HAYAT NAZLI

4

by @maryamannour71

Chapter.4 

 

Duk da yadda jikinta ya yi tsami ƙasanta na mata zugi bai hana ta tashi ta daddafa ta saka kayanta ba tare da ta samu ƙarfin halin zuwa gida ba, to me za ta ce masu, wane zai yarda da abun da za ta ce? Ita kanta bata yarda da kanta ba ballanta wanda za ta faɗawa yadda daren birthday ɗinta ya kasance, abu guda da za ta iya tuna shi ne, barin Nadiya a kan cewa za ta restroom sauran kuma dukka duhu ne. 

 

Amma da ta yi wani tunanin kuma sai ta ji to me ya sa za ta ji tsoro alhalin ita kanta bata da masaniyar ya a ka yi hakan ta faru, dole ne ta je ta fuskanci su ta karbi dukkan wani hukunci da za su yanke a kanta, dan bata ga dalilin ɓoye kanta da take ba kenan ma kamar da son ranta komai ya faru? Dole ne ta fuskanci su hakan ne kadai za a iya yin binciken abun da ya faru har a gano gaskiyan lamari. Da wannan ƙaramin ƙarfin guiwar da ta samu ta miƙe ta haɗa kayanta, ta juya za ta fita kenan kamar ance ta kalli gefen da ta ɗauki takalminta idanunta suka sauka kan wani bracelet mai ɗaukan ido, ɗauka ta yi tana kallon abin hannun very unique dan bata taɓa ganin irinsa ba. Gashi dai sai shining ya ke yana daukan ido. Haka kawai ta ji son tafiya da shi duk da bata san wa ya mata wannan aika aikan ba but ta tabbata wannan abun na sa ne tunda a iya sanin ta bata san 'yan gidansu da shi, hakan yana nufin duk wanda ta ke tare da a daren jiya shi ke da wannan bracelet. 

 

Zuwa lokacin gari ya waye hasken rana ta fito, dalilin da ya sanya ta yi rolling din mayafinta ta rufe rabin fuksarta yadda ba mai ganin fuskarta bare a gane ta. Gabanta ne ya yi mummunan faɗi ganin dandazun jama'a da kuma ƴan jaridu a bakin HOTEL security sun hana su shiga ciki, birki ta ja ta tsaya a gefe tare da nazartar su. Kar dai abin da ya faru da ita ne har ya isa kunnensu shi ya sa su zuwa dan ganewa idanunsu? to amma ai babu outsider da ya gani balle har maganar ta fito kuma koda ta fito ya yi saurin da za'a tara ƴan jaridu da mutane har haka. 

 

Sai dai ganin danƙareriyar Mercedes–Benz baƙa mai tinted na barin harabar hotel 'yan jarida suka yi ca a kanta security sun hana su isa wurinta  su yi interview din mai motar da kallo ɗaya za ka san dukkan wanda ke cikin motar nan babban kutsa ne da ya ci ya sha ya tada kai, ko kuma wani babban ɗan siyasa. 

 

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke jin dalilin taruwar ƴan jarida wurin, ba tare da ta tsaya jin ko wanene ta raɓa cikin mutane ta fita. Allah ma ya sa ta na fita ta samu mai adaidaita sahu ta faɗa suka tafi, tunani ta soma na ta fara zuwa gidansu ko kuwa gidanta? Cikin wannan yanayen ta san ko wanne babu sauke a ciki, hakan ya sa ta yanke shawarar zuwa gidanta ta fara fuskantar Zaid in ya so daga baya ta je gida. 

 

Koda suka isa, sauka ta yi ta kalli mai napep din ta ce. "Dan Allah ka yi hakuri bara na shigo na ɗauko maka kuɗin don babu a hannuna." Da to ya amsa ya nemi waje ya parker yayin da ita kuma ta shiga cikin gidan, shiru ta tarar da falon Zaid baya nan shiru sai ƙarar AC da ke tashi, ajiyar zuciya ta sauke na ganin baya falon dan har ga Allah bata shirya haɗuwa da shi a yanzu ba don bata san da wani ido za ta kalli shi, ita kanta har yanzu bata gama fita daga shock ɗin abun bare shi da ya ke tunanin wani abun. 

 

Motsin da ta ji na tashi daga kitchen ne ya sa cikin sanɗa ta nufi wurin, Nadiya ta gani a tsaye ta na haɗa wanke wanke. "Aunty kina buƙatar wani abu ne?" Cewar Nadiya tare da tsoma hannayenta daga ruwan wanke wanken. "Ehem, hmm wanda ya kawo ni a napep yana waje please i don't have any cash with me, idan akwai a wurinki please ki bashi na biya ki daga baya." To ta ce ta raɓa daga gefe ta fice, ɗakin da ke downstair wanda ya kasance a matsayin na ta ta shiga, wurin wata tsohuwar jakarta da ke rataye a hannun drower inda take adana ƴan kuɗaɗenta ta nufa ta buɗe ta ciri kuɗi kana ta yi waje don biyan mai adaidaita sahun. Bayan ta biya sa kuɗinsa ta koma ciki, a palour ta samu Nazli zaune kan sofa yayin da ta zubawa screen ɗin wayarta ido sunan Mommy ya fito ɓarau ɓarau amma ta kasa ɗagawa, cikin sanyin jiki ta tsaya kusa da ita kana a hankali ta ce. "Aunty a na kiran ki." Ba tare da ta bata amsa ba ta ce. "Ina Zaid bai dawo ba?" "Ehh, bai dawo ba." Ta amsa, kaɗa kai ta yi ba tare da ta kuma ce wa komai ba ta haura sama Nadiya ta bi bayan ta ido. 

 

Koda ta shiga ɗaki darect bathroom ta shiga ta yi wanka tare da gasa jikinta da kyau ta yi wankan tsarki kafin ta fito hannunta riƙe da towel tana tsini gashinta, rai a jagule haka ta shirya cikin simple rigar atamfa ta gyara gashinta ta yi parking. Dadduma ta shimfiɗa ta tada sallar asuba da bata yi ba. 

 

Bayan iddar da sallar kwanciya ta yi a nan kan daddumar ta faɗa a tunani, duk wani ƙoƙarin ta na tuna abin da ya same ta a jiyan bayan barin ta hall ɗin nan ta kasa, ƙarshe ma da ta matsa ciwo kai ta soma, ba tare da ta sani ba bacci barawo ya yi awon gaba da ita a nan gurin. 

 

Throughout the rid ba mai magana a cikinsu, kowa da abin da ya ke tsaƙawa a zuciya, Zaid shi ke tuƙi Neesah na gefen mai zaman banza, sai kuma Mom da Dad da ke zaune a baya. Har suka isa ya danna horn mai gadi ya buɗe masu gate ya kutsa kan motar ciki. 

 

Ko bari a yi parking da kyau Dad bai tsaya yi ba cikin ɓacin rai ya buɗe ƙofa ya fita, gaba ɗaya shiru suka yi ba tare da sun iya tsaida shi ba illa binsa da idanu har ya shiga ciki, cikin kunya Mom ma ta fita, godiya ta yi wa Zaid tare da bashi haƙuri ta nufi ciki cikin ɗacin rai, ta rasa wani irin tunani ma za ta kama. Kai tsaye ɗakin Daddy ta nufa sai dai ta ji ƙofar a rufe, kamar ta kwankwasa sai kuma ta canja tunani ta koma ɗakinta. Koda ta shiga kasa zama ta yi sai safa da marwa take, ajiyar zuciya ta sauke ta koma ta zauna, kamar kuma an mintsine ta ta jawo wayarta ta dannawa Nazli ƙira sai dai bugun duniya bata ɗagawa. 

 

–––––– 

 

A hankali Neesah ta juya ta kalli Zaid da ya kifa kansa kan sitiyarin motar, wani irin yanaye ne ta tsince kanta a ciki ganinsa a haka. Ita kanta har yanzu bata gama digesting ɗin abun da ya faru ba, abu na ƙarshe da ta yi tunanin 'yar uwarta za ta aikata kenan. "Zaid please, am really sorry for what my sister did, duk da ba mu san gaskiyar abin da ya faru ba but ina ganin ya kamata a bata dama let hear her side of the story." Ta faɗa ba don akwai wani bayani ko shaidar da zai iya wanke Nazli daga zargi bayan abin da suka ganewa idanunsu... 

 

**** 

 

Bayan barinsa gidan sirikansa darect gidansa ya nufa, koda ya yi parking kasa fita ya yi sai da ya ɓata kusan 30 minutes a ciki motar bai fito ba, ƙarar shigan saƙo wayarsa ne ya jawo hankalinsa gareta, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ganin saƙon da mahaifiyarsa ta tura masa. "Zaid ina kake, ya kuma Nazlin an ganta kuwa?" Umaimah ta faɗa min abin da ya faru, muna ƙiran wayarka ma baka ɗaga ba fatan komai lafiya?" 

 

Sanin fa idan bai tura mata reply hankalinta ba kwance zai yi ba ƙarshe ta ce za ta zo nan din kuma ba zai so zuwan ta a yanzu cikin wannan yanaye da suke ciki, dan haka ya tsaita kansa ya yi mijin ƙoƙarin danna duk wani damuwa ya ƙira ta. Bugu biyu ta ɗaga, bayan sun gaisa ta sake tambayar Nazli inda ya shaida mata tana lafiya. Daga nan suka soma hira sama sama duk da ita ce ke jan ragamar hirar, lura da kamar da damuwa a tattare da shi ya sa ta tambaya sai dai ya nuna mata gajiya ce kawai ta hidimar jiya. "To na bar ka haka, ya kamata ka je ka kwanta ka huta yau asabar bari ma ka ce za ka tafi aiki." "Okay Mommy sai anjima." 

 

Da a da ne kamar yadda ya shiga gidan nan haka abu na farko da zai yi shi ne saka ta a ido, saboda kewa da zumuɗin ganinta. Sai dai a yau ba sakata a idoj ba, ko sunanta ne bai son ji a wannan lokacin. kai tsaye daƙinsa da ke upstairs kusa na ta ya shiga. Gan gado ya kwanta ya yi rigingine ya zubawa rufin daƙin ido, tunani ya faɗa na da me ya ragi Nazli haka ne da ta zaɓi saka masa da wannan tukuicin? A kullum burinsa da ƙoƙarinsa a kan yadda zai faranta mata ta ji daɗi ne, ba shi da buri da ya wuce ya ga ta fara sonsa, shi ya sa ma da ya samu ya aure ta ya amimce da dukkan wace doka da ta gindaya masa, ya bata lokacin da ta buƙata ba tare da gajiyewa ba ya ke nuna mata ƙauna duk a tunaninsa zuciyarta za ta narke ne ta fara jin wani abu a kansa. 

 

Ashe shi kaɗai ke kiɗansa yana rawansa bai sani ba, bai taɓa jin ya ya yi nadamar auren nan da kuma dana sanin faɗawa cikinsa ba sai a yau, duk wani wulaƙanci da kuma cin kashin da ta ke masa ya zaɓi ya juri domin a ganinsa mai wucewa ne, ya san da zarar ta fara son shi komai zai gyaru kuma girman son da ya ke mata ba zai iya rabuwa da ita ba, shi ya sa ya ji ya gani duk abin da take biye mata kawai yake haka zalika da ta nuna ba za ta iya raba daƙi da shi bai musa ba duk da a zahirin gaskiya bai so hakan ba amma domin faranta mata ya bata abin da take so. 

 

Duk wannan abun da ke faruwa a tsakanin su ba wani daga cikin iyayensu da ya sani, a tunaninsu zaman lafiya da ƙaunar juna suke ba su san kallon kitse suke wa rogo ba. Yanzu da ya zauna ya sake tunani sai ya ji sam laifinsa ne, domin tun farko ta nuna masa bata sonsa bata ra'ayinsa amma ya nace, da ya san inda son zuciyarsa zai kai su kenan da ko mutuwa zai yi ba zai ko ji sha'awar auren balle har ya tilasta mata ta hanyar iyayensu mata ba. Sai yanzu da ya zauna ya ke ganin wautarsa da kuma rashin maida hankali da bai yi ba, kenan tana da wanda ta ke so amma ya masu kutse shigar sauri? shi ya sa ta tsane sa duk ƙoƙarinsa bata gani. 

 

Ya gama yanke shawarar da ya tabbata ita ce mafita a gare su gabaki ɗaya, a hankali ya furta. "I have to fixed this, duk laifi na ne dan haka ni ke da alhaƙin gyarawa." tashi ya yi ya buɗe ƙaraman bedside drower ya fito da ƙaramin jotter da pen. Shiru ya yi na ɗan daƙiƙa kafin ya buɗe shafi na farko ya soma rubutu a ciki. 

 

Bayan ya gama ne ya yage inda ya yi rubutun ya naɗe takardar ya miƙe ya fita, bedroom ɗinta ya nufa sai dai jin ƙofar a rufe ya sanya shi komawa. A kan mirror ya a je wasiƙar ya shiga bathroom mintuna kaɗan ya fito ƙungunsa ɗaure da towel. Wardrobe ya buɗe ya fidda kaya marasa nauyi ya saka kana ya dauke takardar wasiƙar sa ya fita daga ɗakin. 

 

NAZLI. 

 

Sai kusan 11:24 ta tashi, a hankali ta tashi zaune tare da dafa kanta da ke mugun yi mata ciwo kamar zai rabe gida biyu, miƙewa ta yi ta shiga toilet ta gama uzurinta kafin ta fita ta sauka ƙasa domin nemawa kanta abin kare don wata masifaffiyar yunwa ce ɗawainiya da ita dan tun jiya rabon ta da wani abu shi abinci, gabanta ya faɗi ganinsa zaune a falon ya ƙura ma staircase ɗin ido kamar ya san da zuwan ta. Kamar ta juya ta koma ciki sai dai babu hali don ya riga da ya ganta, gaba ɗaya ta manta ma da abin da ke ya faruwa zuwa wani lokaci da ta san za ta same shi a palourn da bata fito ba. 

 

Ganin bata da wata mafaka ya riga da ya ganta ya sa ta ƙarasa sauƙa a hankali ta soma wasa yatsun hannayenta, gabansa ta ja ta tsaya ba tare da ta ce komai ba gabanta sai tsananta faɗuwa ya ke, so take ta buɗe baki ta yi magana amman ta kasa to daga ina ma za ta soma kare kanta? "Zaid please forgive me am sorry, na san duk yadda zan maka bayani ba lallai bane ka yarda ba amma dan Allah ina roƙan Alfarmar ka bani damar wanke kaina a wajen ku, abin da kuke tunani ba haka bane i can explain." Ta faɗa a sanyaye. "Ni kaina ban san ya hakan ta faru ba ban san me ya zo kaina kawai na farka ne na ganni a haka, ko kafin na yi wani yunƙurin kun shigo amma wannan ba halina bane, kuma ka sani." Wannan karon zama kusa da ƙafafunsa ta yi ta soma basa haƙuri da kuma labarta masa iya abin da ta sani, sai dai a fa wajensa tamkar kare kanta take tunda har yanzu ba za ta iya zuwa a tsarƙaƙe ta nemi gafara ba tana masa ƙarya bayan abin da ya gani da idanunsa ba labari a basa bare ya ce sharri a ke mata, hakan ba ƙaramin ƙara karya masa zuciya ya yi ba ya ji abin da ya ke ƙoƙarin aikatawa daidai ne. Ya miƙe mata farar takardar, cikin rashin fahimta ta ce. "Takadar me cece wannan?" "To your freedom." Saurin ja da baya ta yi wani bugu zuciyarta ke buguwa da sauri da sauri. "No! You can't do this to me, Zaid please karka mini haka." Kallon gefe ya yi ya lumshe idanu yana mai danne kansa da kai zuciya nesa, a hanakli ya buɗe idanun kana kamar walƙiya ya haɗa fuska babu alamun wasa ya ce. 

 

"Baki da zaɓi a kan haka, lokacin da kike tarayya da samarin ki na banza ai baki tuna da ni ko aurena da ke kanki ba kike cin amanata, duk so da ƙauna da na ke nun miki bai hana ki rufe ido kina ha'intata ba ta bayan ido na ba. Wato ga soko mara tunani me bakin iyayi da za ki iya juya son ranki ki faɗa masa dukkan wata ƙarya da yaudara, to bari ki ji Nazli ina son ki san duk wani abu da kike min ina shiru ba don komai bane sai dan.... sai kuma ya yi shiru ya juya mata baya ya ce. "Zama na da ke ya kare dan haka ki tattara ina ki ya ina ki  ki bar mini gida dan ni ba zan zauna da mazinaciya ba mai bin maza da aurenta, na gode ma Allah ma da ya sa na gane ma idanuna tun abu bai nesa ba da Allah kadai ya san me zai faru a gaba, sai da a ka gargaɗe ni kan auren nan amma na yi kunnen uwar shigu na afka masa wai ni nan uwa masoyi to ga inda son ya kaini."  

 

Ya tako ya fuskance ta ya zuba fuskarta da ta gama jiƙewa da ruwan hawaye baki buɗe tana kallonsa kamar yau ta taɓa ganinsa, sabon kaɗuwa da mamakin kalaman da ke fitowa daga bakinsa, wanda kamar ruwan dalma take jinsu a zuciyarta yadda suke tsaka ko wani nama da tsoka na zuciyarta yana wucewa. Ya ce...