BABI NA SHA DAYA
by @maidambu41
KARFE DUKKA KARFE NE...!!!
{Zanen ƙaddarar Falilah}
BABI NA SHA DAYA
🌸 Assalamu Alaikum Yan’uwa Mata.
Kowace mace tana son ta ga kitchen ɗinta cikin tsari da kyau, tare da kayan zamani masu inganci. Amma abin da kan hana mutane shi ne tara kuɗin saye lokaci guda.
Shin tara kuɗin saye ne ke miki wahala?
Ko kuma idan kin tara sai wasu buƙatu su sa ki kashe su?
Ki kwantar da hankalinki, domin MA KITCHEN ta zo da mafita.
Mun buɗe Adashen Kayan Kitchen domin ki mallaki kayan da kike buri cikin sauƙi, ba tare da wahalar tara kuɗi lokaci guda ba.
✨ Abubuwan da za ki samu:
✅ Kayan kitchen na zamani masu inganci.
✅ Farashi mai sauƙi.
✅ Adashe mai sauƙi da kwanciyar hankali.
✅ Ana kai kaya zuwa duk inda kike.
✅ Biyan kuɗi a hankali cikin sauƙi.
Za a fara nan ba da jimawa ba, In shaa Allah.
📞 WhatsApp/Call: ***
📲 Shiga WhatsApp Group ɗinmu domin samun cikakken bayani da fara rajista:
***
🌹 Arha ta fi bashi, adashe kuma ta fi bashi kwanciyar hankali. Ki yi rajista tun da wuri, ki mallaki kitchen ɗin mafarkinki cikin sauƙi.
MA KITCHEN – Muna tare da ke har ki cika kitchen ɗinki da kayan da kike buri. 💚
Sai da ta kai wani irin tsoron kowa na gidan nake, kusan a kullum sai ya zo ya min tijara wanda zai saka ni kaina naji tsoronshi da kuma abinda yake min, sannan ta gefen Suwai ta hana shi koda shiga dakina ne, ba wannan ne matsalar ba dukan da yake min ya fara razana rayuwata, har na gama rayuwata sau daya Hajja Mama ta dake ni yau ga wani kato da bai san darajata ba yana dukana, haka yasa na koma wata sakarai kayan dakin da nake da shi ma da yarshi tayi yaji wai kayan dakinta ya lalace kishiya tana mata gori shine ya kwashe kayana ya bata, shima yadda abin Talya faru wani suna muka je, tun kafin mu dawo aka kwashe kome hatta suturan sakawa na, haka yasa na koma dakin na zauna Shiru Ina sauke ajiyar zuciya, Ina son nayi kuka amma idan na tuna yanzu wata uku kenan rabon da na ga wani nawa ya tako inda nake, sai nayi shiru na hadiye kukan ba wai don ban iya kuka bane kawai kukan ne baya zuwa min.
Wani abin da ya kara min tsoron auren shine yadda lokaci guda yan gidan, suka fara min gori da cewa sai da ba lalace aka bashi aurena, wani irin abu ya tsaya min take suka fara guduna ba me yarda na taba kayansa, kai haka ko da na bi Matar gidan zuwa wani wurin zan ga ana nuna ni sai na daina ni daya nake rayuwa ga Suwai da ta kasa ta tsare,
Wata na biyar ci da safe bayan nayi sallah asuba, nayi mafarkin Mr aljani. Yana mika min hannu, zuba min duka aka yi tare da daka min tsawa, yadda na tashi a firgice Ina kallon Salisu. Na zauna ina sosa wurin, "ki fita ga aiki can jaka karamar karuwa, ga mace har mace amma bata da amfani me zai saka na kwanta da ke ne ma." Haka na mike na fito na fara aikin, har na gama wurin karfe sha biyu da abincin ranar da na daura, yara suka dawo, Akwai wani is Yaron Matarshi na biyu Mai suna Karibu, yana fita da masu farauta to yau da ya dawo wai ashe dawa tayı kyau, wurin karfe daya da wani na wannan ranar, ina tsugune ina wanke tsakin da zan yi talge, kawai naji an daura min abu me sanyi, a wuyana, shafa abin nayi ashe maciji ne, ni dai ban san me ya kuma faruwa ba domin a wurin na zube.
After wasu hours da ya biyo baya, na farka na ga Hajja Jume a gaban gadon da nake tana zaune, "Hajja jume?" Na Kira sunanta ni na zata mafarkin da na Saba yi ne, ta ce min. "Alhamdulillahi barka da arziki yau ai kwana uku Kenan kına kwance." Dafe kaina nayi Ina son na
Tuna abinda ya faru, amma ina kaina fara ciwo ya fara min, ganin yadda na rike kaina, yasa suka kara min allura, na koma. Sai da na kara kwana biyu kafin na farka daidai Yayuna wanda muke uba daya suka zo ban da yan dakinmu.
Lumshe idanuna nayi ina son nayi kuka amma na kasa, sai nayi ta sauke ajiyar zuciya. Ya Kabiru wanda shi ne dan Hajja Warisa na biyu ya ce min. "Ai an raba auren, Fisabilillahi lilly kina zaune Ana miki irin wannan cin zarafin ki yi shiru? Kin ga jikinki yadda Nurse Binta ta ce duk duka ne, haba Falilah sai ki biyewa Ya Man after you know your right sai ki kashe kanki? Kin san jininki har nawa ya haura?" Murmushi nayi Ina kallon shi tare da jin maganarshi.
Sai na koma kamar wata wawuya, domin tunda nayi sallah na koma na zauna tea na sha, sannan na kwanta, kamar ance na d'aga kai idanuna ya sauka akan Ya Nafi'u. "Daddy" na furta a hankali, shima idanunsa yayi jajjur, zuwa yayi ya zauna a gefena, "Daddy!" "Shiii!" Ya furta min a hankali na daura kaina a kafadarshi, hawaye na zuba min, a hankali nake wani irin kuka, mun shaku da Ya Nafi'u irin shakuwar da kowa ya gani sai ya ji zuciyarshi ya motsa, a haka har barci ya dauke ni, sai da barcin yayi nauyi sannan ya kwantar da ni, bude idanuna nayi zan mishi kuka. "Ina nan ai!" Haka yasa na lumshe idanuna, na cigaba da barcin.
Hira suka shiga har zuwa lokacin da Aunty Zuhra ta zo daga Kaduna, ganin yadda na nikewa Ya Nafi'u, bata iya boye min ba domin faɗa ta yi ta min, ina murmushi kawai ita ta zauna a wuria na tsawon kwanaki goma, ranar da aka sallame ni, Kaduna muka wuce da ita, duk da bani da iddar Salisu sai da kai wata biyar kafin na fara zawarci, sai dai ranar da Ya Man yasan ina Kaduna da kansa ya zo ya min koran kare, haka yasa na wuce Kano, wurin Daddy,
Tun da na faɗa mishi ina hanya Daddy ya zo tasha ya zauna jirana, har muka iso. Ya dauki akwatina ya saka a motar, muka wuce gidansa da yake dan ladi na sidi, tunda na dawo Kano ban kara sha'awar aure ba sai da Hajja Mama zasu tafi umara suka biyo Kano, ta saka ni gaba da faɗa dole nayi aure, haka naji fadar ban wani damu ba sai bayan ta dawo aka yi wani rasuwa a can muka je taaziya nan na haɗu da Muhmud baban Hamida. Ya ganni a rasuwar kuma shima akwai dan zumunci a tsakanin iyayenmu, tunda ya ganin shi kenan ƙaddarata ta ta sauya,
Duk da bana son nayi auren nan, amma saboda Hajja Mama nayi ba wai ina son auren bane, kawai nayi ne don kada ta cigaba da damuwa a kaina ne, haka yasa aka yi auren da sharadin Zan fara aikina, shima Muhmud, akwai nashi matsalar, babu abinci sannan a yadda na fuskanci lamarinsa na gano wacece ni, sai ya tsiro min wani hali baya nimana idan kuwa na nime Shi sai na biya shi, sai Allah ya jarabce ni da son zama dashi saboda haka duk wata na dauki Albashi nake biyanshi. Amma baya gani duk da haka mahaifiyarshi gani take kamar na mallake mata d'a ai shima bakinsa ba kanin kafarshi bane haka yasa na dauki nauyin gidan har da na kishiya da yaranta. A ban tab'ata damuwa ba kawai bana son Ya Man ya ce naki zaman aure yasa na sakawa raina dukabinda zai faru zan iya handling dinsa; amma ina duk yadda naso na shanye sai na fahimci akwai wani shirun da baya bukatar kawaici domin kowa a cikin gidan daukar advanger yake akaina daga mijin yan uwansa mahaifiyarshi. Zama dai yaki dadi haka nayi ta hakuri. A watan da nayi mafarkin mr aljani a satin aurena ya kare ba don naso ba sai dai bni da yadda na iya kuma akan fada da muka yi da matarshi.
duk da muna cikin gari daya amma gidanmu ya haramta a gare ni, ina ji ina gani na wuce kano ashe na fito da karamin cikin hamidah tunda na dawo na samu transfer zuwa kano, na cigaba da kula da kaina tare da taimakon Daddy. Haka yn uwana suna tsaye bisa kaina, har na haifi ha,idah ubanta ko tsinke bai turo min ba. A yadda ya dauka ko zamu damu da shine sai ya ga ba haka ba, dole na kula da yarinyata, watan hamidah goma sha bakwai muka hadu da doctor mu'awiya, dan gayu dan kwalisa wanda yake cin lokacinsa da tsinke. Ba ni da zabi akan doctor Mu'awiyu sai dai tun baayi nisa ba na fahimci ko anyi auren nan akwai matsala babba, amma haka na saka kaina cikin takalminsa. Har aka yi auren sai dai kwana daya tal mahaifinsa ya ce ya zaba ko shi ko ni, ina ji ina gani ya sake ni ba zance naji zafi ko ciwo amma lokacin da na kira Ya nafi'u na gaya mishi ban ji kuka ba sai da Ya hamza ya zo naji kuka ya zo min kawai na fashe da kuka, ashe akwai yarinyar da suka yi zai aura amma yaki shine babanshi yayi alkawarin duk wacce zai aura matukar ba yarinyar bace sai ya saka ya sake ta like yadda ya faru da ni yanzu haka, a yau aurena uku.
Dukda ban san yadda yan uwana suke kallona amma ina jin wani irin ciwo wanda ina ganin daddy na manta da w
Da (88ani b'acin rai, murmushi me hade da hawaye na isa inda yayi parking motarshi, yana tsaye yya harde hannunsa kirjinsa, ko da na isa gabanshi bude min kofar motar yayi yakai Ni gidan Ya Bana. A lokacin na fahimci matukar ka wuce zaman gida gaskiya babu inda zaka ka zauna lafiya sai gidan iyayenka ko dakin mijinmu.
Don ma Ya bana yana tsaye Amma iskancin da Abidah take min sai Allah,. A daddafe nayi wata biyar a gidan, sai ga Alhaji Sani, wanda muka haɗu a asibiti, kamar ba zan fadawa Soyayyar shi ba amma lokaci kaɗan na ji zan aure shi........