JODAH

19

by @sadisakhna

m

 

______👑 *JODA* 👑_____ 

 

              

Na  

 

*Sadi-sakhna* 

 

Ƴar mutan Jama'are 

 

 

THE TRIO OF TALES  

(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)  

 

 

@sadisakhna on Arewapen 

@SAKHNA03 On Wattpad 

*** on Whatsapp 

 

 

LITTAFI NA 1 

 

 

👑*Warƙa ta (19)*👑 

 

 

"Miye wannan hammar mai wannan takardar da aka bani take nufi,kafi kowa sanin menene mafarkina menene burina,amma meyasa zaka saka ayimin haka saboda son kanka da biyan buƙatarka. Iya kulada kai ina matuƙar ƙoƙarina,to amma meyasa sai nabar dukkan mafarkaina saboda kai, meyasa Hammar?" 

 

Ina kuka nake faɗin maganganun,ganin bazai kaini ba yasa na wurga masa takardun,duk abinda nakeyi ko gezau bayyi ba,ballantana ya nuna hankalin sa ya tashi. Mutum mai irin wannan yanayi haka taya ciwon zuciya yakamashi,koda yake bai taba faɗamin komai dangane dashi ba bayan sunansa kaɗai. 

 

Saida nayi kuka na na ƙoshi na fara sheshsheƙa kafin ya miƙo min ruwan dayake gefensa,karba nayi nasha sosai kafin na ajiye kofin. 

 

Ɗaukar takardar yayi saida ya karanta rubutune na ajami,da akayi da wassulan larabci,wanda yake nuna rubutun Guru al'azhar ne babu makawa,an koreni daga gasar kuma nakoru kenan. 

 

"Banine maƙasudin korarki daga gasar ƙiraan ba Joda,koma nine amma ba kai tsaye ba. Ko kin manta kwananki uku kenan baki ziyarci majalisi ba,hankalinki yana kaina saboda kinason ƴan ci,sannan gefe ɗaya kuma kinason Ɗaukaka,meyasa kikeda zalamar haɗa biyu ke kaɗai? Wannan baban dayake nan bangaren maganin shine yasaka aka cireki,saboda yanaso ki ƙware a bangare ɗaya, baki gama karanta takardar bama da alama da kin lura da saka hannunsa akai" 

 

Fizge takardar nayi naƙara karantawa,tabbas baba almahdi ne yasaka aka cireni,to amma miyasa,naga nace masa zanyi iya dukka,miyasa zai saka a cireni?. 

 

"Saboda ki kulada ni sosai kisamu kyautar ƴan ci,sabani ki raba ƙafa biyu baki samu dukka ba," 

 

"Niba dolene saina ci gasa ba,inaso nayi nasara amma idan banyi bama ko banza zan tsira da ilimin da ake koyarwa a wajen,idan ina matsayin baiwata baza'a koyar dani irinsa ba,shiga gasar zai bani damar koyon abubuwan danakeso. Kai bawane mai gata sam bazaka gane hakan ba koda nayi maka bayani. Tunda na buɗi idona a wannan nahiyar nagane cewar babu abinda zai samamin daraja sai nasamu ilimi nakuma ƙware a wani abu dazai amfani al'umma komin matsayinsa yana neman wannan abun.  Mahaifina ya rasu anyi masa binnewar mushe,mahaifiyata bansan a wanne hali take ciki ba,wanda nasamu a sama taka ina rayuwa dasu sune suka ragemin,kuma a yanzu yawanci sun dogara akaina ta hanyar duba lafiyarsu dakuma ƙokarin tsaya musu akan haƙƙinsu. Abubuwan da akewa bayi na zalunci bazai taba ƙarewa ba matuƙar ba'asamu mutum ɗaya dazai tsaya ba,wannan mutum ɗayan nakeson zama. Idan kuwa hakane taya kake ganin hankalina zai kwanta?" 

 

Harna gama bayanin ya zuramin ido yana kallona,wannan karon naga alamun maganganuna sun shiga ransa sosai. Yayi kaman bazayyi magana ba sai daga baya yace. 

 

"Bakya bukatar cin gasar ƙiraan a cimma wannan burin,ko yanxu kina dauke da ilimi mai ɗumbin daraja wanda kowa komai matsayinsa zai nemi wannan ilimi naki a gareshi,shine ilimin kiwon lafiya. Sannan kinada basira dakuma kaifin hankali,in kikayi amfani da wannan abubuwan dakike dasu zasu kaiki inda bakya tsammani.  

Wajen gasar ƙiraan ba wajene na gasar mace ba,saboda mataki mataki ne kuma yanada matuƙar hatsari,akwai gwaje gwaje a cikinsa da mace bazata iya ba,shiyasa a tarihi ba'a samu macen data ci ba. Kuma bama iyawarne bazayi ba ko kinci baxasu baki matakin farko ba saboda dayawa daga cikin matasan wajen masu shirin zama sarakuna ne aka turosu domin su ci wanann gasar a matsayin gwajinsu na zama sarakuna. Yanzu kika gama faɗin cewar ana rashin adalci ga bayi,kinga kuwa hakan bazai bari a baki sakamako daidai da abinda kikayi nasara akai ba koh?" 

 

Nazarin maganganun nasa nayi kuma fah haka ne,suda idan bamuda lafiya baa mana magani yanda ya dace,sannan idan aka zaluncemu babu mai waiwayarmu sune idan na dage naci gasa zasu bani haƙkina. 

 

"Barinki wajen shine abinda yafi alkhairi,duk lokacin dakika nuna cewar kina ƙwazo da ilimi a lokacin zakiga maƙiya sun tammaki haiƙan sun kawar dake daga wajen" 

 

Dukka dai zancensa hakane,duk da inason nayi masa musu amma kuma gaskiya yake faɗa. Numfasaw nayi daga ƙarshe kafin nace. 

 

"Shikenan zancenka hakane tabbas wajen yanada haɗari duba da yanda yatara ƴayan sarautu wanda basusan Tausayi ba ga talakawa kokuma bayi. Na haƙura zan jira Allah yakawomin mafita, ko kuma idan Allah yabani sa'a nasamu ƴanci zan shiga duniya nemo ilimi" 

 

"Wani hanzari ba gudu ba,zaman mu kina jinyata mai zai hana nafara koyar dake litattafan da ake a majilisin,harma da Shari'a da dabarun sarauta idan kinaso dukka zan koya miki,da sharaɗi zaki dawo gabaɗaya kina kula dani,in kin fita to saida uzuri mai ƙarfi" 

 

Wani kallo nayi masa na kasan mai kake fada kuwa,ya kulada hakan sai yayi murmushi tareda daukar takarda da kuma alƙalamin dayake gefensa. 

 

Rubutu yake tayi har na tsawon wasu daƙiƙu kafin ya miƙomin. Karba nayi ina karantawa jerin litattafai ne sun fi hamshin ya rubuta sunyayensu da kuma marubutansu,ɗagowa nayi na kalleshi da buƙatar ƙarin bayani.  

 

"Duk wani littafi da kika gani a wannan waje na haddacesu kaff a cikin kaina,banda waɗanda nake kan karantawa kokuma wanda ba hadda nayi musu ba sukuma ban rubutamiki su ba. Tun ina yaro banida wani lokaci saina bincike dakuma karatu,babu wanda yasan da wannan bangare nawa sai mariƙiyata saikuma ke da yanzu na faɗamiki. Duk wannan karatun danayi ko kaɗan ban taba cin karo da wanda nasa ilimin ya burgeni ba sai ke. Ni ina karanta ilimin ne saikana da lafiya zaka buƙata,sai gashi kekuma kina da ilimi ne da in bakada lafiya zaka buƙata,saboda duk tarin ilimina bazai amfaneni da jinyar danake fama da ita ba,dole saina nemi taimako daga gareki wanda a da nake ganinsa tamkar ilimi marar Daraja. Joda bazan boye miki ba yanda kika tafiyar da lamarinki yana burgeni matuƙa,ba ƙaramin baiwa bane Allah yabaka ikon ceton bawansa sannan kuma ya yassaremaka ilimin zakayi aiki dashi. Shekarata goma ina fama da wannan ciwon a boye babu wanda yasani,daga bayane da mariƙiyata tagane mai yake damuna sai take haɗamin wani Shayi na citta da tafarnuwa idan nasha nakanji daɗinsa amma ciwon baya tafiya naji kaman babu shi irin na yanzu. Tukwicin ƴanci da za'a baki nayimin magani wannan banine zan baki shi ba dama sakamakon jarrabawarki ne,dan haka a matsayin ni tawa kyautar zan koyar dake dukkan ilimin dakike buƙata,,indai har nasani to zanyi ƙoƙarin sanar dake" 

 

Dukkan jikina sanyi yayi danaji maganganun sa,ba taba yimin doguwar magana data shafi rayuwarsa ba irinna yau ɗin,sai naji tausayinsa yakamani,inaso na tambayeshi to bashida iyayene da har ciwon ya daɗe a jikinsa bai sanar dasu ba. Sai kuma na fasa domin na kula idan bawai shi yayi niyyar fadan abu ba bayaso a dameshi da tambaya. Numfasawa nayi tareda cemasa na amince,indai har da gaske yake ya haddace wadannan tarin littatafai to aini gaba takaini nasamu malami a bagas. 

 

Tari yafara yana dafe zuciyarsa da hannayensa,tashi nayi da sauri na isa inda yake ina Bubbuga bayansa ruwa na miƙo masa yasha kafin na taimaka masa ya jingina da bangon ɗakin. Sannu nake jera masa amma babu wanda ya amsa sai maida numfashi dayakeyi a hankali,tunowa nayi yau baisha magani ba. Da sauri na juya zan fice,sai kuma naji ya riƙe hannuna. Juyowa nayi muka haɗa ido. Wani sanyi naji ƙafafuna sunyi,narasa menene a cikin idanuwansa da suke sakani shiga wani yanayi dayake baƙo a gareni. 

 

Saina na tattara dukkan ƙarfina kafin nasamu muryata tafito waje. 

 

"Wai maganinka zan ɗauko na manta ashe yau baka sha ba" 

 

"To aikece maganin nawa,a rashinki kusada nine zan buƙaci wancan maganin,ko nasha idan bakya kusa bayamin aiki,yanzu ma bacin ran da kika shigane na dage ina miki bayani har zuciyata ta amsa,kinga laifinki ne kenan dakike kuka a gabana" 

 

Shuru nayi ina kallon ƙasa,laifina kuma ta ina,ruhin mu a hade yake da innayi kuka zai shafeshi? 

 

"Baki yarda ba ko da maganata,To kici gaba dayin kuka a gabana inaga baki shirya ganina na warke ba " 

 

Da sauri na ɗago kaina,wai gaske yakene yin kukannawa ne yasaka ciwonsa tashi,nikuma a suwa?  

 

Jawo hannuna yayi har nazo na zauna a gefen gadonsa,bai sake hannunba har ya ɗaukeshi ya manna Akan ƙirjinsa inda zuciyarsa take bugawa cikeda rauni kaman zata tsaya. Saurin zame hannuna nayi tareda ɗan ja baya kaɗan. 

 

Cikin murya mai sanyi yadan zai gane nace. 

 

"Shikenan zan kiyaye bazan ƙara abinda zai bata maka rai ba,sannan duk da halin jinya da kuma mai magani bai kamata mu dunga samun kusanci kamar haka ba, domin hakan haramunne tunda ba aure mukayi ba kuma kai ba uban gidanane ba,karmu jawo fushin Allah akan mu. Bari kajirani yanzu zanje in haɗa maganin nakawo maka, ga Abokinka baya nan ballantana ya zauna dakai kafin na dawo." 

 

Daga haka nayi saurin fita daga ɗakin ko zan dainajin wani abu dayake fizgata izuwa gareshi,wanda na rasa menene. 

 

Har ta fita idonsa bai ɗauke daga kan kallon ƙofar ba,dan guntun murmushi yayi kafin yace. 

 

"Joda kenan narasa meyasa ta ko'ina kinyi a macen danakeso ta zauna a gefena,amma kuma sai gashi bakizo a matsayin da nawa matsayin zai amsheki ba,duk da haka tunda iyakar da take tsakanina dake ita ce aure kokuma mallaka,to zan mallakeki ta yanda babu wanda zai amfana da wannan ɗumbin baiwar da Allah yayi miki saini kaɗai. Insonki Joda amma nasan ƙarfin tazarar da take tsakaninmu bazata bari mu kasance a yanda nakeso ba. Tsanar bayin danayi ne da maƙasƙanta allah ya jarrabeni dake" 

 

Bayan wata Ɗaya....... 

 

 

Wayyo Allah na ban taba sanin Koyar da karatunsa akwai wahala haka ba saida na yarda akan ya koyamin,ko  yaya nayi kuskure saina maimaita shafi ɗari na wajen,tun inayi a marmari har sai na dawo ina haki. Amma kuma nayi ƙarya idan nace bansamu ilimi mai zurfi ba da kuma yawa. A iya wata biyar ɗinnan na karance bangarori da dama na shari'a da sha'anin mulki,saboda shine abinda yafi iyawa, ga baba Almahdi shima bai barni ba da bangaren magunguna da litattafansu. Sannan nakan saci hanya zuwa Wajen baba guru yin hadisi da Qur'ani. Bakomai ne yasakani wannan haɗamar ba sai illa inaso nasamu ilimi matukar iyawata kafin nabar wajennan watarana nayi dana sani. Domin a jikina nakejin nakusa tafiya. 

 

Addah rahila tana so na dunga yimata rainon Aminullah amma tun rana ɗaya danaxo karatu dashi yayi ta kuka Hammar  ya hanani zuwa da duk wani abu dazai ɗaukemin hankali,gashi in muka fara karatun sai ya sauyamin zuwa wani daban,babu alamar wasa a tattare dashi.  

 

Ciwon zuciyarsa yayi sauƙi sosai,don yafara fita ɗaukar wani darasi a wajen Baba guru wanda tun bana ganewa har na fara gane karatunnasu saboda tare muke zuwa ni nake rakashi,abinda yabani mamaki shikaɗai akewa karatun babu kowa, zuwa yanzu nafara shakkun cewa shiɗin bawane,ba inda akewa bawa wannan karamar. To amma idan nace ba bawa bane to waye kenan. Dan haka saina tattara lamarin sanin matsayinsa a raina.  

 

Yanzu ma rubutu nakeyi nayi takarda ashirin,yanzu rubutuna ya ƙara ƙyau kuma saurin rubutun ma yaƙaru sosai. Bana komawa sansaninmu sosai,haka gasa na tattara na watsar, iyakaci na sashen maganin saikuma idan zanbi ɗaliban kararun baba guru da daddare bayan isha. 

 

"Har yanxu baki gama abinda nasakaki ba" 

 

Ɗago fuskata nayi na kalleshi,yana sanye da fararen kaya na saƙi yayi ɗamara da wani zanzaro baƙi na fata, inna ce bayyi kyau bama nayi ƙarya. 

 

"Wannan kallon ai saiki cinyeni,to ki gama gani gi bari ni inada mata a garinmu har anyimin baiko" 

 

Wani  damm naji gabana ya buga na rasa menene,da sauri na tashi tsaya ina fuskantarsa. 

 

"Dagaske kake hammar?" 

 

Murmushi yayi yana zaune akan karamin gadon dayake ɗakin,ruwa ya ɗauka yasha ya ajiye kafin yace. 

 

"Bankai ayimin baikon bane da har kika zabura haka? Ki tattaramin kayana zan tafi" 

 

Narai narai nayi da ido ganin yafara daukar jakarsa,dagaske yake tunda ya warke tafiya zayyi kenan? 

 

Har ya ɗauke duk wani abu dazai buƙata ina nan tsaye ban motsa ba,saida yace. 

 

"Lafiyanki ko kinzama gunki ne,zan koma masauƙina mana,ko zanyi ta zama a ɗakin jinya ne uhm?" 

 

Ohh sai a sannan na tuna ashe  fah bananne ɗakinsa ba,gabaɗaya na manta. Fara tattara sauran shirgin nayi tareda cewa. 

 

"Hammar wai ina abokinka ne,yau sati biyu kenan ban ganshi ba lafiya?" 

 

"Kina nemansane zayyi miki wani abun?" 

 

"Meyasa idan nayi maka tambaya ne maimakon kabani amsa sai ka jefamin nima tambaya,kawai na tambaya ne babu abinda zayyi mun" 

 

"To na aikeshi zuwa gida kaiwa saƙo,tafiyar da nisa shiyasa bai dawo ba" 

 

Har zan tambaye shi inane garinnasu saikuma nayi shuru kaman an mannamin gam a baki. 

 

Bamusha wahalar tattara kayan ba kusan dukka bayine suka kai kayan, sosai na tsaya na gyara masa ɗakin tass sannan na jera masa kayan inda zai buƙata. Har na gama na gyaran bai dawo daga masallaci ba. Abincinsa da aka kawo na ajiye masa kafin nima na tafi. 

 

Haka rayuwa tacigaba da garawa,shaƙuwa tashiga tsakaninmu sosai wanda har so ma yasamu damar shiga batareda ɗayan mu ya ankara ba. Kullum wajen zamanmu shine lambu,anan muke karatu da kuma hirarrakin da suka shafi duniya,hakan ba karamin lafiya yake ƙara masa ba da kuma kore masa kaɗaici, haka kawai wani lokacin nakega yana min kama da abokina hamad,amma yafi hamad haske,siffar mazaje da kyau. 

 

Na mato gabaɗaya akan soyayyar sa,tun bana gane soyayya na faɗa harna zo na gane. Shima soyayya ta ta bayyana ƙarara akan fuskarsa amma ko sau ɗaya bai taba furtata ba. 

 

Rana ɗayane dayaga Lukman yana koyamin amfani da takobi naga bacin ransa ƙarara,ganin hakan yasa nafara baya baya da lukman ɗin. Ni kaina ina mamakin yanda na sakashi a raina har yayi zurfi haka,bana son bacin ransa haka zalika duk wani abu daya shafi lamarinsa da dukkan iyawata nakeyi. Adda Aneesa tasha gargaɗina akan nabi a hankali kasancewar bansan daga ina yake ba. Sunyi ta bani misali da zuwan hamad,  da kuma yanda yayi batan layar zana a duniyata,to kuma ga wannan ma yazo yasake buɗe ƙofar zuciyata yashiga,shigar da tafi gaban na Hamad.  

 

To amma yazanyi ko naso yin baya baya dashi saina kasa,saboda ko banje ba har bakin sansaninmu yake zuwa yaƙirani. Gashi bawa amma kuma a hankali nima nazama baiwarsa. Duk wani abu daya shafi rayuwarsa,kama daga tayashi saka kaya,kaimasa ruwan wanka,abincin dayake so da kuma maganin dazai sha duk ninakeyi. Ko naji zugar su Addah Rahilah nace bazanyi masa ba sai ya bani tausayi. Domin in banje nakaimasa abinci ba da maganinsa to ranar haka zai wuni da yunwa. Shiyasa ko badan komai ba nakeyi masa hidima a matsayinsa na malamina kuma majinyaci na. Suma ganin bazan sauraresu ba yasa suka daina yimin maganar suka zubamin ido kawai. 

 

 

Sadi-sakhna ce ✍🏼 

 

Comment  

Like  

Share  

Follow