ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

17

by @gureenjoh

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO


✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN 

(GUREENJOH)


@Gureenjo on Arewapen

@Gureenjih6763 on Wattpad 


ADABI WRITERS ASSOCIATION


#THE TRIO OF TALES 

(THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY)


TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. 


GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.



*SHAFI NA SHA BAKWAI*


Ammar da yake driving cikin mamaki ya ce 

"Me ya faru?”


“Just turn...mu bi wanchan hanyan yi sauri.”


Kaman yadda Irshad ya buƙata haka ya juya da sauri suka bi hanyar, Allah ya taimaka ya hange su ya nunawa Ammar akan ya bi bayan motar haka ya cigaba da binshi har gaban wata makaranta da aka Rubuta Asasul Islam, daga dan nesa Irshad ya dakatar da Ammar idanunsa na kan motar har jidda ta sauka ta shige cikin makarantar.


Sun ɗan jima tsaye har driver din ya ja ya bar wurin.


“lafiya kam Shehi?”


Girgiza kai yayi 

“Lafiya, mu je”


Juyawa Ammar ya yi ya kallesa 

“Haka kawai ka sa muka zo nan?”


“Akwai abin da na yi tunani ne amma kaman ba haka ba ne, mu je kawai”

Ya amsa yana jingina da kujerar idanunsa a lumshe yana tunano fuskar Jiddah especially idanunta da suke cike da wani irin yanayi hade da kwallah.


Haka Ammar ya juya suka nufi gidan Ustaz Abdallah, Irshad ji yake kaman kar su isa, sai lokacin yake jin da ma bai saka wa Maamah ranar akan zai zo nan ɗin ba don shi bashi da abin cewa mace.


"Manya-manya babban shehi ko in barka daga nan ne ka ƙarasa ciki kar in kalle maka mata?"


Tsiririn tsaki ya ja ya buɗe idanu yana kallon Ammar din.


“Me kake kallona haka? Ka ga ka sauƙa mu isa ciki a yi a kawo maka ita nan da kwana kusa mu ma mu samu mu shige daga cikin nan”

Ya fada cikin zolaya da dariya.


"Ammar ka kiyayeni! da ma na hanaka aure ne?”


“Eh mana baka ji su Abba na cewa shekaru ya kamata a bi ba, daga zaran ka yi nima zan samu na yi na gaji da cin tuwon Maamah idan kai baka gaji ba"


Murmushi kaɗan Irshad ya yi bai ce komai ba sai kallon gidan da yake, har ga Allah bai san me zai shiga ya yi ba ko ya ce.


"Ammar ka nema mana iso”


“Ni ne ma na ke son matar kenan”

Kallon please irshad ke mishi, ya sani dama ko kwana zai yi wurin ba lallai ya iya shiga ba muddin shi kaɗai ya zo.


Sauƙa Ammar yayi ya samu mai gadi akan yayi musu iso wurin mai gidan ya ce Shehi ne.


Mai gadi ya wuce ciki chan sai ga shi ya fito yace ya sanar za’a fada mishi yanzu, ba’a jima ba sai ga shi ya fito, kamilallen dattijo ne kuma malami fuska a sake yake yi wa su Irshad da suka fito daga cikin motar maraba, wani irin daadi yake ji na kasancewar Irshad a cikin gidansa da sunan nema da 'yar cikinsa babu abin da ya kai mishi wannan farin ciki ya san Na’imatu ta gama dacen mijin kwarai kuma ta kerewa sa’a.


Iso ya yi musu har babban parlornshi suka gaisa sossai har yake tambayar shehi Uban gidansa don ya kwana biyu ma ba ya Nigeria.


"Sheikh na nan yana maganan shigowa ma kwana kusa in shaa Allah”


“Masha Allah, Allah ya tabbatar"

Daga nan ya miƙe ya wuce ciki, chan aka kawo musu ruwa da snacks da drinks.


Shi dai Irshad gabadaya a takure yake Ammar na ta murmushi don dariya yake bashi wlh kaman me tsoron mata, chan sai gata ta shigo da sallama suka amsa sai dai muryar Ammar ce ta fita shi gogan chan ciki ya amsa sanye take da hijab yadin Mercedes Golden yellow har ƙasa, fara ce kuma kyakkyawa kanta ƙasa ta shigo cikin palorn dan dosanuwa tayi kan kujerar tamkar mai tsoron wani abu.


"Barkanku da zuwa ina yini?"

Ta fada cikin kamillalliyar muryarta, daga jin muryar ka san ma'abociyar karatun alqur'ani ce don su suka iya ba har kalmomin hausa hakkokinsu.


"Barka dai malama Na'imatu kina lafiya?"


"Alhamdulillah"

Ta faɗa jin murya daya ne ya amsa ya sa ta ɗan dago sai suka haɗa idanu da Irshad da shi ma a lokacin ne ya kalle ta.


"Ina yini"

Ta gaishe shi, ya amsa chan ƙasa 


"Alhamdulillah"


Ammar ya katse shirun da ya biyo baya tana ta wasa da fingers dinta ta ji yana cewa 

"Ya fama da school na ji kina Part 3 ko?"


"Alhamdulillah! eh ina Part 3 a nan BUK"


"Wani program kike yi"


Ta amsa 

"Arabic and Islamic Studies"


"Masha Allah, ubangiji ya taimaka"


Ta amsa da Ameen ya rabbi.


Irshad ya dan yi shiru kenan dalibarsa ce ma bai san da ita ba, kuma babu yadda za'a ce bata san shi a makarantar ba hakan ya sa introducing kanshi da yayi niyya ma ya fasa.


Miƙewa ya yi.


"Ki gaishe da mutanen gida"


Ya kalli Ammar dake kallonshi baki sake ya juya ya fice daga parlorn a dole Ammar ya yi mata sallama shi ma ya bi bayan shi.


A jikin mota ya same shi 

"Shehi wani irin hira ne wannan?"


"Me hirar ya yi?"

Baki sake Ammar ke kallon sa.


"Haka ake hira tsakanin saurayi da budurwa? Ba kyau wulakanci ka sani kuma"


"wulakanci? Kai ma ka san ba halina ba ne, Ammar Ammiey cewa tayi in zo in ganta ba gashi kuma na gantan ba? Sai me kuma?"

 Ya faɗa yana tsatsare Ammar din da idanunsa.


Ammar rasa ma abin cewa yayi don takaici.


"Allah ya sa a sake saka ka dawowa zan ga wanda zai biyo ka don ni ba da ni ba"


Ya juya yana kallon Ustaz Abdallah da ya fito yana cewa har sun fito ko ruwa basu sha ba inji Na'ima.


Shehi ya ce 

"Yamma yana yi ne ina da karatu a masallaci kan magrib"


"Masha Allah, Allah ubangiji ya taimaka na gode sosai da sosai a gaishe da su Alhajin"


Ammar ya amsa suka yi musabaha kan suka shiga mota suka bar gidan.


Driving Ammar ke yi yana tuna wai hirar da Irshad yayi ya yi tsaki ya fi dubu, tattausan Murmushi mai kyau Irshad yake saukewa don shi dariya Ammar ke bashi kaman bai san halinsa ba? Shi dai harkar mata kam ba ya tunani yana da wannan baiwar. Ko ya ce lokacin dogon magana da su ne bashi da shi amma bai kushe ta ba tana da natsuwa kuma tana da ilmi ga kyau daidai gwargwado kuma ta fito daga gidan tarbiya wannan qualities za su sa ya zubawa Ammiey idanu su yi duk abin da suka ga shi ne daidai.


Gida kai tsaye suka yi parking... Baƙin jallabiya ce jikin shi yau bai dora alkyabbar ba amma baki da farin gutra da kuma Agal suna kanshi, iska ke dan kada ɗankwalin yana komawa bayanshi yana kuma bayyana fari sol din fatar wuyanshi zuwa kunnuwasa, yana gama sa kafafunsa ƙasa suka jiyo salati da kuka.


Da ɗan hanzari ya daga kai ga bangaren sai ya ga Sumayya ce tafe da sauri tana kuka.


Ammar yayi hanzarin tare ta Shehi na zagayowa bangarensu.


"Menene? Me ya faru?"


"Ya Ammar Daddah...! Daddah ce ta zame ta faɗi a toilet ta kasa tashi"


"Subhanallahi!"

Shehi ya furta yana nufan sashen, Ammar ya rufa mishi baya tun kan su fita su Maamah suka fice Wani Yayansu na aurar da 'ya akwai walima kuma duk Daddah ta saka su Goggo hindatu binsu sumayya ce kawai aka bari ta zauna da ita.


Sun same ta kam kafarta da kugunta ba karamin bugu wa suka yi ba.

Ammar da Irshad suka ɗaga ta suna mata sannu har mota, sumayya ta shiga baya Ammar ya shiga mazaunin driver Shehi ya shiga seat na gaba suka fice daga gidan Baba Lawan na ta Allah ya kiyaye ya bata lafiya.


Asibiti suka yi wa tsinke, a kan wheelchair aka ɗora Daddah wasu nurses suka tura ta zuwa ciki.


Likitan da ke duty lokacin ya karɓi file din su, Ammar ne ke ba da umurnin a kai ta Amenity duk da sun sani nan din ne mutanen gidan suke kwanciya.


"Ranka ya dade Amenity din nan ya zama out of bond, mun samu wani patient da ake tunani lassa fever ce da shi hakan ya sa mun dakatar da shiga gabadaya ward din sai tests results din shi su fita, akwai dai side ward"


Shehi ya ce 

"Ba komai a kai ta chan din"


Likitan ya gyada kai yayi wa nurses din hannu suka wuce da ita, ya bi bayan su su Ammar ma suka rufa musu baya.


Shehi na sanya kafafunsa ɗakin idanunsa basu sauƙa akan kowa ba sai Diva Without intending to ya cigaba da Kallonta har lokacin tana kwance ido rufe hannayenta bisa cikinta drip makale a ɗaga, gashinta kuma baje a kan pillow. Something about her face made him pause ko cikin bacci fuskar rashin mutuncin nan bai chanza ba, kallon seconds ya yi mata ya ɗauke kai ya mayar ɗayan gadon da ake kokarin kwantar da Daddah don gado biyu ne ɗakin.


Ko a fuska bai nuna alamar sanayya ga Diva ba ya ƙarasa kusa da jaddah ya tsaya daga kanta yana mata sannu, kamshinshi na Asad Elixer da ya haɗa da Art of Arabia I ya cike ɗakin.

Sai a lokacin Ammar ya kai idanunsa kan su Diva da tsantsar mamaki yake kallonta Shaly ce kawai a ɗakin zaune gefenta.


Ya kalli Shehi sai dai Shehi ya basu baya ne, bai da tabbacin ya kula da ita.

Me ya same ta haka? Ya tambayi kanshi duk da babu mai bashi amsa.


Likitan da ya shiga duba Daddah ne ya sa ya mayar da hankalinshi kansu, ta gurɗe ne a kafa dole aka yi mata duk abin da ya kamata ta sha wahala kam amma tayi dauriya da addu'a, shaly sai kallonsu take yadda duk hankalinsu a tashe kan matar da ta tabbatar kakarsu ce duba da girmanta.


"Sannu Mama"

Likitan ya faɗa yana kallonta kan ya kalli su Irshad.

"Za ta huta, ga drugs a je a karɓo ta sha ko zuwa safiya sai a yi hoton bayan a tabbatar babu inda yake da wani matsala kan a sallameta"


Ammar ya karɓi takardar.

"Toh Dr. Mun gode sossai"

A tare da Likitan suka fita ya wuce pharmacy.


Sumayya ma ta fita ta yi don ba za ta iya zama Irshad na wurin ba sai ta fito gaban dakin don ta kira su Maamah.


Shaly ta miƙe ta nufi toilet da ke cikin dakin.

Tana shiga wata nurse na shigowa, kan Diva ta tsaya da tray na magani, a hankali ya ɗaga idanunsa ya saukar kansu ta cire drip ɗin tayi mata wasu allurai a canular ɗin kan ta mayar, garin juyawa ta buge sandar drip din sai da yayi taga taga ita ma ta kusa faɗuwa amma ta samu tayi balancing ta juya ta kalli sandar ganin babu abin da yayi ta fice.


Sandar drip din ya zubawa idanu ganin yana rawa da alama ya bar jikin ramin kuma nurse din bata kula da hakan ba, ya bi ruwan da ido har kan hannunta dake kwance akan shafaffen cikinta, zai ɗauke ido ya ga ta motsa hannun ta sauƙar gefenta hakan ya ƙarasa jan IV stand ɗin zai faɗo kanta without thinking twice ya miƙe ko kan karfen ya faɗo mata ya tare, a hankali ya mayar da shi cikin ramin dake jikin gadon ya riƙe igiyar ya gyara da kyau don ta ɗan harɗe shi jikin hannunta.


Just then, diva's fingers twitched.


Idanunta suka ɗan buɗu a daidai ya kalli fuskarta sai ya kawar da idanu ya bar wurin as if ma bai tsaya kanta ba.