MARTANI BY RUKAYYA YUSUF IBRAHIM (A. Y. M Creatives)
Episode 3
Babu ƙawa ko guda daya aka tattara A'ishatu da mutane biyu Daga dangin mahaifinta da kuma biyu daga dangin Ummanta suka kaita gidan mijinta bayan dimbin nasihar da Umma tayi mata kan zaman aure.
____
Episode 03
Tunda shirya-shuryen tariyar amaryar Ashraf ya ta shi.
Yaya Rumana ta tara mutanan gidan har masu aiki akan cewa" kada fa su kuskura su nuna cewa ba ƴar aiki ba ce ita, ta toshe bakin ƴan aikin da kudi don tasan halin wasu daga ciki, san nan ta tsorata su akan duk wanda taji ko taga yana shi-shigewa amaryar zata kore shi".
Haka zalika tayi zama da Zeenah domin tasan zata bata matsala. Amma cikin ikon Allah tayi nasara a kanta.
Ango kuwa babu abinda ya shafeshi da zancan amarya a cewarsa ya zuba ƴan uwan nasa ido ne, tunda sun ki jin maganarsa.
____
Tunda masu kawo amarya suka doso unguwar da za a kai A'ishatu hankalinsu ya tashi, ba dan komai sai dan ni'imar da suka hango.
Gida ne na alfarma wanda komai yaji daidai gwargwado, kallo daya zaka ne cewa tabbas masu gidan sun tara sun tada kai .
Zeenah ce tarbi Amaryar kamar yadda suka tsara , Yaya Rumana na ƙasan kujera .
Su Mama Rahana suka miƙa amanar A'ishatu hannun Zeenah kamar yadda aka ce musu ita din matar wan mijin ce.
Daga bisani kuma aka wuce da ita wani part wanda Zeenah ta kalli Yaya Rumana ta ce" ta rakasu".
Babu musu Yaya Rumana ta miƙe tana gyara daurin zaninta kamar ƴar aikin gaske , tayi gaba suna bin ta a baya .
Mama Rahana ce ta kalli inda aka bude musu a matsayin mallakin A'ishatu, ta shiga tunanin girma da daukaka ta Ubangijin samai da ƙassai.
Sai a yanzu take jin tabbas wannan auran na A'ishatu akwai alkhairi, a irin tarbar da ƴan uwan mijin suka yi musu na karamci da girmamawa. San nan ga uwa uba wannan tamfatsetsen guri wanda aka kashe dukiya wai na A'ishatu ne.
Cikin faduwar gaba ta riƙe kirjinta sakamakon wani tunani da ya dirar mata a zuciya, tayi saurin kawar da tunanin ta hanyar kiran Ubangiji.
Part ne guda wanda two bedrooms ke ciki da toilet sai katon kitchen.
Kana shiga falon kafar bene ita take maka maraba, wanda aka ce duk abunda ke kasa shine ɓarin A'ishatu .
Saman kuma ɓarin mijinta ne, ɗaki daya aka shigar da ita suka zaunar da ita bakin gado .
Daga nan Yaya Rumana ta fita ta basu guri don tasan akwai fadan da zasu yi mata a matsayinsu na ƴsn uwansa, kamar yadda akewa kowacce amarya in kawo ta gidan miji ake yi.
Ai kuwa kamar jira ta ke Gwaggo lami ƙanwa ga mahaifin su A'ishatu ta fara cewa" lallai su Sani, yanzu sun san wannan gidan ne shine zasu zabe ki ga namu yaran? Ko da yake kowa ya hau tashar kwadayi zai sauka ata wulakancinki. Don na rantse da Allah gidan daga gani na ƴan yankan kai ne, gida kamar ba a ƙasar da muke ciki ba".
Da mamaki Mama Rahana suke kallonta , dayar wacca ita daga dangin baban A'ishatu take ta ce " haba lami menene haka" .
Gwaggo lami ta kaɗai tana hare-hare.
Babu wanda ya sake cewa komai har tsawon lokaci kafin Mama Rahana ce ta ce" A'ishatu ki kwantar da hankalinki kinji. Allah ne ya kashe ya baki cikin dubban al'umma don haka ki yi addu'a ki godewa Allah.
San nan kar kiyi wasa ko sakaci da neman tsarin Allah , don tun yanzu kinga yanda ƴan hassada suke neman a mayar da bakin cikinsu a fili".
" Ke! Rahana ki fita a idona wallahi" cewar Gwaggo lami.
Murmushi Mama Rahana tayi kana ta ce" ba dani zakiyi wannan haukan ba Malama, A'ishatu Allah ya baku zaman lafiya zan tafi na bawa Mama Hadiza labarin ƴarmu na cikin amincin Allah" ta juya ta fita sauran ma suka biyota.
Yayin da Gwaggo lami ta bita, tana kare mata zagi Ita dai Mama Rahana ko kulata bata yi ba .
Tunda suka fita A'ishatu ke kuka mara sauti, ta ma rasa wani tunani ya kamata tayi ne.
Haka ta zauna babu motsin kowa sai ita kaɗai kamar mayya, kiraye-kirayen sallar magriba ne yasa ta miƙewa ta buɗe wani guri da take kyautata zaton toilet ne.
Shiga tayi ta kama ruwa san ta daura alwala.
Inda akwatunan ta suke da aka jera mata su ta bude daya ta ciro hijab , ta dauki dadduma ta tada sallah.
Bayan ta idar ta dade tana fadawa Allah damuwarta da kuma neman farin ciki da zaman lafiya a wannan sabuwar rayuwar da zata fara yau.
Bata tashi daga gurin ba har sai da aka kira Ishaqi tayi. Hakan ma motsin shigowar mutum din da taji ne.
Zeenah ce da Yaya Rumana suka shigo riƙe da kwandon abinci .
Suka ajiye a gefe, A'ishatu ta gaishe su kanta a kasa.
Murmushi Zeenah tayi ta dafa A'ishatu kana ta ce" Matar Ashraf kuma ƙanwata da nake matuƙar ji da ita.
A ganin farko da maganaina sukai miki naji wata nutsuwa ta shige ni, ina fatan ace yadda kamanninki suka nuna kamala haka dabi'unki suke".
A'isha ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannunta kafin Zeenah ta ce" Sunana Zainab amma ana kirana da Zeenah.
Da mijinki da ni ƴan mata zar mike , ma'ana Mahaifiyarsa yayar Mahaifiyata ce. Kuma na zo na auri Yayansa Labib.
Wannan kuma mai aikin mun ce Yaya Rumana, tana da kirki sosai kuma ita zan ara miki ta dinga yi miki aikace-aikace kafin a samo miki wata" A'ishatu ta ɗaga kanta tana kallon Yaya Rumana da aka kira a matsayin me aiki.
Zeenah ta katse ta da cewa" ina fatan zaki saki jiki damu nan kusa amarya , kuma duk kinji bayanin da nayi miki ko?".
Cikin tausasa harshe A'ishatu ta ce" eh naji Aunty in sha Allahu kuma zaku same ni , fiya da yadda kuke zato Allah ya sawa zaman namu albarka ".
Zeenah ta kafeta da ido kamar mai tunani sai kuma ta ce" da Aunty kika kira sunana A'isha?".
A'ishatu ta saurin kallon Zeenah cike da mamaki.
Zeenah ta share ƙwallar da ta fara zubo mata da cewa" bani da wa bani da ƙanwa ko ƴaƴan ƴan uwa A'ishatu. Tunda na taso babu mai fadar sunana da girmamawa sai yau ko masu ai sai dai suce hajiya nagode sosai A'ishatu, naji dadin samunki a ma tsayin matar dan uwana " ta miƙe da sauri tana cewa sai da safe ki rufe kofar kinji".
A'ishatu binsu tayi da kallo har suka fita ganin cikin sakanni yanayin Zeenah ya canza.
Ta sauke ajiyar zuciya tana bin kwandon abincin da suka ajiye mata.
_____
Suna fita daga barin A'ishatu Zeenah ta juyo tana kallon Yaya Rumana tana cewa" don Allah Yaya kar mu ruguza rayuwar yarinyar nan, she is too young ace ta dauki ragamar abunda bata shuka ba".
" Me kike nufi ne Zeenah?" Cewar Yaya Rumana.
" Ina nufin ku barta ta tafi ta auri wani su samu zuri'a, don Allah babu Lallai Ashraf shima ya haihu. Kin san irin abunda muka aikata a baya kuma kin san cewa baza muyiwa Allah wayo ba".
Shiru Yaya Rumana tayi kafin ta ce " kinga zo mu tafi don Allah, babu wani abu Mun riga da mun tuba ga Allah kuma nasan Ubangiji yaji rokon mu".
Murmushi Zeenah tayi suka shige ciki ba tare sun sake wata magana ba.
______
Ashraf tunda ya fita Masallacin Jumma'a bai dawo sai ƙarfe goma na dare.
A lokacin ƴan uwansa na zaune a falo suna ta kiran wayarsa amma yaki dagawa.
Zeenah ta dubi Labib ta ce" Allah bazan juri gani ya wulaƙanta yarinyar nan a daran farkon su ba, yarinya bata ji ba bata gani ba".
Yaya Rumana zata yi magana sai gashi yayi sallama.
Tunkan ya zauna Zeenah ta ce" Ashraf kaji tsoron Allah, ace ranar auranka sai yanzu zaka shigo gida bayan ko a da ba haka kake yi ba".
Kallonta yayi baice komai ba har ya zauna san nan ya ce" to me zan mata in nazo ?".
Duk suka tsira masa ido da mamaki, Labib ya ce" Ashraf karka aro dabi'un da ba naka ba don Allah".
" Yaya Labib don Allah ki bar ni na huta , ba dai kun aura min ita ba, kuma kuna buƙatar samun zuri'a ko? To ku ƙyalle ni zanyi duk abinda kuke so amma sai na yi bincike akan wacca zan bawa dama ta zamo uwar ƴaƴana" ya ta shi foo! Yayi gaba zai fita.
Ta fi Zeenah tayi tana dariya tare da cewa " Allah sarki ai yarinyar nan ita ya kamata tayi bincike akan wanda ta aura kafin ta haɗa zuri'a da shi , ko da yake ba ma sai ana haihuwar ba. Ni dai fatana idan har kasan kai ma dan uwan daya ne ka sallami yarinya kar a cuta da kuruciyarta".
"Zeenah ! Wai me yake damunki ne? To in ma bana haihuwar menene ribar ki, naga ke ma ba haihuwar kike ba ko ince ba ma ki da mahaifar da zaki haihu".
Hawaye ne ya zubo mata kana ta ce" tabbas bani da wata riba, illa naga a cikin zuri'ar nan ba a sake haihuwa ba tunda ni ma bazan haihu ba gwara kowa ya rasa, ko kaga laifina?.
Sai kuma ganin yarinyar nan ya ɗarsa min tausayinta , don nasan cutarta za ayi , shiyasa na ce ka sauwake mata domin ciwon ƴa mace na ƴa mace ne".
"Uhumm Zeenah kenan , bakinki sai dai ya sari dan kashi mai wari , domin ko gado ake to nagsji haihuwa tunda kin san uwata ba daya ta haifa ba.
Kuma da kike cewa kina tausayin yarinyar duk na banza ne , tunda ke a kowane fanni na rayuwa sai kin nuna son kai a ciki, munafuka banza mara mutunci".
" Kai ne banza! Ba ni ba wallahi kuma tunda ba zan haihu ba kuma baza kuyi ba munafukai kawai".
Gaba yayi bai sake tanka mata ba, Labib yaja kujerarsa zuwa dakinsa yayin da Rumana tayi shiru tana tunanin wannan zama na doya da manja tsakaninsu da Zeenah sai kace ba ƴan uwa ba.
Ita kuwa Zeenah daki ta bi Labib tana huci , babban bakin cikinta shine ta tuna cewa ba bu mahaifa a jikinta.
___
Ashraf idonsa a rufe ya nufi part dinsa, a lokacin A'ishatu na kan dining ta zuba abinci sai jujuyashi take ta kasa ci.
Yanayin gidan da yadda take jin jikinta sai take jin kamar ba amarya take ba.
Takun sa da kuma ƙarar buɗe kofar da mukulli ne yasa ta dawo daga duniyar tunanin nata.
Tsirawa kofar kallo tayi don ganin me shigowa.
Saurin miƙewa tayi ganin wanda ke ƙoƙarin shigowar, sai yanzu take tuna sunan mijin nata da taji an ambata wato "Ashraf".
Daman shi suke nufi. 'Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un " shine abunda take maimaitawa a zuciyarta.
Juyuwar da zaiyi sai yayi daidai da haɗa idonsu guri daya.
Jim yayi yana tunanin ina ya taɓa ganin fuskar dan ba zai iya tantancewa ba.
____