HAYAT NAZLI

2

by @maryamannour71


Chapter 2. 

 

Bayan ta tashi a aji kai tsaye tourism ta nufa inda Neesah ta shaida mata ta na jiranta, ita ba ma'abociyar shiga gurin ba ce musamman da ya kasance da wuya ka ga mutumin kirki a gurin, sau da dama idan ta ma Neesah magana a kai sai ta ce mata ita kawai iskan gurin ke burgeta after all ba gurin kiɗa ko snooker ko gurin shan shisha ta ke zama ba. Daga waje ta tsaya ta fito suka nufi parking space inda ta adana motarta, tuƙi ta ke babu wanda ya ce da kowa komai, hankalin Nazli na kan titi Neesah kuma na wayarta. 

 

"Wai ni mene ki ke a waya haka ki ke aikin murmushi?" "Ba komai nothing serious." Sai kuma ta aje wayar gefe kafin ta fuskanci Nazli ta ce. 

 

"Uhmm, Sis please ina neman wata alfarma a gurin ki...!" "Alfarma?" Wace iriyar alfarma kenan Aunty Neesah, kin san i can do anything for you muddin bai fi ƙarfi na ko saɓawa addini ba." "Yeah na sani, ina son ki raki ni wani wuri ne please kar ki ce a'a Sisy." Ta faɗa ta tare da haɗa hannaye biyu ta marairaice fuska, da mamaki Nazli ta dube ta ta ce. "Wani wuri?" "Eh, kar ki tambe ni ina ne idan muka je za ki gani, kin san an ce gani ya kore ji." Nazli ta yi shiru na ƴan daƙiƙo kan ta ce. "Yaushe ne kuma tafiyar?" Cikin ko in kula Neesah ta ce. 

 

"Takwas na dare." Wani irin zaro ido Nazli ta yi tare da taka birki babu shiri, ta fuskanci Neesah da ke kallon ta da mamakin abun da ta yi ta ce. Ƙarfe takwas na dare?" Kin san abin da ki ke faɗi kuwa?" Ta ɗan kaɗa kai. "Ki yi haƙuri Neesah, amma ba zan iya zuwa ba. sanin kanki ne ina da aure, ta yi ki ke tunanin zan fita cikin wannan lokacin a zatona ke mai tsawatar min ne idan kin ga na yi ba daidai ba a matsayin ki na ƴar uwata kuma Yaya a guna." Ta yi maganar cikin rashin daɗin rai. Cikin rashin jin daɗin kalaman ta Neesah ta ce. "Haba sis, ji yadda ki ke magana sai ka ce zan kai ki banzan wuri da bai dace ba, ba wani abu ba ne idan bakya son zuwa amma maganganun da ki ka yi ban ji daɗin su ba, ai ko zan cutar ba dai na cutar da ƙanwata ba." Jin haka ya sa Nazli cikin sanyin muryar ta ce. "Ba haka na ke nufi ba, kawai na ga lokacin fitar ne bai dace ba kuma Zaid ma ba zai amincin ba." "Kar ki damu na fahimta." "Ina kuma za ki tafi ba mu isa gida ba." ta faɗa ganin ta na ƙoƙarin buɗe murfin motar. "No kar ki damu ba sai mun je gidan ba hakan ma ya wadatar, wani lokacin na zo gidan ki." Daga nan bata tsaye jin me Nazli za ta ce ba ta fita tare da barin wajan ta tsaida napep ta tahau suka wuce, shiru Nazli ta yi ta zuba ma bayan ta ido ba tare da ta samu zarafin tsaida ita ba, sai ta ji ba ta kyauta ba. 

 

Cikin sanyin jiki ta tada mota ta hau titi, a hanya ma haka ta ke tsake–tsaken zuci ita dai haka kawai bata jin fitar. koda ta isa gida da ta watsa ruwa ta ci abinci kwanciya ta yi kan kujera bacci ya soma fizgarta, ƙarar notification da ya shigo wayarta ya sa ta buɗe ido ta duba, massage ne daga Neesha. "Ki shirya by 8 zan zo ɗaukan ki, idan damuwar ki Zaid ne to na masa magana kuma ya bada izini." Sai ga ƙiran Zaid ya shigo, inda ya ke tabbatar mata za ta iya zuwa babu damuwa shima yau ba lallai ya shigo da wuri ba dan aiki ya musu yawa a office yau. 

 

Shiru ta yi ta kaɗa kai ba don ta so ba ta tura ma Neesah saƙon amincewar ta, dan har ga Allah ba ta san me ya sa ba haka kawai jikin ta ke bata kamar wani gagarumin abu da zai faru, tun da ta wayi gari yau ta ke fama da faɗuwar gaba da bata san dalili ba. 

 

~~~~~~_ 

 

BAYAN SALLAR ISHA. 

 

Zaune ta ke cikin palour ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, hankalin ta na kan talabijin yayin da ta ke jingina da bayan kujerar da ta ke zaune a kai. Sanye ta ke cikin wani tsaɗadɗan lashi baƙi da a ka mar ɗinkin fitet gown da ta zauna cas a fitet jikinta, simple makeup ne a fuskarta ta yi ɗaurin Zarah Buhari. Yayin da wuyarta ke sanye da sarkar gwal da ɗan kunnenta, sai farin mayafinta da ta ɗaura a kafaɗa. A hankali ta ke kaɗa kafa lokaci zuwa lokaci ta ke duba agogon rolex da ke tsintsiyar hannunta. Siririn tsaki ta yi ta tana tunanin abin da ya tsaida Neesah har haka bayan ta ce karfe 8 za su tafi su dawo kan lokaci amma har 8 ta wuce a na neman 9 babu ita ba inuwarta. Miƙewa ta yi ta jawo wayarta da son ƙiranta sai kuwa ga na ta ƙiran ya shigo, picking ta yi ta kara a kunne ba tare da ta yi magana ba ta tsungumi jakarta ta yi waje. 

 

"Wow..! ma sha Allah ƴar gidan Daddy shalelen Mommy Babyn Zaid, wannan kyau haka?" Ai sai ki saka na koma na canja wasu kayan." Neesah ke maganar a sanda ta ga Nazli na fitowa. "Ohh please kar ki saka kai na ya yi girman, ba ma wannan ba me ya tsaida ke har haka?" Na faɗa miki ba daɗewa zan yi ba ƙololuwa idan na yi awa ɗaya zan koma gida." "Sorry little Sis na ɗan tsaya na yi wani uzuri ne amma yanzu ba gani ba." Ta yi maganar cikin son kaucewa ƙarshin kalamanta na ba za ta haura awa ɗaya ba, illai kuwa bata sake maganar ba ta ce. "Uhm shi ke nan yanzu tashi motar mu tafi please." 

 

A hanya Neesah sai zuba ta ke tana jan Nazli da hira wacce ita daga uhm sai uhm uhm ta zubawa titi ido, ƙarshe da Neesah ta dame ta da surutu lumshe ido ta yi kamar mai bacci alhalin ba baccin ta ke ba. A yadda motar ke falfala gudu kan titi da bugun zuciyarta ta ke, wani irin tsoro da fargaba ne ke laluɓe ta tun ba su iso wajan da za su ba. Jin tsawuwar motar ne ya sa ta buɗe ido ta soma kallon wurin. Zare ido waje ta yi lokacin da ta yi arba da sunan wajan. 

 

"Hotel?" Neesah me mu ke a nan?" "Kai...can you just relax ki kwantar da hankalin ki mana idan muka shiga za ki gani ai, afterall ba wurin shan jini zan kai ki ba." "Na sani amma Hotel fa Neesah?" Me ki ke tunanin zai faru idan wani ya gan mu for crying outloud, kin san dai waye Daddy a garin nan kuma idon shi na ko ina, just imagine an kai masa wannan rahoton ko abokan hamaiyya suka gani?" Duk cikin ruɗu Nazli ke maganar sai faman kare fuskarta ta ke, sabon tsoro ma ta kasa fita daga motar. 

 

Wannan ba shi ne karon ta na farko zuwan Hotel ba, tunda sau tari idan za' yi wani event kamar abun da ya shafi kasuwanci ko birthday party wani lokacin ta kan bi Daddy idan za su saka hannun jari a wani company to ya kan zo da ita dan ta ƙara fahimtar wasu abubuwan afterall ita za ta karɓe shi zuwa wani lokaci. But this? Bata san a wani mizani za ta ɗaura shi, wani gutun tsaki Neesah ta saki zuciyarta cike fal da haushin Nazli ji ta ke kamar ta mangare ta, Allah ya sani ba dan umarnin Daddy ba da ta bar ta a nan ta yi gaba abin ta. ta ja kwafa tana tunanin da da hali ta samu superglue ta manne wannan bakin nan na ta da bai gajiya da tambaya, Fita ta yi ta zaga ta buɗe ƙofar kana a zafafe ta ce. "Ke wai me ya sa ki ke abu kamar wata bagidajiya ce?" Haba wise up mana, da ki ke iƙirarin wani zai gan mu ce mi ki a ka yi iskanci ya kawo mu?" Ko kuwa iskanci kaɗai ke kawo mutum Hotel?" ta numfasa ta ja ajiyar zuciya ta sauke kana ta maida kallon ta gare ta cikin danne fushinta ta ce. "Kin ga Nazli please don't make this hard for me already, dan Allah ki fito mu tafi me ki ke jira na baka na zuba da mun shiga za ki san abin da ya kawo." Cikin sanyin jiki Nazli ta fito suka nufi ciki, gaba ɗaya a ɗarare ta ke. 

 

Babban Hotel ne da masu zuwa wurin sai babban ƙusa wanda ya ci ya sha har ya tada kai, ko dai babban ɗan kasuwa da ya ke cikin lokacinsa. Elevator suka shiga suka sauƙa a hawa na uku kan su bi wani corridor da zai sada ka da wani hall, suna isa wurin Neesah ta ce. "Sisy ki yi gaba ina zuwa bari na ɗaga wannan ƙiran." Gyaɗa kai kawai Nazli ta iya mata ta yi gaba dan yanzu ita abun ya soma bata tsoro, cikin sanyin jiki ta yi shahada ta shiga hall ɗin sai dai ta na saka ƙafa wutar wurin ta ɗauke. Wani irin tsoro ne ya kamata da sauri ta juya za ta koma ta ji ƙofar gam a rufe, bugo ta soma murya na rawa ta ke faɗin. "Please! somebody help..! Neesah, Aunty Neesah ki buɗe." 

 

Tunanin kunna wutar waya ne ya zo kanta, ta na kiciniyyar fiddo wayar daga jaka sai wilik wutar ta dawo. Sai tafin hannaye ya biyo ba da waƙar happy birthday to you da a ke. Wani irin juyi ta yi da sauri tare da ƙarewa hall ɗin kallo ganin yadda a ka ƙawata shi da decoration ɗin flowers da baloon's, ga kuma ƙaton hoton frame ɗinta a ka manna a bango da manyan baƙi a ka rubuta. HAPPY BIRTHDAY SWEET NAZLI. 

 

Fitowar su Daddy,Mommy, Zaid da sauran jama'ar daga wajan maɓoyar su ya sa Nazli kai duban ta gare su, hannu ta saka a bakinta ta na mai jin hawaye sun taru a idanunta, kana da gudu ta faɗa jikin Daddy ta saki kukun farin cikin ganinsa dan for a momment ta ɗauka mutuwa za ta yi dan ta tsorota sosai. cikin mamakin da bai gama sakinta ba ta ɗago ta kalli shi ta ce. "Daddy wannan fa?" How comes ban san komai a kai ba?" Wai tsaya ma, kuna nufin yau birthday na ne ban sani ba?" Murmushin da ke nuna irin soyayyar da ya ke wa ƴarsa Daddy ya yi ya dafa kafuɗunta ya ce. "Ina zan manta ranar da ki ke zo duniya?" ranar da ta fi min ko wacce rana farin ciki, ranar da a ka haifa min princess ɗita." "Yes sweetheart, ina zamu manta da wannan ranar, wannan rana ce mafi girma da soyuwa a wajen mu. Dan haka muka zaɓi yi miki wannan suprise ɗin, hope you like it." Cewar Mommy. "Ohh Mommy i loved it, shi ne ba wanda ya faɗa min." Ta faɗa cikin kwabe fuska, Zaid da tun ɗazu bai yi magana bane ya ce. "To ya zai zama suprise idan muka faɗa miki?" Wannan reaction ɗin da ki ka bada shi ne big deal." 

 

"Aikuwa dai, Mommy ba ki ga yadda ta wahalar da ni ba wajen kawo ta wurin nan ba." Kwabe fuska ta yi ta turo baki gaba irin shagwababbun yaran nan ta ce. "Mommy kin ganta ko?" "Ke Neesah shiga taitayin fa yauwa, bayan wahalar min da ƴa da ki ka yi har ki na da bakin ƙorafi?" "Ai shi kenan Mommy na yi shiru tunda bakya ganin laifin ƴarki sai nawa." "Ba dole ba, yarinya bata miki komai ba amma ke sai neman tsokanarta ki ke." Jin daɗin an goyi bayanta ya sa ta cire kai tare da mata gwalo yayin da Neesah ta harareta ƙasa ƙasa yadda ba mai ji ta ce zan kama ki ne yarinya." 

 

Tahowar cake da a ka shigo da shi mai hawa uku ya sa kowa haɗuwa wuri ɗaya a ka saka Nazli a tsakiya, yayinda ta hura candle ɗin sama kana ta yanka cake ɗin suka soma mata tafi. Ɗaddy ta fara ba a baki kafin Mommy Neesah koda ta zo kan Zaid a kunyace ta saka mishi a baki shima ya bata a baki. Nan kowa ya soma bata gifts cikin farin ciki da jin daɗi ta ke amsa, koda a ka zo kan daddy cewa ya yi na shi ba yanzu ba zai yi announcing ɗinsa anjima. 

 

Kowa ya zazzuna a ka soma serving snacks da su drinks shagali a ke na manyan mutune babu wani hayaniya, cool music ne ke tashi. Mutane za ka ga sun haɗu cikin group group daga masu maganar business da masu hirar luxury life sai kuma masu hirar ƙawatuwar wajan da kuma irin daular da a ka kashe. 

 

Can gefen masu rabon abinci da abun sha kuwa, daga cikin masu rabon ne tsaye a a ɗan wani lungu ya laɓe sai faman waige waige ya ke, dukkan almun rashin gaskiya sun bayyana a tattare da shi, a hankali ya saka hannu cikin aljihun wodonsa ya fito da wani abu kamar powder da ke nannaɗe cikin wata farar takarda ya juye cikin ɗaya daga cikin lemokan da ke tray za a yi serving wa bak'i ya juya da kyau ta yadda ba mai fahimtar komai, mikewa ya yi ya gyara tsayuwarsa ya kakkabe hannayensa ya gyara nicktie ɗinsa kafin ya d'auki trayn ya nufi cikin hall, koda ya zo shiga suka had'a ido da wani waiter d'an uwansa ya masa alama da Kai kan ya raba ya shiga. 

 

zaune ta ke da wasu ƴan mata suna magana ta ga Zaid tsaye shi kaɗai ya na latsa waya, murmushi ta yi tare da ɗan matsawa ta bar wajan ta nufe shi. "Hy, Zaid ya ka tsaya a nan kai kaɗai ne?" Ɗagowa ya yi ya kalle ta kan ya ce. "Na ɗan ɗaga waya ne." ya furta tare da nuna mata wayar hannunsa, da okay ta amsa kana cikin son jansa da hira ta ce. "Gaskiya na ji daɗi sosai am happy, duk da kun kusa bani heart attack da wannan suprise na ku, but is worth it." Murmushi ya yi ya ce. "Idea ɗin Mommy ce, ta ce ta na son bawa ƴarta mamaki ta na son ta ga dariyar shalelenta ta kafin ɗayan suprise ya zo." Ya faɗa tare da sakin wani murmushi da shi kaɗai ya san ma'anar sa, ba tare da ta maida hankali wurin kalamansa ba ta ce. "Iya wannan ma ya ishe ni ya faranta min rai matuƙa." "Am glad to hear that." Daga haka suka ɗan yi shiru ba cewa komai a cikin su sai dai idan suka haɗa ido kuma su sakar ma juna murmushi, kowa da abin da ya ke saƙawa a zuciyarsa. Nazli ganin wannan ce damarta na fallasa masa sirrin da ke zuciyarta ya sa ta ɗan muskuta ta ce. "Uhm, dama maganar da na ke son mu yi ɗazu ce ko zamu iya yin ta yanzu?" Gyara tsayuwarsa ya yi ya ya maida wayarsa cikin aljihu ya harɗe hannayensa a baya kana cikin nuna girmama maganar da za ta yi ya ce. "Ba damuwa go ahead, ina sauraran ki." Sosa kyarta ta yi alamun ta na cikin taraddadin maganar da za ta yi, ta ce. "Dama ina son na sanar da kai ni Nazli na... dafata da a ka yi a baya ba zato ba tsammani ya sa ta saurin juyowa dan ganin wanda ya katse mata hanzari, Daddy ta gani tsaye da wasu manyan mutune da a kallo ɗaya ta fahimci daga cikin Abokan kasuwancin su ne. Faɗaɗa murmushinsa Daddy ya yi yana shafa kanta ya gabatar da ita wajensu, ya nuna Zaid da ke daga gefe ya ce. "Wannan kuma sirkina ne, na san ma kunsa shi." 

 

"Let's catch up letter." Zaid ya raɗa mata kunne bayan ya gaisa da baƙin Daddy ya ba su waje, haka nan ba don ta so ba ta gyaɗa masa kai ya tafi ta maida hankali wurin hirar da daddy ke wacce galibi kan harƙallar kasuwanci ce. Duk ƙoƙarin Nazli na ganin sun keɓe da Zaid su yi magana abun ya gagara, dan da ta samu dama sai wani abun ya gifta. 

 

Yanzun ma zaune take da wasu ƙawayen su na makaranta da Neesah ta yi inviting na su, sun tutseta gaba sai tsiya suke mata wai ashe dama da aurenta ba su sani? dama ba wanda ya san da auren cikin ƙawayen sai mutum ɗaya ce da ta kasance aminya gare ta wato Elham, amma ta yi mamakin rashin ganin ta wajen sai ta yi tunanin ƙila Neesah ce bata gayyace ba don da wuya a ce Elham ta san wannan party ba zo ba. 

 

Ta na hankalce ta da Zaid da Neesah da ke tsaye can nesa da su suna magana kuma ga dukkan alamu abu mai muhimmanci suke tattauna a kai duba ga irin yadda suka maida hanakli kan hirar. Can sai kuma ta ga cikin fushi Neesah ta bar wajen, sosai abun ya bar ta da tunanin me ke faruwa? Ganinsa tsaye shi kaɗai ya sanya ta miƙewa ta na ƙoƙarin zuwa wajensa ta ji kamar daga sama an dafata ta tare da ƙiran sunanta. "Barka da zagayowar haihuwa Aunty, Allah ya ƙaro shakaru masu Albarka." Cewar Nadiya da shigowar ta wajen kenan ta ke bilayin nemanta cikin mutune, miƙewar ta yi Allah ya sa ta hangota. "Ohh! Nadiya, amin na gode. Yanzu ma na ke tunanin ki na ke son faɗawa Zaid ya sanar a kawo ki." "Eyyah Aunty, ai Aunty Neesah ta turo driver ya kawo ni." "Ta kyauta gaskiya, dan ko bata yi ba ni zan sa a kawo mun ke." Ta faɗa cikin jan hannunta suka zauna kan kujera, a hankali suka soma hira jefi jefi inda Nazli ke tambayar ya jikin ƙaninta da bashi da lafiya take amsa mata da sauƙi. Suna cikin haka wasu ƴan mata daga cikin ƙawayen Neesah suka yi joining na su. 

 

Nadiya kam gaba ɗaya a ɗarare ta ke sai nuƙu–nuƙu take sam ta kasa sakin jiki, sai da ta shigo wurin ta sake raina kanta ganin duk manyan mutane ne daga ƴar governor sai ɗan.... ko ƴar babban ɗan kasuwa, sai ta ji ta raina kanta. Fahimtar hakan ya sa Nazli dafata ta sakar mata murmushin kar ta ji komai ta saki jiki, waiter ne ya zo ya aje musu abubuwan motsa baki kan table na su. Ƙin taɓawa komai Nadiya ta yi sai da Nazli ta saka baki tukun ta ɗauka, Nazli kam drink da ya aje mata gabanta ba tare da tunanin komai ba ta ɗauka ta soma sipping a hankali yayin da suka cigaba da hira.  

 

Idanunta ne suka fara lumshewa kanta ya sara mata, ta soma ganin uku uku. "Lafiya Nazli?" Yarinyar da ke kusa da ita ta faɗa cikin damuwa ganin yadda yanayen ta ya sauya kamar mai jin jiri, ita ko Nazli wani irin zafi jikinta ke, Hall ɗin ta soma ganin ya na juya mata, baya baya ta yi za ta faɗi  Nadiya ta yi saurin riƙo ta, murya cike da damuwa ta ce. "Aunty lafiya?" Ko bakya jin daɗi ne?" Ta jefo mata tambayar, ƙaƙulo murmushi ta yi tare da girgiza musu kai ta yi. "Lafiyana kawai kai na ne ke ɗan ciwo." Ta amsa su ba don ciwon kan kaɗai ke damunta ba, wani irin zafi ta ji jikinta ke ga wani irin yanaye da soma jinta ciki....