17
by @sadisakhna
______👑 *JODA* 👑_____
Na
*Sadi-sakhna*
Ƴar mutan Jama'are
THE TRIO OF TALES
(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)
@sadisakhna on Arewapen
@SAKHNA03 On Wattpad
*** on Whatsapp
LITTAFI NA 1
👑*Warƙa ta (17)*👑
Ture wanda suke gaban ƙofa nakeyi har na samu na isa cikin ɗakin. Addah Rahilah ce a kwance cikin mawuyacin hali,tayi fulo da cinyar addah Aneesa. Gabaɗaya jikinta ya jiƙe da gumi shirkif,babu abinda take fitarwa sai nishi mai tsanani. A gefenta kuma Inna Yawuro ce ungozoma ta gargajiya wacce itace take yiwa bayi magani idan abun yayi tsanani,sannan duk wata haihuwa idan baiwa zatayi ita ake ƙira.
Tsugunnawa nayi na kama hannun ta,domin bansan mai zance ba,ɗago idonta tayi wanda suka wujijjige saboda wahala,runtse hannun nawa tayi a cikin nata tareda tara dukkanin ƙarfinta tace.
"Joda ki taimake ni da ilimin da Allah yabaki na rabu da wannan wahalar,Ina sabon ilimin dakike cewa Allah yabaki ki gwadashi akaina na yarda Joda,kwana uku kenan ina abu ɗaya tunda kika tafi"
Jikina ne naji duk yayi sanyi,hawaye ne ya fara gangarowa a kumatuna,ni wacce irin mutum ce ne,da Allah ya azurta da baiwa amma bazan maida hankali da wanda suke kusada ni ba sai na nesa. Tun safe iya tacemin batajin daɗi,amma ban tashi zuwa ba sai yanzu dana gama abinda yake gabana,ina ta burin samawa wanda ko sunansa bansani ba magani,ganan wacce take min kallon ƴar uwa na barta a wahale. Share hawayen idona nayi kafin na sake matsawa kusa ina kallon cikin. Tareda faɗin Ban makara ba Insha'allahu zan taimaka mata harta haihu lafiya da izinin Allah.
Kallon inna Yawuro nayi wacce tayi bake bake banda ruwan jiƙo babu abinda take ɗirka mata.
"Inna ko zaki ɗan matsa kaɗan zan duba cikinne"
"Yau jimin yarinya da iyayi,in kin duba mai zaki gani,duka duka yaushe ma kika fara ƙirgen dangi da har zaki taimakawa mai naƙuda"
Shuru nayi ban ce mata komai ba,saida Addah Aneesa tasaka baki tukunna tareda janta gefe cikin sigar lallami da girmamawa.
Kallon mutanen da suke bakin ƙofa nayi tareda yimusu alamar suyi shuru,da zan iya ma dama korarsu zanyi,saidai nasan baxasu tafin ba,domin al'adarsu ce in mace zata haihu a zagayeta kaman tana rabon nama,inda mayu ma su lalata haihuwar.
Hannuna na ɗora akan cikinnata na tsawon wasu daƙiƙu inaso naji mai yake ciki,sama da ƙasa nakai hannuna amma sam banji alamar Kan jinjirin ba,kamar an cemin nakai hannuna gefe,ai kuwa naji kansa ta gefe guda,ɗaya gefen kuma kaman motsin ƙafafu. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un na furta a hankali. Kallonta nayi da fuskar tausayawa,dole ne tasha wahala domin ko shekara zatayi a haka bazata iya haifar cikin ba .
Tashi nayi da sauri kafin na fita na matsa inda addah Aneesa take.
"Addah Aneesa zanje wani waje yanxu na dawo,akwai abinda zan duba,kafin na dawo ku tanadi man zaitun a tafasa ruwan gishiri mai kyau,kafin nadawo kar wanda ya tabata kinji addah Aneesa"
Ɗagamin kai tayi alamarr taji,kai tsaye bangaren ajiye litattafai na nufa,babu wanda ya katseni saboda kalar kayan dayake jikina.
Cikin sauri nafara duba littafin ina fatan Allah yasa na sameshi,domin naga anyi magana akansa cikin littafin da baba Almahdi yabani,littafine daya ƙunshi Tiyata da kuma matsaloli na Hihuwa ga mata.
Can bayan duba na wasu daƙiƙu na samoshi a kasan wasu littafai,ɗaukowa nayi na buge ƙurarsa tareda buɗewa.
Kitab al-Tasrif,Marubuci: Al-Zahrawi. Shine a shafin farko,buɗewa nacigaba dayi har nazo kan inda nakeson dubawa. Saida na tabbatar na ɗau abinda nakeso kafin na ajiye kana na juya da gudu zuwa sansanin namu. A bakin ƙofa naji nayi karo da mutum,dukkanmu muka ja da baya kowa yana sosa inda ya buge, wannan mutuminne dana ganshi tareda Mai ciwon Ƙirjinnan. Kallon mamaki nakeyi masa kan mai yake anan,sabanin shi da kaman dama yasan zai sameni anan ɗin.
"Uhmm kayi haƙuri bansan kana shigowa ba,ina fatan dai bakaji ciwo ba ko?"
"Ahah haba karki damu,dama tun ɗazu nake nemanki sai yanxu naga kin shigo kuma kin iyo nan shine na biyoki"
"Kana nemana amma lafiya?"
"To ba lafiya ba,ciwon ɗan uwana ne yatashi shine yace na nemoki"
Da mamaki na kalleshi,domin banyi tsammanin ya tunada abinda yafaru tsakaninmu ba jiya balle har yasaka a nemoni,saboda kallon dayayimin yau da safen bayyi kama dana sanayya ba. To amma hakan ma wata damace da zan shiga jikinsa domin cimma burina,ta hakanne kaɗai zan samu wanann damar.
"Shikenan kace masa ina zuwa amma yanzu akwai wani abu mai gaggawa daya tasomin tukunna"
"Ki tsaya kiji yana cikin mawuyacin hali,sannan shiɗin.........."
Ban ƙarisa jin mai yake cewa ba,saboda runtumawa danayi da gudu nabar wajen. Sansaninmu na nufa,sai haki nakeyi saboda gudun danayi.
Ina zuwa na tarar addah Aneesa ta haɗa dukkan abinda nace. Har sannan mutane cike a ɗakin,saida Addah Aneesa tayi musu magana kafin suka fita suke leƙowa ta taga.
Tsugunnawa nayi tareda ɗaga rigarta ina kallon cikin hannu nasaka ina mammatsawa ta yadda zan gane ainihin yanda jaririn yake. Bayan na gama wanke hannuna nayi na saka a ƙasanta na gano adadin buɗewar bakin mahaifarta,hannun jaririn naji hakan yasa na leƙa,tabbas hannu ne dan har fatar jikin ta bushe alamar ya daɗe da fitar da hannun. Kallon Inna yawuro nayi cikeda mamaki tareda cewa.
"Inna shin kiga hannun jaririn yafito kema?"
"Ehh na ganshi mana ai kowama yaganshi,nikaina danagani nasan babu abinda zan iya,saboda yawanci in haihuwa tazo da haka to saidai ayi ɗan ƙoƙari saboda baza'a bar mutum yana raye ba'ayi komai ba. Amma in haka tafaru to yaronne yaso tafiya da uwarsa,Allah yayi kabarinsu tarene"
Cikeda mamaki da takaici nake kallonta tana faɗin hakan,amma bazanga laifinta hakan shine halayyar mutanenmu,Fasihmman ma rayuwar baiwa wayake ta ita.
Muryar mutum mukaji da taga,mijin Rahila ne yayi sa'a wani ya karbi aikinsa saboda yazo wajen matarsa,kuma duk akan kunnensa inna takeyiwa matarsa da ɗansa fatan mutuwa.
"Ƙaryane ɗana da izinin Allah bazayyi ajalin Ummansa ba,zasu rayu mucigaba da rayuwa tare,Joda ta yarda dake sosai,tanacewa bazata haihu ba ita sai dake a gefenta,kuma tanaso ki gwada iliminki akanta,Addu'arta ce ta karbu dan haka ki taimaketa dan girman Allah da dukkan fasaharki"
"Jaririn ne yazo ta kwance,maimakon kansa a cikin mararta ƙafafunsa kuma a sama,sai yazo kansa a gefe ƙafafunsa ma a ɗaya gefen. Shiyasa yagagara fitowa, kuma indai ba'a gyara ba bazai iya fitaba"
"Innalillhi to ko mayyace takamata ta juya ɗan kai,banda haka ban tabaji ba wai jinjiri a kaikaice ikon Allah"
Wata matace tafaɗa tana tafa hannu da sallalami. Ɗaya ma ta cafke. Wacce sukeyi ƴar tsama da joda ɗazu.
"Kokuma mai bayanin ce mayyar ba,in ba maye ba waye yake ganin abinda ke ciki,mayya ce shiyasa tagani"
"Kuma fah zancenki dutse,mayune kaɗai suke ganin abinda ke cikin mutum,in har tagyara ɗannan to kuwa ta tabbata mayyace"
Ɗan murmushi nayi dajin furucinsu,wanda sukayi amfani dashi suka ɗaureni,wato idan na ceceta ni mayyace sai a fara ƙyamatata idan kuma na barta banyi komai ba ta rasa ranta sai a ce dama babu abinda na iya duk kurarine.
Numfasawa nayi na kalli Addah rahila wacce yanzu bata ihun sai juya kai kawai takeyi saboda azaba,to ai ko jefeni za'ayi saboda zargin maita banajin zan iya barin wannan baiwar Allah cikin wannan wahalar alhalin inada ikon taimaka mata.
Hannu na saka babu bata lokaci na tura hannun yaron ciki,saida na tabbatar ya shige yanda yake kafin yafito.
Inna yawuro ce takasa haƙuri tace.
"Kekuwa ƴar nan kanki ɗaya kuwa,ba maitaba inaga tabin hankali ne dake. Kinsan iya adadin yunƙurin da tayi kafin aka samu kan ma yafito,amma shine zaki saka hannu ki maidashi ciki. In ɗa bai kasheta ba aike zaki kasheta da kanki."
Ko inda take ban kalla ba bare na kulata,domin a yanzu bata ita nake ba.
Hannun na miƙawa Addah Aneesa nace ta miƙomin man zaitun ɗin danace a ajiye. Bayan ta miƙomin karba nayi na zuba akan cikinnata,saida na tabbatar yasha mai sosai yana santsi kafin na ajiye kwalbar a gefe.
Hannayena na saka ɗaya ta sama ina tura kan yaron ƙasa,ɗaya kuma ta ƙasa wajen ƙafafunsa ina turasu sama. A hankali nakeyi,idan naga tayi nishin ciwo saina tsaya ta huta,a haka a haka cikin ikon Allah har na samu na gyara masa zamansa,kaman jira jikinta yakeyi nauyin kan yana shiga matararta gadan gadan haihuwa ta taso.
Ko daƙiƙa talatin ba'a cikaba ɗan ta ya sullubo duniya,saidai bayan ya fito babu kuka da ake zato daga dukkan kowanne jariri idan yashigo duniya.
Ɗaukarsa nayi jijigashi,ƙirjinsa na danna sai naji kaman ruwa ya shaƙe wuyansa. Juya kansa nayi ina dukan gadon bayansa,kowa a wajen ta zararren ido yake kallona,alamar zan kashe jinjirin daya faɗo duniya yau. Cikin sa'a kuwa hakan yayi aiki domin wani ruwane kalar rawaya yake fitowa daga bakinsa,saida ya amarsa tukunna muryarsa tafara fitowa kaɗan kaɗan.
Ajiyeshi nayi a cikin wani tsumman saƙi,kafin na kalli Addah rahila wacce baccin wahala ya ɗauketa. Kallon Addah Aneesa wacce takeyimin murmushi dakuma ɗagamin babban ɗan yatsanta alamar jinjina. Nima dariyar nayi ina sauƙe numfashi tareda yiwa Allah godiya a zuciyata,nasan komai nake shine yabani iko.
Ban koma sansanin gasar tamu ba anan na kwana,saida na tabbatar Addah rahila tana lafiya itada jaririnta,har yanxu bata wani magana sosai sai ɗaga kai kawai,sai kuma bacci. Na haɗa mata magungunan dazata buƙata ciki harda su hulba saboda gyaran nono.
Kafin wayewar gari gabaɗaya Jami'ar ta karaɗe da labarin abinda nayi a wajen haihuwar,saboda abune da bakowa yataba gani ba,nima a littafi na karanta kuma nayi kasadar gwadawa.
Hankalina kwance na fito daga sansanin namu zan tafi Majalisar karatu, sai farin ciki nakeyi ganin na baro Addah rahila a zaune tanashan kunun tsamiya,yaronta ma yasha nononsa ya ƙoshi komai lafiya.
Muryar lukman naji ya min cemin na tsaya,tsayawa nayi ina kallonsa har ya kariso,fuskar nan tasa kamar gonar Auduga dan farin ciki.
Bayan mungaisa wani ƙaramin takobi ya miƙomin a cikin gidansa,anyi masa ado da zinare dakuma Jan dutse. Yayi kyau sosai,amma ban karba ba sai kallonsa akan yayi min karin bayani tukunna.
Takobin mahaifiyata ne Sarauniyar garinmu Dukkah kafin Daular songhay su cimu da yaƙi su kashe mutane,su rushe gidaje sannan su maida wasu bayi. Takasance macece gwarzuwa kuma mai tsaya akan ra'ayin adalci,har numfashinta na ƙarshe daya fita daga jikinta yaƙi takeyi domin kare mutanen da suke nata. Tun ina yaro itace jarumata,saida aka kasheta a gabana nikuma aka maidani bawa na daina ganin kowa a matsayin Jarumi a idona sai yau wannan kallon ya farfaɗo kuma akanki, hakan yasa naje na tono wannan takobin danayi tsawon shekaru da binneshi. Badan komai ba sai mamallikiyar takobin yau naga zarrarta a jikinki, bata sigar yaƙi ba saita sigar fikira. Na baki wannan Takobinne domin ki zaburar da wannan bangaren na jikinki dayakeson zubar da jinin masu zalunci da tauye haƙƙi. Ki jajirce komai wahala har kikai ga cimma nasara,bawai daga Karon farko ki sare ba."
"Ohh dama ka gane ni ne ranar kodai addah Rahilah ce ta faɗamaka?" Nayi maganar cikeda kunya,kenan duk suntumani da akayi tayi da ƙasa yana kallo kuma yaganeni ashe.
"Haba Joda ai indai wanda yasanki ne yana kallo zai ganeki,karki damu basai kinje fagen horo ba,nida kaina zan koyamiki idan har kin shirya fara koyon a karo na biyu"
"Nagode da wannan tayin to amma miyasa zaka bani Takobi mai daraja haka wanda yake na mahaifiyarka,bayan kanada mata kuma yanxu ga yaro"
"Su zan karesu da dukkan ƙarfina,sannan Rahila batada zuciyar iya rike takobi. Tun a lokacin da kika saka hannu kina juya ɗan cikinta da ƙwarewa da kuma jarumta kuma akayi nasara kika ceto rayuwarsu dukka. na saka a raina lallai kin cancanta na baki tukwuici da wannan takobi. Dan haka dan Allah kada ki maida hannun kyauta baya. Suɗin rabin jikina ne,kin cececi rabin jikina kuma ahalina,bakomai bane don na baki kyautar wannan takobin"
Karba nayi tareda yimasa godiya,sannan nace masa zan nemeshi idan na shirya,saboda na kula idan ba karbar nayi ba bazai daina wannan maganganun ba. Gashi ni sauri nakeyi zan tafi majalisa. Tun ranar da akamin duka zuwa filin horon yafita a takaina,shiyasa banji kyautar takobin ba har raina. To amma gaskiyarsa,nafara tara maƙiya gashi banida mai kareni sai Allah,dan haka dole natashi tsaye na zama jaruma. Kuma sainaji Mahaifiyar tasa ta burgeni,ta mutu jaruma a idon ɗan ta abinta. Uhmm ko ina tawa uwar take Allah masani.
Koda naje Karatu banga wannan mutumin ba shida abokinsa,iya bayin mu ukune kacal a wajen. Duk da shigata wajen nagansu suna Tsugunne a tsakiyar rana sun sunkuyar dakansu. Dukkan ɗalibai matan kuma suna zaune da kayan marmari a gabansu suna sha suna taɗi.
Salubewa nayi nabar wajen ganin basu hangoni ba. Don nasan tilas ne nima jona musu zanyi da zama a ranar,nikuma ban shirya kamuwa da zazzabi ba inada abinyi.
Sashen mutumin jiyan na nufa kao tsaye,saidai ina zuwa na tarar wajen wayam babu kowa, a raina nace to kodai aljanu ne,basa wajen karatu sannan basa nan wajen ma,gashi su baƙine ballantana nace sunyi wani wajen.
Har na juya zan tafi naga wata ƴar takarda akan karamin tebur ɗin dayake ɗakin.
"Inkinzo baki sameni ba ina Ɗakin jinya"
Naso tafiya can ɗin,amma ganin Malamin da zai bada karatun yazo yasa na zauna acan baya naji abinda yake faɗa,ana gamawa kuwa kamar abin ƙiftawa nabar wajen. Ni ba jaka bace bazan yadda suyita cutar dani ba. Sukuwa sauran bayin kana kallonsu kasan sunsha wahala,ko kaɗan banji tausayinsu ba domin har sannan ban manta abinda sukayimin ba a jiya.
Shiga sashen maza nayi ina rarraba ido kozan ganshi amma babu alamarsa dagashi har abokinnasa. Kodayake waye zai kawo bawa nan wajen.
Juyawa nayi na fito daga wajen,da ummu hajar naci karo tafito daga bangaren mata,hannunta duk jini. Wani waje taje da ruwan ɗumi mai gishiri a ciki ta wanke hannunta kafin tajuyo ta kalleni.
"Joda dazu naji bayi suna maganar wai kin juya jariri a ciki daga makaifa ya dawo yanda yakamata ya kasance,kuma kinyi nasarar har aka haifeshi lafiya"
Sunkuyar dakaina nayi batareda na amsa ba, kai Duniya ba faɗi komai yafaru kafin wasu Daƙiƙu ya wanzu a ko ina kowa yaji.
Jinayi ta dafani hakan yasa na ɗago na dubeta,murmushi takeyi fuskarta babu alamar damuwa.
"Danaji labarin nayi mamaki sosai,lallai basirarki takai inda takai,yanxu ina wani abun idan nasamu lokaci zaki koyar dani kinji. Yanzu wata ce take haihuwa to kuma yazo da zubar jini kuma ina tunanin itama jaririn ba daidai yake ba. Inaga muje ki duba kigani,kinga nima saina kalli ya akeyi na samu karin ilimi"
Da mamaki na kalleta,kenan bataji babu daɗi ba da ban tambayeta ba nayi aikin. Kodayake nakasa fahimtar ta ne,tanada faɗa dakuma dokoki amma kuma batada hassada da ƙyashi. Har tayi gabana na katseta ta hanyar tambayarta
"Am ummu hajar nace dan Allah ko akwai wani marar lafiya da aka kawo mai ciwon zuciya?"
Dan jimm tayi kafin tace.
"Shin Baba Almahdi ya baki kulada shine?"
"Ehhh kuma mun haɗune a wajen gasa,sannan na ganshi sanye da kayan bayi shine nayi mamakin mai zai kawoshi nan wajen?"
"Duk ba wannan ne abun maganar ba,saboda nima abin ya ɗauremin kai,amma kuma baba Almahdi yaƙiyimin bayani akansa,yana ɗaya daga cikin ɗakuna masu ɗaɗɗaya anan zaki ganshi idan kin duba. "
"Yawwa to nagode barina duba "
"Ahhh keda nace kizo ki tayani ceton matar nan,ga mai bukatar kulawa ta gaggawa"
Hmmm bazaki gane bane,wancan ɗin jarrabawa ta ce shiyasa.
Ba yanda na iya haka na bita na tayata karbar haihuwar har muka gama lafiya,wanann ma haka mutane sukayi ta mamakin salon dana nuna a wajen.
Kafin lokaci ƙanƙani sunana har ya karaɗe ba iya jami'arba harma da cikin gari ni ban sani ba.
Sadi-sakhna ce ✍🏼
Comment
Like
Share
Follow