HAYAT NAZLI

7

by @maryamannour71


Chapter. 7 

 

"Ai na ɗauka wanda ya fito ya ce ya na sonka to ya fi wanda ya ce bai sonka." "Dad Mom dan Allah ku yi haƙuri fahimce ni wallahi ba niyyar na aikata abin da kuke tunani ba, ni kai na ban san ya hakan ta faru ba kawai tashi na yi na ganni cikin wannan yanaye, ban farga da abin da ya faru ba ku ka same ni amma ku kun sanni, Dad kan san irin tarbiyyar da ka bani ba zan taɓa aikata abu makamancin haka da son zuciyata ba please believe me." 

 

"Wace yarda za mu kuma baki bayan wacce muka baki a baya ki ka watsa mana kasa a ido, kasan ma mai tsakuwa, ashe idan so da gata ya yi ma mutum yawa shima illa ne?" Ban tab'a miki fad'a kan duk abin da kike ba saboda ina ganin yarinta ke ɗawainiyya da ke da kin girma kin san ya kamata za ki gyara ashe ashe ban san abun na ki gaba ya ke ba baya ba. Kenan da Allah bai nuna mana jiya mun gani da idon mu ba da haka zamu yi ta zama cikin duhu."  

 

bawon Allah Zaidu yaro me hankali da nutsuwa Allah kaɗai ya san irin abun da kike aikata masa amma d'an albarka koda wasa bai tab'a nuna mana koda a fuska ne kullum na tambayesa ya zaman ku ya ke sai ya ce kuna lafiya babu wata damuwa ashe shi damuwa ta zamar masa ruwan sha." 

 

Nazli ta ɗaura hannu a kai ta rasa da wani irin yare za ta masu da su fahimce ta su yarda da abin take fad'i su bata dama ta ganar da su amma kamar tunzura su ma take yanzu da Zaid ya yi magana kam bata da wani hope d'in za su yarda da ita, yanzu babban tashin hankalinta ma shirun da Dad ya yi ta san sakamakonsa bai zai yi mata kyau ba. 

 

Suna cikin wannan hali Nadiya ta fad'a da gudu cikin palon hannunta rik'e da wayar Nazli da ke ring ta mika mata, Nazli bata ko kalli inda take ba hankalin ta na kan Dad tana jirin abin da zai ce, har wayar ta tsinke wani kiran ya shiga Nazli bata da niyyar amsar wayar hakan ya sa Mom karb'an wayar ta duba. Da tsantsan mamaki ta furta. "Suger?"  

 

Furucin da ya saka Nazli da Abban ta kallon ta suma da mamaki a fuskokin su barin ma ita Nazli da ta fad'a tunanin waye wannan kuma da ta ji Mom ta ambaci sunan sa, sai dai bata fita daga mamakin ba Mom ta nuna masu screen d'in wayarta da sunan Suger Daddy da ya bayyana barau barau alamun an san da number tunda har saving d'in ta a ka yi. Ganin kallon da suke bin ta shi ne ya sa ta saurin girgiza kai alamar ba ta san ko waye ba. Ba tare da yin wani tunani ba Mom ta danna pick ta saka a hands free. "Hey sweet love ya na ji ki shiru ne daga cewa za ki kira ni idan kika gama settling d'in kurar da ke gabanki amma ba ki kira ba yanzu miss call nawa na miki amma ki ka kasa dagawa?" wait karki ce min saboda wannan so call husband na ki ya sa baki neme ni ba?" 

 

Cikin sauri Nazli ta mike bata san ya aka yi ba sai ganinta ta yi a gaban Mom ta kwace wayar ta soma magana a zafafe. "Hy who are you?" Ina na san ka kuma daga ina ka samu wannan number?" "Ohh love, ni yau kike fadawa ina kika sanni?" Har kin manta da soyayyar mu you forgot what we have, wait don't tell me kina tare da that so called husband of yours ne than I will understand. Ko kin manta the romantic night we share last night sweetie am so happy kin sa na ji dadi sosai. Please i can't wait yaushe zamu sake haduwa ne?" Wait karki ce ba za ki samu damar fita ba kawai zai na zo har can gidan ki ba kamar yadda muka saba inda wancan sokon mijin na ki baya nan" Ya fad'a cikin shakiyanci ya na dariya, a zafafe murya na rawa da dumbin tashin hanakli da ya ninke wanda ta ke ciki ta ce. 

 

"who the fuck are you!, ka bayyana kanka mana idan ba tsoro ba, yaushe na sanka ina na taba ganin ka?"ka ji tsoron Allah Why are you lying on my head me na maka me kake so daga gare you stupid idiot!!  

 

Ta ƙare cikin muryar da ke bayyana tana gab da yin kuka dan har ta soma hawaye, wannan wani irin masifa ce ke bibiyar ta? Daga wannan sai wannan. "Okay let pretend baki sanni ba, but I hope baki manta alkawarin haduwar mu a yau ba ko because babe i so much miss your warmth andd...ba sai na karasa ba kin san me na ke nufi ai, the love we share ji..."  

 

Ina bata ma jira jin me za ce ba ta yi kukun kura ta yi wurgi da wayar nan take ta faɗi ai sai ga wayar da a ka saka makudan kudade wurin siyan ta ta waste ta yi kaca-kaca a wajen. 

 

Bata tsaye a nan ba ta soma tattakata ta sai fad'i take. "Lies lies lies! I said i don't know, ban sanka ba ban sanka why are you lying." Gaba d'aya fa ta fita a hayyacin ta kamar zararriya haka ta koma, Mom ce ta yi k'arfin halin mikewa ta kamo ta ta soma girgiza ta. "ke me haka!" Ki nutsu mana me haka kike?" Amma ina Nazli bata ko jinta dan  ba ta ita take ba a yanzu burin ta Dad ya yarda da ita tana son ta ji muryarsa koda zagin ta zai yi ko duka ne idan zai sauko ya saurare ta to duk wani abu da zai biyo baya me sauki ne. 

 

 Ta zame hannayenta daga riƙon da Mom ta yi mata tare da nufan Dad da gudu ta rik'e kafansa ta soma magana. "Dad na san you trust me ko babu wanda ya yarda da ni, ka san abin da zan yi da wanda ba zan iya ba, please punish me ta ko wacce hanya ce if you would but dan Allah shurun ka nan haka yana kashe ni talk to me Dad ai ka san abin da zan yi da wanda ba zan yi ba, please ka yarda da ni." 

 

Sai dai zafafan maruka da suka sauko a kuncin ta ba zato ya sa yin baya ta zauna d'abas a k'asa dafe da kuncinta, ba ita ba, hatta Nadiya da ita Mom kanta sai da suka shiga wani irin shock da abin da ya wakana. 

 

A dukkan tarihin rayuwarta, ba za ta tab'a iya cewa ga rana kaza da Dad ya tab'a daga hannu da niyyar taba lafiyar jikinta, kai ita fa ko fada zai mata to da laluma cikin nustuwa ya ke nuna mata kuskurenta, sai ga shi yau ta kai shi bango har ya iya ɗaga hannu ya marita, lallai abun ya fi karfin tunanin su. bata gama fita daga wanana mamakin ba ya sauke mata wasu zafafan marukan da sai da ta ga taurarai, shuuuu! Haka ta ji gaba daya jinta da ganinta saida ya dauke na wucin gadi. Sama sama ta ke jin muryarsa ya na fadin. "Ni za ki zubarwa da mutunci a gari?" Da mutuncina da ƙimata da abin da za ki saka min kenan?" Me kika nema kika rasa in ce auren nan ke kika same ni da shi na kuma biye miki na baki abin da kike so duk da rai na bai so hakan ba amma don faranta maki na yi hakan, dama zaman auren da ki ka je yi kenan ina nan na bud'e baki da hanci ina k'afafan wai ni na aurar da 'ya ashe abin da ki ka je shukuwa kenan?" Yanzu da ki ka tattara kayan ki kika zo min gida me kika zo yi min?" 

 

Ya ja numfashi kirjinsa sai sama yake ciwon hawan jininsa na gab da  tashi dan da kyar ma ya ke jan maganar daga bakinsa, ya kad'a yatsa ya nuna mata hanyar kofa ya ce. 

 

"Ki had'a ina ki yana ki ki bar min gida ba na son sake ganin koda inuwar ki ce a kusa da gidana. Ni Alhaji Muktar Ɗan Maraya na cire ki daga ahalina ban son sake ganin ki kar ki sake nuna min fuskarki idan ba ba haka ba, ranki sai ya yi mummunan b'ace. daga yau bani da 'ya mai suna Nazli." Ya kalli Mom da Nadiya wanda har yanzu mamakin abun da ya faru bai gama fita daga jikinsu ba ya ce. "Ku shaida da ga yau babu me sunan Nazli cikin a ahalina bani da ya me wannan sunan, na cire ki daga jeren 'ya'yana, kar na kuma koda inuwar ki ce ta kusanci iyalina ku je wajen waɗan da kika zaɓi ɓata min da kuma tsabawa ubangijin ki akansu su zame maki iyaye da yan uwa, amma ni Muktar bakya cikin ahalina." 

 

Yana kaiwa nan da maganarsa ya nufi k'ofa zai fita Nazli ta rik'e kafafunsa sa kamar za ta shide saboda kuka tana fad'in. " Dan Allah Dad karka mun haka kar ka juya min baya idan ka yi min haka mutuwa zan yi, am sorry ka yafe min ka gafarce ni ka yanke min ko wani irin hukunci ne ne I will accept it amma ban da wannan ba zan iya ba ba zan iya d'auka ba, zan iya matuwa idan ka yi min haka Dad don son ka da Annabi Dan ma'aiki karkawa 'yarka haka idan har kai ma ka iya juya min baya a wannan lokaci ina zan tafi waye zai amshe ni idan kai da ka kawo ni duniya ma ka iya juya min ba?" Dan Allah ka yi hakuri ba don halina ka yafe ni, ina zan saka raina na ji sanyi, dan soyayyar ka da Annabi kar ka min haka."  

 

Idan har zuciyar imani ce gare ka a wannan lokacin sai ka zubda kwalla sai ka tausayawa Nazli koda zuciyarka dutse ce to sai ta motsa, baiwar Allah cikin wuni guda ta zabge ta fita hayyacinta ba abin da ke tashi sai gujin kukunta da ke tashi. Shi ne silar haduwan gaba d'aya ma'akatan gidan zuwa suna kallon wannan iko na Rabbi suna tunanin abin da zai saka Daddy d'au fushi irin wannan da har ya ke ik'iraren ta bar masa gida. 

 

Duk yadda ya so kwance k'afarsa ya fita tun kafin zuciyarsa ta raunana ya sauke kalamansa ba tare da ya shirya ba amma ina ya kasa saboda yadda ta yi anfani da dukan k'arfin ta ta yi masa rik'o bana wasa ba.  

 

Murya a kaushashe ya ce. "ki sakar min k'afa na wuce." Bata sake shin ba sai ma k'ara rik'on da ta yi tana fadin. "To ka janye maganarka?" Ka yafe min?" "Nazli! Ki sakar min k'afa tun kafin ranki ya yi mummunan b'ace." 

 

"Dan Allah Daddy ka dube ni da idon rahama kar ka hukanta ni da laifin da ban aikata ba bani da masaniya a kai yadda kuka gani haka nima na farka na gani, wallahi mutuwa zan yi ba zan iya rayuwa babu kai ba." 

 

"Wallahi idan baki sakar min k'afa ba sai na tsine maki." Ai da sauri ta sakar masa k'afa ta yi baya tana kallo ya haura sama ba tare da ko waiwayenta ba, zuciyarta ta karye ba su ankara ba ta sulale a wajen sai kawai gani suke yi ta fad'a wurin bata numfashi. "Nazli!!