19
by @gureenjoh
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO
✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)
@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad
ADABI WRITERS ASSOCIATION
#THE TRIO OF TALES
(THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY)
TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.
GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.
*SHAFI NA SHA TARA*
"Kaiiii...ya nee? Ka saurara faaa Diva ce nan sai ka jira wallahi"
Ta kalli Pablo tuni ya fahimci me take nufi.
"Ku yi shiru Kaka ce nan kwance"
Ya faɗa yana dan murmushinsu na dabanci sai suka fara shafa kai.
"Tuba muke Oga Malam! Kaka barka dai ya jikin dai?"
Da kyar ta amsa
"Alhamdulillah"
Suka shiga mata kirari da addu'a irin dai ladabin 'yan daba, shi dai Shehi tuni ya dauke kai daga gare su.
"Allah ya bar mana ke Kaka, Allah ya baki lafiya ai lahira ba yanzu ba sai ya jira wallahi"
Ta girgiza kai tana adu'ar Allah ya shirya, Diva ta miƙa musu fruits din tace su sha tuni suka shiga sha suna mata hira hankalinsu ya bar kan su Sheikh.
Su ma da yake da ma ba hankali suka wani mayar kansu ba Ammie ta zubawa Daddah abin kari ya karɓa yana zama gefenta sai da suka gaisa kan ya dibo ya shiga bata cikin kulawa.
Goggo Dija ta ce
"Yau kuma soyayyar ce ta motsa?"
Shehi bai ce komai ba sai Daddah ce da ta hadiye abincin bakinta tace
"Sa ido dai babu kyau Dija ina ruwanki da shiga shirgin Amarya da angonta"
Ammie da Goggo Dijan suka shiga dariya shi dai bai ce komai ba sai ɗan murmushi da yayi har ya gama bata breakfast din ya goge mata baki da tissue ya miƙe.
"Daddah zan tafi, akwai abin da kike so in dawo miki da shi?"
Cikin natsuwa da kulawa yayi tambayar da harshen fulatanci.
"Babu abin da nake so Shehi na gode, Allah ya tsare ya ba da sa'a ubangiji ya kareka"
Ya amsa da Ameen kan yayi wa Ammie sallama ya juya.
Dole ta gabansu zai wuce kan ya fita hakan ya sa dole idanunsa suka sauka kan gadon tana kwance a yanzu Idanunta lumshe yayinda sauran mutanentan suke ta hira tsakanin su suna cinye duk abin da aka kawo mata, girgiza kai yayi kawai ya fice, zaman Daddah a dakin ya zama dole ne kawai amma da babu abin da zai sa ya bari ta zauna da waennan yaran.
Ita kuma Diva ta tafi cikin tunanin abin da ya faru da ita ne da kuma wanda ya taimaka mata, waenchan mutanen basu yi kama da kananun mutane ba kuma a jiya Shaly ke sanar da ita Jagaban ya kasa natsuwa, tashin hankalinshi kaman yana da alaƙa da mutanen da suka yi mata wannan rauni, don tun da ya bar asibitin sau daya ya dawo shi ma a tsaitsaye.
Duk yadda za ta yi nazari sai ta rasa makama, tsoronsu yake ji kenan ko kuma dai ya koma gefe ne ya yi aiki a kansu? Meyasa idan da Jagaban suke da dabi za su taɓa ta? Meyasa suka rubuta mata JJ a baya? Waye JJ? Dole ta binciko saboda ba za ta bar su ba, ba su isa su sha ba wallahi.
Idanunta da suka rine ta buɗe tana tuna kaɗan daga cikin plate number din su ta kalli Pablo
"Akwai Ice?"
"Akwai Diva amma bai kamata ki sh..."
Kallon da ta mishi ya sa ya zaro tube din kawai ya bata, Skipo ya kunna lighter tana ɗorawa a bakinta suka haɗa idanu da Ammie bata ji ko ɗarrr ba ta cigaba da kallonta dole Ammien ce ta kawar da idanu a ranta tana yi mata fatan shiriya da kuma adu'ar Allah ya tsare mata zuri'a ya shirya su don ba zata iya daukar wannan a ahalinta ba.
Abin da Daddah ma ke tunani kenan har ta kasa shiru tace
"Yarinya ke da ake maganan ana zargin Wuka ya taɓa miki Ƙoda ke ce da shaye shaye?"
Idan akwai abin da Diva ta tsana to shisshigi ne, shiru tayi kaman bata ji ba don kar ta zabga mata rashin mutunci.
"Ki kiyayi duniya, wannan abu babu amfanin da yake miki sai ma iyaka ya cutar da lafiyarki, ke macece gidan wani za ki je kuma za ki so ki haihu bakya tunani wannan rayuwa ya taɓa ki a gaba?"
Har lokacin Diva bata nuna ta san da ita take yi ba sai Ice ɗin da ta cigaba da sha, su Pablo suna tsaitsaye su ma duk babu wanda ya kalli Daddahn.
Goggo Dija ce tace
"Ke ma dai ki yi shiru mana Mama, ba rayuwarsu ba? Idan ba ma don babu yadda aka iya ba sun isa ma ko Numfashi ki haɗa da gurbataccen nasu da kwaya ya lalata?"
Pascal ya miƙe yana juyowa Diva ta ɗan yi fito sai ya tsaya.
"Ku je kawai!"
Kwafa yayi sun ci sa'a Diva tana hana su da sai sun yaga bakin mace wallahi.
Tuni suka fice daga ɗakin don ta ce su tafin.
Pabloo ya tsaya tace shi ma ya je Hajjo ta zo.
Shima ficewa yayi suka barta ita kadai sai da tayi high kan ta kwanta tana sake lumshe idanu daidai nan duka 'yan matan gidan suka shigo.
Mufida ce ta ɗora Idanunta kan Diva sai ta zaro su gabadaya waje, sauran ta taɓa chan ƙasa tace
"ku wannan ba Diva ba? Wannan da ta mari Malam Bala? Wacce Ya Ammar ya nuna mana hotonta?"
Tabbas sumayya ta ganta amma ta rasa inda ta santa ashe ita ce! Kuskus suka cigaba da yi duk tana jin su amma bata son shiga harkarsu don bata kaunar wani abu ya sake haɗata da malamin ɗansu ya riƙe wa'azinshi ta riƙe rayuwarta.
Su Mufida dai sun kasa zaman kirki suka gudu saboda tsoron kar su mata laifi duk da bata tanka kowa ba kuma bata buɗe idanu ba.
****
Shi kam Irshad Company ya fara zuwa, yana da office duk da ba zama yake ba Audit team ya nemi gani waenda su ne a ka'ida duk abin da ya shafi wani ɓarna a company bincike ne ko sauransu su suke yi a sirrance kuma shi ne Head of Internal Audit & Compliance dayawa basu sanshi ba saboda Assistant dinshi ne ke kula da komai don haka karamin meeting suka haɗa farko ya fara da Introduction kowa ma yayi introducing kanshi kan ya shiga abin da ya kawo shi.
Ya tattauna da su akan abubuwan dake faruwa ya nemi jin aikin da suke yi a ƙasa, bayan ya duba kananun ayyukan yace duk za su ajiye su dukufa kan ɓace bacen kudi daga ina ake samu kuma su wa suke amfana, ya musu babban gargadi akan rike sirri hakanan idan ya kama cin amana ba zai bari ba su team ɗin Audit ba'a san su da fitar da magana ko cin amana ba saboda su ne masu tsage gaskiya duk yadda take a cikin company.
Daga nan suka buɗe file na bincikensu, ya sallami sauran Assistant dinshi zai fice ya dakatar da shi
"Hashim!"
Ya dawo daga baya
"Yes Sir"
"Zan wuce yanzu, ka tabbatar ka kiyaye abin da na ce and make sure na ga komai a email dina before asr"
"In Shaa Allah"
Daga nan ya wuce, shima Sheikh fitowa yayi ya tafi office na Abbiey sun ɗan yi magana kan ya fito ya tafi office na Ammar shima sun yi magana akan binciken ya nuna mishi inda nashi binciken ya kwana da yadda Digits na kudi ke karuwa yana saka hannu bai sani ba, tattare duk bayanan ya sa Ammar yayi ya tura mishi a email akan da dare zai nazarci takardun.
Daga nan suka fito tare da Ammar din suka yi sallah a masallacin company kan Shehi ya wuce BUK don gabatar da lectures.
***
Har ya gama lectures ɗin bata cikin natsuwarta Allah ya gani tana jin shi har tsakiyar ranta a da crushing kawai take amma tunda ya bayyana matsayin wanda za'a haɗa su ta ji tana mutuwar son shi, sai dai kash ta ɓangarenshi ko kallon inda take bata ga ya yi ba.
Bata wani damu ba sanin da ma yana da wannan kamewar za ta mishi uzuri kila sai an ɗaura kan ya fara nuna mata soyayya, ta ki faɗawa kawayenta komai tana jin su kaman yadda suka saba kullum suna ta yabonshi, ko da aka tashi lectures din ma office dinshi yaje yayi alwala ya fito zuwa masallaci bayan ya yi la'asar ya fito ya nufi gida a hanya ya wuce su da mota ta bi motar da kallo tana ji kaman zuciyarta ne ya tafi da shi.
****
Gida ya je, da wanka ya fara don jin shi yake a gajiye kwarai, Wata farar jallabiyar ya sake sakawa amma a yanzu Ghutra kawai ya sa ya rufe kanshi ya feshe jikinshi da turarukansa lattafa's masu kamshin natsuwa kan ya fito sashen Mamaah ya nufa.
"Wa'alaikassalam warahmatullah Shehi ka dawo?"
Ya amsa yana zama daga ƙasa
"Eh maamah sannu da gida, Ammar bai shigo ba?"
"Ya shigo amma ya ce min kanshi na ɗan ciwo zai kwanta ya huta sai dare za shi asibitin"
"Ya kamata ma su sallameta ai ta karasa jinyar a gida zaman asibitin ba daadi yake mata ba"
Mamaah tace
"Aikam, ni ba zaman ba ne ba ma yadda aka haɗata daki da 'Yan daba masu shaye shayen nan ne bai yi ba samm babu wanda ya san me za su aikata suka sha suka bugu don abin ba gaskiya yake faɗa musu ba"
Ji yayi wani abu ya motsa mishi a rai, ya ɗan lumshe idanu ya buɗe
"Allah ya shirye su"
Ta amsa da Ameen kan ta miƙe ta kawo mishi abinci kaɗan ya ci ya ce mata zai shiga asibitin don da dare yana da karatu ba zai samu zuwa ba.
Allah ya tsare tayi mishi ya fito, daga harabar yake tsinkayo hirar su Mufida na irin tsoron da suka ji yau na ganin Diva, hawwa take cewa
"Abin mamaki kuma a asibitin ma fa shaye shayen ta take, wani irin bala'i ne wannan ka mutu a buge?"
Mufida tace
"Baki ji Goggo Dija na faɗawa Goggo hindatu har rashin kunya suka so yi wa Daddah ba don ta nemi yi musu nasiha?"
"Ta ce ita Diva din ce ma ta hana su amma na yi mamaki an ce bata daukar wargi komin girma ko tsufanka ya aka yi bata dauki mataki kan Daddahn ba?"
Cewar Aisha
Sumayya tace
"Ni dai fatana a sallami Daddah bata ɓarkawa daya daga cikinmu ciki ba don fa zubar da jini a wurinta ba komai ba ne"
Motsinshi da suka ji ya sa suka juyo sai suka natsu, suka gaishe shi ya amsa kawai ya wuce.
Malam Bala na nan don haka key ya bashi ya fitar da motar shi kuma ya shiga suka fice zuwa asibitin, a ranshi saƙe-saƙe ne mai yawa haka kawai yake jin wani iri ambaton Allah ya cigaba da yi har suka isa ya sauka suka nufi ciki da malam Bala hannunshi rike da fruits dayawa da Shehi din ya sa suka tsaya suka saya.
Shehi ne a gaba hannayenshi goye a baya yana tafiya cikin natsuwa, Malam Bala na daga bayanshi har suka isa ɗakin ya buɗe kofar ya shiga Malam Bala na sanyo kai wa zai gani?
Salati ya saki har ledojin hannunshi na shirin kubucewa su watse Allah ya taimaka ya riƙe kammm, salatinshi shi ya ja hankalin dukkansu har su Daddah.
"Malam Bala lafiya?"
Shehi ya dawo da baya yana tambayarshi ganin yadda ya firgice.
Da ido yake kifkifta mishi Diva, a hankali Shehi ya juya ya kalleta itama su take kallo amma fuskarta a kame kaman ko da yaushe.
"Shi kuma wannan lafiya?"
Skipo ya yi maganan yana sake kallonshi da kyau don tabbatar da ba mahaukaci ba ne.
Irshad ya hade rai
"Haba Malam Bala, me haka kaman mala'ikan mutuwa ka gani?"
"Ranka ya dade ai bata da maraba da mala'ikan mutuwa, duk inda take mala'ikan na tare da ita"
Goshi Irshad ya ɗan shafa yana ɗan girgiza kai idanunsa suna fallasa yanayinsa na surkin haushi, bacin rai da takaici hade da kuncin da yake ji a ran shi yace
"Ka natsu, babu abin da za ta maka not under my watch"
Yana kai nan ya karɓi ledojin ya wuce ciki, da sauri malam Bala ya bi bayanshi yana sake Satan kallon Diva din da ta dauke kai ma daga garesu sabon wayan da Jagaban ya kawo mata take dubawa ya sanar mata nata ya farfashe tayun motanta duka sai an sake saya don sun lalata.
Shi kuwa malam Bala na zuwa ya gaishe da Daddah sama sama ya ce wa Sheikh zai jira a waje da sauri ya fice.
"Amma lafiya malam Bala ke nan a firgice?"
Goggo Hindatu da ita ce ta karɓi Goggo Dija da Ammie da basu wani jima da fita ba Sheikh din ya shigo da alama ma sun yi saɓani ne a hanya tace chan ƙasa kasa da fulatanci.
"Wannan ita ce ta kusa kashe shi fah Mama"
Zaro ido Daddah tayi ta juya tana kallon Diva ashe hatsarinta ya kai haka? Hanjin cikinta ya kada kenan shiru ta mata tana ta mata nasiha da ta yi niyya tuni za ta kashe ta a banza tunda kashe mutane take?
"Shehi ni dai a sallameni ba zan kara awa guda a asibitin nan ba"
Ta faɗa da iyaka gaskiyarta.
Zama ya yi a kujeran gefen gadon
"Za'a sallameki Daddah ba Likitan ya ce da yamman nan zai dawo ya duba hoton ba?"
Kai ta gyaɗa mishi
"Idan ya zo zai sallameki ki kwantar da hankalinki"
Diva ta ɗaga ido tana kallon pascal da ke ba wa Obafiyan da Skipo labarin Dagar da suka yi da Kawunshi akan wai zai kama shi ya kai shi Rehabilitation center saboda kawai Mamanshi ta kai mishi ƙararshi.
"Kun ga 'yar tseren da muka yi wai? Yo hauka nake na tsaya ya kama ni ya kai a ɗaure kaman kare ko rago?"
"Ya aka yi ya kyaleka to?"