15
15
***Wani irin baƙon yanayi yake ji a game da ita wanda bai taɓa jin irinsa akan wani ba sai ita kaɗai, na farko jin ta yake tana yawo cikin jinin jikinsa tamkar rayuwar su na manne da juna wuri guda, na biyu kuma wani irin abu mai girma yake ji game da ita shi ba tausayi ba sannan kuma shi ba tsoro ba to menene wannan abun? Shine tambayar da yake ta faman yiwa zuciyarsa amma ya kasa gane ko menene saboda kowanne seconds da awanni jin abun yake yana sake girma, hannunta yaji ta fincike daga cikin nasa har tana kokarin fama ɗaya hannun dake ɗauke da cannula,
"yi a hankali....." ya fada yana sake bude idanuwansa a kanta, babu abinda yake tunawa sai irin yanda ta sandare masa ɗazu ta faɗi a jikinsa shi kansa yasan ba dan yana cikin firgici da tsoro ba ai da an samu matsala, fuskarshi ɗauke da murmushi ya zuba mata ido yana kallonta yayin da ita kuma ta kawar da kanta tare da juya masa baya, wani knocking din ya sake jiyo ana yi nan ya tashi yaje ya bude, suhana ya gani dauke da farfesun kayan ciki da kuma tea acikin dan madaidaicin mug,
"yawwa thank you...." ya fada bayan ya karbi farfesun da tea din, juyawa tayi ta fita shi kuma ya karasa bakin gadon anty Mimi ya zauna,
"tashi ki sha tea din gashi an kawo...."
"ni bana jin yunwa...."
"ko bakya jin yunwa ki dan daure ki sha kici wannan farfesun zaki ji dama dama please ..."
"na ƙoshi...."
"to zan jiraki har zuwa lokacin da zaki ji yunwa sai kici koda kuwa hakan na nufin zan kwana ne anan...."
Kallon sa tayi fuskarta a turbune nan ta ga yana kokarin ajiye tea din da farfesun,yunƙurawa tayi ta tashi zaune ta mika masa hannu alamar ya bata nan ya mika mata ta karɓa ta fara shan tea din tana cin farfesun duk da ba wani dadinsa take jiba dan gaba daya bata da apatite ma, ido ya zuba mata yana kallonta ko kiftawa baya yi kamar wanda yau ne ya fara ganin ta, sai da taji tana kokarin yin amai sannan ta barshi ta mika masa ta sake komawa ta kwanta, jin ana kiran sallar la'asar ya sa shi tashi ya fita zuwa masallaci ana idar da salla ya sake komawa bedroom din nata, a hanya suka yi arba da Ammi wacce itama ta fito daga wurin anty Mimin, a iya saninsa babu wata kunya ko surukanta tsakanin shi da Ammi amma sai ya ji yana dan jin nauyinta yau, har ƙasa ya durkusa ya gaisheta ta amsa cikin kulawa sannan ta wuce shi kuma ya tashi ya shiga wurin anty Mimi wacce ya tarar tana bacci suhana kuma tana gyara mata bedroom din wanda harma ta gama ta kunna turaren wuta dakin ya fara gaurayewa da kamshi mai dadi na turaren bakhoor, fita tayi ta barshi yana tsaye yana kallon anty Mimin bayan fitar suhana ya karasa gefenta ya zauna, hannunta da idan ya kama take ta faman fusgewa tana ture shi yanzun ma hannun ya kama ya riƙe cikin nasa yana murzawa a hankali bayan ya dan hada jikinsa da bayanta kaɗan hannun nata laushi tamkar na jaririn da yazo duniya yanzu fatarsa bata jima tana shan iska ba, duk tayi wani buzu buzu da ita kamar wacce ta shekara tana jinya,wayar shi ya ciro daga aljihu ya saka a silent saboda kar akira shi karar wayar ta tada ita daga wannan daddadan baccin da take yi dan Allah kadai yasan yaushe rabonta da samun bacci, yana nan zaune a gefenta bai matsa ba har sai bayan da aka kira sallar magriba sannan ya tashi ya fita ita kam har lokacin baccin ta take yi ba kakkautawa. Sun fito daga masallaci shida Irfan yaga kamar su Abba da daddynsu harda yaya faruk zasu je duba anty Mimi, bai bisu ba wuri ya samu ya zauna wurin hajiya har sai da suka fito suna maganar basu samu dubata ba ma saboda sun tarar da ita tana bacci sannan ya faki idonsu ya sulale ya koma cikin dakin,
Inda ya mayar mazauninsa wato gefenta nan yaje ya zauna yanzu dinma ya kama hannunta yana wasa da yan yatsunta, bai san dalili ba haka kuma bai san me yasa ba kawai ya samu kanshi da kissing hannun nata sannan goshinta, ita dai bata san me yake yiba dan wani mugun bacci mai nauyin gaske take yi, sallar isha ce ta sake tayar dashi bayan sun fito ya zauna suka yi dinner da su hajiya da sauran iyayensu maza kamar yadda suka saba, shi dai kam yau baya jin zai bar part din hajiya shiyasa bayan kowa ya baje an watse ya shige bedroom din anty Mimi harda saka key ya rufe ƙofa, kan gadon ya hau ya kwanta kusa da ita yaja duvet ya rufe musu rabin jikinsu ya zaro wayar shi a aljihun wandon jeans din da yake jikinsa, ɗan short video yayi mata ita kadai sannan yayi musu tare tana ta bacci bata san abinda yake yi ba, text massage ya turawa mommy cewar zai kwana a family house wurin Irfan, ya san ba zata ce komai ba dan dama ya saba kwana tun suna yara wani lokacin sai yafi 1 month idan ta raya masa, latse latsen shi yake ta yi a waya har kusan 12 lokacin ne ya ajiye wayar kan bedside drawer dinta ya kwanta bayan ya shige jikinta sosai. Bayan asubah ya farka nan ya ganta har lokacin bata farka ba, shifa baccin nan nata fa kuma ya fara bashi tsoro, bacci tun jiya da safe wuni guda, awa nawa tana bacci, Allah Allah ya rinka yi a idar da salla ya koma ya tashe ta, Irfan na ta son ya zauna a masallacin saboda akwai ƴar takaitacciyar nasiha da ake yi kullum amma yaƙi yace zai rinka jiyowa daga dakin anty Mimi,
Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya shiga cikin bedroom din sakamakon ganinta da yayi a zaune kan gadon fuskar ta duk ta kumbura da idanuwanta duk tana jinsu sunyi mata nauyi, da kallo ta bishi har ya karasa shiga cikin dakin ya zuba gwiwowinsa a ƙasa ya dafa gadon yana kallonta,
"sannu..... Ya jikin?"
"Bani ruwa insha..... Mai sanyi" yaji ta fada ba tare da ta amsa sannun nashi ba, tashi yayi ya fita downstairs ya dauko mata bottle water mai sanyi ya koma, bude mata yayi ya mika mata ta karɓa yana kallonta bata ajiye robar ba sai bayan da ta shanye ruwan tas, komawa tayi ta kwanta ta juya masa baya mintuna kadan wani baccin ya sake kwasheta, zama yayi gefenta ya zuba mata ido a hankali ya kai hannunshi goshinta ya ɗora idanuwansa na kanta ko ƙiftawa baya yi,
Tun bayan da ya dawo daga masallaci bai matsa ko nan da can ba har 10 ta ɗan gota a lokacinne yan dubiya suka fara shigowa suna duba ta kuma hayaniyarsu ce ma ta tashe ta daga baccin da take yi, da kanta ta cire cannula din dake hannunta dan ta dameta sannan ta takura mata, breakfast suhana ta kawo musu amma tace a bari sai ta fara yin wanka sannan zata ci, jin hakan da ta faɗa ya sanya kowa dake cikin bedroom din fita, shima Afeef bin Irfan yayi suka fita zuwa part din Irfan, wanka yayi ya saka farar jallabiya sannan ya koma dan yasan yanzu kam ta gama shiryawa, knocking yayi sau ɗaya kuma bai zauna zaman jiran a bashi izni ba ya tura kansa cikin dakin, tana zaune gefen gado daure da towel da cup a hannunta tana shan tea,
"ya jikin naki?" ya tambaya yana kallonta kamar yau ne ya fara ganin ta,shuru yaji babu amsa nan ta cigaba da shan tea dinta har ta sha rabin cup din sannan ta ajiye ta tashi a hankali ta wuce gaban closet ta ɗauki doguwar riga ta shan iska ta saka bayan ta feshe jikinta da turare, komawa kan gadon tayi ta zauna fuskar ta duk a cunkushe, tea din da yaga ta rage ya dauka ya fara sha yana ta faman aikin kallonta, kwanciya yaga ta sake yi ta dan lulluba da duvet duk da ba bacci zata yi ba,
Zaman kurame suka cigaba da yi har Ammi ta zo, kallon Afeef Ammi tayi bayan sun gaisa tace,
"Afeef ai ya kamata kaje gida ka huta kaima, ka samu kayi bacci...."
"A'a Ammi babu komai.... Bana jin bacci, I don't want to leave her side...."
"duk da haka ko baka jin bacci kana bukatar hutu, tun jiya kake zaune anan kuma daga ganin idanuwan nan naka baka samu isasshen bacci ba da daddare, kaje gida ka huta......"
"to Ammi bari naje zuwa azahar sai na dawo...."
"A'a azahar ai baka wani huta ba, kaje zuwa dare sai ka dawo, zan turo suhana ta zauna tare da ita kafin ka dawo..... Kana bukatar hutu kaima kaji...."
"to Ammi..... Bari naje, Allah ya bata lafiya"
"amin, Allah yayi maka albarka"
Tashi yayi ya fita, duk abinda yake faruwa anty Mimi tana jin su, bayan ya fita Ammi ta zauna tana kallonta,
"wannan yaron yana ta faman kokari a kanki..... Tunda kika kwanta yake dawainiya dake baci ba sha..... Ubangiji Allah ya saka masa da alheri, hakika wani hanin ga Allah baiwa ne" tana jin Ammi har tayi ta gama dai bata tanka ba, so take ta tambayi jikin yaya Aliyu amma ta rasa wa zata tambaya, so take taji har yanzu bai samu lafiya bane ko yaji sauki? Ta san bata isa ta tambayi Ammi ba ko hajiya shiyasa ta ja bakin ta tayi shuru amma kuma tana son sanin halin da yake ciki. Koda Afeef ya koma gida kamar yadda Ammi ta saka shi every 30 minutes yake kiran Irfan yaji ya jikin anty Mimi, bayan sallar la'asar video call ya kirashi yace yaje bedroom dinta yana son ya ganta, tashi Irfan yayi daga kusa da hajiya ya nufi upstairs wurin anty Mimi, kai gaskiya Afeef fa kamar ya shiga da yawa dan abubuwan da yake yi sun zarta hankali, tana kwance tana baccin dai kamar jiya yau ma din ta wuni tana bacci ne, kallonta yake yi ta cikin wayar tashi,
"hankalinka ya kwanta yanzu?" Irfan ya fada cikin tsokana,
"ba sosai ba, me yasa zaku barta ita daya?"
"ba ita daya bace wallahi ita da suhana ne na jiyo motsin ta acikin toilet...."
"ok tom sai na zo, anjima nima zan shigo, bana son in saɓa umarnin Ammi ne"
Magriba nayi ya tafi shida Manal, yanzun ma jallabiya ce a jikinsa amma baƙa ta ciki yasa wando jeans, niyyar shi yau ma ya kwana wurinta amma tunda ya shiga dakin shida Msnal yaga tana ta faman ɓaɓɓata rai iya Manal kadai ta amsawa shi kuma tayi banza dashi, fita yayi zuwa masallaci saboda lokacin salla ya yi, bai koma wurinta ba sai bayan sallar isha bayan su abba sun gama zaman majalissun su, tare da daddy Manal suka tafi shi kuma ya zauna kuma a lokacinne ma yake jin labarin yaya Aliyu yaji sauki dan yanzu daga wurinsa yaya faruk ya dawo. Daren yau kam bata jin bacci ko kadan, lokacin da Afeef yaje bedroom din jinsa yayi ta garkame kayan ta da key nan yayita knocking amma taki budewa,
"sauki ya samu kenan...." ya fada cikin ransa tare da juyawa ya koma wurin Irfan, kallonsa Irfan yayi amma sai bai ce komai ba saboda yanzu wasu abubuwan da suka shafi anty Mimi da shi babu bukatar ya rinka tsoma bakin sa sai dai ya zuba ido kawai dan sun fi kusa............