GUMBAR DUTSE

G_D - 18

by @khadeejacandy

Sannu a hankali Batula da fara sabawa da garin Sabau, bata yi sabin kawaye ba amman ta saba mutanen gidan sai kuma sauran yan'uwanta da daman ta san wasu, wasu sa'aninta ne wasu kuma sun girme mata, wasu kuma a yanzu suke tasowa.

Sai dai hakan be hanata marmarin kawayenta ba, mutanen kauyen da ta baro da kuma karatuntu, babu ranar da bata kebe kanta a daki ta yi kuka saboda haka, sabo ai turken wawa ne, no matter what Mutum yake samu dole yayi marmarin inda ya saba. Banbancin zamanta a can da nan kadan ne, domin kusan aikin wahalar ɗaya, a can tana talla da dibar ruwa girki da kuma wanke tufafin Umma Hindu, a nan din ma haka take yi, talla ce kawai bata yi sai aka maye mata gurbin tallar da daka, abun da bata saba ba, kuma bata maraba da shi, duk kuwa da kasancewarta yar kauye, daka na daga cikin abun da Batula ta tsana, sai dai dawowarta garin nan ya saka dole dakanta take kullum, idan bata yi surfe ba, zata kirba garin kuno ko hura, idan ta gama kuma ta tafi daji yin itacen da za a'ayi girkin gobe da su. Kusan kullum haka take.

Arzikinta ɗaya kullum tana samun abun da zata ci har sai ta rage, domin kowa yayi girki a gidan akwai kwanonta, ko kwado aka yi sai an bata, ga kuma wanda Umma Hindu take yafa mata idan ta yi, bata zuba mata mai yawa amman dai ta kan bata tun da ta san idan ta rasa karfin surfi ba zata amfana mata komai ba.

Yau kam tun asuba ta farka tana yi sallah ta hau surfin gero, saboda hurar da za a yi ma mutanen birni ta gidansu Zulfa'u da suka aiko hatsin tun jiya da dare. Ko da hasken safiya ya fara fitowa Batula ta gama surfe tiya biyu ta hau wankewa, ta san Umma Hindu bata bawa kowa sadaka kasarinta sai dai ta siyar, dan haka tana wankewa ta dauka ta nufi gidan da ake siya ta siyarta karbo kudin ta shiga daki kamar wanda zata yi sata, tana sanda ta daga filon Umma Hindu a hankali ta sakaɗa mata kudin sannan ta fito, ta warwarda gerun ta koma can gefe ta zauna.

Tana ta lissafin rayuwa, indai rayuwarta a haka zata kare da surfe da wahala, to ita kan bata more ba, a can tana ganin duk wata wahala da take sha gurin Umma Hindu kamar zata wuce saboda Musa, tana ganin idan ta yi aure zata bar gidan ita ma ta gina nata gida da tata rayuwa, amman me? An rusa duk wannan, tun da an shafa mata bakin fentin da bata san a ina aka samo shi ba, ga shi tana da nakasa da ba kowa zai iya aurenta ba.

Ko iya saka talkamin nan da yan mata sa'ainta suke ita bata iyawa? To ko waye zai so ta kasance matarsa?.

"Batula... Zo ga dumame"

Ta tattara tunaninta ta aje gefe daya, ta tashi da kuzarinta ta nufi Baba Maijidda ta karbi dumame tuwon dawar ta zauna ta fara ci, bayan ta cinye ta dauraye hannunta ta wanke kwanon ta mayarwa mai shi tana mata godiya, haka take kullum idan aka bata abinci.

Ko da karfe biyu na rana ta yi Umma Hindu ta gama dawo tare da Batula, aikin Umma Hindu kawai mulmula dawon ta kada idan yayi ta cire, daka da tankadewa gaba daya Batula ce ta yi, an gama aikin jikinta a gajiye likis ga bachi tana ji amman bata isa ta yi ba Umma Hindu ta fara mata masifa.

"Dauki kije ki kai musu, kuma idan kin nace dan dai kawai tana yar'uwa ne, amman ba haka muka dawo ba, kawai na karbi haka ne saboda yar'uwa ce"

Batula ta daga mata kai a ladabce sannan ta dauki kwayar dawo ta tiya biyu ta dora akai babu ko ganwo ta saka hannayenta ta tare ta kama hanyar fita.

"Kuma ki yi a hankali idan kika barar ke zaki biya"

Bata dai ce komai ba ta kama hanya, rana na dukan kafafuwanta domin ranar yau akwai zafi 43°C ce, tana tafe tana kallon mutane wasu sun santa already tun da garin mahaifiyarta wasu kuma sanin dawowar nan da ta yi ta sati biyu kawai suka mata, wasu ma yanzu suke ganinta. Ta yi tafiya mai dan nisa sannan ta isa unguwarnsu Mama Zulfa'u. Ta tarar da taro kofar gidan maza da mata wasu zaune wasu a tsaye, yanayin fuskar jama'ar dake kofar gidan be nuna mata yanayi marar kyau ba, dan haka tunanin mutuwa bata zo mata ba, sai tunanin roko ko kuma wata hidimar, daman ta ji su Baba Maijidda suna zancen yadda ake yawan sadaka idan mutanen burni suka zo, daman kuma gidansu Mama Zulfa yana daga gidajen da suke da kyau a karkarar.

  Ta ratsa mutanen ta shiga ciki gidan sai da ta dan tsaya jikin kofa ta buga sannan ta karasa, haka take musu idan ta zo madadin sallama da bata da baki. A lokacin da ta shiga cikin gidan sai da maida kanta kasa ta doshi bangaren Mama Zulfa daf da zata sauke kwayar ta daga kai ta kalli mutane, sai ta yi arba da fuskokin mutanen biyu da taba gani.

"Batula an gama dawo?"

Ta daga kai, sannan ta tura kwayar gaban matar da ta kirata da Batula.

"Batula..."

Ta dago ta kalleshi sai ta maida kanta kasa, ba tare da ta yi masa alama da ta waye shi ba.

"Me kike nan? Idan ban yi mantuwa ba wannan yarinyar a garin Rorau na santa, gidan Malam Salisu"

Yayi maganar a hankali yana dan mamaki, Batula dai bata ko dago ba sai wasa take da yatsunta da suka fara wani maroro saboda daka, bata son ta nuna ta san kowa musamman namiji saboda gudun kar ace tare su ke.

"Batula ai lallai kuwa ka santa, ai can suke dama da auren uwar rikon nata ne ya mutu suka dawo nan"

Mama Zulfa ta fada bakinta cike da goro. Turaki ya dan bata fuska

"Subhanallahi, tohm kuma ba a gyara ba?"

"Babu gyara, ance saki uku ne, kuma ko ba uku ba ne, nake ga kamar ya gaji da zama da ita Hindu ne, a yadda ake ce mana"

"Batula kin gane ni?"

Ta daga kishi kai ba tare da ta kalleshi ba.

"Tohm ina karatun kin kare?"

Ta girgiza kai.

"A nan kina karatun ne?"

Nan ma ta sake girgiza kai hawaye na fadowa idonta, amman ta yi hanzarin sharewa.

"Tohm me kike nan? Zaune kawai kike baki cigaba da karatun ba?"

Nan ma dai ta daga kai. Yana ta kallon hannayenta dake nuna alamar ba su saba da wahala ba.

"Surfau suke a nan, can na bada ayi maka da wo ai, ba mamaki ma ita ta yi, kasan yaran mu na nan akwai kokari ba irin naku ba"

Tana maganar tana dariya.

"Ba wani kokari wahala ce kuka saba musu da ita tun suna kanana, a ina kike nan? Gurin wa?"

"Gidansu Mai Zaiti, Batula fa kama kunne Mai zaiti ce, yan'uwace ai dan dai baka sani ba ne, ai da shi Kaka Mai Zaiti, da Kaka na gidan nan yan wa da yan kanene, Batula jikar Baba Auta ne, kasan shi kadai ya rage cikin yayan Kaka Mai Zaiti"

Turaki ya bude baki yana jin hira na masa dadi.

"Kaka Mai saiti na nan tsallake? Batula diyar jikarsa ce kenan? Shi Baba Auta shi ya haifi mahaifiyarta?"

"Eh, amman ba Baba Auta ya haifeta ba, yayanshi, shi kuma ya rasu Baba Auta kanen Kakanta ne auta, ita yar wajen margayiya Fati ce, shiyasa da ta rasu ai sai aka maida sunan ita margayiya ga wannan amman ake kiranta Batula, ta yi ta haihuwa ba su tsaya ba, sai ga wannan ita kuma data tsaya Allah be nufi zata rayuta gani ba, sai yar'uwarta aka barwa rikonta, tun tana jaririya ta tafi da ita can inda take aure, a can ta girma sai yanzu dai da auren ya kare suka dawo, Batula ba uwa ba uba sai yan'uwa"

Turaki ya sake duban Batula yana murmushi.

"Ashe dai yar'uwa ce ita ma, zumuncin na mu yanzu ya zama sai a hankali shiyasa na kusa ma ba kowa ka sani ba balle na nesa"

"Ai kana ma kokari Alhaji, ba kowa ke irin abun da kake ba, kai kake da kudi kuma kai kake bibiya, ko da yaushe kana zuwa, kuma idan abu ya tashi zaka aiko ko ka zo da kanka, hidimar al'umma kuma kullum kana ciki, Allah dai ya saka da alheri, ya maka albarka"

"Ameen, ai haka ake ta tafiya, idan baka gina lahirar ba sai lokaci ya kori maka baka ankaro ba, haka dai ake matse wasu sabgogin ayi wasu, Batula kina son ki cigaba da karatun nan? Ko aure za ki yi?"

Ya tambaya yana kallonta, ta girgiza kai.

"Aure ai sai miji ya samu"

Ya kalli wata tsohuwa da ko hakora bata da.

"Tana da wanda zata aura ai, hira fa muke da ita sosai kawai dan kuna nan ne kuma babu abun rubutu, idan na je gurin Malam Salisu idan ban ganta ba har aikawa nake a kirata, ashe ma yar'uwa ce"

"An watse, fitini aka yi a garin can fa, ko da ta zo nan ance jina jina, kasan duk lokacin da baka yi sa'ar uwar riko ba, tohm sai ka sha wuya, duk haka muka yi, yan'uwan uba sun gana mana azaba, Allah dai ne yace za mu rayu"

Turaki ya girgiza kai.

"Allah ya kyauta, kina son a maid ki makaranta a nan din?"

Batula ta dago da sauri ta washe hakora. Sai ya nuna ta fuskarta yana dariya.

"Ji ta sai yanzu ta sake fuska, dadina da yarinyar nan akwai son karatu"

Duk suka yi murmushi ban da mace daya dake ta yauki kamar miyar karkashi. Batula ta hada ido da wata kyakkyawa mata mai kalama dake kusa da Turaki.

"Kin gane ni?"

Matar ta tambaya, Batula ta daga kai Turaki ya kalleta

"Kin santa ne?"

Matar ta daga kai tana murmushin kasaita.

"Mun taba haduwa da ita, lokacin da Mai Yaki ya rasu, kasan an fada mana rasuwar da yamma, muka ka mo hanya, sai muka ganta yashe a hanya, farko ma mun dauka ko gawa ce sai da Direbana ya fita ya duba, yace tana numfashi amman kamar bata san inda kanta yake ba, fuskarta a kumbude sai muka sakata mota, muka kawowa kusa da nan kuma sai tayar ta yi faci, dole ya buga min tintin saboda lokacin Sallah yayi, shi kuma yaje ya gyara motar, har aka saka ta cikin titin nan yarinyar nan bata san inda kanta yake ba, ni har tsoro na ji ko wani abun aka yi mata aka jefar da ita, ko kuma bata da hankali ne, ko da ta farka bata min magana ba, na lura dai kamar tsoro take ji sai na nuna mata hanya, tun nan ta fara gudu, ina ta mamaki ko ya same ta haka ta fadi a hanya, ashe ma yar'uwa ce"

"Ikon Allah, Allah yasa ku kuka tsinceta da ta fada mugun hannu ai da yanzu kila ba wannan maganar ake ba, ance fa can ita uwar rikon azaba take gana mata, ko zuwansu garin nan ba tare suka zo ba, ance barinta ta yi a hanya wai ta kawo kanta a kafa, ita kuma ta tari abun hawa ta zo, kila ma lokacin ne kika hadu da ita"

Baba Zulfa tana ta zuba zance, Turaki na kallon Batula cike da tausayawa, da can tausayin nakasa yake mata, a yanzu kuma har da na maraici da jin cewar bata dace da uwar riko ba.

"Ba haihuwar ba wani lokacin, idan ka mutu wa zai rika maka yayan? Wani babu ruwansa da kusanci matukar ba na shi ba ne ba ya nuna kauna"

"Ranka ya dade, duk yadda duniya ta lalace akwai na kirki, ba a zama ɗaya"

"haka ne, Batula wannan uwargidana ce Nana Khadija, ita ma yar'uwarki ce domin ni da ita duk jini daya ne"

Batula ta sakarwa matar da ta taimake ta murmushi tana daga mata hannu.

"Wannan kuma amarya ta ce, Nabila"

Wanda aka kira da Nabila ko dagowa bata yi ba balle ta kalli Batula, sai wasa take da karamin yaron dake jikinta.

"Wacan kuma kanwata ce sunanta Zinatu, ita ma yar'uwarki ce, kin ga yanzu kin san wadanda ba ki sani ba saboda wata rana"

Zinatu ta dagawa Batula hannu tana murmushi ita ma Batula ta daga mata tana maida mata da murmushin. A ranta kuma tana mamaki ashe su ma masu kudi suna yin har mata biyu, da kananan shekarunsu, ta san ba zai yayu ace Alhajin ba shi da aure ba, amman bata yi zaton har mata biyu ba, ko da yake duka matan biyu yara ne musamman amaryar, domin daga ganinta uwargida ta yi kanwa da ita.

"Zan maida ke makaranta da yardar Allah, ko da na manta sai ki tunawa Mama Zulfa, zan aiko ayi miki komai, daman na fadawa Malam Salisu zan dauki nauyin karatunki har jam'i a idan kina so"

Dadi ya cika Butula, Turaki ya yaye mata daya daga cikin bakin cikin dake cinta, ya raba ta da kewar karatu, kuma ta san zata yi sabbi kawaye. Ta daga mashi kai tana masa godiya, sai ya saka hannu aljihu ya ciro kudi ya mika mata, ta ki karba ta girgiza masa kai.

"Karbi mana, yau na saba baki kudi"

Ta ki karba sam, saboda tsoro take kar tafi ta kudin wani zancen ya taso.

"Kawo ajiye idan ta tafi ai aika mata da su, ko kuma a siya wani abun daga nan a aika mata da shi"

Batula ta mike tsaye ta musu bye bye sai a lokacin Nabila ta kalli Batula tana yatsina fuska.

"Har yanzu baki saka talkami ko?"

Batula ta juyo ta kalli Turaki tana dariyar kunya, sannan ta fice da sauri. Tana tafe tana tsalle a hanya zuciyarta ta cika da farinciki tana ta murna, damuwarta ta ara mata lokacin farinciki sai ta manta da wani kunci da bakinciki da ke rayuwarta. Ta shiga gidan baki har kunne kana ganinta kasan tana cikin farinciki dakin da Umma Hindu take ta shiga sai ta zauna kasa ta dafa kafafuwanta.

"Ke lafiya?"

Ta fara mana na kurmancin nata tana fada mata makaranta za a maida ita, ta yi hakan ya kai sau goma sannan Umma Hindu ta gane me take nufi, daman yanzu sai ta dade tana mata bayani take fahimta, ba kamar da suna can garin ba, ta kan rubuta mata yan'uwanta su karanta mata, a nan kam babu wanda zai karanta mata a ciki gidan domin duka yaran gidan basa boko, sai talla ko daka, ba kamar wacan garin ba da suka dan fi su wayewa da karbar karatun boko da na Allah.

Umma Hindu ta tabe baki, ko kadan bata nuna ta jidadin abun ba, balle har ta yi murna. Sai da aka biyo da kudin da Turaki ya ba Batula sannan ta yi farinciki, ta nunawa kowa kamar ta jidadin za a maida Batula makarantar.

  Ana kusan Magariba, Batula ta kama hanyar gona, gurin yin itatuwa, daman kullum da yamma ko da dare sai taje ta yo karan da za 'ayi girki da su gobe. Idan ta tafi da wuri sai ta dawo ana magariba, idan kuma aka samu tsabanin haka har Isha'i tana kaiwa.

Tana cikin yin kara tana tarawa guri daya, har sai da suka yi yawa suka yi tuli sannan ta daure da igiyar da ta zo da ita, sai kuma ta fara waige waige tana neman wanda zai dorata domin karan yau ya fi na kullum yawa, can ta hango wani mai shigar yan birni tsaye kusa da wani bakin doki, sai ta karasa inda yake ta zagaya ta gabansa inda zai ganta.

Idonta ya fara dauka akan kirjinsa da rabi yake waje sakamakin maballan rigar dake bude, kirjinsa ya ginu ginuwa mai kyau wanda ya dauki hankali ta kirga tsaguwar data kaso gida shida a kirjin nasa, kasan black t-shirt din daure a kugunsa, ta daga kai ta kalli fuskarsa mai cike da haiba, kansa na sanye da hula facing cap baka, ya juya gaban hular zuwa baya. Slowly take kallon bakinsa hancinta ta gangara har cikin idonsa, a nan nata idanuwan suka sarkafe ta kasa cire nata idon, sai ta hade hannayenta ta masa gaisuwa sannan ta nuna bayansa, mutumen dake ta kallonta yana jinjina kokari da karfin halinta ya juyo ya kalli inda take nunawa, ya juyo sai ta hade hannayenta alamar rokonsa.

"In doraki?"

Ta daga kai. Ya kalli ko'ina na dajin, ya hango wasu mutanen nesa da su wasu kuma na hada hadar barin gonan nakin saboda gabatarwa magariba. Ya juya ya nufi gurin da ta tara karan ta bi bayansa suka isa tare, sai ya saka hannu biyu ya cira karan masu uban yawa ya dora mata akai.

"Miye sunanki?"

Ta masa alama da makoshinta da bakinta sannan ta girgiza masa hannunta. Matsawa yayi ya kai hannunta gurin wuyanta, sai ta matsa baya, kamin ta sake matsawa ya riko makogoron wuyanta da hannunsa daya.

"Me sunanki?"

Ta fara numfashi da karfi, tana ji wani abu ya rike mata wuya da karfi, ta wani abu mai motsi daya taso daga cikin kanta yayi cikin cikinta tayi zillo zuwa makoshinta.

"Ba.... Bal.... BALL.....  BAT... BATU... BATU.. TU... LA... BATULA...."

Ta furta daker a rarrabe, tana hakki idonta kamar zak fito tsabar tsoro da rudani. For the first time ta ji sautin muryarta, for the first ta gyara yin magana kuma ta ji maganar ta fita, ta yi baya baya tana kallonshi, sai ya kalli hannunsa yayi murmushi ya sake kallonta. Ba shiri ta jefar da karan ta juya jiki na rawa ta fara gudu ko waigowa bata yi ba, har ta isa gida.