GAJERIUN LABARAI

MAFITA NA KE NEMA !!!

by @jikankaila2014

MAFITA NA KE NEMA !!!

Jibrin Yusuf Kaila 

Kunci da ɓaci rai ya zamo abokin rayuwa ta ,ya zamo tamkar amini na,kullum tare mu ke da shi,duk da ba a so ya kasance agun ɗan adam,amma ni ya zarge ni,har na sallamar da farin ciki a zuciya ta,wanda ma na ke ga kamar sai dai mu hadu a lahira,bayan mun shiga rahamar Ubangiji, wato in mun shiga Aljannah fiddausi,wanda kowa ya ke fatan ya samu, duk Musulmin duniya.

Kasan tuwar mai afkuwa ta fari da ni wato ƙaddara, wanda kowa zai iya faru dashi,sai dai mutane sun kasa fahintar cewa Ƙaddara tana faɗawa kan kowa ,kuma kowa ba a son ran sa ba take faɗa masa ba.

Wata waƙiyar ƙaddara ce ta faru da ni :wato fyaɗe da aka yi mun,wallahi ban son kallamar ta fito a baki na, domin tsabar tsanar da na yiwa kallamar,balle masu aikata ta.

Wanda yin mun fyaɗen Ɗan gidan Audu ne wato Idi, hakan ya sa aka kai shi kotu,sai dai akwai sanayya tsakanin gidan mu da gidan su,hakan ya sa aka yanke shawarar a aura mun shi saboda ciki ya shi ga,amma gaskiya Ina da masoyina,kuma mu na son juna.

Ashe kalmar da mata su ke cewa "Namiji Ba shi tabbas" ashe wasu ne.Hakika masoyi Haidar namiji ne,wanda kowace mace zata so ace ta samu kamar sa,kuma haka kowace uwa zata so ace yarta, ta samu miji kamar shi.

Duk da ƙaddara ta afku akai na, Haidar bai guje ni ba,duk da wanda aka mata fyade ana kyamarta,koda kowa ya son ba a son ran wanda aka yi wa fyaɗe ne ba,amma ya ce haka zai aure ni,duk da gulmace-gulmace na yan garin mu.

Sai dai Kash!!!, iyaye na suka take kafa akan cewa ,Idi wanda yayi mun fyaɗe, shi ne zai aure ni,duk da ina soyayya da wani, kuma yace ya amince zai aure ni, amma iyaye na suka ce, su ba za su ba shi ni ba.

Na yi kokarin matuƙar wajen kai wa gun Hajiya Mairo wata yar fafutuka ce,amma itama ta yi bakin kokarin ta, bata samu nasara ba ,wanda silar haka sai da suka kai ta kotu,wanda a karshe sai da suka aura mun shi.

Bayan anyi auran, yanzu baya ba ni abinci sai de na fita na nemo, Idan ya tarar bana nan yayi ta faɗa wata rana ma sai ya dake ni,su kuma iyaye na idan na je gun su, sai ayi ta bani hakuri. MAFITA NA KE NEMA !!!