GAJERIUN LABARAI

RAMA CUTA....

by @jikankaila2014

RAMA CUTA......
‎Daga Jibrin Yusuf Kaila
‎Audu Jangali ne ya fara sani a harkar shaye-shaye,shi ne mutumin da yake taimako na, a duk lokaci da na shiga damuwa! A wajensa ne kawai nake samun sauƙi, shi yake bani dubu ɗaya ko dari biyar.
‎ Idan na shiga damuwa ko na rasa kuɗin da zan ci abinci , don abinci yana gagarata,sai na wuni ina neman abinci, amma bana samu abinda zan saka a bakin salati, sai dai ko ruwa , shima sai wani ya siya Pure water ya rage min ko kuma an bada sadaka, Idan na je gun ƙannan mahaifina banda hantara da zaburata ba wanda zai ja ni ya tambaye ni abin da yake damu na, har yasa na haƙura da zuwa wajen su.
‎Ina so na yi karatu amma babu wanda ya damu da ni, ga ‘Yayansu babu wanda baya zuwa makaranta, duk kan su na fi su da shekaru, sai dai a cikin dangin mahaifin nawa babu wanda ya kula da rayuwata.  
‎ Oga Audu Jangali shi ne ya damu da ni ya kuma ɗauki al’alata, ganin cewa ba ni da wani masoyi kamar sa, shi yasa na yanke shawara na zama yaransa , daga farko bai amince ba, amma da ya lura ina ta ƙwaƙuma masa kaina sai ya yarda, dama ya ƙi yadda ne saboda ban goge a harkar safarar muyagun ƙoyoyin da yake yi ba. 
‎Babbar sana’arsa ita ce, aika mugayen ƙwayoyi da tabar wiwi ko wanna lungu da saƙo na jihar nan, ma’ana dai shi Dila ne na kayan maye. Na kasan ce mutum mai biyayya, don haka sai ya maida ni na hannun damansa, farkon fara shaye-shaye na na fara da Taba da Syrup, daga baya na zama Ogan kaina. 
‎Kwatsam!!! Sai rana ta ƙwacewa Oga Jangali aka kama shi da Coken, wanda silar haka aka yanke masa hukunci gidan yari na dindin, Costumes ɗinsa suka dawo guna karɓar kayana don ni suka sani......
‎Na dauki wani Al’ƙawari kamar yadda suka barni rayuwata ta lalace, su ma kuwa haka zan yaudari ‘yayansu , na lalata su bizinillah, kuma Alhnmdulilah kaso Hamsin cikin ɗari na zama sila wajen gurgunta tarbiyar yaran. 
‎Na taso cikin maraici Babana ya rasu tun Ina wata bakwai a cikin mahaifiyata. Mahaifina mutum ne wanda Allah ya masa buɗi, ya kasance tamkar Katanga,majingina ga danginsa da unguwarmu,hakan yasa yake da ƙima daraja a gun al'umma, shekaru 20 suka yi ko bari mahaifiyata bata taɓa yi ba, hakan yasa suke cike da farinciki a lokacin da likita ya sanar dasu mahaifiyata, ta samu juna biyu, kamar yadda ummah take bani labari , kusan buhu biyar na Shinkafa ya raba saboda nuna godiya ga Allah.
‎ Ya kasance ɗan kasuwa, yana saida kayan abinci; Shinkafa,Taliya,Wake da sauran kayan masarufi kuma manomi ne. A lokacin da na kai wata Tara sai Allah ya jarabce shi da cutar ƙoda bai kai sati biyu ba, don har an fara masa wanki sau biyu. Allah ya karɓi rayuwarsa.
‎Mahaifina bashi da iyaye sun rasu, sai ƙanansa su uku Iya Lami, Hajjo da Baba chiroma. Tun lokacin da aka yi bakwai ɗin mahaifina na rasuwarsa, mahaifiyata ta fara ganin sauyi, don ko suna da kyar akayi min haƙiƙa, ma’ana aka yanka min Ragon suna, kuma duk rufin asiri da suka samu sun manta mahaifina ne sila.
‎ Gidan Baba chiroma da yake ciki, shi ya siya masa har da lefen auransa kaso 80 shi ya masa, su kuwa Iya Lami da Hajjo, duk Tsaraba da Gara ta auransu shi ya musu, kai hatta da Gadon aurensu.... Amma tun da ya rasu muka shiga cikin halin ƙaƙa na kayi,ni da mahaifiyata.
‎ Yan unguwarmu kuwa abin kamar haɗin baki, takai majaifiyata ko abinci da zamu ci da kyar take samu ta bani. Wani abun takaici da ba zan manta ba shi ne, a cikin Abokan mahaifina akwai wanda yace sai ya biya bukatarsa idan zai taimaki mahaifiyata, a lokacin ina fama da wani ciwan kai mai masifar ciwo. A bin mamakin yana ɗaya da ga ciki mutanan da mahaifiyana, ya sha ɗawainiya da su , don mutum ne mai cin bashi, ya sha fito dashi daga gidan kaso. 
‎Tun da na fahinci babu mai kaunata, ni kuwa na dau al’ƙwari sai na lalata ‘Ya’yan ‘Yan uwana da yaran unguwarmu domin an ce “*Rama cuta ga macuci ibada ne*”, don yanzu Yayan Ƙanan Babana , duk sun zama Manya dila masu sarafar Kwaya da tabar Wiwi. Rabi da kwata Matasan unguwarmu duk zama yan kwaya da Yan sara suka, ta silata
‎Officer" Mutane nawa ka kashe?
‎Mutum goma ne, Wanda na sara kuwa ba San adadin suba officer.