3
Chapter.3
Mintuna kaɗan ta soma jin tashin zuciya, tashi ta yi ta dafa Nadiya ta ce. "Bari na je restroom." "To bari na raka ki Aunty." Nadiya ta faɗa tare da miƙewa Nazli ta tsaida ita ta hanyar faɗin. "No zauna abin ki ina zuwa, yanzu zan dawo." Bata jira mai za ta ce ba ta doshi hanyar corridor ɗin da suka biyo ba tare da ta lura da Nadiya da ta ƙi zama ta bi bayan ta ba. Sai wani layi take tana mai jin kamar za ta faɗi, ganin inuwar mutum a gefen wajen ya saka ta matsawa tana mai tambayar. "Dan Allah ina ne restroom?" A hankali ɗan saurin ya juya ya na mai ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, suka haɗa ido da Nadiya da ta ƙifta masa idanu.
"Can." Ya furta tare da mai nuna mata saitin wani ɗaki da aka tanada domin buƙatun waɗanda suka kama hall ɗin, saboda yadda idanunta ke rufewa bata kula da ɗaki bane ta doshi wajen. Nadiya ce ta yi saurin riƙe hannunta ta tura ƙofar suka shiga ciki ta ɗaura ta a bakin gado, da wayo da dabara ta amshi wayarta kana ta juya da nufin barin ɗakin ta ji ta riƙe hannunta, dalilin da ya sanya zuciyarta harbawa. "Ruwa, zan sha ruwa." Can ƙasan numfashi ta yi maganar idanunta sai faman rufewa suke alamun kwayar ta soma aike.
Zuciyar Nadiya ta motsa tuna abin da suke ƙoƙarin aikatawa, amma ko me ta tuna ta yi saurin kawar da wannan tunanin tare da fincike hannunta ta yi waje. Tana fita ta ɗaga waya numbern da ta yi saving da sunan Boss ta turawa da saƙon "Aike ya kammala saura na ka." A hankali ƙasan maƙoshi ta furta. "Am sorry, ina fatan ki yafe min." Ta yi saurin maida kwallar da ke barazanar kwace mata ta saita kanta kafin ta bar wajen cikin sassarfa ta koma cikin hall ɗin ta zauna kamar ba abin da ya faru.
°°°°°°°
Nazli kuwa tunda Nadiya ta fita tana nan kwance ta kasa koda motsi ne jikinta ya yi mata nauyin da ta kasa koda ɗaga yatsa ne, duk sanyin AC ɗakin bai hana ta haɗa uban zufa ba, wani irin zafi ta ji yana hura ko wani ilahirin jikinta ta na mai jin kamar garwashi a ke hura mata a ƙasan ta. Wata irin buƙatuwa ce da bata taɓa sanin ta na da ita ba ta ji na taso mata, ta kai hannu wuyanta ta na shafawa a hankali jin yadda moƙoshinta ya bushe.
Cikin fitar hayyaci take ƙirin sunan Daddy, a cikin wannan halin ta ji motsin buɗewar ƙofa an shigo tare da maida ƙofar a ka rufe, motsin sawun ƙafa da ke tunkarota ya sa cikin mutuwar jiki da sanyin murya da ke nuna ta galabaita magani na aikinsa ta ce. "Z..Za..Zaid. Is that's you?" Jin shiru ba 'a amsa ta ba ya sa ta soma ƙoƙarin tashi dan ganin wanda ya shigo, sai da jin faduwar mutum a kanta ba zato ko tsammani ya sa ta sakin yar ƙara tana me yin baya yaraf suka fada kan gadon a tare, mutsu mutsun ƙwace kanta ta soma duk da bata da wani ƙarfi a lokacin amma ganin yadda a ka mata rumfa da sakar mata nauyin da ya kusan dauke mata numfashi. Jan numfashi ta soma ja a sama tare da saka hannu biyu tana turesa da dukkan iyakarta ganin dai da gaskiyan a ke son aikata lahira bata shirya ba. Ɗib ta dauke wuta na wucin gadi a sanda ta fahimci wannan fa ba Zaid bane, numfashi ta ta sauke jin turarin da kuma yanayen jiki ba irin na sa bane, duk da tana cikin hali na gushewar hankali amma ba hana ta fahimtar wannan ba Zaid bane. Wannan ya fi shi kauri da cikar halitta, ko daga girma da faffaɗan kirjinsa da ko rantsuwa ta yi ba za ta yi kaffara ba yana daga ƙarfe, hankali ta daura hannu kan Six packs dinsa da ɗamsen hannunsa, sai kuma da sauri ta janye ta soma kiciniyar ƙwace kanta, ita ce harda danna masa cizo amma a banza wai an mintsini kakkausa.
Ta cikin dim light ɗin ɗakin ta kalli fuskarsa da ta gaji da kyau tana tunanin inda ta san wannan bawon Allah kuma daga ina ya ke, kokawa ta soma yi da idanun ta tana cigaba da ware su a kansa jin yadda suke faman lumshewa, kan ta ce kwabo figure ɗin namijin ya danne ta, kafin a hankali ta ji ya kai hannu fuskarta zuwa sauran sassa na jikinta yana shafawa a hankali.
Kokawa suka soma yi tana ƙoƙarin ƙwacewa shi kuma ya saka hannu ya danne ta a cikin faffaɗan gadon, ba zato ta ji ya fara rabata da dukkan wani sutura da ke jikinta a zafafe ya soma shafa ta ta ko ina, baki ɗaya sai jikinta ya mutu ɗan sauran hankali da ya rage mata ya gushe, a yadda ya ke taɓa dukkan wani sashe na jikinta sai ta tsinci kanta da dukkan abin da ya ke mata tana na'am dashi.
"Im going to make you feel good." Shi ne kalmar da ya faɗa kafin ya haɗa bakin su guri guda, yana mai kissing wuyanta wanda ta ke jin kamar shi ne kawai abin da ya kamata ta ji yana kaimata a duniyar ta a wannan lokaci,duk wani abu da ya faru tsakaninsu a gaba ba za ta iya fassarasa ba.
=========
GRAND HALL.
A can ƙasan hall kuwa, Dad ne ya dubi Mommy yana tambayar inda Nazli ta ke don lokacin bata na shi kyautar ya yi, sai dai amsar da Mommyn ta bashi ne ya saka shi tsayawa da karanta takardar mallakar babban shopping mall da ya gina da sunan ta da son mallaka mata shi a yau a matsayin birthday gift daga gare shi.
"Me ki ke nufi da ba ki san ina ta shiga ba?" i thought she's on your watch, ta ya za ki ce ba ki san ina ta take ba?" Ya yi maganar a zafafe cikin ɗaga murya da har ya saka mutanen da ke kusa kallon su suna tunanin ko me ya ke faruwa kuma? "Wallahi Alhaji ban san ina ta je ba, yanzun nan fa babu jimawa na ganta cikin ƙwayenta, daga na kauda kai na wani lokaci ban ganta ba." Ta ƙare maganar a sanyaye, shi dai Daddy bai ko bi ta kanta ba ya wuce cikin ɗunbin jama'ar gun ya na mai neman ƴar lelensa. Mommy ma cikin sanyin jiki da kuma kunyar tsawar da ya yi mata a bainar jama'a ta bar wajen ta nemi Neesah tana tamabayar ko ta na da masaniyar inda Nazli tafi.
Abu kamar wasa ya zama babba, hankalin Daddy in ya yi dubu to ya tashi, tun mutunen wurin ba su lura basa fahimta har suka fara tambayar abin da ke faruwa. A karo na ba adadi ya sake gwada layin wayarta da a ke nuna masa yana shiga amma ba'a daga ba wanda hakan ba ƙaramin sake dugunzamar da hankalinsa kan ina ƴarsa ta ke ba, domin Nazli mutum ce da wuya ka ƙira layinta ka ji ya shiga kuma bata ɗaga ba musamman da ya kasance ƙiran daga Abbanta ne.
Take ya bada umarnin security da a duba lungu da saƙon hotel ɗin kafin ya dubi manager ɗin wajen ya umarce shi da a duba CCTV ɗin wajen daga awa uku da suka gabata zuwa yanzu, kaɗa masa kai manager ya yi tare da mai sake ba shi assuring ɗinsa tana nan ba inda ta tafi kuma za su ganta daga nan ya bar wajen cikin sassarfa domin cika aikinsa.
Duk wannan badaƙalar da ake Nadiya na gefe ta tsure wuri guda ta na kallo, cikin ta ne ya ɗuri ruwa jin batun duba CCTV take ta soma shiga panic zufa ta karyo mata. Sai dai text massage da ya shigo wayarta ya sa hankalinta ya dan kwanta kana ta aiwatar da abin da saƙon ya umarta.
Kashe wayar Nazli da ke wajenta wacce dama tuni ta sakata cikin silence kana ta faki idon mutane ta zura ta cikin manyan tables dake wajen kana ta nemi wuri daga can nesa ta zauna sai zare ido take kamar wacce aka kama tana yiwa sarki karya.
Cikin tashin hankali da ya bayyana matuƙa a fuskarsa Zaid ya kalli daddy cikin kwantar da murya ya ce. "Daddy please relax in sha Allah na san ba nisa ta yi ba am very sure she's around here." Ya faɗa cikin kwantar da hankali more like kansa ya kewa asuring, kai kawai Dad ya iya kaɗa masa ba tare da ya samu zarafin iya cewa komai ba ya bubbuga kafaɗarsa tare da barin wajen, ɗan ajiyar zuciya Zaid ya sauke bayan barin Dad ya na tunanin ina Nazli ta shiga haka ne ba tare da sanin kowa ba? Neesah na zaune kan kujera kusa da Mommy inda ta ke sake gwada layin Nazli a karo na ba adadi, dan ita fa har yanzu bata yarda cewa wani abu ya same Nazli ba tafi tunanin ko ta shiga restroom bata gane hanyar dawowa bane, amma tsantsan damuwar da ta gani a fuskar iyayenta ya sa ta fara shiga damuwa. Kamar an ce ta ɗaga kai sama carab idanunta suka fad'a a na Nadiya da ke rakuɓe gefe. "Ke! Nadiya zo nan, ba ɗazu ɗazun nan kuke tare da ita ba?" Ta kalli Mom ta ce. "Mom, Dad, ku tambaye ta ta san inda Nazli ta ke." Ta faɗa cikin huci ta na mai aika ma Nadiya harara don ba ƙaramin ƙin yarinyar ta ke ba haka kawai take jin tsanarta a zuciyarta musamman da ya kasance Nazli na ƙaunar yarinya, a cewar ta daga zuwan ta ta shiga tsakaninta da ƴar uwarta wannan soyayyar da shaƙuwar da suke da yanzu babu, daga taimako suka liƙewa ahalinsu ba zuciya.
Ƙurrr! cikin Nadiya ya ɗuri ruwa, tsoro ne ƙarara ya bayyana a fuskarsa tsoron a gano da akwai saka hannunta cikin ɓatan Nazli ya sa ta yi saurin maye gurbinsa da hawayen ƙarya ta yi kalan tausaye kana ta soma faɗin. "Wallahi ban san inda Aunty take ba, rabuwar mu da ita ta ce min ta yi baƙo za ta je ta sa me shi daga haka ban san komai ba wallahi." Ta faɗa cikin shesheƙa
"Baƙo?" Gaba ɗaya suka juya ganin Zaid da ya gama magana a waya kenan ya juya zai koma ciki carab kalamanta suka faɗa a kunnensa. "Ehh, idan ba ku yarda ba ma ku tambaye mutunen da muka zauna tare, har son binta na yi amma ta hana kuma ta hane ni da na faɗawa kowa shi ya sa ban yi magana ba." Kamar yadda ta ce din ne koda a ka tambaye ƴan matan wurin da suka zauna tare ɗazu sun tabbatar da abin da ta faɗa haka ne, sai dai a cewarsu ba su san abin da ya tashi ta ba amma tabbas ta ce za ta wani guri kuma bata yarda kowa ya bi ta ba. Zuwa lokacin sun tabbatar da ba sace ta a ka yi ba ta na cikin hotel ɗin nan sai dai ina ta shiga ba.
Wasa wasa fa tun ana irga mintuna har a ka soma irga awanni, haka nan taron birthday ya watse kowa na tofa albarkacin bakinsa kan an nemi birthday girl an rasa. Kowa da abin sa ke ayyanawa daga masu zaton Alkhairi sai masu akasin tunanin haka.
Bayan kowa ya watse ya rage mutanen gida kaɗai da kuma Nadiya da ke nuna fake damuwarta. Manager ne ya shigo, darect wajen Dad da ke tsaye yana safa da marwa ya tsaye. "Yes manager, kun gano inda ƴata ta ke ne?" Su wa suka ɗauke ta?" Gaba ɗaya a daburce ya ke tambayar domin sam ba ya cikin nutsuwarsa dan guts ɗinsa na sa ba shi kidnapping ɗin ta kawai a ka yi. Ɗan gyaran murya manager ya yi ya ɗan sunne kai alamun girmamawa kafin ya ce. "Sorry sir, mun duba cctv camara ɗinmu and we are sorry to say this, but an samu matsala da Cctv ɗin wanda hakan ya sanya ba mu kai ga ganin komai ba ta dauke, buts... ya cigaba. "Akwai staff na mu da ya ce kamar ya ga gilmawarta ɗazu." Ai kamar jira suke a tare suka ce. "Ina ya ganta?" "Uhhm,ya ce ya ga lokacin da ta bi corridor da shigarta ɗaki." "Ɗaki??." Suka furta a tare. "Ehh, haka ya ce, amma ba zamu tabbatar da iya gaskiyar shi ba sai mun je mun duba." Ba tare da ko wannen su ya iya cewa komai ba suka mara masa baya yayinda shi kuma ya jagorance su zuwa ɗakin.
=======
A hankali ta soma buɗe idanunta har ta bude su tass a pop din ɗakin, hannu ta kai goshinta ta soma murzawa a hankali kafin ta kai idonta dakin with confusion ƙarara a fuskarta, a zabure ta tashi jin jikinta babu kaya sai duvet da take rufe da shi, kallanta ta mayar ƙasa inda ta yi arba da kayanta a ƙasa a watse, wani irin azaba ta ji daga ƙasanta lokacin da ta yi ƙoƙarin tashi daga kan gadon a kiɗime ta na ambaton Ubangiji.
"Me ya faru da ni?" Shi ne abin da ta ke maimaitawa ta na kukan da ta kasa tsayarwa dan ƙololuwar tashin hankali da ta shiga. A daddafe ta ja kayanta ta na ƙoƙarin sakawa tana kuka da tambayar yadda ta ganta a ɗakin da yanayen da tsinci kanta a ciki, tuna fa yau birhday ɗinta ne kuma an shirya mata suprise party, wani irin tashin hankali ne ya kuma kamata ta fashe da kuka. Ta san ko ta fita ba za ta tarar da kowa ba sannan ta san dole suna can hankalinsu a tashe suna neman ta, me ma za ta faɗa mu su? Za ta je ta ce tashi ta ganta a ɗaki kwance babu a kaya a jikinta ƙasanta na mata zafi al'uamun namiji ya kusance ta amma ƙwaƙwalwar babu komai na image ɗin abun da ya faru da ita komai? Ta na cikin wannan tashin hankalin ta ji an turo ƙofar da ƙarfi da hakan ya sanya ta yi baya ta jawo duvet ta rufe jikinta da sai faman kerma ya ke. Sai dai abun da ta gani ya kusa sanya bugun zuciyarta buguwa, a kiɗime ta kai hannu baki tana mai tushe gunjin kukun da ke barazanar kauce mata, ta ma masa furta komai sai kai da ta ke girgiza masu cikin ƙololuwar tashin hankalin da ke barazanar dauke numfashinta.
Su kuwa mutuwar tsaye gaba ɗayan su suka yi a bakin ƙofar, barin ma Dad da Zaid waɗanda suke a gaba sai Neesah da Nadiya da Mommy wacce idanunta ba su faɗa a ko ina ba sai kan stain ɗin jini da ke kan beedsheet, bata buƙatar a sanar da ita abun da ya faru dukkan mai hankali da tunani zai san me ya wakana cikin dakin. Sai dai abin da ya ɗaure masu kai shi ne wannan stain ɗin da ke gadon, me hakan ke nufi? Allah ya sa ba abin da ta ke tunani bane da kuwa Nazli ta cuce su ta ci amanarsu ta kuma karya masu zuciya da har abada tabon ba zai taba goguwa a zukatan su ba.
Dad kam ba ka iya karantar yanayensa illa ido da ya zubawa yarsa ya na kokarin aje ko wani abu a ma'adanarsa ya fahimce abin da ke faruwa duk da ƙwakwalwarsa ta riga da ta bayyana masa sai dai zuciyarsa bata aminta da hakan ba. Numfashinsa ne ya soma sama yana sauka a hankali, Zaid kam mutuwar tsaye ya yi zuciyarsa ta tarwatse tamkar cufin gilashi da idan ya fadi ya tarwatse ba zai taba haduwa ya koma daidai ba, no matter how it been fix kuwa sai ka same sa da yoyon ruwa..ba zai ta taɓa gyarawa ba ko ya gyarun to ba zai koma daidai ba. Wa zu zafafan hawaye ne da bai san lokacin zubarsu ba suka wanke masa fuska, ko ba a fada masa ba ya san Nazlin sa ne ta kwana da wani namijin ba shi ba, abun takaicin ma da aurensa a kanta. Duk kokarinsa a kanta dan ganin ya yi dukkan mai wuya ya jawo hankalinta ta so shi ashe bai san aikin banza ya ke yana batawa kansa lokaci ba.