GAJERIUN LABARAI

GWARZONA

by @jikankaila2014

Ƙunci da damuwa ne suka zamo min dabaibayin da ya sarƙafe min rayuwa, ba ni kaɗai ba har ma da ƙanwata Falmata. Farinciki kuwa ya zamo tamkar wani baƙon abu na almara da ake labarin ya faru a wani ƙarni can baya. Mun kasance abin nunawa a cikin jama'a, daga unguwarmu har cikin illahirin ƙauyenmu, ana ta kyararmu tare da ɗora laifin abin da ya faru kan ƙanwata, ana kuma zargin ni ne nake zuga ta sai ta nemo haƙƙin ta a wurin waɗanda suka cutar da ita. Mutanen da a wajen jama'a babu wanda ya kai su kirki da mutunci a duk faɗin ƙauyenmu.

Muna gida za mu ji maƙwafta suna mana habaici da yasar mana da ƙananan maganganu na ɓata suna. A taƙaice dai rayuwa ta yi mana ɗaurin gwamen jaki. Ta kai ko da mahaifiyarmu ta shiga cikin hidimar biki ko wani taro na mata, sai a yi ta jifanta da maganganu. 

Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raji'un! Babban abin tashin hankali ma shi ne yadda aka je aka karɓi lefen da aka kawo na ƙanwata, duk da yadda saurayin yake sonta. Ya kuma amince zai aureta, amma danginsa suka ce ba zai aure ta ba. Haka muna ji muna gani aka karɓi kayansa, abin da ya zama silar jinyar mahaifiyata!! 

Na taso tun ina yaro da son ‎karance-karance. Ina son karanta littattafan tatsuniya, na tarihi da kuma na nishaɗi. Kai, har ma da jaridu! Ina da tsananin sha'awar son zama ɗanjarida musamman ganin yadda ake tattaunawa da yin sharhi, akan batutuwan da suka shafi al'amuran zamantakewa da cigaban ƙasa. Bayanansu na ƙara min sha'awa saboda gudunmawar da suke bayarwa, wanda nake ganin kamar nima zan iya watarana.

Sai dai ta yaya zan iya zama ɗanjarida yadda har zan riƙa yin rubuce-rubuce da talifi har al'umma su amfana? Wannan ita ce babbar tambayar dake yawan zuwa min raina, ga kuma abin da na karanta a makaranta ba shi da alaƙa da aikin jarida balle har na sa ran fatan zama ɗanjarida watarana, har nima a riƙa wallafa rubutuna a jarida. Kullum saƙe-saƙena ba sa wuce haka. 

Bayan na ƙara girma na cigaba da karanta littattafai, kuma babu shakka karatun da nake yi ya canja min tunanina na zama marubuci. Sai dai yadda zan zama marubuci shi ma ya zama wani babban al'amari dake damuna. Kurɗa-kurɗata ya sa na faɗa wani zauren wasu marubuta a manhajar Whatsapp da niyyar ko banza nima zan iya zama marubuci. A cikin wannan zaure na samu damar karanta littatafan da wasu marubutan ke turawa cikin sauƙi. 

Sai dai abin da ya faru da ƙanwata, ina ga da bukatar na yi wani rubutu a kan waɗannan abubuwan, don bayyana haƙiƙanin gaskiyar abin da ya faru. A farkon rubutuna na fara ne da gajeren labari, duk da yake gani nake kamar ba zan iya ba. Na fara tura labarin da na rubuta na farko ne zuwa ga zauren Marubuta na manhajar Whatsapp.

Alhamdulillah, na lura jama'a da dama sun karanta labarin. Ƙalubalen da na fara samu a matsayina na marubuci shi ne rashin iya amfani da daidaitacciyar Hausa a wajen rubutu. Ba na iya bambanta Hausar baka da rubutacciya. Sai dai kuma na ji daɗin fara fitar da rubutuna ga jama'a, duk da kasancewar ina da damuwa kan yadda zan inganta rubutun don ya zama ina iya yin sa bisa ƙa'idoji da dokokin rubutu cikin daidaitacciyar Hausa. Babbar magana!
‎Na fara tura labarin ne ga wasu 'yan'uwana marubuta akan su duba su gyara min. Na yi sa'a wasu sun kula ni, wasu kuwa ko ci kanka basu ce min ba. Yayin da wasu suka ɗauki alƙawarin duba min, wasu kuwa kuɗi suka ce sai na basu. Na fara ne da rubutun gajeren labari. Haka na yi ta shan fama da wasu marubuta, har dai na sare na haƙura, don yadda na ga ake fuskantar ƙalubale.

 Wata Asabar ce da yamma na ga wani sakon na wani bawan Allah mai suna Malam Abba Abubakar Yakubu, wanda ya yi min sallama cikin kalamai na ƙarfafawa akan wani gajeren labari da ya gani na rubuta, inda har ya bani shawara akan na cigaba da rubutu, amma na mayar da hankali wajen karatu. Wannan maganar ita ce mabuɗin da ya fara ƙarfafa mini gwiwar shiga duniyar rubutu. Da kaɗan-kaɗan na cigaba da amfani da basirata ina rubuta gajerun labarai, da nufin isar da wasu saƙonni ga al'umma, har dai duniyar rubutun adabin Hausa ta fara sani na.
‎***** ****** ******
‎Ɗakin taron ya cika maƙil da jama'a, yayin da ko'ina ya yi tsit ana sauraron gabatar da sunayen waɗanda suka yi nasara a wata gasar rubutun gajeren labari da aka gudanar. Ni dai ina zaune a ciki ko a jikina, don ban sa aka ba in ji barawon tagiya. Ba zato ba tsammani sai na ji an kira sunana da aka yi, Sammani Sale! Abin ya bani mamaki matuƙa, duk da yake na nasan na shiga gasar nima, amma ban kawo a raina cewa zan shiga cikin waɗanda za a karrama ba, a matsayina na sabon marubuci. Ko a lokacin da aka kirani sai da aka maimaita tukunna sannan na tabbatar da cewa lallai ni Sammanin ake nufi, na miƙe jikina a sanyaye na fita. 

Mahaifiyata tana yawan faɗa min cewa, a cikin kowacce nasara akwai wani tsani da yake taimaka wa mutum wajen kaiwa ga nasara, a nesa ko a kusa. Ni dai a raina nasan a duniyar rubutu ba ni da wanda ya taimake ni in ba Malam Abba Abubakar Yakubu ba. 

Kamar yadda dokar Gasar take marubucin labari ne yake fita ya bayyana abin labarinsa ya ƙunsa. Don haka nima na gabatar da nawa dalilan da saƙon da labarina yake son isarwa. Wannan shi ne muhimmin lokacin da na daɗe ina jira, don na bayyana wa jama'a abin da na daɗe ina ɓoye shi a zuciyata. Cikin ƙwarin gwiwa na fara bayyana cewa yana da kyau sosai jama'a su daina ɓoye abin da aka cutar da da su don neman haƙƙinsu, da kuma kira da a hukunta waɗanda suka aikata laifi, don ya zama darasi ga sauran mutane masumugun hali. 

Labarin da na rubuta yana ƙunshe ne da labarin wata yarinya da ta fallasa wanda ya yi mata fyaɗe, duk da tsangwama da kyara da ta riƙa fuskata, a sakamakon ta dage sai ta nemo haƙƙin. Hakan sai ya zamo mata abin ƙyama da gorantawa a tsakanin al'ummarta. Har aka riƙa muzanta ta a shafukan jarida da zaurukan sada zumunta ana amfani da labaran ƙarya don kawar da kan mutane daga abin da ya faru a kanta, da kuma wanda ake zargi. A ƙarshe dai ta yi nasara, kuma nuna wa jama'ar ƙauyensu cewa, wanda aka cuta ba ɓoye kansa zai yi, ya yi ta damuwa cikin ƙunci ba, zai fita ne ya nemi haƙƙinsa, ta hanyar da ta dace. Ta haka ne za a rage mugun iri a cikin al'umma, aka kama wanda ya aikita mugun aikin nan da hukunta shi.

Na samu nasarar tsara wannan labari ne da taimakon malamina kuma ɗanjarida Malam Abba Abubakar Yakubu.‎

 "Ina roƙon mahukunta wannan gasar yayin da za su bani kyautar nan, da su gayyato min wannan haziƙin ɗanjarida Malam Abba Abubakar Yakubu don yabawa da irin gudunmawar sa a rayuwata. Ina so in sanar da jama'a cewa wannan labari da na rubuta ba ƙirƙirarren labari ba ne, ya faru ne da gaske kuma akan ƙanwata! Shi wannan ɗanjarida shi ne ya taimaka min har aka fallasa mutumin da ya yi wa ƙanwata fyaɗe, kuma shi ne tsani na wajen samun wannan gagarumar nasara a wannan Gasa, da ma cikin duniyar rubutu bakiɗaya."

 Ɗakin taro ya kaure da tafi da kalamai na murna da fatan alkhairi. 

Ina mai roƙon Malam Abba Abubakar Yakubu da ya fito da ya karɓi wannan kyauta da hannunsa, domin shi ne ya cancanci karɓar wannan karramawa, kasancewar shi ne, GWARZONA kuma GWARZON wannan gasa.

Raf...raf...raf...aka cigaba da tafi cikin nuna yabawa ga abin da na yi, yayin da gwarzon nawa ya taso daga cikin jama'a ya nufi dandamalin da nake tsaye tare da masu miƙa shaidar karramawa.