunan zuwa ka gaishe da ni?"
" Bare ma nayi tunanin ganin ʼyaʼyanka."
" Wallahi ku da Allah, shi zumuncin nan shine abin wulaƙantawa a wurin ku ko.?"
" In banda lalacewa irin ta zamani,Haruna a ce wai kaine zaka shafe wata da watanni baka taka ƙafarka a cikin gida na ba."
Uncle Mukhtar da tsautayi ya ce " haƙuri za'a yi Hajiya kin san yadda aiki yake."
Wata uwar harara ta yi mashi ta ce " ai gara kowa da kai,gara shi bai taɓa yin shekara bai zo ba."
" Amma kai yanzu tsakani da Allah ka faɗa man yaushe rabon da naga ƙafarka a ƙofar gidana da sunan kazo ka gaishe da ni?"
Ƙasa ya yi da kansa ya ce " a dai yi haƙuri hajiya in shaa Allah za'a gyara."
" Amma kin san ni ban fiye shiga kano ba hajajju."
Kallon banza ta yi mashi ta ce " wallahi Mukhatar idan baka yi man shiru ba ma sai ranka ya baci."
" Aikin ai bai hana ka ka ɗauki ʼyaʼyanka ku fita ƙasashe daban daban ba."
" Ni na rasa zumunci irin na wannan zamanin wallahi, ni fa na saki nono uwarku ta kama amma a ce wai zaku iya shafe wata da watanni ban ga ƙafarku a gidana ba ai shikenan."
Saukar da kanshi ya ƙara yi ya ce " a dai yi haƙuri hajjaju zamu gyara in shaa Allah."
Taɓe baki ta yi ta ce " in gani a ƙasa,wai ana biki a gidan su kare, ya ce in gani a ƙasa."
Dad ne ya dawo ya same su, Hajiya Mama sai mita take yi.
Dariya ya yi ganin yadda hajiya mama ke ta mita sannan ya zauna gefen uncle Haroon.
Haka ta yi ta mita su dai sai haƙuri suke bata.
Ƙara yin ƙasa Safiyyah ta yi da kanta ta ce " wallahi ban san inda Ayaanah take ba."
" Abu ɗaya na sani wata rana da safe Barira ta gama shirya ta zata tafi school tana yin breakfast Barira kuma ta koma ɗaki zata ɗakko mata school bag."
" Tahowa ta yi da gudu tana faɗin aunty Barira na ƙoshi da tea ɗin nan."
" Bata lura da tahowa ta ba hanyar dining ɗin ita ma ta taho da gudu da cup ɗin a hannunta."
" Bige ni ta yi tea ɗin ya zube gaba ɗaya a ƙasa."
" Haushin tea ɗin da ta zubar yasa na ja ta na fito da ita, garage ya yi ƙura sosai ban damu da tana da Asthma ba na ce sai ta share shi duka."
" Ni kuma na koma ɗaki,tun daga wannan lokacin ban ƙara ganin Ayaanah ba."
" Kuyi haƙuri ku yafe man,Shema'u ce ta bani shawarar na saka boka ya rufe min bakin duk wani wanda yake da alaƙa da Ayaanah, kuma ya mantar da su maganar Ayaanah na kusa da na nesa."
" Shiyasa babu wanda yake iya yin maganarta."
Mamy ta yi ƙasa da kanta saboda at this point bama ta san me zata ce ba.
HAYDAR da yake jin zuciyarshi kamar zata fasa ƙirjinshi ta fito ya miƙe tsaye har yana ganin duhu a cikin idunshi ya yi hanyar fita.
Zannur da ya san halinshi sai ya biyo shi a baya don kar ya yi wani abu da zai illata kanshi.
Ganin ya shiga ɗakinshi ya kulle yasa ya fahimci yana buƙatar kaɗaici ne sai shima ya zauna a ɗaya daga kujerun compound ɗin yana tunanin ta inda zasu fara neman Ayaanah.
Uncle Haroon ne ya ce " hajjaju iyayen yaron nan sun zo kuma a yadda na fahimta gaskiya mutane ne su masu mutunci."
" Kuma Alhamdulillah kafin su tafi sai da muka tsaida lokacin da za'a yi bikin."
Sai a lokacin ta yi dariya ta ce " masha Allah, yaushe aka saka bikin?"
" Sati biyu aka saka."
" Allah yasa muna da rabon gani." Ta faɗa murmushin fuskarta yana ƙara faɗaɗa.
Tunda aka faɗa mata lokacin da aka saka bakinta yaƙi rufuwa sai murmushi ta ke yi.
Uncle Mukhtar ne ya ce " hajjaju za'a aurar da ta gaban goshi baki yaƙi rufuwa."
Murmushi ta ƙara yi ta ce " ina kuwa baki zai rufu zan aurar da ta gaban goshi."
Miƙewa ta yi ta ce " ni bari na je na fara shirye shirye na tun yau, da ni so nayi ma na koma gidana jibi amma yanzu kam tafiya ta fasu."
Bayan hajiya mama ta tafi ɗakinta uncle Mukhtar ya ce " a kira mana madam muyi sallama kafin mu tafi."
Wayar shi dad ya ɗauka ya kira mom,yan mintuna kaɗan sai ga ta tana sakkowa.
Tana zama uncle Mukhtar ya ce " iyayen yaron nan sunzo kuma alhamdulillah mun tsaida sati biyu a matsayin lokacin bikin."
Murmushi mom ta yi ta ce " toh Allah ya nuna mana da rai da lafiya."
Suka ce ameen.
Uncle Mukhatar ne ya ƙara cewa " toh madam mu zamu koma."
" Da wuri haka engineer? Ai na ɗauka sai gobe kuma zaku koma."
Uncle Haroon ne ya ce " jirgin ƙarfe huɗu duk zamu bi shiyasa."
Jinjina kai ta yi ta ce " toh Allah ya kiyaye."
Uncle Haroon ya ce " ameen." Sai kuma ya ƙara cewa " muna godiya madam da irin kulawar da ake yi wa hajjaju."
" Duk wanda zai zauna da tsoho sai ya yi haƙuri."
Murmushi mom ta yinta ce " haba dai ai hajiya nima uwa ce a gareni, haƙuri ya zama dole, kuma ita ma ai haƙurin take yi da ni."
" A irin shekarun hajiya ai babu ma rikicin da take yi."
Jinjina kai uncle Haroon ya yi ya ce " haka ne kam."
Bayan sun tafi ta ɗauki wayarta ta shiga kiran babbar aminyarta don ta sanar mata da an saka lokacin bikin Jay.
Bayan Mamy ta ɗaga sun gaisa ta ce " ina da baƙi zan kira ki anjima."
Bayan ta kashe kiran mom momma ta miƙe tsaye ta ce " duk yanda nake tunanin ki kin wuce haka Safiyyah, ba zance kar ki dawo min gida ba, saboda gidan mahaifinki ne,amma bana son na ga ƙafarki a cikin gidana ba tare da kin nemo musu ʼyarsu ba."
Wurin Mamy ta juya ta ce " hajiya mungode sosai da karramawa,kuma ina me ƙara baki haƙuri don Allah ki yi haƙuri, bai kamata kalmar haƙuri ta fito daga baki na ba,amma dai ki yi haƙuri,kuma in shaa Allah nima ta ɓangare na zan yi iya bakin ƙoƙarin da zan iya wurin ganin an gano idan yarinyar nan take."
Kallon Addah Fatimah ta yi da Hamma Khaleel ta ce " ku tashi mu tafi, ke kuma ki nemi wani gidan har zuwa lokacin da zaki nemo musu ʼyarsu."
Bayan sun tafi Safiyyah ta tashi zata fita Mamy ta kira sunanta,juyowa ta yi ta ce " ina zaki je yanzu idan kika fita daga gidan nan?"
Girgiza kai Safiyyah ta yi ta ce " nima ban sani ba Mamy,amma da akwai kudi a hannuna ina jin zan yi renting apartment ne da zan zauna."
Hannunta mamy ta riƙe ta ce " haƙƙin kulawa da ke a kanmu yake, duk da nasan abu ne mai matuƙar wahala ALIYU ya cigaba da zama dake a matsayin mata."
" Don haka zaki iya zama a nan gidan."
Jiddarh dake ɗaki mamy ta ƙwalawa kira,tana fitowa ta ce " ki raka Safiyyah ɗakin da yake kusa da naki."
Toh ta cewa mamy sannan ta ce " aunty Safiyyah muje."
Tashi ta yi ta bi bayanta amma duniyar da zuciyarta gaba ɗaya sunyi mata duhu.
Bayan uncles ɗin Sadeeq sun baro gidan su Jay suka ƙara kiran baban su Sadeeq suka ƙara yi masa bayanin abinda ake ciki.
Bayanin abinda ake ciki zai fara yi musu sai ga sallamar Sadeeq.
Amsawa suka yi Abbah ya ce " yawwa babana shigo."
Bayan ya zauna ya gaishe da su,sannan Abbansu ya ce " dama yanzu nake shirin kiran ka sai gashi kuma ka zo."
" Yanzu muka gama waya da iyayenka suka ce man sunje har ma sun taho,amma basu taho ba sai da aka saka ranar bikin."
Aunty dake zaune gefen Abbah ta ce " masha Allah, Allah ya sanya alkhairi."
Mama dake zaune a gefe ita ma ta ce "ameen."
" Yaushe aka saka bikin?"aunty ta ƙara tambaya.
" Sati biyu aka saka ." Abbah ya bata amsa.
" Allah ya nuna mana lokacin."
Sadeeq dake zaune kanshi a ƙasa ji yayi kaman ya tashi ya yi ta rawa don murna.
Abbah ne ya juyo ya kalli Sadeeq ya ce " toh baba na a ina zaka aje ita ʼyar tawa?"
Sadeeq da kanshi ke a ƙasa ya ɗan ɗago kaɗan ya ce " a gidana dake Gwarinpa nake son ta zauna."
Jinjina kai Abbah ya yi ya ce " toh shikenan Allah ya yi ma albarka."
"Ameen"
Aunty ce ta kalli mama ta ce " yaya muje muma mu fara namu shirin kar lokaci ya ƙure mana."
Gyaɗa kai mama ta yi ta ce " ai kuwa dai tunda an saka shi a ƙurarren lokaci."
Bayan Jiddarh ta kai Safiyyah ɗaki mamy ta ɗauki wayarta ta kira mom.
Bayan mom ta ɗaga suka ƙara gaisawa mom ta ce " baƙin har sun tafi kenan?"
" Sun tafi."
" Ai ina ganin maganar nan ba a waya zamuyi ba bari na zo gidan kawai."
" Bari kawai ni na zo,nima akwai maganganun da zamuyi da ke."mamy ta ce haka.
Mom dake saurarenta ta ce " toh shikenan sai kin zo."
Tun bayan da ya baro gidan Saleemarh yake ta shawagi akan titi ya kasa samun ƙwarin gwiwar tun karar hanyar gidanshi.
Sai da ya gaji don kanshi ya ɗauki hanyar da zata kai shi gidanshi.
Layla dake ta zagaye parlourn taji ƙarar shigowar motarshi,ajiyar zuciya ta sauke bayan ta ji yana buɗe ƙofar parlour.
Kujera ta nema ta zauna kamar ba ita ce ke zagaye zagaye a parlourn ba.
Sai da yaji gabanshi ya faɗi da ya ganta zaune a parlour,ƙarasawa ya yi inda take ya ce " Babe na daɗe ko?"
Bata bashi amsa ba ta ce " Raj meyasa Ummah ta kira ka? Wani abu ya faru ne? Me ta ce maka da kaje?"
Ta jero mashi tambayoyin nan.
Har ya buɗe baki da sunan ya faɗa mata duk yadda suka yi Ummah,sai kuma kawai ya fasa ya ce " ba wani abu bane,ta zo wani taro ne shine ta ce naje mu gaisa."
Sai a lokacin taji hankalinta ya kwanta saboda tana da tabbacin ba zai yi mata ƙarya ba,duk da wani bangare na zuciyarta yana faɗa mata ba haka maganar take ba.
Tashi ta yi ta wuce ɗakinta don dama abinda ya zaunar da ita kenan.
Bayan ta tashi Raj ya yi wata ajiyar zuciyar da be san yana riƙe da ita ba.
Knocking aka yi,aunty Naja dake parlour tana gyarawa ta buɗe ƙofar.
Gefe ta matsa ta ce " mamy sannu da zuwa."
Murmushi mamy ta yi ta ce "yawwa Naja sannu da aiki."
Sama ta wuce ɗakin mom, tana shiga ta tarar mom na toilet tana yiwa Ayaanah wanka.
Gefen gadon ta zauna tana jiran fitowar su.
Mom na fitowa riƙe da hannun Ayaanah ta ga mamy zaune a gefen gadon sai ta ce " ashe har kin zo."
Mamy da tunda suka fito hankalinta yana kan Ayaanah ta ce " Bilkisu dama Ayaanah na nan gidan baki sanar da ni ba.?"
Kallon mamy mom ta yi ta ce " kin san ta ne?"
Da matuƙar mamaki mamy ta ce " HAJARA ce fa Bilkisu."
Baya ta yi har tana shirin faɗuwa ta dafa gadon ta na ta maimaita" innalillahi wa'inna ilaihi raji'un."