HAULA HABEEB

BABI NA GOMA

by @amdeeytejjdunique587

BABI NA GOMA










A parlour kuwa, ’yan ɗaurin aure ne suka dawo. Daddy ne a gaba, su Salim suna biye da shi, da su Uncle Bulama, amma banda Habeeb, don shi sashensa ya wuce kai tsaye da abokansa. Shi ma Salim ɗin wucewa ya yi ɗakinsa. Kallon Mommy da fitowarta main parlour kenan, tana yi wa masu aikin abinci magana Daddy ya yi, sannan ya ce ta same shi a ɓangarensa. Daga haka ya wuce. Sai da ta gama maganar da take yi, sannan ta rufa masa baya.

A can parlour na Daddy kuwa, kowa ya hallara, duk manyan family ɗin har waɗanda suka zo aure. Bayan Mommmy ta shigo, Daddy ya ce ta je ta kira mai Gwaggo.

Haula

Yau tunda ta tashi take jinta wata iri. Ta kasa morar kanta. Tunda ta yi sallar asuba da ƙyar ta kwanta, ta kasa tashi a inda ta kwanta, don ko gado ta kasa samun arziƙin komawa. A inda ta yi sallah a nan ta kwanta. Ba irin maganar da Gwaggo ba ta yi mata ba, amma ta yi shiru, ba don ta kasa tashi ba ko ba ta ji ba, sai don yadda take ji an ɗaure ta. Ba ta taɓa jin irin wannan yanayin ba tunda take.

Yanzu ma Gwaggo ce ta shigo ta same ta a inda ta bar ta tun ɗazu. “Haula, wai ke, yau me ke damunki? Tun safe kike kwance a nan, ba irin maganar da ban yi miki ba kin share ni. Ko abinci ba ki ci ba, ga shi har rana ta yi. Ko ba ki da lafiya ne?” Cewar Gwaggo cikin kulawa.

Kuka kawai ta fashe wa Gwaggo da shi. Nan hankalin Gwaggo ya tashi, a rikice ta fara tambayar ta me ya faru, me ke damunta. Ta rungume ta tana rarrashinta haɗi.

Sai da kukan ya fara sassautawa, kafin ta ce, “Gwaggo, ba na jin daɗi ne, kuma lafiyata ƙalau. Wani yanayi nake ji kawai, wanda ba zan iya ba shi suna ba, amma tunda nake ban taɓa jin irin haka ba.” Cikin kuka ta ƙarashe maganar, don ita kanta ba ta san me ke damunta ba.

Sake rungume ta Gwaggo ta yi. Ta yi mata addu’a, ta tofa mata, kafin ta ce, “Ki tashi ki ci abinci. In sha Allah, ko ma me zai faru alheri ne.” Ta janyo farantin da ta haɗa mata abinci a ciki. Shayi ta fara ba ta a baki, a hankali ta karɓa, sai da ta sha rabin kofi sannan ta kau da kanta. Abincin shi ma ta buɗe lafiyayye, sai tiriri yake yi yana tashin ƙamshi. Ƙofar da aka ƙwanƙwasa shi ya katse hanzarin da za ta ɗaga mata abinci a baki.

Tashi Gwaggo ta yi ta je ta buɗe ƙofar. Mommy ce ta bayyana. Saƙon da Daddy ya sanar mata ta yi, wucewarta ta yi ba ta jira ta amsa ba. Cikin mamakin dalilin kiran ta dawo cikin ɗakin. “Ki ci abincin, ina zuwa. Alhaji ne ya aiko a kira ni, ina zuwa yanzu.” Mayafinta ta ɗauka ta yafa, ta fice, kafin Haula ta fara tsare ta da tambayoyin da ita ma ba ta san amsarsu ba.

Salim

Tunda ya shiga ɗakinsa, ba abin da yake yi sai kuka. Sai da ya yi mai isarsa kafin ya ba kansa haƙuri, domin ya san soyayyar da ya daɗe yana rainonta, yau ta zama ba tashi ba. Wani ya ɗauka, wani da shi kansa ko a hasashe bai taɓa hasaso hakan ba. Sai dai abin da ya sa wa ransa shi ne, ya haƙura ya bar wa Allah komai, don ba soyayya kaɗai ba, hatta rayuwarsa zai iya haƙura ya salwantar da ita saboda Habeeb. Duk da soyayyar da yake yi wa Haula ba ƙarama ba ce, amma an ce idan so cuta ne, haƙuri ma magani ne. Kuma zai yi wannan haƙurin ko da zai zama sanadin yankewar numfashinsa. Ya san Allah zai rabauta shi da kyakkyawan sakamako a nan gaba. Kuma ya yi alƙawari, da yardar Allah, ko a fuska ba zai taɓa nuna ya taɓa son Haula ba. Don ya yi la’akari da kalmar nan ta Bahaushe da yake cewa, “Matar mutum kabarinsa.” Lallai gaskiya ne, matar mutum kabarinsa.

Idan ba haka ba, ai ba da ita aka tsara auren ba, ba ma wanda ya yi tunani ko hasashen haka. Idan ma fasawa aka yi kuma aka nemi wacce za a ɗaura da ita don gudun jin kunya, ai akwai ’yan uwa da dangi masu ’ya’ya mata da yawa. A cikin gidan nan ma akwai. Amma da yake duk ba matarsa a ciki, ita ɗin ce dai matarsa. Sai Allah ya yi ikonsa a kai. Abin da ba a taɓa tsammani ba ya faru. Kenan dai, ko da ba ta aure shi a yau ba, duk daren daɗewa, ita ɗin ba rabona ba ce.

Shafa kansa ya yi, yana jin ’yar natsuwa na sauka masa. Yanzu abu ɗaya ke damun sa, yadda za a yi zaman tsakanin Haula da Habeeb. Ya san halin kowa a cikinsu, kuma dama ba shiri suke yi ba a tsakaninsu. To, yaya kenan? Ya tambayi kansa. Sai kuma ya sake ba kansa amsa. Allah da ya haɗa, ai Ya fi kowa sanin dalilin da ya haɗa. A yanzu ma, shi zai yi komai, amma zai sa ido sosai shi ma, wajen ganin an samu daidaito a tsakaninsu. Yana fatan kuma Allah ya taya shi. Ajiyar zuciya ya sauke yana jin komai ya shuɗe masa. Tashi ya yi, ya ɗauro alwala, ya yi nafila, ya yi addu’o’in neman samun sauƙi a zuci da dangana. Sannan ya yi musu addu’ar samun zaman lafiya a rayuwar aurensu.

Lallai duk wani tsanani na rayuwa da bawa zai shiga, ko na rashi, idan ya zauna ya saurari zuciyarsa ta fuskar da za ta ba shi mafita mai ɓullewa, ba tare da ya rufe idonsa daga ganin gaskiya ya zama makaho da gangan ba, to za ka samu mafita. Idan ka miƙa lamuranka ga Ubangiji, ka ba shi damar zaɓar mafi alheri, to ba za ka taɓa taɓewa ba, don Allah ba zai taɓa zaɓa maka da zai dame ka ba. Lallai haƙuri babban lamari ne da ke taka rawa a rayuwarmu, wanda zai kai mu ga matakin da ba mu taɓa zato ko tsammani ba.

Daddy

Gwaggo ta yi wa Daddy ƙuri da ido, tun lokacin da ta fara fahimtar inda zancensa ya dosa, har zuwa yanzu da ya kai ƙarshen zancen nasa. Kasa cewa komai ta yi, sai saukar da kai ƙasa da ta yi.

Daddy ya ce, “Ki yi haƙuri Gambo. Na san ban yi miki adalci ba da na yanke wannan hukunci, tunda ban ji ta bakinki ba. Amma na yi hakan ne saboda gudun jin kunya a gaban dubban mutanen da na tara a wurin, waɗanda suke ganina da mutunci. Kuma ina da yaƙinin ba za ki yi musu ba ki ba ni kunya, don a tunanina ni ma ina da hakkin yanke hukunci a kan Haula a matsayina na Uba a gare ta. Fatan za ki yi mini alfarma.”

Da ƙyar Gwaggo ta tattaro yawun bakinta ta haɗa kalma, don Daddy ya riga ya ɗaure ta da jijiyoyin jikinta. Sai dai ba za ta bari yarinyar ta cutu ba. 
“Alhaji! Duk wannan ba matsala ba ne, don kai ma Uba ne a wurin Haula kamar yadda kake gani. Sai dai har yanzu yarinya ce, ba ta kai wacce za ta iya ɗaukar haƙƙokin aure kuma ta sauke su ba. Alhaji, ba wai ina ƙalubalantar abin da ka yi ba ne, amma abubuwa ne da ke Hajiya, a matsayinki na mace, idan muka tattauna da ke za ki fahimce ni.”

Daddy ne ya ce, “Ko ma menene, ina fatan dai ba za ki tankaɓar da ƙoƙon barata a gare ki ba. Za ku iya magana.” Daga haka ya miƙe, ya shige ya haura bedroom ɗinsa.






Ɗakin Mommy

“Ina sauraronki,” cewar Mommy bayan sun dawo ɗakinta ita da Gwaggo.

Gwaggo da ke zaune a gefen kujerar da ke ɗakin ƙwaya ɗaya, ta ɗago ta kalli Mommy, kafin ta mayar da kanta ƙasa ta fara magana. “Hajiya, ina fatan za ki duba maganganu da fuskar fahimta. Ba wai ba na so na ba ku Haula ba ne, don ba wanda ba zai so ya haɗa zuri’a da iyali masu nagarta kamar ku ba. Kawai dai duba da rayuwar Haula ce. Yarinya ce ƙarama, duk shekarunta sha biyar, duk da wannan ba matsala ba ne, don da tana ƙauye ne da yanzu ta yi aure. Amma abin da nake so ki gane, Haula yanzu ne take girma. Kin sani, kuma kina kallo, yanzu ne take ƙirgar dangi. Watan da ya wuce kuma shi ne wata na farko da ta fara ganin baƙonta na wata. Ba ya da haka. Haula ba ta da hankali da natsuwar da za ta fahimci mene ne rayuwar aure da hakkokin da suke kanta a matsayinta na matar gida a yanzu. Ba ta san mene ne rayuwa ba, sai shirme da shiririta. Abin da nake ƙoƙarin ɗora ta a kai kenan, sai ga shi an yi mini shigar sauri.”

Mommy ta kalle ta cike da mamaki. Wa zai ga ’yar wata dukiya irin HAZ Family ya dinga irin wannan maganar? Ita dai a iya saninta, irin dukiyar da suke da shi, ko jinjira suka ce suna so za a ba su, balle wannan gandandan da ita. Sai da ta sake kallonta, kafin ta ce, “Me kike nufi Gambo? Ina fata dai ba kina nufin ya sake ta ba? Duk waɗannan abubuwan, kafin a ɗaura ne za a yi batunsu. Abin da ba a yi ba, shi ake da sauran wani tsaiko da shawara a kai. Wanda ya faru kuma, sai dai a yi addu’a kawai. Kuma na ga kin fi kowa sanin waye Son, saboda ke kika rene shi. Iya kulawa zai ba ta, ba zai taɓa cutar da ita ba. Sannan shi ma a wani ɓangare, dole zai ɗaga mata ƙafa. Kuma idan kin lura, wannan auren haɗi ne na Allah, saboda ko hasashe ba wanda ya hasaso faruwar hakan. Allah shi ya san dalilin da ya sa ya haɗa wannan auren. Kuma matar mutum kabarinsa. To, mu bi lamarin da addu’a da fatan alheri, sai mu ga alherinsa. Ko ba ki duba komai ba Gambo, ki duba alfarmar da Alhaji ya roƙa a wurinki, ko don mutuncinsa.” Mommy ta kafe ta da ido tana jiran amsarta.

Gwaggo ta kasa magana, duk da akwai magana a bakinta. Sai dai an riga an yi mata dabaibayin da ba za ta iya kuncewa ba.

Murmusawa Mommy ta yi, kafin ta ce, “Ki je sadakinta na hannun Daddy. Na san zai neme ta zuwa anjima. Za mu kawo kayan lefe da komai da komai, kamar yadda ake yi wa kowace yarinya. Gobe za ta tare, ba ɓata lokaci, tunda an riga an ɗaura.”