GADAR TSAUTSAYI 35
by @nusybee143
Page 35
A zabure suka kalle ta,ko a jikinta ta miƙe da system ɗinta a hannu ta koma ɗakinta,suka bi ta da kallo cikin mamaki da firgici
Rabi'u ya sake zama da Shaheeda akan ta duba ƙudurinta,ta dube shi cikin idanu ta ce "yaya na yanke maganata,a yi hakan kawai
Lokacin da na je ina neman a taimaka min akan wata gagarumar matsala wulaƙanta ni aka yi, yanzu kuma ba lokacin neman taimako ne, lokacin taimakawa kai ne,don haka ka yi shiru kawai yaya"ta miƙe tana yar dariya ta ce"kar ka damu yaya,iya manyan gwamnati kawai zan yiwa,babu ruwana da sauran mutane"ta yi tafiyarta ɗakinta hankalinta a kwance ,shi kuwa ya bi ta da kallo,a tsorace yake, don yana tsoron a kama ta,ko wani abu ya same ta
A ranar ta shirya Mubarak,da daddare ta ce zata kai shi gidan wata ƙanwar mahaifiyarta, Azeema cikin jimami ta ce"shikenan yanzu za mu rabu da Mubarak, sai mun kawo maka ziyara ko?"
Shaheeda tana murmushi ta ce"ai ba mazauniyar ƙasar nan ba ce,a Chad take da aure,tana zuwa duk bayan shekaru biyar, kin ga kuwa ganin Mubarak ba yanzu ba"yanayin Azeema ya canja, Shaheeda ta goya Mubarak tana murmushi ta saka hijabinta ta fice daga gidan
Tana tafiya tana sharar ƙwallar rabuwa da ɗanta,amma har a lokacin zuciya tana sake ingiza ta akan ta kai shi inda zai fi samun kulawa da tsaro, sannan kuma ta daina ganinsa a kusa da ita yana sake tayar mata da mikin baya,a yanzu Mubarak ne kaɗai abin da ya rage da zata rinƙa kalla tana tuna baya tana kuka,gwara ta ɗan yi nisa da shi, ko zata fi samun ƙwarin gwiwar aikata abin da yake ranta
Wajen ƙarfe ɗaya na dare Shaheeda ta shigo wata unguwa ta masu ƙaramin ƙarfi, saboda yanayin unguwar ga kuma katangun gidajen da suka fara zaizayewa,a wannan duhuwar Shaheeda ta lallaɓa ta ajiye Mubarak wanda yake ta shan baccinsa hankali kwance, sannan ta rakuɓe a jikin wani gini tana kallon ɗanta
Ta kai kusan awanni uku a tsaye a wajen kafin ta ga wani dattijo ya fito yana ta sauri,da alamu ladani ne zai tafi kiran Sallah masallaci,ya ci karo da Mubarak da har zuwa lokacin bai farka ba,kuma shima dattijon albarkacin fitilar hannunsa ne ya sa ya ganshi
Ya ɗan razana da farko,ya fara ambaton sunan Allah da sauri, sai da ya samu nutsuwa sannan ya sake dubawa, tabbas jariri ne ɗan kimanin watanni huɗu,ya ɗauki yaron ya shiga gidansa
Bai juma ba ya sake fitowa ya tafi masallacin da zai je
Tana ji bayan ya idar da kiran sallar ya sanar da cewa ya tsinci jariri a wajen gidansa
Bata tafi ba sai da aka idar da sallar asuba,ta yi kuka sosai, musamman da mutane suka taru a bakin gidan dattijon,ya tabbatar da cewa zai riƙe yaron,har ma wasu suka ba shi shawara ya sanar da gidan marayu, sannan ya nemi izinin ɗaukar yaron
Shaheeda bata koma gida ba sai wajen tara na safe,tana zuwa ta fara haɗa nata kayan, sannan ta ce wa Azeema itama ta haɗa nata
Ita dai Azeema sai kallon yadda ta yi sanyi take yi,bata yi mamaki ba, don rabuwa da ɗa akwai ciwo
Sai da ta ci abinci sannan Azeema ta ce"ya kika baro su?ashe ma a can za ki kwana"
Shaheeda ta ce "eh kin san yau zata tafi,sai da na raka su har tasha sannan na dawo gida"
Azeema ta ce "Allah sarki!
Allah ya tsare hanya, Allah ya kiyaye"Shaheeda ta ce"Ameen
Kun gama shiryawa ne? gobe ne tamu tafiyar fa"
Azeema ta ce"mun gama,ranar tafiya kawai muke jira"
Washe gari suka nufi tasha su uku, Shaheeda ta kama shatar mota ƙarama,suka ɗauki hanya suka nufi Abuja
A can Abuja bayan sun sauka ɗaki mai kyau ta kama musu haya a hotel,ita nata dabam su ma nasu dabam, kowa ya wuce ɗakinsa don hutawa
Kwanansu uku ta samar musu gidan haya a cikin Abuja,ta biya kuɗin haya 4m,sannan suka koma can
Already ta siya abubuwan da ake buƙata,babu ɓata lokaci suka fara gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali
Sai dai damuwa maimakon ta ragu a wajen Shaheeda sai ta ƙaru sosai,don haka ta komawa shan ƙwayoyin da take sha sosai, musamman ma don ta ragewa zuciyarta yawan tunanin iyayenta da ɗanta Mubarak
Mutumin da take siyan ƙwayoyi a wajenta shine ya fara nuna mata sha'awar siyar da su,da farko ta yi tunanin hakan zai iya zamar mata cikas ga rayuwarta,amma da ya kwaɗaita mata kuɗaɗe masu yawa sai gashi tuni ta amince,kuma cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ta zama dealer a harkar
Tun tana siyar da abinta iya cikin gida har ta fara fitar da su,tun Rabi'u yana tsoro da tunanin kar asirinta ya tonu har shima ya shiga ya taya ta,shi baya shan komai amma kuma yana taimakawa sosai wajen siyarwa
Saboda neman costumers Shaheeda ta fara yawon zuwa clubs,wani lokacin ma idan aka yi order na ƙwayoyin ana ba ta location na zuwa club ɗin
A can ta koyi shan shisha,sai ya zamana ma ta mayar da rayuwarta ta zama idan babu shisha babu abin da take iyawa,sau tari idan tana aikinta na hacking ta kan ajiye shisha a kusa da ita,tana aiki tana zuƙa,
Zuwa yanzu Rabi'u, wanda ya samu laƙabin Oga boss a wajen tashi sana'ar ta ƙwayoyi ya fara taka ƙasa,tuni Azeema ta koma makaranta ta fara karatu, kuma har zuwa yanzu suna tare a gida ɗaya a Abuja
Tsawon shekara guda suka ɗauka a haka kafin Shaheeda ta yi tunanin zuwa ta duba ɗanta, kamar yadda ta saba haka ma yanzu ta yi ɓat da kama ta tafi Kano, kuma kai tsaye ta nufi unguwar
Ta samu gidan,amma kuma mai gidan Allah ya yi masa rasuwa sati biyu da suka wuce,hakan ya ƙara mata karsashi,ta nuna cewa ta'aziyya ta zo yi,ta bayar da kuɗi 200k
Matar tana ta yi mata godiya amma ita a fakaice ɗanta take kallo, wanda ya lafe a jikin matar yana sauke numfashi
Kallonsa ta yi ta kasa jurewa,ta ce"Mama ba shi da lafiya ne?"
Cikin jimami Mama ta dubi yaron ta ce"Abubakar ai ya kwana biyu yana jinya,shi dama daga damina ta zo ko sanyi to sai dai a yi ta lallaɓawa,kuma ga yadda ake fama da rayuwar"
Shaheeda ta bayar da wani kuɗin 100k ta ce"gashi Mama a kai shi asibiti, ba'a wasa da jinya"Mama tana murmushi ta ce"to baiwar Allah kin bayar da wasu kya sake bayar da waɗannan kuma?kin ga....."
"A'a Mama kar ki damu, Allah dai ya raya miki su ya yi musu albarka,ni zan tafi, Abubakar Allah ya ƙara sauƙi"ta miƙe don fita
Mama ta yi ta yi mata godiya, sannan ta raka ta har bakin ƙofa, Shaheeda ta fice daga gidan zuciyarta a raunane,don sai ta ji kamar ta karɓo ɗanta
Bata koma Abuja ba sai da ta sake komawa unguwar su Abubakar bayan sati biyu,tana tsaye tana tunanin yadda zata ganshi sai ga su sun dawo daga yawo,yana riƙe a hannun ɗaya daga cikin yaran Mama, sauran ƙannensa suna biye da shi
Da dabara da hikima ta yi zuzzurfan bincike game da Mama da ahalinta,anan ta gane kafin rasuwar mai gidan ma babbar yarsu Fauziyya ta rasu tana aji ɗaya a jami'a, sannan suna fama sosai da rayuwa
Da haka ta samu take tallafa musu lokaci lokaci,amma bata taɓa bari sun gane ita ba ce
Bayan watanni shida Shaheeda tana zaune a ɗakinta wayarta ta yi ƙara, ba tare da ɓata lokaci ba ta ɗaga
Mutumin ya sanar mata da cewa ƙwayoyi yake buƙata,suka yi ciniki,ya gaya mata location ɗin da za ta kawo masa
Bata ɓata lokaci ba ta je don kai masa,sai dai tana zuwa a maimakon sabon customer ɗinta sai ta ga ƴan sanda,kuma ba tare da ɓata lokaci ba suka yi ram da ita
Kwananta biyu a kulle babu wanda aka bari ya ganta,dama bata da kowa da ya damu da ita sai Oga boss da Azeema,su ma an hana su ganinta,amma a rana ta ukun sai gashi an bayar da belinta an fito da ita ba tare da wata matsala ba,bayan kuma an tabbatar mata da cewa ba za'a bayar da belinta ba,sai an gurfanar da ita a kotu
Tana daf da fita daga harabar police station ɗin wani ɗan sanda ya taho da gudu yana kiran "Madam!ji mana!"babu musu ta tsaya ya waiga tana kallonsa,ya ƙaraso ya miƙa mata wani kati ya ce "wanda ya yi belinki akwai number ɗinsa a jikin katin,ya buƙaci mu ɓatar da file ɗinki, kuma mun ɓatar,ya kamata ki yi masa godiya"
Shaheeda ta amshi katin tana ƙare masa kallo, kafin ta juya ta fice daga police station ɗin ba tare da ta yi masa magana ba
Tana shiga gida Oga boss da Azeema suka ɗago suna kallonta a firgice,kuma a cikin mamaki, Azeema ta miƙe da gudu ta rungume ta tana murmushi, kafin ta ja hannunta ta kai ta don ta yi wanka ta shirya
Bayan awa guda Shaheeda ta kammala shiryawa,ta ci abinci sannan suka zauna suna jajanta abin da ya faru
Oga boss ya dube ta ya ce"sau uku ina zuwa amma ana ce min wai ba zan ganki ba,sai an tura ki kotu, hankalina ya tashi sosai,yau kuma abin mamaki sai gashi kin dawo gida,ya aka yi kika fito haka?"
Shaheeda ta sauke numfashi sannan ta ba su labarin duk abin da ya faru,sun yi mamaki sosai,kuma sun yi farin ciki, Oga boss ya ce"ai kuwa tunda an ba shi number ɗinki ya kamata ki kira shi ki yi masa godiya, idan ya kama ma ki je ki yi masa,sai mu raka ki,amma ya kika gani?"
Shaheeda ta girgiza kai ta ce"ba wannan ne abin dubawar ba,abin dubawar shine dole ba haka nan ya fito da ni ba,akwai dalili,idan don Allah ne akwai waɗanda suka fi ni buƙatar hakan, waɗanda suka yi ƙaramin laifi meyasa su ba'a fitar da su ba?'
Shiru Oga boss ya yi, kafin ya ce"haka ne kuma,gaskiyarki,amma dai ya kamata ki yi masa godiya"babu musu ta karɓi wayar hannunta,ta saka numbern da ke jikin katin ta danna kira
A mutunce suka gaisa da mutumin, cikin girmamawa ta ce"Alhaji na ga karamci na gode,na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi "
Shiru ya ɗan yi na ɗan lokaci kafin ya ce"amma ban gane mai magana ba"tana ɗan murmushi ta ce"Fati ce, yarinyar da ka yi beli ɗazu "
Alhaji ya yi murmushi ya ce"oh na gane! ƴar kasuwa kenan"murmushi kawai Shaheeda ta yi, Alhaji ya cigaba da faɗin"idan ba za ki damu ba zan iya ganin ki zuwa gobe?"sai da ta ɗan yi shiru tana nazari, kafin ta ce"eh babu damuwa,turo min location ɗin"daga nan suka yi sallama
Tana kashe wayar ta bawa su Oga boss labarin yadda suka yi, Oga boss ya ce "to ki je,amma fa ki yi taka tsantsan,ko ma na raka ki kawai"Shaheeda ta ce"ba sai ka je ba,nima ya kamata a ce na kai lokacin da zan iya ƙwatar kaina,zuwa anjuma in sha Allah zan je"Oga boss ya ce"to shikenan babu damuwa, Allah ya tsare,sai ki kula "Shaheeda ta ce"babu matsala "
Ai kuwa bayan magriba ta shirya ta tafi location ɗin da aka tura mata, ba'a bar ta ta shiga ba sai aka yi mata iso, Alhajin ya ce a bar ta ta shigo
Ta yi mamaki mai tsanani ganin mutumin, Alhaji Sa'idu wada, ministan ilmi na lokacin,bata nuna masa a fuska ta yi mamaki ba ta gaishe shi,ya amsa yana murmushi, sannan ya sa aka gabatar mata da kayan sha,har da tukunyar shisha da ƙwayoyi
A yatsine ta kalli komai ta ɗauke kai,ta ce"Alhaji ai ni bana cikin yanayin yanzu,kai dai ka gaya min abin da kake buƙata,ma gani,idan ina iyawa na yi, idan bana iyawa kuma na kama gabana "Alhaji yana murmushi yana shafa gemunsawya ce"haba zazzafa za ki iya mana
Yanzu dai bari na fara ta kan abu na farko,an ce ke ɗin mai siyar da ƙwayoyi ce,kina da kwastamomi a hannu,don haka nake son mu yi magana,ina son a rinƙa shigo min da ƙwayoyi daga waje,har ma da cocain da sauran kayayyaki,amma ke nake so ki zama agent,idan kika yi haka zan yi miki biya mai kyau,sai adadin miliyoyin da kike so zan ba ki,kuma zan tsaya miki kar wani jami'in tsaro ya yi nasara akanki
Sai kuma abu na biyu, yarinya tun sanda na fara ganinki na ji kwaɗayinki, shine nake so idan zai yiwu a bani dama,na yi miki alƙawarin miliyoyin kuɗi idan hakan ya samu,zan mallaka miki irin gidan da kike so,mota kuwa sai wadda kika zaɓa,amma menene ra'ayinki?"
#Nusy_bee