14
14
***Ba anty Mimi kadai ba hatta hajiya da Irfan da Manal da kuma suhana gaba ɗaya jikinsu yayi mugun sanyi da jin halin da anty Mimi take ciki a yanzu,
Anan ta bar handbag dinta da sauran kayanta kawai ta wuce upstairs, tana shiga ta fada kan gado ta fara kukan da sautinsa ke fita, tayi kuka sosai tamkar idanuwanta zasu fice kafin ta iya hakura tayi shuru tana jan zuciya wacce tayi mata wani irin nauyi, suma su hajiya acan falo din suna cike da jimami suna ta faman jajantawa ahaka Afeef ya shigo ya same su,
"Wai me yake faruwa ne naga kamar duk kunyi wani tsuru tsuru......? "
Ajiyar zuciya Irfan ya sauke ya kalleshi yace "Anyi suspending din Anty Mimi a hospital sannan an kwace license dinta......"
"Innalillahi..... Yaushe? Akan me?"
"yau ɗinnan...... Saboda ta zama confused...... Komai bata yin sa yanda ya dace, suna da gaskiya dan za a iya samun rashe rashen rayuka saboda she's not herself a yanzu even the management board noticed she's not herself soo they are right....."
"where is she?" Afeef ya tambaye shi yana kallon sa, da hannu ya nuna masa upstairs alamar tana can, babu ɓata lokaci ya tashi da sauri ya nufi bedroom dinta, knocking yayi sau biyu kafin ya murɗa handle din kofar ya shiga, har lokacin tana kwance pillow din da take kai ya jike da hawaye tana jin wani irin nauyi akan kirjinta tamkar zai fasa mata zuciya her heart was heavy and even breathing hurts the pain is too much,
"anty Mimi......" jin muryarsa ya sata tashi zaune kamar an mintsineta, a hankali ya karasa gaban gadon yayi kneel down agabanta yana kallonta itama tana kallonsa cike da baƙin ciki da kuma jin haushinsa fuskarta sharkaf da hawaye,
"anty Mimi am very sorry......."
"what are you doing here? Are you happy now? Now that you have destroyed my life are you happy?? I love my job..... I love to consults..... I love to diagnose and prescribed........ I love to see people cured, I love seeing people live happily because of me but now i can't do it anymore because of you, ta sanadinka komai nawa ya lalace ya tabarbare..... Shikenan burinka ya cika ka raba ni da komai nawa kuma ka rusa duk wani mafarki nawa, Afeef ba zan taɓa yafe maka ba... I will never forgive you, because of you everything of mine got ruined and fell apart....."
" anty Mimi dan Allah kiyi hakuri everything will be alright...... Am very sorry..."
"Get out....." ta fada cikin tsawa,
Hannunta yayi niyyar kamowa yaji ta sake daka masa tsawa "I said get out....." her voice shook with rage and heartbreak,
Babu shiri ya tashi ya fita dan ya gane kamar yanzu bata cikin hayyacinta tana cikin tsananin fushi da bacin rai she was in extreme anger and deep sadness, falo ya koma wurin su hajiya amma kuma shima jinsa yayi ya shiga damuwa saboda gaskiyar abinda ta fada haka dinne duk ta dalilin shi ne wadannan abubuwan suke faruwa tabbas shine sila. Tun a ranar da abin ya faru labarin dakatar da itan da aka yi ya karade ko wanne lungu da saƙo na cikin asibitin sai jajanta mata ake yi yayin da masu murna kuma keyi suna cewa she deserves it shiyasa kwana tayi bata yi bacci ba dan damuwa, yanda take cikin damuwa haka shima ya samu kansa cikin damuwar shiyasa jikinsa a sanyaye ya fita daga cikin bedroom dinta lokacin da ta kore shi, falo ya koma wurin su Irfan ya samu wuri ya zauna duk ransa babu daɗi taɓashin da yaji Irfan yayi shine ya sanya ya kalleshi ba tare da yayi magana ba,
"tashi muje masallaci lokacin salla ya yi....."
Tashi yayi suka fita tare kuma har lokacin ya kasa magana, acikin masallacin ma duk hankalinsa ya rabu biyu rabi na can wurin anty Mimi dan haka kawai yaji yana tausaya mata wannan halin da take ciki, bayan sun idar da salla sun fito anan farfajiyar gidan suka zauna Irfan na ta hirarshi shi kadai dan shi Afeef din tamkar kurma baya uhmmm bare uhmmm uhmmm, daga karshe ma gida kawai ya tashi ya tafi duk da yaga su Abba sun fara dawowa,
Bai shiga part din mommy ba kawai ya wuce nasa, tunanin anty Mimi ne fal ransa dan ya san yanzu tana can watakila har lokacin bata daina zubar da hawaye ba wanda yake jinsu suna taɓa har cikin ransa her sobs cut straight through his heart, ya san tana masifar son aikinta kamar yadda ta faɗa mishi haka tana farin ciki da zumudin taga marassa lafiya sun warke sun samu lafiya wannan kam ko shima shaida ne saboda yanda take tattalinsa take kulawa dashi a duk sa'ilin da ciwonsa ya tashi, babu abinda yake gani a wannan lokacin sai fuskarta sharkaf da hawaye wacce take ɓoye da bakin ciki da kuma fushi (deep sadness), gefe ɗaya muryar ta mai sanyi da daɗi tana yi masa yawo cikin kunnuwa sa a lokacin da take zazzaga masa masifa,
Wayar shi ya ɗauka ya fara kiran layinta amma har tayi ta katse ba a dauka ba kuma dama yasan baza a ɗaga dinba duk da zai yi wahala idan tana nesa da wayar tata, wani kiran ya sake gwadawa amma bata ɗauka ba, ai ko bata fushi dashi haka bata faru ba yasan da wuya ta dauka bare kuma ga abinda ya faru, yanda bata runtsa ba shima bai wani runtsa sosai ba, washe gari bayan yayi wanka yayi breakfast ya fita asibiti ya fara biyawa zai duba yaya Haidar dan har lokacin ba a sallame shi ba kimanin sati biyu kenan, Daddy ya gani shima yana fitowa daga wurin su yaya Aliyu din,
"Afeef ina zaka je?"
Jin tambayar da daddy yayi masa yayi banbarakwai tunda yaya Aliyu na asibitin ai ba bukatar a tambaye shi ina zai je,
"Daddy zanje duba yaya Aliyu...."
"wuce ka koma...."
Bai yi musu ba kuma bai ce komai ba bai tambayi dalili ba ya juya ya koma ya shiga motar sa ya fita zuwa family house yana ta tunane tunane cikin ransa na dalilin hanashi shiga duba yaya Aliyu da daddy yayi to ko yau dinma wata rigimar aka sake? Shi dai bai da amsar komai dan haka ya hakura ya shiga cikin part din hajiya, sam bai samu ganin anty Mimi ba saboda tana cikin bedroom dinta ta rufe ƙofa ɓam kamar yadda take yi idan bata gadama ba, wuni guda yayi a gidan dan sai bayan da suka yi sallar isha sannan ya tafi amma duk da haka bai ganta ba idan ya kirata a waya kuma bata ɗauka gashi tunanin ta da wani irin mikin tausayinta sun ƙi barin zuciyarsa ta huta his heart ached for her while his mind raced with worry. A gajiye kuma a kasalance ya koma gida kamar wanda yayi wani aikin ƙarfi, tunaninsa ɗaya abinci da bacci shin anty Mimi tana samun wadannan abubuwan guda biyu? Duk da dai Irfan ɗazu yace masa su Abba sun kirata sun yi mata nasiha kuma sun kwantar mata da hankali akan ta fitar da komai daga cikin ranta kar ta damu komai zai daidaita a yanzu dai ta samu ta bawa kwakwalwarta dama ta huta sosai ta yadda komai nata zai zama daidai.
Kullum yake zuwa gidan kuma acan yake wuni saboda gaba daya tunaninta ya hanashi sakat bare sukuni, baya iya tuna komai sai ita haka kuma baya jin daɗin komai, amma har yanzu bai yi tozali da ita ba tsawon kwana hudu kenan, bashi kadai ba kusan kowa ma baya ganinta, yau dai tunda yaje gidan ya haura upstairs ya tsaya a kofar ɗakinta yana knocking tare da magiyar ta bude masa ƙofa,
"Anty Mimi please na roƙeki da girman Allah ba dan ni ba kiyi hakuri ki bude min in ganki koda na 1 seconds ne, dan Allah ba dan ni ba, i know i mess up but am sorry..... Kiyi hakuri"
Sama sama take jin sa saboda wani irin ciwon kai ne da zazzafan zazzabi suke rinjayarta, jiri yana ɗan ɗaukarta haka ta sauka daga kan gadonta tana dafa bango taje ta buɗe ƙofar, blue din riga ce a jikinta marar nauyi kanta babu ɗan kwali gaba ɗaya gashin kanta ya barbazu ya sauka kan shoulder dinta amma kallo ɗaya zaka yi mata zaka gane a galabaice take dan tayi bala'in fita hayyacinta,
"me ya..... Dawo.... Da.... Kai??" yaji ta faɗa sai dai yanda tayi maganar a rarrabe shine ya sake tabbatar masa da ba ƙalau take ba,
"na zo ne kawai in ganki..... Na kasa daina tunaninki acikin zuciyata...... You are always on my mind.... I didn't stop thinking about you"
Baki yaga ta bude amma sai ta gagara magana kawai yaga ta dafe kanta sannan ta tafi luuuhhhh zata faɗi, cikin sauri kuma cikin zafin nama ya tarota ta faɗa jikinsa sharafff, gani yayi kamar bata numfashi cikin tashin hankali ya soma jijjigata,
" Mimi...... Mimi..... Mimi...." ya fara kiran sunanta cikin ƙaraji daidai lokacin Dr jalila ta hawo upstairs din,
"what's wrong with her? Me yake faruwa?"
"kawai faduwa naga tayi nima ban sani ba..... Bari in dauketa a kai ta hospital..."
"no ba sai ka kaita hospital ba..... Muje ciki"
Cikin sauri ya dauketa zuwa cikin bedroom dinta ya ajiyeta saman gado duk ya birkice kamar ba soja ba gani yake kamar cewa za ayi ta mutu, handbag dinta yaga Dr jalilan ta bude ta ciro joter da pen ta dan yi rubutu, mika mishi tayi tace,
"fita ka samo mana wannan......" cikin sauri ya karɓa ya fita jikinsa yana rawa, ai bai bi ta kan kowa ba yawuce ya fita zuwa pharmacy duk hankalinsa yana can gareta, tsoro yake ji sosai wanda bai san ko na menene ba, gani yake idan ya koma za ace masa ta rasu,
Zuciyar shi na bugawa ya koma gidan bayan ya siyo abunda Dr tace masa wanda drip ne wurin guda shida manya da kanana sai allurai, lokacin da ya koma samu yayi dakin nata cike dasu hajiya da Ammi, suhana, Irfan harda yaya faruk, tana numfashi amma bata ko motsi, shi kam lokacin da ta fadi ma ai kamar numfashinta ɗaukewa yayi haka ya gani, karɓar ledar hannun shi Dr jalila tayi tace su jira su awaje babu matsala insha Allah zata samu lafiya, firfita suka yi gaba dayansu aka barta ta fara kokarin saka mata drip.
Bayan wani dogon lokaci biyu Dr jalila ta fito daga cikin bedroom din, Afeef ta gani yana ta faman kaiwa da kawowa,yana ganin ta fito ya karasa wurinta,
"Dr how is she?"
"she feels better...... A samu dai taci abinci ko babu yawa......"
"thank you....." daga haka ya shiga cikin bedroom din, da kyar ta iya ɗaga kanta ta kalleshi lokacin da ya shiga kananan kaya ne a jikinsa jeans da t shirt wanda suka yi mutukar karɓarshi, gefen gadon ya ƙarasa ya zauna har jikinsa na haduwa da nata, hannunta ya kamo ta fincike da dan guntun karfin da take dauke dashi,
"sannu..... Ya jikin naki?"
Banza yaji tayi masa, a hankali ya kai hannunsa saman goshinta wanda yake zafi ɗau, hannun nashi ta ture, yana kokarin yin magana yaji knocking daga bakin ƙofa, bada izni yayi cewar a shigo nan suhana da Irfan suka shigo harda hajiya tana biye dasu,
" sannu yajiki?" gaba daya suka tambayeta,
"da sauki..... Abinci dai za a kawo mata taci...." ya fada yana kallonta tare da kai hannunsa kan nata ya hada ya riƙe,
"ni bana jin yunwa...." ta fada tana kawar da kanta gefe fuskar ta a daure,
"anty rabon ki da abinci fa tun kafin abin nan ya faru.... Please ki daure kici wani abu" jin abinda suhana ta fada yasa hajiya fadin "zo muje ki kawo mata abinci.... Ai dole taci abinci, haka zata yi ta zama da nufinta?"
Fita suka yi gaba ɗaya suka bar ta da iya Afeef kadai, fuskar ta ya zubawa ido yana ta kallo kamar yau ne ya fara ganin ta wanda tana jin hakan a jikinta...........