KAIFI ƊAYA

16

by @ummishatu1111

16



***Kamar zai yi kuka saboda bata barshi ya kasance acikin dakin ba, haka kuma baccinshi sama sama yayi domin kowanne bugun zuciyarshi  tunaninta ne gaba daya ya kasa gane wanne irin yanayine wannan ya samu kansa and it's not just pity anymore its turning into something deeper, ita kam anty Mimi tana can cike da tunani kala kala hakika wannan sharadin da Abba ya saka mata tsakaninta da Aliyu yayi mata tsauri da yawa tunda ko babu komai ɗan uwanta ne bai kamata a raba su har haka ba, tashi tayi ta lallaba ta fita zuwa wurin hajiya wacce har ta kwanta amma dai ba bacci take yiba,

"hajiya wurinki na zo.... Dan Allah wata alfarma nake nema, ki taimaka min ki rokar min Abba akan ya sassauta min wannan sharadin da ya saka, wallahi yayi tsauri da yawa, ai ko babu komai yaya Aliyu dan uwana ne tayaya za ace ko gaisawa baza muyi ba? Naji na yarda bayan gaisuwa babu abinda zai kara hadani dashi amma a bani dama in duba shi ko ta waya ne  dan Allah hajiya "

"Kinga ki kiyaye ni da maganar duba Aliyu dinnan fa, yadda uwarsa take tashen rashin mutunci yanzu wallahi komai zai iya faruwa tom...."

"ni babu ruwana da Umma iya yaya Aliyu nace...."

"shikenan na baki dama kiyi masa ya jiki, zuwa gobe da safe shikuma Alhaji ƙarami zanyi masa bayanin komai..."

"yawwa hajiya nagode...."

Ai sai taji har taji kwarin jikinta, da sauri ta koma bedroom dinta ta zauna ta dauki wayarta ta fara neman layin yaya Aliyu, babu kowa cikin dakin sai shi kadai dan umma ta fita saboda suna sa ran za a basu sallama zuwa gobe,

"Mimi..... Mimi ashe dama zan sake ganin kiranki cikin wayata?"

"yaya Aliyu kayi hakuri ka san ba laifina bane ai, babu yanda zanyi ne.... Abba ya hanani magana da kai bare ganinka...... Ina cikin tsaka mai wuya....."

"Mimi nafi ki shiga masifa..... Iyayen mu basu duba mana ba, Afeef baiyi mana halacci ba bare adalci...... Yaci amanar mu kuma ya ha'incemu, dan Allah mimi kar ki bari yayi nasara a kanmu, kar ki bari yaci galaba akan ki, don't let him win, wallahi yanzu duk duniya bani da makiyin da ya wuce wannan yaron, na tsane shi kuma na tsani koda sunansa ne bare ganinsa i hate him with passion.."

"ka kwantar da hankalinka yaya Aliyu, insha Allah sai inda karfina ya kare, ba zan taɓa yin rayuwa dashi ba matsayin miji, yanda kake jin ka tsane shi to ni ina jin tsanar shi fiye da haka, ya zalunce ni ya cuceni ya rabani da kai sannan ya rabani da aiki na, anyi suspending dina an kwace license dina duk saboda shi..... Gaba daya ya gama rusa rayuwa ta...."

"kika ce anyi suspending dinki an kwace license dinki? Saboda me? Yaushe?"

Labarin abubuwan da suka faru gaba daya ta fara zayyane masa daidai lokacin umma ta shigo,

"Allah ya rufa asiri ya kiyaye gaba insha Allah everything will be alright..... I will talk to you tomorrow morning....." katse wayar yayi yana kallon umma wacce tun shigowarta ta tsaya ta kafe shi da ido tana kallonsa,

"umma me ya faru ne?"

"kai Meyasa baka da zuciya ne Haidar? Me yasa baka kishin kanka? Yarinyar da ubanta ya gama wulakanta ka uwarta ta gama tozarta ka ita kanta ta nuna bata san da kai ba yanzu kuma me zata fada maka? To daga yanzu babu kai babu ita, tunda sun guje ka sun zaba mata wani sun aura mata ka bar su suje alhaki kwikwiyo ne.... "

Shuru yayi cikin ransa yana cewa ai inaah bazai taɓa iya rabuwa da mimi ba dan ba ya jin zai iya rayuwa babu ita he can't do without her, itama anty Mimi bayan sun gama wayar wani sabon sonsa take ji acikin ranta, ko bata fada ba ta san bazata taɓa rabuwa da kwayar sonshi dake cikin zuciyarta kullum tana sake kara yaɗo da rassa da girma ba. Ita dai anty Mimi bayan sun kammala wayar shuru tayi tana jin wani sanyi har cikin ranta sakamakon muryar yaya Aliyu da taji, tana yi masa wani irin sone wanda bata san yanda zata misalta ko kwatanta shi ba, wani irin farin ciki take ji cikin ranta tun bayan da taji muryar tasa, tana rungume da wayarta a chest dinta ta kwanta lamo taji karar shigowar massage, a hankali ta cire wayar daga kirjinta ta bude massage din, Afeef ne taga ya turo mata da,

"Mimi me yaya jikin naki? How do you feel now? Allah ya baki lafiya.... I miss you...... Sleep well...."

Tsaki tayi tana jin wani irin haushinsa cikin ranta, ta ajiye wayar a zuciye, jin karar shigowar wani sakon yasata sake tunzura saboda duk tunaninta shi dinne sai dai tana dubawa taga yaya Aliyu ne, cikin jin dadi fuskarta dauke da murmushi ta karanta massage din tare da yi masa reply. 

Kasa bacci Afeef yayi yana ta kallon Irfan da sai baccinsa yake yi cikin kwanciyar hankali babu abinda yake damunsa sabanin shi da tunanin anty Mimi ke kokarin zautar dashi ko kuma fitar dashi daga cikin hayyacinsa, ganin da yayi mata daga ita sai towel lokacin da ya shiga bedroom dinta yana kokarin haukatar dashi gaskiya anty Mimi kyakkyawa ce ta bugawa a jarida ko kuma mujalla, fatar jikinta kadai wani irin kyalli take tare da daukar ido ga laushi da santsi, lumshe idanuwansa yayi tare da lasar lebensa na ƙasa dan babu abinda yake bukatar gani ko kuma yake so a daidai wannan lokacin sai ya ganta gashi ga ita koda kuwa ita din ba zata kula shi ba, text massage ya tura mata duk da ya san zai yi wahala ta kula shi amma dai ba zai iya daurewa ba dole sai ya tura mata, bayan ya tura mata video din da yayi mata ranar da ya kwana a bedroom dinta ya fara gani yana ta maimaitawa kamar wanda ke son haddacewa ahaka har bacci ya dauke shi. Kwana yayi cur yana mafarkinta shiyasa washe gari ya tashi cike da farin ciki da wani irin zumudin son ganinta, yayin da ita kuma ta kwana da tunanin Aliyu acikin ranta da hanyar da zasu bi su koma ma'aurata su cigaba da rayuwar su hankali kwance. Bayan yayi wanka ya shirya bai saurari Irfan ba ya fita zuwa part din Hajiya kaka wacce ke karyawa tana yi sai faman mita take na yau ba abata abincin karyawa da wuri ba bayan ita kuma ba zata iya wannan horon yunwar ba, sanye yake da farar t shirt sai bakin jeans yana ta faman zuba kamshi,

"Hajiya anty Mimi ta tashi?..." yace da hajiya bayan sun gaisa, 

Wani kallo hajiya tayi masa kafin tace "bana son munafurci lele.... Da ni kake tambaya idan ta tashi, ko wuri daya muka kwana da ita?"

"yi hakuri kawai tambaya ce..."

"to ban sani ba tunda ni dai ban ganta ba...."

"to bari naje na duba da kaina"

"da dai ya fi maka"

Tashi yayi ya nufi upstairs inda anty Mimi ke zaune da laptop a gabanta gefe daya kuma glass cup ne ajiye dauke da coffee aciki, knocking yayi sau ɗaya daga haka ya bude kofar ya shiga bai jira ta bashi izni ba, kamshin turarensa da taji ne yasa ta ɗago manyan idanuwanta ta kalleshi,

"sannu ya jikin?..... Kin samu sauki ko akwai sauran abinda yake damunki?"

Wani mugun kallo ta yi masa kafin ta gyara zamanta ta kalleshi cikin takaici tace,

"Afeef wai me kake so dani ne?"

Ɗan jim yayi saboda bai fahimci maganar tata ba, idanuwanshi yayi kokarin sakawa cikin nata amma sai ta kawar da kanta gefe tana sake daure fuska,

"Anty Mimi wallahi babu abinda nake nufinki dashi sai alkhairi....... Kawai dai abinda na sani yanzu shine ina jin wani abu mai girma a tattare dake wanda ban san menene ba......"

"Afeef ka dai san ni ba sa'ar aurenka bace......"

"Anty Mimi abinda nake ji a game da ke yafi karfin tunanina sannan bazai bani damar hango age gap din dake tsakanin mu ba...... Ina ji a raina da zuciyata ba zan iya rabuwa dake ba" ya fada cikin wani irin yanayi wanda ta kasa fassara shi, 

"Afeef aurena da kai bazai ɗore ba, dole zamu rabu koda kuwa hakan zai kawo karshen zumuncin dake tsakaninmu....."

"Insha Allah babu abinda zai rabani dake sai mutuwa....." ya fada yana lumshe idanuwansa bayan ya hadiye wani irin yawu,

Gani yayi ta matso kusa dashi sosai har numfashinsu na haduwa suna gwaruwa da juna, rigar baccine a jikinta light pink mai santsi mai gajeren hannu da botira gaban rigar, botiran dake gaban rigar tata yaga ta fara budewa zuciyarta na tafarfasa,

"Na san abinda ke ranka bai wuce son ka hada shimfida dani ba.... Ai abinda kake so kenan ko ka ɗandani zumata kamar yadda ka taɓa faɗa..... Tunda so kake ka sanni matsayin ƴa mace bismillah...... Let's have sex sai hankalinka ya kwanta ka sakeni....." tana gama faɗa yaga tana kokarin zame rigar daga jikinta dan har ta kammala bude botiran gaba daya..............

Hmmmmm...... I'm stopping here, the free pages are over, soo what will happen next? Will Afeef divorce anty Mimi? Will the secret come out? Will yaya Aliyu give up and let them live in peace? Will the secret they buried remain a secret or will it come out for everyone to hear? All of these are in the continuation of the story,


Mimis heart is broken......

And Aliyu he's not done yet.....

Someone is about to pay, someone is about to break someone is about to confess.... The secret is about to explore...... What comes next will shake you, divorce? Secrets? War with the parents?  The continuation of the story is waiting for you, Don't get left behind 👇👇👇


Pay via 7044644433,Moniepoint micro finance bank, send your evidence of payment to ***.


1000 Naira only




*_Ummi Shatu_*👌🏻