6
Chapter.6
A ɗan ruɗe take tambayar. "Nadiya! Me ya faru me ya kawo kuka kuma a na zaune ƙalau?" Bata ce komai ba sai ƙara ƙarfin kukun da ta yi, hankalin Nazli ba ƙaramin tashi ya yi ba, tunani ta soma kodai an mata wani abu da bata so ne? Gaba ɗaya sai ta ruɗe ta manta da ta ta damuwar rabon da ta ga Nadiya na kuka irin haka tun lokacin da a ka gundilewa ƙaninta ƙafa,tunanin ƙanin na ta ne ya sa ta fad'in. "Khalifa ne ko jikinsa ne ya tashi?" Ta girgiza kai alaman a'a.
"To me ya sa ki kuka?" "Babu." "Kamar ya babu, haka kawai ki zauna ki soma kuka ki ce babu?" Ban yarda ba me ya faru?" Ta tambaya wannan karon babu alamun wasa a cikin muryarta, Nadiya ta goge fuskarta ta ja ajiyar zuciya a hankali ta ce.
"Na tuna su Mama ne ina son komawa gida." Nazli ta girgiza kai da wauta irin na Nadiya. "dan kina son zuwa gida sai ki zauna kina kuka ba za ki iya bud'e baki ki yi magana ba Nadiya?" Ta sake girgiza kai ta ce. "To karki damu dama ai kin ce min yau kike son zuwa, idan kin shirya ki min magana driver zai kai ki." Ta faɗa daidai sanda a ka masu knocking ta bada umarnin shigowa, Zulai mai aiki ce ta gaishe ta kafin ta ce.
"Hajiya Babba ke ƙiran ki." Dam! Gabanta ya faɗi, ta yi shiru kamar ba za ta yi magana sai kuma ta ce. "Tom ina zuwa." "To Uwar masu gida." Zulai ta faɗa tare da jan kofar ta fita.
Kallon Nadiya da ita ma na ta idanun na kanta ta kasa magana, wata sabuwar fargaba ce ke ziyartarta kamar ta tashi ta kulle ko ina ta boye kanta daga kowa da komai sai dai ta san babu hali hakan ba mai wuya bane, a hankali ta miƙe ta saka hijabi tare da bude bedside drower inda ta saka takardar sakin da Zaid ya bata ta ɗauka kana ta fita.
MOM.
Ganin zaman cikin ɗaki ba zai fishe ta ba ya sa ta tashi ta watsa ruwa ta saka kaya ta fita, kai tsaye kitchen ta nufa, turus ta yi ta tsaya ganin ba abin da ka a ɗaura na abinci. Cikin ɓacin rai da take ciki ta soma kwalla ma masu aiki ƙira ta soma bambami kamar za ta ari baki.
"Wani irin iskanci da lalaci ne wannan, yau weekend sarai kun san Alhaji na nan amma saboda sakarci ko tukunya ba ku ɗaura ba, to wa kuke jira ya ɗaura maku?" Duk cikin ɗaga murya take magana sai duk sun kasa motsi sun gume guri guda sai ban haƙuri da suke bata duk da ita ce da laifi ba su ba tunda sai ta ba su go head suke iya tabuƙa komai a kitchen ɗin, amma ganin uwar dakinsu a haka ya sa su yin shiru kar su jawa kansu dan da gani yau a wuya take tana neman wanda za ta juyawa bambamin bala'i da ke nukurkusar ta, a cewarsu.
"To me na zuba min na mujiya kuna kallo ko sai ya fito ya ga ba a gama komai ba?" Gaba ɗaya kun lalace ba abin da kuka sani sai sakarci idan ba'a ce ku yi abu ba za ku yi hankali ku yi abin da ya dace ba." Ta yi maganar tare da fiddo masu da kayan miya da za su yi anfani da, ta buɗe deep freezer ta cire nama da ganda ta aje masu kana ta ce. "Yau miyar ɗanyar kuɓewa za'a yi." Ta juya ta kalli Zulai da ke nuƙu nuƙu da kai tana son magana amma bata ga fuskan yin hakan ba. "Ya dai?" Me ya faru, akwai abin da ya kamata na sani ne?" Cikin rawar jiki Zulai ta russuna ta ce. "Ehh Hajiya, dama Hajiya ƙarama ce ta zo ɗazu kuna bacci na san ba lallai bane ki sani."
Cak Mom ta tsaya da ɗauraye tukunyar tuwo da take ta zuba masu ido ɗaya bayan ɗaya kafin ta ce. "Nazli?" Yaushe kuma ina take yanzu?" "Ai tana ɓangaren ta Hajiya, tun ɗazu suka zo kuma da manyan akwatina ta shigo da gani zuwan kenan babu komawa." Mom ta murtuƙe fuska ta kalli y'ar aikin da ta yi maganar cikin sigar gulma da alama ta manta da wanzuwar Mom a wajen take son yin gulma, da sauri ta sunkuyo da kai cikin rawar murya ta ce. "A gafarce ni Hajiya subutar baki ne amma ba abin da na ke nufi ba." Mom ta ja kwafa tare da maida kallon ta kan Zulai ta ce. "Kin tabbatar Nazli ce kodai Neesah kike nufi?"
Cike da tabbatarwa ita ma ta ce ehh. "Je ki ƙira min ita." Shi ne abin da ta faɗa ta juya kan sauran da suka kasa kunne suna jin abin da ke faruwa. "Ku kuma me kuke jira da ba ku fara aikin ba?"
Ta fito masu da dukkan abin da suke buƙata kana ta fita palour ta nemi kan sofa ta zauna, a hankali take kaɗa kafa tana jiran zuwan Nazli ta ji ba'asin dawowarta gida a wannan lokaci, a zuciya kuwa fata take ba abin da take zargi bane ya faru.
Tana nan zaune Zulai ta zo ta sanar da ita zuwan Nazli hannu kawai ta ɗaga mata ta tashi ta koma kitchen, mitina ƙalilan a tsakani sai ga Nazli ta shigo da sallama a bakin ta.
Zuba mata ido Mom ta yi tunda ta shigo take binta da wani irin kallo da ita kaɗai ta san ma'anar fasararsa, idonta na kanta har ta karasa shigowa ta nemi waje a ƙasa kusa da ƙafafunta ta zauna. Zamanta ya yi daidai da fitowar Dad daga ɗakinsa, sanye da jallabiya fara hannunsa riƙe da carbi yana ja a hankali.
Ganin wacce bai yi zato ko tsammanin gani a lokacin ne ya sa ya ja ya tsaya ba tare da ko wanne daga cikinsu ya lura da fitowarsa, Mom ta kalli Nazli a karo na ba adadi ta ce. "Ke kuma lafiya kika dawo gida?" Ta yi maganar cikin jefa mata wani kallo da ke ƙunshe da ɓacin rai takaici da kuma haushi, ba tare da Nazli ta yi magana ba ta miƙa mata takardar sakin wanda ita ko buɗewa bata yi ba bare ta san me ya rubuta da kuma adadin sakin da ya yi mata. Mom ta dafa bakinta da sauri kana cikin rawar murya da buguwar zuciya ta ce.
"Wannan takardar me cece haka?" Duk da hankalinta da tunaninta sun riga da sun tabbatar mata da abin da ke faruwa amma bata son yarda, ta san duk abin da zai je ya dawo Zaid ba zai taɓa mu su haka ba yaro ne mai hankali da nutsuwa wanda ya san ya kamata. Duk da a wannan gaɓar ƴar ta su ce bata da gaskiya amma akwai wani ɗan ƙaramin hope da suke da shi a kansa, ba tare da ta jira me za ta ce ba ta buɗe takardar sai dai tun kafin ta gama karantawa idonta ya cika da kwalla ta soma furta. "Innalilahi wa'inna ilahir raji'un." Ai kamar Nazli na jiran waɗannan kalmomi su fito daga bakinta ta ɓarki da wani sabon kuka har da sheshsheƙa.
A hankali Dad da shima jikinsa ya yi sanyi ya tako cikin palon ba tare da sun lura da shi ba ya karb'i takardar daga hannun Mom ya soma karanta rubutun da ya bayyana saki ɗai ɗai har uku lokaci guda a bisa kamata da laifin tarayyah da wasu maza, inda a ƙarshe ya ƙaƙare da saƙon ban haƙuri ga su iyayen. Shiru Dad ya yi ya zubawa takardar ido kamar hannun da ya yi wannan rubutun zai fito ya goge tare da ɗau nauyayyon kalaman da ke kunshe a ciki, wani irin zafi ya ziyarci zuciyarsa amma bai ce komai ba ya zaga ya zauna kan kujera. Ya kalli Mom da ita ma ke jimamin abun ya sauke idanunsa kan Nazli da ya ke jin kukunta har ƙasan zuciyarsa.
Ya cire wayarsa daga aljihu tare d latsawa Zaid ƙira, sai dai har wayar ta ƙarashi ringing ba'a ɗaga ba ya sake gwada ƙira, a ƙalla sai dai ya ƙira sau uku a na huɗu ne a ka ɗaga Dad ya saka wayar a handsfree yadda kowa ke jin muryar Zaid ta ɗayan ɓangaren.
"Abba barka da warhaka." Zaid ya faɗa cikin girmamawa kamar yana gabansu, shima ya amsa kamar babu wani abu a kasa kafin kai tsaye ya daura kan dalilin kirin na sa ya ce. "Dama kan maganar ka da Nazli ne, ta zo mana da wani batu mara dad'in ji muna son sanin ya gaskiyar maganar?" Sai da a ka d'auke sakanni har suka cire ran zai magana suka ji a sanyaye ya ce. "Dan Allah Abba ku yi hakuri da abin da na yi na san ban yi daidai ba, amma abin da ta fad'a maku haka ne babu karya a ciki ina ganin hakan shi ne ya fi mana alkairi a tsakanin mu."
"Amma Zaid baka tunanin ka yanke hukunci cikin gaggawa ba tare da kwakkwaran bincike ba?" na san abin da ya faru jiya ne ya sa ka yanke wannan hukunci amma ina mai tabbatar maka rashin fahimta ne 'ya ta ba za ta tab'a aikata abin da kake zargin ta da shi ba." Dad ya fad'a ba don shi kansa bai yarda da abin da ya gani ba mussaman yanaye da suka riske ta a ciki, sai da a wani sashe na zuciyarsa akwai wani kankanin yardarsa a kanta. "Ehh Zaidu, mun san da ciwo amma komai ya na da maslaha kuma gaggawa aikin shaidan yanzu ba damar gyara abun?" Cewar Mom. "Yanzu ma bata b'ace ba, idan har za'a bi wata mazhabar ma ai saki uku lokaci d'aya a matsayin d'aya ya ke. Amma da akwai buk'atar malamai cikin lamarin dan haka zan k'ira Malam Hadi sai ya k'ara mana fahimta idan da yuwar maida auren sai a yi kawai, ko ya kika ce Hajiya?" Daddy ya fad'a inda Mom ma ta bada goyon bayan ta ta hanyar d'aga masa kai, yana shirin katse kiran ya kira Malam Hadin ne suka ji Zaid ya ce.
"A'a Abba ba sai an kai ga haka ba, a gaskiya na zauna na yi tunani sosai kafin na yanke wannan hukuncin da nake ganin ya dace da mu."
Ban so sanar da ku abin da ke faruwa ba, amma ina ga ya zama dole ku sani saboda bana son na cigaba da shiga hakkin ku, na sani duk da son zuciyata ne ya jawo min amma abun da kuke tunanin haka ne ba shi ne ba." "Me kake nufi kenan Zaid?" Zuciyar Nazli ne ta tsinke jin ya na shirin tona mata asiri, ji take kamar ta shiga cikin wayar ta toshe masa baki ko zai yi shiru sai dai aikin gama ya gama ranar wanka ba'a boyen cibi, duk da ta yi nadamar abun amma yanzu lokaci ya kure mata ta rasa damar gyarawa. Suka had'a ido da Dad ta yi saurin sunkuyar da kai kasa ita kam yau ta kad'e har ganyen ta. Dad ya ce. "To Zaid akwai abin da ke faruwa a tsakanin ku ne da mu bamu sani ba?"
"Eh Abba, da ban yi niyyar fad'a muku ba amma ina ganin ya zama dole ku sani ko dan wanke kai na a gun ku ku dai na ganin laifi na. Allah ya ga zuciyata na so Nazli da zuciya d'aya, duk da kin ta a gare ni bai hana kullum sonta ninkuwa a zuciyata ba. Sai dai na yi iya k'ok'arina na ganin na saka mata so na a ranta koda k'ank'ani ne amma sam bai yuwa ba saboda akwai wanda take so ba ni ba. Duk iya zaman da muka yi na d'auka ta soma jin wani abu ne a kaina duk da har lokacin bata canza zani ba na irin zaman da muke yi sai dai abin da ya faru jiya shi ya sake tabbatar min Nazli bata sona kuma ba za ta tab'a sona ba saboda tana da Wanda take so." nan ya soma labarta masu irin zaman da suke cikin gidan, daga zuwan ta gidan ta gindaya masa sharud'a ya yake kuma bi ba tare da Musa ba bai boye masu komai ba hatta raba daki da suke sai da ya fad'a.
Tunda ya soma magana palon ya yi tsit sai muryarsa da ke tashi ta cikin wayar, jikin Nazli ya soma kyerma ta matsa can gefen kujera ta rakube ta san ita kam yau sai Allah. An ce labarin zuciya a tambaye fuska tun daga yadda ta ga yanayen fuskarsu ta sauya daga mamaki al'ajabi zuwa tsantsan b'acen rai ta san babu mai lallashin ta bare sauraron ta. Masu iya magana suka ce, Juma'ar da za ta yi kyau, tun daga narba Ake gane ta!
Dad godiya ya yi wa Zaid ya katse kiran, ya ma rasa me zai ce sai zuba mata ido da ya yi yana tunanin abin da zai saka ta yin haka. Idan bai manta ba da kanta ta kawo masa batun son aure duk da a lokacin bai amince ba saboda shi a ganinsa har yanzu yarinya ce tana da buk'atar maida hankali kan karatun ta dan yana da buri sosai a kanta yana son ta yi karatu mai zurfi ta yi achieving d'in duka goals d'in ta kafin a zo kan batun aure. Saboda dagewar ta kan batun sai ya yi tunanin k'illa da gasken take buk'atar auren afterall macece ita tana da desires dalilin da ya sa bai zurfafa ba ya bata abin da take so. Ba zai manta ba a na washe garin d'auren auren ma ya k'ira ta d'akinsa a sirrance ya sake tambayar ta kan ta fad'a masa idan tana jin bata son auren shi mai goyon bayan ta ne kar ta ji shayin komai amma ta nuna ita aure take so.
Yanzu da ya ke kallon ta sai ya ga ta ma raina masa hankali ta zubar masa da mutunci, duk yadda ya yi tunanin dalilinta na aikata hakan bai samu amsa ba.
Mom kuwa ba komai bane ya fad'o mata ba sai stain d'in jinin da ta gani a lokacin da suka shiga suka ganta, duk da hakan ya saka ta tunani amma bata zurfafa ba sanin ita macece akwai lalura ba lallai ya kasance abin da take tunani bane. Sai yanzu komai ya soma zama a kwakwalwar ta.
Cikin mutuwar jiki Dad ya ce. "shin abin da ya fad'a haka ne?" Ja baya ta soma tare da girgiza kai dan wani irin tsoronsa ne ya d'arsu mata zuciya lokaci guda ganin abun da bata taba gani a idanunsa, wato haushi ɓacin rai da kuma tsantsan nadama, tsawar da ya daka mata wacce ba ita ba har Mommy sai hanjin cikin cikinta suka motsa Nazli ta kusan sakin pisari a jiki. Murya na rawa ta ce. "e..e.eh." ya runtsa ido da karfi cikin wani yanaye ya ma kasa furta wata magana, Mom ce ta samu karfin halin faɗin.