RIGAR ARO

16

by @pherty001





Tun daga wannan lokacin bai ƙara ƙoƙarin cewa zai taba ta ba, sai dai kawai hannunta normal da ya saba riqe wa, har zuwa wannan lokacin bata jin komai akan sa ita ba soyayyar ce a gabanta ba shiyasa ko yaya sameer bata jin sa a zuciyarta balle Faruq, Her heart was completely locked,
kawai abinda ta saka a gaba hanyar da Binnani zai neme ta da kansa, wanda wannan shi ne babban burinta a rayuwa kuma a lokacin zata nunawa Waleeda asalin kowacece ita, cos sai ta zame mata qarfen qafa da ba za ta taba barinta ta taka rawar gaban hanci ba.
Suna cikin tafiya a mota faruq ya dube ta " Tafiya zamu yi da Daddy gobe, yana son fara dorani akan business ɗin sa shiyasa wannan karon yace muje tare" Nurayyah ta jinjina kanta tace" hakan yayi kyau" suka yi shiru na ɗan wani lokaci kafin tace " "I need driver, ina ta gayama it seems Baka son Nemo min driver, matsayina bazai saka na riqa driving da kaina duk inda zanje ba, and Ina so na fara program", Faruq ya juyo ya dube ta da mamaki yace "program kamar me kenan?
Tace" kuɗi zaka bani, I mean kuɗi masu nauyi, Ina so naje qananan makarantu na primary nayi sponsoring yaran da iyayen su basu da qarfin kai su secondary a matsayina na matar gwamna, kasan da yawa yara daga primary iyayen su suna cire su makaranta, wasu zasu zauna gida tallah wasu kuwa kasuwa zaa tura su, ka fahimce ni", Faruq ya dube ta da mamaki na yadda take lissafa masa abubuwan da zasu cinye maƙudan kuɗi a yanzu da abubuwa suke a matse, Faruq yace "but Nurayyah ke ba matar Governor bace meyasa sai kin yi? Kuɗi zamu kashe a banza fa ko kin manta?
Tace" ba'a banza bane, idan suka cigaba da karatu suka sami ilimi ta dalilin mu lada zamu samu, ni dai ko acikin kuɗin aure na ne kawai ka bani, sadaki da komai, idan lokacin auren yayi ɗaurawa kawai zaa yi tunda bazaka iya bani kuɗi ba idan ina so", ta qarasa maganar tare da rungume hannuwanta a qiriji ta juya masa baya tana kallon titi alamar tayi fushi, hakan da tayi ba qaramin burge shi tayi da shagwaba ba, yace "shikenan zan bayar, wallahi zan bayar, ai kin fi qarfin karban bashi a hannuna dan na fashe na auren ki, a kyauta zan baki, auren mu kuwa biki zaa yi sosai na ji da faɗa", jin haka bai sanya ta sauko daga fushin da take yi ba, cikin fushi tace "maganar driver fa, and zaka qara min mota biyu da securities tun da tare zaku je da mahaifin ka kafin ku dawo", ya ja numfashi cikin damuwa ganin yadda take kallonsa ya sanya shi saurin cewa "shima zan san dabarar da zanyi, just smile pls bana son fushin nan", bata yi murmushin ba ta juyo tana kallon sa kafin tace "har zuwa yaushe zaku dawo? Yayi jim kadan kafin yace" 2 to 3 weeks haka" ta gyada kai batare da tayi magana ba ta juya tana kallon hanya.
Faruq kuwa shiru yayi cikin tunani tun da ya haɗu da ita bazai lissafa iya adadin kuɗin da ya kashe saboda ita ba,  kusan duka abubuwan da take buƙata shi ne yake siya mata, shine kullum biyan mutane su zama security idan zata je makaranta ko kuma inda aka san ita matar governor ce, shine kullum cikin siya mata kayan sakawa, takalmi, jaka da sauran su, account ɗin sa yayi low sosai kuma bai ga ribar hakan ba tun da ko kiss ɗinnan bata bari yayi mata, sai asarar  kuɗi da yake a banza, ya lashi takobin cewa duk zai fanshi kuɗin sa a daren ranar auren su ya sani wallahi bazai raga mata ba sai ta biya komai na dukkan abubuwan da ya dade yana asara a kanta, sai yayi mata raga raga batare da tausayin ta ba kamar yanda itama bata tausayin sa idan sha'awar sa ta motsa, and yanzu bashi da kuɗi sosai ma da take so ya bata kuma har ya biya securities ɗin mahaifin sa suyi mata aiki na tsawon sati biyu zuwa uku da za su yi basa nan, sai ya soma tunanin ko kudin mahaifinsa zai dauka ya bata, bai taba yi wa mahaifin sa sata ba amma gashi zai yi akan wata mace, ba dn yana son ta yana son ma mallakar ta ba me zai saka shi yin haka, baya son ta guje shi taje gurin wasu tun da yaga yanda ake crushing din ta duk sanda suka fita tare shiyasa yake ta haquri yana danne wa har ayi auren ta gane kurenta komai son da yake mata sai ya fanshe wannan budurcin tun daga falo zaa fara, mtsew ya ja tsaki a karo na ba adadi cikin bacin rai.
Bayan tafiyar sa haka ya barta da mota biyu bayan na yaya Sameer a hannunta suka zama uku, ya biya securities din mahaifinsa guda biyar sai driver Lawal, duk wannan ƙaryar ta daina yi a unguwar su sai ta fito nesa da unguwar su inda suke jiran ta take shiga mota suje da ita duk inda take so, haka motar yaya sameer  gidan su fadila take kwana kullum sai taje ta kai motar ta dawo a napep tunda gidan su babu gate na ajiyewa and sameer yace baya son mahaifinsa ya gane motaar bata gida, duk wannan wahalar ta daukar wa kanta har bata hango tsabar wahalar da take yi ma, her eyes were completely fixed on the ultimate prize of social revenge and luxury status, kwana uku da tafiyar su ta shirya suka nufi Rigasa primary school, motocin suka shiga compound din a jere kamar da gaske wani babban dan siyasa ne ya kawo ziyara makaranta, lokacin ɗalibai da malamai suna cikin harkokinsu cos an tashi breakfast, lokacin da suka shigo duka yaran suka tsaya daga wasa da abinda suke suna kallon motocin da suka shigo a jere, Malamai suka fara fitowa daga office jin hayaniyar yara na gudu suna kaucewa motocin, Principal ma ya fito daga ofishinsa yana kallon motocin cikin mamakin sanda SUV ta farko ta tsaya kafin sauran motoci suka tsaya bayanta, ɗaya daga cikin security ya fito sanye da baqaqen suit da earpiece a kunnen shi, ya nufi principal ɗin cikin girmamawa suka soma gaisawa,
"Good morning sir." Principal ya amsa yana kallon sa, "Good morning." Security ɗin ya ce "your guest has arrived." Principal ya ɗan yi mamaki cos baisan da zai yi baqi ba, "Who is the guest?" Security ya yi murmushi yana faɗin "She's the wife of a governorship candidate Mrs Al'Qaseem Binnani." principal ya qara cika da mamaki ko me zai kawo matar dan takarar gwamna garin, cikin rudewa yace "welcome...please....please" malamai ma suka rude nan aka soma tattara dalibai ana kora su aji, aka bude mata mota, ta ziro qafafunta da ke sanye da high heels cikin nutsuwa kafin ta fito, ta fito sanye da doguwar rigar atampa applique, ɗinki yayi mata kyau kuma ya dace da jikinta, babban mayafi ta sanya dan ta nuna da gaske matar aure ce, idanun ta boye cikin farin glass sai facemask da ta sanya kada a gane ta, sai handbag da tayi wa wani irin riqo na daukar hankali, ga ma'aikata na ƙafar yaɗa labarai ta Liberty Television dake Kaduna suna haska labarin shigowar Mrs Binnani kai tsaye, suna bin bayansu da kyamara suna nuna komai cikin tsari,
Principal ya ƙaraso da sauri "Madam, you're highly welcome." cikin murmushi da ba a gani saboda face mask tace "Thank you so much."
Malamai suka riqa zuwa suna mata sannu da zuwa, "You're welcome, ma, It's our honour, We appreciate your visit. Nurayyah ta haɗe hannuwanta cikin girmamawa tace 
"Thank you, I appreciate the warm reception."
Daga nan aka nufi office ɗin  Principal da ita, security biyu na bayan su tare da sauran malamai while ita kuma suna gaba ita da principal, masu dauka suna haska live sai sauri suke kada a wuce su suna bin komai cikin tsari yanda ya dace, Lawal driver aka bar shi can wajen motoci sai kallon su yake yana mamakin yarinyar da qarfin halin ta, wlhy idan ka ganta a wannan lokacin sai ka dauka da gaske matar governor din ce saboda zubin manya da take da shi, ga diri ga kyau da take dashi, suka shiga office,
Principal da kansa ya ja mata kujera, "Please have your seat." Nurayyah ta zauna cikin nutsuwa, aka sake gaisawa again cikin girmamawa.