Chapter 25
Bayan Sadeeq sun gama magana da Abbah ya koma ɗakinshi,wayarsa ya ɗauka ya shiga kiran Jay.
Bayan ta ɗaga ta yi sallama ta gaishe da shi, bayan ya amsa ya ɗora da faɗin " shine ko kira kiyi congratulating ɗina ko?"
Da ɗan alamu mamki ta ce " wani abu ne ya faru?"
Dariya ya yi ya ce " kar ki ce baki san an saka lokacin bikin mu ba?"
Shiru ta yi tana tunani can kuma ta ce " wai don Allah dagaske kake?"
Dariya ya yi ya ce " wallahi da gaske nake an saka lokacin bikin mu nan da sati biyu."
Dummmm taji ƙirjinta ya buga,kalmar sati biyun tana ta maimaita kanta a cikin ƙwaƙwalwarta.
Murmushin ƙarfin hali ta yi ta ce " Allah ya nuna mana."
" Ameen "
" Me kike ganin ya kamata mu shirya?"
" Kamar me kenan." Ta tambaye shi.
" Events ɗin da zaki yi."
Shiru ta yi sai kuma ta ce " walima kaɗai zan yi bayan ita babu abinda zanyi."
Jinjina kai ya yi ya ce " amma zan shirya dinner idan kina ganin babu matsala."
Shiru ta yi bata amsa sai ya ce " ko akwai matsala ne?"
" A'a." Ta bashi amsa.
" Yawwa toh shikenan zamuyi magana gobe, yanzu akwai wasu abubuwan da suke buƙatar attention ɗina."
Ita ma dama neman hanyar da za'a yi ending call ɗin take,sai ta ce " toh shikenan goodnight."
Wurin da zata samu ta yi kuka take so ko nauyin da zuciyarta ta yi zai ragu.
Tunani ta yi idan ta zauna a ɗakin Munarh zata iya zuwa ta sameta,kuma bata da amsar da zata bata idan ta tambayeta dalilin da yasa take kuka.
Tunuwa ta yi da ɗan ƙaramin library ɗin da dad ya gina mata a lokacin da take school,tana gama tunanin haka ta fito daga ɗakinta ta nufi ɗan ƙaramin library ɗin da baya da nisa sosai da ɗakinta.
Sai da ta tabbatar da babu wanda yaga shigarta ciki sannan ta rufo ƙofar ta ciki.
Zama ta yi akan kujerar dake gaban wani desk ta fashe da kuka.
" Yanzu kin yi wa kanki da kuma zuciyar ki adalci da har zaki bari ki auri wani? Zuciyarta ta tambayeta.
" Amma ai ya haramta a gareki,meyasa zaki cigaba da dakon son wanda ya haramta a gareki?" Wata zuciyar ta bata amsa.
" Ya kamata ki sani kina yaudarar kanki ne kawai ta hanyar sawa ranki cewa ya haramta a gareki bayan kin san cewa ke da kanki ƙarya kike yi." Wata zuciyar ta ƙara faɗa mata haka.
Ji tayi kamar ta ƙwalla ihu saboda yadda take jin kanta ya yi nauyi ta rasa wani kalar tunani zata yi saboda tasan ita da kanta idan ta ce ya haramta a gareta tasan ƙarya take yi.
Ita ce dai ta saka wannan tunanin a ranta.
Ganin ta kasa samun solution ya sa kawai ta ƙara sautin kukanta.
Sai da ta yi me isarta sannan ta shiga toilet ɗin da ke library ɗin ta wanke fuskarta sannan ta koma ɗakinta.
Sadeeq kuma bayan sun gama waya ya kira wani designer da yake masa ɗinki bayan ya ɗaga ya ce " mutumina biki na za'a yi nan da sati biyu,ina son ayi man ɗinki me kyau wanda zai tabbatarwa da kowa eh lalli fa nine angon."
Dariya ya yi ya ce " kar ka damu mutumina zan yi maka ɗinkin da duk wanda ya kalleka sai ya ƙara, zan yi maka ɗinkin da ko wanda bai sanka ba yana ganin ka a ranar zai tabbatar kaine angon."
" Yawwa godiya nake,yanzu abinda za'a yi shine kayi calculating sai ka faɗa man total ɗin na saka maka kudin."
Bayan sun gama da me ɗinki ya rinƙa kiran mutane kowa da irin abinda zai yi,har dai ya gama kiraye kirayen shi ya yi shirin kwanciya bacci.
Tun bayan Layla ta shiga ɗaki Raj yake ta safa da marwa a parlourn ya rasa wani irin tunani zai yi, bai san ta wani yanayi zai faɗawa Layla zai ƙara aure ba.
Tunani ya rinƙa yi kala kala,wata zuciyar ta ce ya kira Shaheedarh kawai a waya ya zugata ta ce ita bata san shi,ya san Ummah ba zata taɓa yi mata dole ba.
Da wannan tunani yaji ya samu nutsuwa sai ya bi bayan Layla shima ya tafi ɗaki.
Da ta buɗe baki da niyyar yin magana sai ta kasa gefen gadon ta samu ta zauna tana ta maimaita innalillahi wa'inna ilahi raji'un.
Hawaye ne ya fara sakkowa daga idonta ta ƙara riƙe Ayaanah gam a jikinta kamar wani zai ƙwace mata ita.
Mamy mom ta kalla ta ce " Aisha don Allah kira man Jaiyanah da hajiya."
Jinjina mata kai kawai mamy ta yi ta fita kiran su.
Yan mituna kaɗan sai gasu sun shigo.
Da sauri hajiya mama da Jaiyanah suka ƙarasa inda take ganin hawaye na fita daga idonta.
" Lafiya Bilkisu kika kama yarinya kika riƙe kina kuka?" Hajiya mama ta tambaya.
Jay ma dake tsaye tana jiran amsa ta ce " mom ko wani abu ya faru ne?"
Hawayen dake sauka akan fuskarta ne suka ƙara gudu ta ɗago da jajayen idanunta da suka rine ta ce " kun san wacece Ayaanah?"
Su biyun duka suka girgiza mata kai alamun a'a.
Kallon su ta ƙara yi sannan ta ce " ita ce yarinyar da Jasrah ta haifa shekaru shida da suka wuce kafin ta bar duniyar nan."
Wani dummm Jay ta ji a cikin kanta,gaba ɗaya ma bata fahimci abinda mom ta gama faɗa ba.
Ƙwaƙwalwarta ta dena aiki.
Hajiya mama da ta yi tsaye kamar an dasa ta ta ce " anya Bilkisu kin san abinda kike faɗa kuwa?"
" wace irin magana ce kike faɗi mara daɗin ji haka."
" Aisha meke faruwa ne?"
Mamy ta sunkuyar da kanta ta ce " lokacin da na shigo na tarar tana banɗaki sai na zauna a gefen gado ina jiran ta fito."
" Tana fitowa ne na ganta tare da Ayaanah shine na ce mata dama Ayaanah na nan gidan baki taɓa faɗa man ba?"
Ta tambaye ni ko na santa ne.
Ni kuma na ce mata Hajara ce fa.
Hajiya mama itama da ta yi matuƙar kaɗuwa ta rasa me zata ce,tayi ta maimaita innalillah ita ma.
Sai a lokacin abubuwan da suka yi ta faruwa suka rinƙa dawowa Jay.
Da farko ranar da aka yi taron buɗe eatry ɗinta kafin zuwan su mamy Ayaanah ta zuba lemo a jikin kayanta aka koma da ita gida a canja mata kaya.
Na biyu kuma bayan an gama taro kafin su mamy su dawo gidan suka ƙara barin gidan ita da Ayaanah.
Sai kuma na ƙarshe da zasu je gidan mamy da Munarh hajiya mama ta ce ba zasu je da ita ba.
Kuka ta fashe da shi tana cewa " ki yafe min Jasrah na ɗauki alƙawarin da na kasa cikawa."
" ki yafe man ʼyar uwata." Ta faɗa tana ƙara fashewa da wani kukan.
Hajiya mama da mamy ne suka yi ta basu haƙuri har suka daina kukan da suke yi.
" Yanzu duk iya tsawon lokacin nan da aka ɗauka da jini na nake rayuwa ban sani ba.?"
" A kullum idan na kalleta ina ji a zuciyata tabbas ina da alaƙa me ƙarfi tare da ita,amma ina barin hakan ne a matsayin son yara da nake da shi."
" Ashe duk tsawon lokacin nan da ʼyar Hajarah nake rayuwa ban sani ba."
" Allah ya jiƙan ki Hajara,yasa mutuwa ta zama hutu a gareki."
" Ameen" suka amsa gaba ɗaya.
Mamy ce ta ce " amma ta ya aka yi Ayaanah take rayuwa a gidan nan.?"
Labari mom ta bata tun daga fitar Jay daga gida har zuwa asibiti da kuma yadda suka yi da baba Tanimu da kuma dawowarta gida tare da Ayaanah.
Jinjina kai mamy ta yi ta ce " Allahu Akhbar."
" Nima zuwan da kika ga nayi duk akan maganar ce."
Jay ta yi excusing kanta ta koma ɗakinta.
Bayan tafiyar Jay mamy ta basu labarin duk abinda Safiyyah ta faɗa musu.
Salati hajiya mama ke tayi tun bayan da mamy ta gama basu labarin.
Can kuma ta ce " wai wannan wane irin zamani ne muke cikinshi ni Hajarah."
" Anya mutane suna tunanin za'a mutu kuwa?"
Mamy ta ce " ga mahaifiyarta mutuniyar kirki, yanzu haka ta yi fushi da ita ta ce kar ta koma mata gida sai a gida na nace ta zauna."
Kamar hajiya mama ta kaiwa mamy duka ta ce " saboda kin fi uwarta son ta ko?"
" ke ga me zuciyar musulunci ko?"
" Toh wallahi tun wuri ma ki koreta, tun kafin ta saka ki cikin masifa."
Tana gama faɗin haka ta tashi ta ce " kinga ni tafiya ta bazan zauna na cigaba da jin kayan takaici ba."
Bayan hajiya mama ta fita mom ta ce " amma Aisha ba kya ganin akwai haɗari a barinta da kika yi a gidanki?"
Girgiza kai mamy ta yi ta ce " barinta ta tafi shine babban haɗari, ta ce min renting apartment zata yi saboda bata da inda zata je."
" Yarinya ce ita bata fi sa'ar su Jay ba, kinga kuwa barinta ta zauna ita ɗaya babu me saka mata ido haɗari ne ga rayuwarta."
Jinjina kai mom ta yi alamun gamsuwa ta ce " haka ne kam,Allah ya shirya mana zuri'a."
Mamy ta amsa da Ameen.