GAJERIUN LABARAI

RUDIN ZAMANI

by @jikankaila2014

RUDIN ZAMANI

"Shine Bakadamiyata a GAJERUN labarai da na rubuta sama da a shiri"

Rubutuwa Jibrin Yusuf Kaila

Wata rana ce wanda na tashi bana jin daɗi, hakan yasa ko aiki gida ban samu yi ba, banda abincin da na yi wa ’yan makaranta ban samu damar yin komai ba. Shi kuwa Abban Yasmin baya gari ma.

Bayan na sallami Yasmin da Fahat sun tafi makaranta, gishin gidewa na yi, barci ya kamani tamkar satar bazata. Kwantsan kuka nake ji, na yata Yasmin ta doso inda nake kwance a ɗaki tana kuka. Jin sa nake sama-sama kamar mafarki, ko nace na afarke firgiji na tashi, domin daga jin kasan kukan babu lafiya.

Na ce: “Yasmin, lafiya?”

Ta amsa da cewa: “Abokaina ne suka ce wai ke karuwace, sun ji ana zance a gidansu, har ma wani video ki suka gani aka ce kece.”

Na ce: “Ni kuma?! Video kuma aka ce nice kuma karuwace? Subhanallah! Waye ya nuna musu?”

Ta ce: “Gani suka yi a gun wayar yayarsu ta nuna. Umma, na ce: ‘Yan gidansu waye?’”

Ta amsa da cewa: “Nuwaira da Walida, ’ya’yan gidan Hajiya Mairo.”

Kafin na rufe baki, na ga kira na kawata wanda muka yi yan matanci da ita, wato Rukayya.

Na amsa, Rukayya ta ce: “Na turo miki wani video ta WhatsApp, buɗe kiga.”

Na ce: “Wani video? Yanzu Yasmin ta zo tana kuka wai a makaranta aka ce ni karuwace ce, har video na aka nuna musu a gidansu. Wai don Allah kawata, faɗa mun, wani video ne?”

Rukayya ta ce: “Ke dai ki buɗe, nima kawata ce ta turo min video.”

Bata karasa zancen ba, ta kashe.

Jikina ya fara kakkarwa!! Cikin tsoro zuciyata na bugawa dab! dab!, cikin sauri na buɗe datar wayata, na shiga. Ina buɗewa, abin da na gani abin ya tsorata ni, domin video ne na tsiraici na, wanda soyayya ta rudar da ni, wanda tsohon saurayina Abdallah ya ce na masa na tura masa video.

Ina gani, sai na fara jin hajijiya tana dibana. In ba don akan gado nake ba, da tabbas zan iya faɗuwa. Video ne wanda ya kai kimanin shekara goma sha huɗu (14 years) da na yi, ga shi yau ’yata an nuna mata, yanzu an fara mata gori. Na shiga uku!

Abdallah tsohon saurayina ne, wanda muka jima muna soyayya da shi, wanda ma ta kai ake ce mana Queen da King, domin na so shi kamar ba gobe. Kaunar da na masa ya sa na mallaka masa rayuwata, babu abin da nake boye masa a rayuwa, domin jin nake tamkar ba za mu rabu da shi ba. Amma a lokacin guda wata gugawa ce mai rabawa ta raba mu da shi.

Ko ya zo gidanmu hira, ko mu yi video call da shi. Amma video call ɗin mun fi yi da daddare. Karfe 9:00pm na dare tana yi za ka same ni a katifata, domin ba na ma yarda 8:40pm ta same ni a tsakiyar gidanmu balle kofar gida, domin ba na son Abdallah ya kira ni ya ji ba na nan. Domin ko a gida ba a aike ni a wannan lokacin, domin an san ina cikin bargo, duk da ba su zaton video call nake da Abdallah ba. Duk ɗaukan su waya nake da shi. Shigar da nake ba ma za su ɗauka ba, har video call nake dashi daga ni sai kayan barci nake kwanciya.

Wasu kayan barci ne wanda na ɗauko a gidan yayata Hajja Fatima, domin ba ta son na ɗauko su. Lokacin da ta gan su sai da ta yi min faɗa. Kaya ne ba irin na ’yan mata ba ne, irin na masu aure ne, don har ta kwace min amma daga baya ta dawo min da su tare da gargadin kar na sa a tsakiyar gida idan ba kwanciya zanyi ba. Domin Umma Inde ta gani da kayan nan sai ta yi min faɗa, duba da yadda kirata take, tabarakallah, balle na sanya kayan nan domin surarar da ke jikina sai ta bayyana. Duk yadda mace ta kai mace, to fa gaskiya na kai. Ina da sura da babu wani ɗa namiji da zai gani bai kyasa ba.

Wata rana Abdallah ya ce: “Haseena, ina neman alfarma a gunku.”

Na ce: “Wace alfarma?”

Ya ce: “Video nude ɗinki nake so ki turo min. Ina gani zan goge.”

Na ce: “What!!”

Ya ce: “Pls, Hubina,” domin haka yake ce min. Idan ya faɗa min haka sai jikina yayi sanyi, don ina son sunan a bakinsa, don ya iya faɗa.

Na ce: “Idan ka gani za ka goge? Ka yi min alkawari ba tare da kowa ya gani ba.”

Ya ce: “Na yarda, haba Uwar ’ya’yana, waye zai ga jikin matata? Hubina, ina gani zan goge, kuma sai na shiga bargo ma, hhhh.”

Na shiga bandaki na ɗakinmu, na yi masa na minutes biyu na tura masa.

Hakika abin da muka yi daga ni sai shi, kuma wannan ya faru kusan shekara goma sha huɗu (14 years). Amma yau gashi ’yata ana mata gori.

Ashe Abdallah bai goge video tsiraicina ba da na tura masa! Duk soyayyar da na nuna masa haka zai ci amanata! Toh, a ina video ɗin ya fito? Ko abokansa ne suka tura a wayarsu, shi ne suka tura a social media! Amma video ya kai shekara goma sha huɗu, amma ta ya ya bullo!! Mutum ba abin yarda bane!!!

Tabbas na shiga RUDIN ZAMANI.

Ƙarshe