HAYAT NAZLI

5

by @maryamannour71


Chapter 5 

 

"Ki je na sallame ki, Allah ya haɗa kowa da rabonsa." Daga nan ya kaɗa ƙafa ya fita ya barta cikin ɗumbin mamakin da ya hana ta cewa komai musamman kalaman da ya yi anfani da su a kanta, sai ta ji kamar ba Zaid ɗin da ta sani bane, wannan wani Zaid ne daban da bata san da shi ba, tabbas koda ita ce ta kamasa a yadda ya yi din to kusan makamancin abin da za ta yi ne, sai dai kalaman da ya yi anfani da su a kanta sun yi tsaurin da duk yadda ta so cire su a zuciyarta kasawa ta yi, sun ƙona mata zuciya matuƙar gaskiye. 

 

A tunaninta koda da gayya ta aikata wannan abu da ya ke zargin ta dashi to bai dace a ce a matsayinsa na mijinta da ke iƙirarin yana ƙaunar ta harda cewa zai iya rayuwa da ita a ko wani yanaye na rayuwa idan ya riske su, a tunanin ta koda zai yi fushi na wani lokaci ne zai bata damar wanke kanta, sai gashi bai ko tsaya ya saurari mai zai fito daga bakinta ba ya yanke mata hukunci ya maida ita ƙaramar bazawara ba tare da tunani ko shiryawa hakan ba. 

 

Ashe duk wadan nan alkawarrurukan da ya ke mata na duk rintse duk wuya yana tare da ita ba abin da zai shiga tsakaninsu duk labarin gizo ne? 

 

A hankali wasu zafafan hawaye suka fara zubo mata ta durƙusa a kan guiwowinta , ta hada kai da guiwa ta soma risgar kuka, gaba ɗaya sai wannan ɗan son da ta fara ji akansa ya soma gushewa illa wani irin haushi takaici da wani abu mai kama da tsana da ta soma ji a kansa. 

 

Nadiya da tunda suka soma masayar yawu ta ke laɓe tana jin dukkan wani abu da ya faru ta yi tsalle ta dire cikin farin ciki, zuciyarta ƙal dan ba wanda ya kaita farin cikin mutuwar auren nan. Ta na jin Zaid ya gama magana ya fita ta fito daga wajan maɓoyarta, ido ta zubawa Nazli ganin yadda ta zauna sai risgar kuka take, ƙaramar ajiyar zuciya ta yi ta ƙura mata ido sai ta ji babu daɗi tunowa da saka hannunta fa shigan ta wannan hali, amma ko me ta tuna sai ta taɓe baki ta nufi wajan ta, a hankali kamar ba za ta ce komai ba sai ta cire hannu ta dafa ta a hankali ta bude baki ta ce. "Please Aunty ki daina kukun nan haka, aikin gama ya gama ke daina ɓata hawayenki da kuma lafiyarki a kan wanda bai cancance ki ba, duk girman laifin da za ki masa baki cancanci haka ba daga garesa, ai kamata ya yi koda hukuncin da zai yanke kenan sai a kai maganar gaban iyaye tukun, a yi komai ba wai ya yi cikin ƙasƙanci haka ba." Ta yi maganar ne daga ƙasan zuciyarta, tun da ta fara magana Nazli ta sausauta kukun na ta zuba kunne tana sauraran abin da take faɗi, tabbas haƙiƙanin gaskiya abin da Nadiya ta faɗa haka ne, amma babu komai ya riga da ya aikata abin da yake tunanin daidai ne a wurinsa, abin da ya aikata ya nuna cewa baya sonta a rayuwarsa ba ya son wata alaƙa a tsakaninsu dan haka me zai sa ta zauna tana ɓata lokacin ta da kuma hawayen ta a kan wanda bai damu da ita ba. 

 

Ta goge haywayenta ta miƙe ta shiga ɗaki, da taimakon Nadiya ta haɗa kayanta cikin trolley, duk wani abu na buƙatun yau da kullum ta ɗauka. 

 

Kasancewar tare da Nadiya ta zo gidan ya sa ita ma bata ga ta zama ba ta haɗa kayanta, duk da halin da take ciki haka ta tuƙa su gida. Tun da suka shiga street ɗin gidansu bugun zuciyarta ya ƙaro, ga tashin hankalin da ya bayyana ƙarara a fuskarta, koda suka isa horn ta danna mai gadi ya buɗe masu gate ta danna hancin motar ciki. 

 

Lumshe ido ta yi tare da ɗaura kanta kan sitiyarin motar, ba abin da jikinta ke sai kyerma, bata san ya za ta je ta fuskance su ba, ita kanta ganin abun ta ke kamar a almara da take son gagguata farkawa don wannan ko cikin mafarkai munmuna ne. Bata san kuka ta ke ba sai da Nadiya da ita ma jikinta ya gama yin sanyi ganin ta cikin wannan yanaye ta dafa ta, kana a hankali ta ce.  

 

"Please Aunty ki daina kukun nan haka, komai da kika ga ya faru da bawa to yana cikin kundin ƙaddarar sa ne, walau alkairi ko akasinsa." Bata ce komai ba illa kai da ta gyaɗa mata, kunce sitebelt ta yi ta sauka, Nadiya ta mika mata ruwan gora ta wanke fuskarta da ta kunbura abunka da farar fata har ta yi ja sabon kukun da tasha a yau. Da fargaba da tsinkewar zuciya ta nufi ciki Nadiya ma da zuciyarta sai bugowa take ta mara mata baya, tunanin abin da zai faru take, ko tace zai sake faruwa, duk da ta san Auntyn ta ƴar lelen Babanta ce da komai ta yi daidai ne a wajansa saboda son da yake mata, sai dai a wannan gaɓar tana tantamar haka, domin a idanunsu da yardarta hakan ta faru ba su san tugu bane daga miƙiya da ke son ganin bayanta da kuma son raba soyayyar uba da 'ya ba. 

 

Main falo suka shiga, sai dai ba su tadda kowa ba sai ma'aikantan da ke zarya suna shawagi, suna ganinta suka soma gaisheta sai dai bata da nustuwar amsawa. Wani siririn corridor da ke kusa da staircase suka shiga wanda zai fito da kai a wani ƙaton part mai zaman kansa, babban falo ne da ya ji kayan more rayuwa, duk wani kayan zamani da sauƙaƙe rayuwa akwai sa a ciki. 

 

complete part ne mai ɗauke da ɗakuna uku, da kuma kitchen sai kuma wurin motsa jiki, a ɗayan ɓangren kuma wata ƙofa ce da za ta fitar da kai ga lambun gidan gefensa kuma swim pool ne da kuma runfuna na hutuwa. 

 

Duk wanda ke cikin gidan to ya kwana da sanin wannan part ɗin Nazli ne da ke cikin gidan, babu mai shiga wurin sai Daddy da ma'aikata da suma suna gama aikin da za su yi suke barin wajen. Waje ne da a ka gina da sunanta , guri ne na musamman da a ka gina da kuma irin tsarin da ta ke so. A cewar Daddy koda 'yarsa ta yi aure ta haihu to tana da babban guri da kuma matsayi a gidan, shi ya sa ya ware mata nata gudun kar a takurata domin farin cikinta da jin daɗinta shine na sa. 

 

Har da kitchen na ta a part ɗin sai ta ga dama take fita babban falo, ko shi daddy wani lokacin idan ya so keɓancewa da yarsa baya son kowa ya dame su ya kan shiga su yi spending lokaci sosai suna hira, ya na tambayar karatunta da kuma hira irin ta baba da 'ya wanda ke matuƙar  ƙaunar juna. 

 

Kan ɗaya daga cikin kujerun palon ta zauna har ma'aikatan gidan suka gama shigo masu da kayansu. ta nuna ma Nadiya ɗakin da ke oposite na ta ta ce. "Za ki iya anfani da wacan ɗakin, idan kina da buƙatar wani abu za ki iya mini magana." Daga nan ta ja na ta trolley ta shiga da shi ciki ɗayan ɗakin, da yake Nadiya bata taɓa zuwa part din ba kasancewar duk zuwan su a iya main falo suke tsayawa har su koma gida so bata san da zaman wannan guri da ya gama ƙawatuwa ya gama tafiya da imaninta. Sake jinjina soyayyar Nazli a zuciyar mahaifinta take, ashe duk inda take tunanin son sa a gareta ya wuce nan. Bayan gama kalle–kalle da kuma taɓe taɓe ta ja na ta akwatin ta shiga ɗakin da a yanzu ya zama mallakinta, sai ta ji wannan part ɗin har ya ma fi babban side din ƙawatuwa ga shi dai bai kai wancan girma ba amma kuma irin tsari da kuma dukiyar da a ka narkar sai ya saka ka tunani duk da wancan din ma ba daga nan ba wajen ƙawatuwan. 

 

**** 

 

Ɓangren sauran ƴan gidan kuwa duk suna cikin ɗakunan su, Daddy ya kulle kansa tunda suka zo ya shiga ya kulle ƙofa ba wanda ya sake jin ɗuriyarsa, Mommy dai ta zo ba sau ɗaya ba tana leƙansa sai dai babu dama don ya rufe ƙofar babu damar shiga ciki balle ta ga halin da ya ke ciki, da ta gaji sai ta koma ɗakinta ita ma ba tare da neman abinci ba saboda halin da suke ciki to yunwar ma ba sai kana da nutsuwa kake bi ta kanta ba. 

 

masu aiki da sun zo tambayar abin da za'a girka a yau din kasancewar ita ke bada umarnin kalan girkin da za'a yi sai dai har suka gaji suka koma Mommy bata buɗe ƙofa ba, su kansu yau sun tabbatar da gidan babu lafiya musamman da suka ga hajiya ƙarama (Nazli) ta zo gidan da niƙin akwatina hakan ya sa kowa ya shiga taitayinsa suka koma na su part wato boysquter kar su cazawa kansu masifa. 

 

Neesah kuwa tun da suka rabo da Zaid ta shiga gidan ba ta nemi kowa ba kai tsaye ɗakinta ta shiga, ta yi wanka ta shirya cikin wasu arnan ƙananan kaya ta tsantsara kwalliya ta fita daga gidan ba tare da kowa ya sani ba. 

 

~~~~~~~ 

 

Shiru shiru har ƙarfi biyu babu wanda ya fito daga cikin iyayen, har uku da rabi babu alamunsu duk a ɗaki suka yi sallah, haka zalika babu wanda ya fito ya nemi abinci a cikinsu, hankalin ma'akatan gidan ba ƙaramin tashi ya yi ba dan haka bai taɓa faruwa ba kowa ya yi zugum tuna tsake tsaken me ke faru? Dan kuwa duk abin da zai saka Hajiya ta rufe kanta a ɗaki to babba ne, har sun fara tunanin ko a kira hajiya ƙarama ne sai kuma suka canja tunani tuna halin da suka ganta a ciki. 

 

Nazli kuwa tana shiga ɗaki ta zube a gado ta soma sauki ajiyar zuciya kamar wacce ta yi gudun tsire, gaba ɗaya jikinta ya yi mata nauyi musamman ƙasanta da har yanzu bai dena mata zugi ba, har yanzu ganin abun ta ke kamar almara, daɗinta ɗaya ma da bata tadda kowa shigowarsu gidan da bata san da wani idon za ta gansu. 

 

Kai dubanta ta yi kan agogon bangon ɗakin da ya nuna 1:47 a hankali ta miƙe ta cire hijabin da ke jikinta ta shiga banɗaki, ta gama uzurinta ta ɗauro alwala ta fito. Wardrobe ɗinta da har yanzu da akwai sauran kayayyakinta da bata tafi da su ba ta buɗe, ta fito da dadduma da hijabi ta tada sallah. Bayan ta iddar ta shafa fatiha ta sake miƙewa, jawo akwatinan da ta shigo da su ta yi ta buɗe kana ta soma jera kayanta cikin wodrobe ɗin. 

 

Tana cikin jera kayan ta ji knocking a ƙofarta, dalilin da ya sanya ta aje kayan da ke hannunta tana shirin sakawa a wodrobe ta nufi ƙofar ta buɗe, Nadiya ta gani tsaye hannunta riƙe da wani abu kamar wayarta da sam ta manta da babinta sabon bata cikin nutsuwarta da tunani mai kyau. Cikin murya mai sanyi ta ce. "Kina buƙatar wani abu ne Nadiya?" Nadiya ta girgiza kai ta ce. "A'a Aunty, wayarki ce na kawo ɗazu kina bacci Yaah Zaid ya bani ita wai cikin ma'aikatan hotel ɗin ne suka bashi suna tunanin na ɗaya daga cikin baƙin da suka halacci taron." Ta faɗa hakan ba don iya gaskiya maganar ba kenan. "Okay thank you." Iya abin da ta ce ta ƙarbi wayar ta koma ciki ta cigaba aikin da ke gabanta, ganin haka ita ma Nadiya ta juya za ta koma palo, ta murɗe handle ɗin ƙofar ta tsaida ita.  

 

"Nadiya."  

 

"Na'am Aunty?" Ta ɗan ƙura mata ido tana nazartar ta kamar ba za ta yi magana ba sai ta ce. "Kin ce abinci kuwa?" Don ita ta manta da wata aba yunwa ma baki ɗaya tun gamuwarta da Zaid da abin da ya faru damuwa ta mantar da ita yunwar da ke nuƙurƙusarta. Kai ta girgiza alamar a'a, bata ce komai ba sanin ita ce dalilin rashin cin abincin na ta tun safe dan ta tabbata halin da ta ganta a ciki ne ya hana ta dafa komai a nan gidan kuma ba sanin ko ina ta yi ba bare ta shiga ta nema ma kanta mafita, sai ta ji tausayenta ya kamata sanin ita fa a ƙarƙashinta ta ke don haka cinta da shan ta kanta ya rataya. 

 

"Zauna ina zuwa." Shi ne abin da ta faɗa kafin ta fita, kai tsaye main falo ta fita sai dai shiru har zuwa lokacin ba wanda ya fito sai ƙaran AC da ke famlan aiki. Kitchen ta nufa ta soma buɗe tukwane ganin babu abinci ya sa ta buɗe gas a tsanake ta ɗaura indomie da ƙwai, ta haɗa shayi a kofi biyu kana ta jera a large tray ta ɗaura bread a gefe ta nufi part d'in ta da shi. Ta samo Nadiya har ta gama jera maata kayan cikin wodrobe ta na cikin gyara gado. A taƙaice ta ce. "Ki bar aikin nan zo ki ce abinci." Bata musa ba ta zauna dan dama yunwar ta ke ji babu halin magana ne ya sa ta yi shiru. "Nan gaba idan kina jin yunwa ki shiga kitchen ki ɗaura girki kar ki tsaya jiran sai an baki ko an maki ta yi."  

 

Ta faɗa hakan tare da ɗau cup ɗin shayi ta soma gurɓa a hankali ta tura ma Nadiya sauran gabanta, idanun Nadiya ne suka ciko da kwalla, ganin kulawarta a gareta amma ita ga abin da ta saka mata da shi. Ta kawar da kai gefe ta goge hawayen da ke barazanar kufce mata ta saka hannu ta soma cin abincin, tabbas haɗuwarta da Nazli alkairi ce. Tun farkon haɗuwarsu taimako ne sila gashi har yau suke kan moriyarta, dai dai da rana ɗaya bata taɓa mata tsawa ko faɗa ne bare hantara ko kyara akasin yadda Neesah ke kullum nuna mata ita ƙasƙantaciya ce mara galihu. Nazli kuwa a kullum nuna mata take babu banbanci a tsakaninsu babu wanda ya fi kowa sai wanda ya fi tsoron Allah, tana girmama mahaifiyarta haka tana kula da ƙaninta da a yanzu ba don Nazli ba za su saka shi cikin waɗanda suka riga mu gidan gaskiya. 

 

Ta musu rana a lokacin da kowa ya kuje su, lokacin da ba su da mafaka ba su da inuwar mafaka, sai Allah ya turo masu ita ta share masu hawayen da ko dangin da suka haɗa jini suka kasa masu, abin da Nazli ta yi masu a rayuwa koda duniya za su naɗe su bata ba za su taɓa biyanta da shi ba. Kasa haɗe abincin bakinta ta yi ta fashe da wani irin kuka da ya saka Nazli babu shiru ta aje kofin hannunta ta kalleta.....