ALWASHI 2

38

by @rufaidaumar

ALWASHI 

      63

Unguwar Wuse, nan suka dosa bayan sun yi shatar mota don ko Baba Dakta ba sa so ya san da zuwansu garin. Koda suka isa estate din wanda ba na zaman mutum daya ba ne, suka yi wa Maigadin bayanin wanda suke son gani. Aka yi sa'a Maigadin ya ce musu bai jina da shigowa gidan ba. Ya ce su jira ya masa magana.  Suka tsaya a farfajiyar gidan mai wuri-wuri, kowa da part dinsa, gidajan sun kai ashirin a ciki. 

"Hey, look, shi ne ko?" 

Muryar Fareed ta sa Areef dake danna waya ya ɗago kai. Dattijo mai cikar kamala, dogo marar jiki sosai. Hatta da yanayin kallonsa, irin na Laila ne. Kamarsu da Laila har ta ɓaci. Kana ganin bafulatanin ka san sun haɗa dangantaka mai ƙarfi da Laila. Areef har Adam Kibiya da ke bin su da kallo na rashin sani ya ƙaraso, bai iya ya ɗauke idanu daga kansa ba. Sai da ya ga ya miƙo musu hannu da sallama, kafin ya yi saurin cire gilashin da ya ɓoye ƙwayoyin idanunsa ya ɗan russuna da girmamawa ya gaishe shi. Ganin haka sai shi ma Fareed ya yi, Adam ya amsa fuska a ɗan sake saboda kamalar da ya gani tattare da su, sam ba su yi kama da mugayen mutane ba. 

"Sannunku dai, bismillah muje ciki."

Ya yi gaba suka bi bayansa.

"They look so much alike."

Fareed ya yi zancen da raɗa yanda Areef kaɗai zai ji, sarai ya ji sa amma bai ce uffan ba. Shi gaba ɗaya ma jikinsa ne ya yi sanyi, tausayin Uba da yaran duk ya mamaye shi. Me ne haɗinsa da Daddy Affan da har ya cutar da shi tsawon shekarun nan? Har dai suka ƙaraso block din Adam Kibiya, babu wanda ya ce uffan sai saƙe-saƙen zuci. Sai a lokacin ya ɗan juyo ya dube su da murmushin da ya ƙara haskawa Areef kamanninsa da Laila ya ce,
  
  "Ku ɗan ban mintuna zan sanar da iyalina."

"Ba damuwa Yallaɓai." Cewar Fareed, daga nan ya juya ya shige. Kusan lokaci guda suka sauke ajiyar zuciya. 

"Wallahi wannan mahaifin matarka ce."

Areef ya jinjina kai. 

"Ko ba ka rantse ba, fuska ta nuna."

***
Shatu na zaune a falo tana jiran ta ga dawowar mijin nata, hankalinta gaba ɗaya ba ya kan tv da ke aiki. Gaba ɗaya fatarta ta ƙara murmurewa ta yi kyau, da ka kalle ta ka san tushe daya suka fito duk da ba sa kama sosai domin ita ta fi kwaso ɓangaren Mahaifinta ba Mahaifiya ba. 

Da sallama ya ƙaraso ciki, ta miƙe tsaye da saurinta. Ganin fuskarta da murmushi ya sa ta sauke ajiyar zuciya.

  "Har sun wuce?" 

"Ko ɗaya, na shigo na ce ki gyara zan shigo da su. Ban taɓa ganinsu ba, amma hankalina ya kwanta da yanayin kamalarsu, in sha Allahu da alkhairi suke tafe."

Shatu ta gyaɗa kai. 

"Allah ya sa, bari na ɗauko hijabi sai a kawo musu abin motsa baki ko?"

"Allah ya maki albarka to." 

Ta amsa suna yiwa juna murmushi kafin ya juya ya fita ita kuma ta nufi hanyar ɗaki. 

Can suka shigo tare da su Areef bakunansu ɗauke da sallama. Iznin zama ya yi musu a saman kujera, duk yanda suka nuna ƙasa zai fi musu haka ya ƙi yarda a dole suka bi umarninsa wajen zaman. Ga Areef nauyinsa yake ji tunda surukinsa ne, ga uwa uba yana fargabar yanda zai ɗauki zantukansu, tuni ya yanke ba zai iya ba sa labarin ƙaddarar da ta soma haɗa shi da Sameera ba, ya gwammace ya nuna masa kawai Laila yake aure don gaba ɗaya Dattijon ya masa kwarjini. 

Shigowar Shatu falon ya katse tunanin Areef, nan suka gaida ta, fuskarta a sake ta amsa kan ta nufi kicin. Adam ya dube su. 

  "Sai dai kuma har yanzu na kasa gane fuskokin naku."

Areef ya gyara zama kansa a ƙasa ya ce.

"Eh haƙiƙanin gaskiya, mu ma yau muka fara ganinka. Amma kuma mun sanka, magana ce mai girma muka zo da ita game da abin da ya shafi iyalinka."

Ai sai Adam ya zabura. Shatu da ta tako, tuni ta ƙaraso ciki da sassarfa ta dire tray din tana duban Areef.

"Iyalina? Su wa daga ciki?" 

Gaba ɗaya ma ya ruɗe, Areef cikin son kwantar masa da hankali ya ce. 

"Mama Kubra da su Laila."

Ai sai Adam da Shatu suka dubi juna kafin ya miƙe ya ƙarasa kujerar da Areef yake ya zauna a gefensa. Duk da rawar da bakinsa ke yi, ga ƙirjinsa na bugu fat fat na farganar abin da zai ji game da su bai hana shi kallon Areef ba ya ce.

"Ina suke? Me ka sani a kansu? Suna raye?" 

Tambayar ta ba Areef tausayi, Fareed ya zuba musu idanu shi ma cike da tausayin bawan Allahn. 

"Daddy, ni da kake gani, mijin ɗiyarka Laila ce. Suna na Areef Sada Bilyaminu, a Katsina nake rayuwa. Mun haɗu da Laila a wani zuwa Kano da na yi. Abin da na sani shi ne, bayin Allahn nan sun sha wahala a rayuwarsu domin har sana'ar kitso sun yi, kafin daga baya Allah ya sada fuskokinsu da dangin mahaifin Mama Kubra dake Maiduguri. Laila ta zauna ne a hannun ɗan Gwaggonta, Daddy Mu'az da ke zaune da iyalinsa a Kano. Mama Kubra tana can Maiduguri cikin ƙoshin lafiya. Ina mai tabbatar maku, rayuwarsu babu wata matsala ta zahiri."

Areef ya fiddo wayarsa ya shiga dannawa, tuni Adam ya soma zubda hawaye ga murmushi saman fuskarsa yana kuma hamdala ga Ubangijinsa. Shatu ita kanta hamdalar take yi sanin irin damuwar da mijinta ke yi duk dare yakan raba shi ne da tunani wasu lokutan, ta san cewa yana kaunarta kuma yana iya kokarin kyautata mata, sai dai hakan ba zai taɓa ɗauke masa damuwa kan iyalinsa ba.

 Kai tsaye ya miƙawa Adam wayar. Fuskar Laila ce tana murmushi babu make up a kan fuskar, ɗaya daga cikin hotunanta da Haseenah ta taɓa aikomasa a baya. Adam har zooming yake yana kallo. 

  "Allahu Akbar, Alhamdulillah ya Rabb."  Ita ce kalmar da Adam ke faɗi yana ƙara maimaitawa, hawaye ba su bar zubo masa ba. Can ya dubi Areef ya riƙe hannunsa gam bayan ya miƙawa Shatu wayar itama tana kallon hoton Laila, faɗi take "Yaya wannan kamar ka yi kaki."

 Shi kuwa faɗi yake. 

 "Nagode ɗana, nagode ƙwarai. Allah ya yi maka albarka. Yanda yau ka faranta min da abin da na yi shekara da shekaru ina dakon jiransa, Allah ya dauwamar da farin ciki a rayuwarka, ya ba ka kariya a dukkanin sa'i."

 Areef da murmushi ya ke amsawa da amin, Fareed na taya shi. 

  Adam ya ƙara karɓar wayar daga hannun Shatu yana ƙara kallon hoton Laila. 

 "Allahu Akbar, wato jini ba ƙarya ba ne. Dubi kamannin Mahaifina a fuskar Laila. Dayake muna kama sosai da shi. Ita Sameera ba ka da hotonta? Ko tana Maiduguri?"

 Ya ƙarashe da duban Areef karo na ba adadi, Areef ya ji gabansa ya faɗi, dama ya san tambayar za ta biyo baya kuma sun shirya amsar da zasu ba shi kafin nan gaba. Ji ya yi gaba ɗaya ƙaryar da suka shiryo ta rushe a kwakwalwarsa tsabar kaifin da idanuwan Areef ɗin suka yi mishi. 

 "Ita tana tare da Mama a can Maiduguri. Ba na jin akwai hotonta a wajensa."

Fareed ya amshe ganin Areef ya kasa cewa uffan ga kallon ƙurillar da Adam ke bin sa da shi. Duk da haka Adam bai gamsu da sauyin Areef din ba don haka jiki a sanyaye ya dubi Fareed. 

 "Ko ta rasu ne?"

Wannan tambaya sai da Areef ya ji kansa ya sara. Fareed ya girgiza kai. Kafin ya amsa Shatu ta riga shi.

 "Haba Yaya, ba ka ji suka ce tana Maiduguri ba? Me ya kawo wannan zance marar daɗin ji?"

Ya sauke ajiyar zuciya. 

"Wallahi kawai jikina ne ya ban hakan dayake na taɓa mafarkin ta mutu ɗin ya kai sau uku. To ai shikenan, bari na kyautata zaton. Allah ya sada fuskokinmu da alkhairi. Ummu Abdallah a haɗa musu abin taɓawa don Allah."

 Zasu yi musu ya hana su, 

"Nan gidanku ne, ku ɗin ƴaƴana ne. Ku sani, kun kawo min labari wanda nake kwana da tashi da burin son jin sa. Don haka kar ku sake ku yi min musu."

Da wannan ya kashe bakinsu suka yi shiru. 

 Can dai ya tuna wani abu da sauri ya dube su.

 "Amma ya aka yi ku ka san inda nake? Ya ma aka yi ku ka gano ina raye?"

Areef ya yi gyaran murya. Wayar ya nemi ya ba sa, koda ya amsa hoto ya shiga laluba, can ya nuna masa. Adam ya kalla amma bai gano ko waye ba. Baƙin mutum ne da hutu ya ratsa sosai, ko da ganin irin shigar da ke jikinsa ya san wani riƙaƙƙen ɗan boko ne. 

 "Who is he? Ban san shi ba. Ko mijin Kubra ne?" 

Girgiza kai Areef ya yi.

 "Ba na jin Mama ta yi aure har zuwa yanzu Daddy."

Har wata ƴar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya zubawa Areef idanu da alamun tambaya. Madadin ya ba shi amsa kai tsaye sai ya nuna masa abokin mahaifinsa ne. Nan ya fara da kwashe labarin Alh Affan kaf ya ba Adam ba tare da ya furta sunansa ba. Alaƙarsu da mahaifinsa Alh Sada, yanda ya dage sai ya auri ɗiyarsa, har ma da yanda ya kasa yarda da shi ya soma zarginsa ya kuma saka a fara bibiyar takunsa. 

 "Sanadin bibiyarsa da aka yi ne muka gano ka, muka san cewa ya kama ka shekara da shekaru saboda zalunci, ya raba ka da matarka da yan uwa. Wannan da kake gani shi ne Alh Affan Muhammad."

Areef ya na kai ƙarshen zancen, Adam ya yi salati da kiran sunan Allah. Lokaci guda yana ƙara kai idanunsa kan hoton amma screen din wayar ta ƙulle, karɓa Areef ya yi ya buɗe masa ya ƙara kallo. Girgiza kai Adam ya yi, idanunsa suka kaɗa. Ya juya ya dubi hanyar kicin, ya tabbatar ba lallai Shatu hankalinta na ga hirar ba.

 "Tabbas shi ne, shi ne wanda na zauna a gidansa matsayin prison ɗina. Kuma ka san abin mamaki? Ka san waye wannan ɗin? 

 Girgiza kai Areef ya yi idanunsa na kan Adam. Shi kansa Fareed kallonsa yake yi don ya ƙagu ya ji me zai fito daga bakinsa. 

 "Bisa binciken da na yi da ma irin zantukan da ke fita daga bakunansa da yaransa da nake wajensu, na tabbatar ba kowa ba ne face Affan, wani maraya kuma agola da iyayen matata Kubra suka raina tun kafin su samu cikin Kubra, bayan ya girma ya yi karatu mai zurfi ta silarsu, ya yi sanadiyyar raba su da numfashinsu duka domin ya mallake dukiyar Marigayi Alh Hammad mariƙinsa, kakan su Laila kenan. Ya yi ƙoƙarin har Kubra itama ta bar duniya, sai dai Allah ya tseratar da ita. Ni na buge ta da motata, na kuma kai ta garinmu cikin yan uwana, a ƙarshe na aureta kuma Allah ya azurta mu da haihuwar twins."

 Adam ya kwashe kaf tarihinsa da ma haduwarsa da Kubra, irin tsanar da Mahaifiya da ƴan uwansa suka gwada mata, kai har ma da korar karen da suka yi mata duka ya labarta musu. 

  Wani irin tausayinsu ya mamaye zuƙatan Areef da Fareed. Adam ya ƙara da faɗin. 

  "Ni na tabbata Kubra ta wahala kafin ta sadu da ƴan uwan iyayenta, saboda tunda take a rayuwa ba ta taɓa taka Maiduguri ba sai a ranar da zuwansu ya yi sanadin mutuwar iyayenta. Ya kuma jefo ta hannuna. Ni kuma don na faranta mata, na hutar da ita tunani da ma kawo ƙarshen gori da hantara da yan uwana ke mata suna shegenta ta, ya sa na shirya ba tare da sanin kowa ba na fita don bincike a Kano ko za'a dace. Saboda tun a labarin da yanayin yanda ƴan fashi suka tare su gaba ɗaya na tsargu, matsayina na ɗan jarida mai zurfin bincike, na kasa samun nutsuwa da cewa babu lauje cikin naɗi, dalili kenan da ya sa na tunkari ainahin gidan da Kubra ta taɓa ban kwatance cewa nan suke da zama. Wannan shi ne silar shiga ta hannun Affan."

 "Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Amma wannan ya cika ƙwallon shege! Bura uban can!"

Fareed ya furta a fusace. Areef ya kalle sa jin ya sakar musu ta Katsinawa. Adam sai da ya murmusa don ya sani cikin jin zafi ya sa shi suɓul da bakan. 

 "Ashe ba banza ba na ji gaba ɗaya na kasa yarda da shi Daddy? Tsintaccen mage ne, butulu! Maci Amana?" 

Areef ya yi furucin ƙirjinsa na wani irin ƙuna. 

 "Ɗana mutumin nan da ka ke gani ba shi da imani, ni na san ya saka a bibiye ni, dalili kenan da ya sa na jinkirta da cigiyar Kubra ko kuma zuwa Maiduguri. Bana son na yi wani action din da zai zaburo da su. Na fi son ya kasance ina da ƙarfin iko da taimakon Allah wanda zan ba Kubra kariya a lokacin da ya samu labarin inda take. Toh Alhamdulillah, zuwa yanzu hakan ya yimin dadi, kuma da himmata zan je Maiduguri na tabbatar babu abin da Affan zai iya yi gareta a yanzu. Zan kuma ga ɗiyata ko?"

 Girgiza kai Areef ya yi.

"Ba yanzu ba Daddy."

Daga Adam har Fareed suka dube shi. 


©Rufaida Umar