GAJERIUN LABARAI

NA ZAMO ABAR KYAMA

by @jikankaila2014

NA ZAMO ABAR KYAMA 

Marubuci Jibrin Yusuf Kaila 

Suna na Lantana Musa a wata ƙaramar hukuma dake jahar nan, mai kimanin shekara 23 da haihuwa, ba sai na an baci sunan ƙauyan mu ba, saboda kar na ƙara faɗa matsalar da na ke ciki, wato halin kyama da gori na yan garin mu ya karu, anyi mun fyaɗe amma na faɗi wanda ya mun, ance na masa ƙazafi silar haka aka ɗaure mahaifina a gidan ɗan kande na sati biyu.

Na kira wannan Marubuci ne, na bayyana masa halin da na ke ciki, domin ya isar da sako na ga mutanan da suke karanta labarin sa, duba da yadda marubuta suna taka gagarumin gudunmawa, wajen isar da sako, da fatan za ku kasance masu ƙoƙarin dena halin mutanan nan idan kuna yi ku dena, idan ba kwayi, sai ku bada shawara akan masu yi su dena, domin yana cutarwa.

"Na gagara kasa fahintar kai na, shin laifin mi na yi, ni da aka yi wa laifi ni za zan zamo abin kyama, ko kuma wanda ya mun aika-aika shi zai zamo abin kyama? Ina wata al'umma ne, wanda aka masa laifi shi yake zamo abin kyama, wanda ya yi abin aika-aikaika shi zai zamo abin jawowa a jiki a gun al'ummar mu. Kullum idan ban yi kuka sau uku ba ko sau hudu tofa na yi sau biyu. A kullum so na ke na kasance mai farin ciki, amma sai na gagara kasa nemo shi, domin farin ciki ya yi ne sa dani, nisan da na har na haƙura da shi, wato na sare da shi, sarewar da irin ta mutumin da ya faɗa rijiya a tsakiyar dokar daji, babu wanda zai ji shi in ba Allah ba."

Sau biyar ana zuwa neman aure na, amma ana fasawa, akwai wanda ya rufe ido duk da maganar yan garin mu, na gulma da munafurci ya ce zai aure ni, amma a karshe satin da za a kawo laifen aure na aka fasa, saboda anje an faɗawa mahaifiyar sa, cewa ai an taɓa mun fyaɗe. Ni yanzu na sallama da yin aure kenan, yanzu aure ya haramta da ni. Ni ban kasance karuwa ba, hasalima ni ba mace ce wanda na ke kula maza ba, ina kare mutunci na da darajar gidan mu, dai-dai gwargwado.

Tabbas banga laifin iyaye da suke boye ya'yan su idan an musu fyaɗe ba, wallahi kalmar ma ban son faɗarta , balle ace na ga wanda ya ke aikata ta . Da zarar ance wancan an yi mata fyade, shi ke nan ta zamo abin nunawa da kuma kyama, da gorin abokai da yan uwanta. Na kan sha mamaki idan na ga karuwar gida suna auruwa, wanda kowa ya san yaran ba sa ji, amma sai ku ga sun auru.

Akwai wata yarinya mai suna Hadiza ta Kowa, wallahi duk unguwar mu, ba wanda bai san cewa yar iska ce ba, hatta iyayenta sun san cewa tantiyar 'yar iska ce. Duk da shekarunta ba su wuce 19-20 ba, amma a halin da ake ciki wannan satin da mu ke ciki za a yi auranta. Kowa ya san halin gidan mu , da irin tarbiyyar gidan mu saboda ƙaddara ta kama ni an yi mun fyaɗe, na zamo abar kyama a cikin al'ummar mu, har nuna ni ake a gari, idan na zo wuce wa.

Wanda ya mun fyaɗe wani mutum ne mai kimanin shekaru saba'in da ɗaya (71). Shi ne mai arziki duk garin mu. Sunan sa Alh. Wada Isa Harde, wata rana ne na je gidansa an aike ni, daman mu na wasa dariya da shi, ni na ɗauke shi kamar Kakana, kwatsam wani lokaci da na je gidan sa Matan sa ba sa nan, ban son ba sa nan ba, sai na tarar da shi a gidan ba kowa, sai yace na je wani ɗaki na ɗauko masa Jakarsa, ko lokacin da na gan shi a gidan sai da gaba na ya faɗi. Ina shi ga ɗakin ya bini ya rufe kofar. Gidan Babba ne, na yi ihu iya bakin iyawa ta, amma ɗan tahalikin sai da yahaike mun. Mahaifina da ya ganni a halin da nake ciki, domin lokacin da dare ne kuma matar Babana ce ta aike ni gun matar sa, mahaifiya ta bata gidanmu. Sai ya kai ƙara gun yan sanda, a lokacin da ya kai ƙara gun yan sanda, sai aka ce na masa sharri a karshe dai, sai manya garinmu da Hakimin garin na mu suka sa aka kai mahaifina Gidan Ɗan kande na sati biyu, suka ce "Ta ya za a ce mutun mai Daraja kamar Alh. Harde, za a ce ya yi wannan mugun aiki." Saboda don ya na raba mu su kuɗi a matsayin zakkah, babu bincike kawai suka yanke hukunci haka .Daga karshe de Babana da aka zalunce shi da yar sa mu muke ba da hakuri.

Haka na samu wata mata wanda aka yi mata fyaɗe ta zamo abar kyama, ita ce ma na ke zuwa gun ta wato gidan ta, anan nake samun sauki.Take bani labarin halin ta shiga itama. Wanda ya mata fyaɗe shi ne mijinta yanzu, duk da ba shi take so ba, amma aka tilasta mata wato iyayenta, kuma tana da wanda take so shi ma yana son ta, amma iyayanta da iyayan saurayin nata ne suka ki daga ƙarshe aka tilasta mata auren wanda ya mata fyaɗe. Abin takaici ma, ba ya kawo mata abinci sai dai ta nema duk sanda ya bushi iska na walaƙancin sa sai ya yayi ta mata faɗa wani lokacin har da duka idan ta yi masa Musu.

Abin da take sana'ar ma,Idan anyi ciniki idan yaga bata kusa sai ya dauke kuɗin, idan tace ya bata kuɗin sai ya musa, ta na faɗar maganar da bata gamshe shi ba, ya rufa ta da duka kamar jaka. Na sha zuwa na ganta tana kuka ko na ga kumburin fuska, idan ta yi ƙara gun iyayan sa ko na ta sai ace ta yi hakuri.