8
Chapter.8
A kiɗime suka yi kanta, Nadiya da sauri ta buɗe fridge ta dauko ruwa sanyi a ka shafa mata a fuska a hankali ta farka, k'ok'arin mik'ewa ta ke za ta bi sawun Dad Mom ta yi saurin rik'e ta ta zaunar.
"Mommy please ki bar ni ko baku ji abin da ya ce ba ki bar ni na je na basa hak'uri na san maganar da ya yi cikin b'acin rai ne amma bai kai zuci ba." Mom da abu ya mata yawa ta ce. "No zauna ki huta barni ni na je na masa magana, kuskure dai kin riga da kin tabka babu damar maida hannun agogo baya amma shima hukuncin da ya yanka yayi tsaure dayawa."
Ta kalli gefen Nadiya da ke tsaye har lokacin da gorar ruwa a hannunta ta kasa tafiya, ba k'aramin tashin hanakli ta shiga ba ganin sumewar Nazli. "Ki kula da ita Nadiya ina zuwa." Daga haka ta haura sama ta same Dad cikin d'akinsa zaune a bakin gado ya d'aura tafikan hannayensa ya talafi kansa ya fad'a tunani. Jin shigowar mutum ne ya sa shi saurin tashi yana k'ok'arin cire agogon hannunsa, a hanakli Mom ta taka har gabansa ta rik'e hannunsa ta ce. "Haba Alhaji hannunka bai ribewa ka yar, duk girman laifin da yaran nan za su yi to bai kai kora daga gida ba. Idan hukuntatan kake son yi sai ka yi ta wata hanyar tunda akwai hanyoyi da dama da za'a hukunta yaro amma ba wannan ba, yanzu idan ta bar gidan ina kake son ta je?" Dama tana da wanda suka fi mu ne Allah na tuba yanzu da zamani ya shigo rayuwa ta canza tana gabanmu ma ga abin da ya faru ina ga bata gabanmu idon mu baya kanta?"
"Dan Allah ka yi hakuri ka yayyafa ma zuciyarka ruwa ka sauke maganar barin gidan nan haka, yanzu baka san halin da ta shiga ba jin furucin nan na ka wallahi baiwar Allah ta gane kuskuren ta kuma ba za ta kuma ba."
Tunda ta fara magana Dad ya yi shiru ya nutsu yana sauraron ta saida ya ji ta kai ayyah ya mata duba d'aya ya kauda kai. "Kin gama?" Na ce kin gama ko kuwa da saura?" Na riga da na na yi magana kuma babu wanda ya isa ya sa na canza min magana, gida dai nawa ne ko?" To na ce ba za ta zauna ba idan kin ga ba za ki iya d'auka ba to hanya a bud'e take za ki iya bin ta ku tafi, lokacin da take shashancin na ta tana zubar mani da mutunci a gari ai bata tuna bata da kowa ba sai ni, tunda rayuwar da ta zabarwa kanta kenan ai shi kenan ga hanya nan ta je ta d'aura daga inda ta tsaya idan kuma baki ji dad'in hukuncin nawa bane sai ki bi ta ku tafi."
Yana kaiwa nan da maganarsa ya shiga bandaki ba tare da ya yi mata duba na biyu ba ya shiga d'aura alwala domin sallan la'asar da ya wuce sa. Saboda bak'in ciki da damuwa Mom kasa motsawa ta yi ta zubawa bayansa ido duk da ya banko mata da kafar hakan bai hana ta zubawa hanyar ido kamar shi ne ke gabanta, yanzu ya yake son ta yi ne taya zai ce idan bata ji dad'in hukuncin na sa ba to ta bi ta. gaba d'aya ta rasa me ke mata dad'i, girgiza kai ta yi a hankali ta juya ta fita.
Kai tsaye palon ta koma inda ta samu Neesah da ta k'ira a waya d'azu da ta aje dukkan abin da take ta dawo gida babu lafiya, zuwan ta kenan bata dade ba ta zauna kusa da Nazli da ta zama mutum mutumi zuwa lokacin kukan ma ya tsaya sai ajiyar zuciya da take sauke lokaci zuwa lokacin. A hankali Neesah ta rik'e fuskar Nazli ta zuba mata ido a hankali cikin kulawa ta ce. "Sis me ya faru me ya same ki ne haka?" Talk to me is it about abin da ya faru jiya?" Ta kalli Mom da shigowar ta kenan ta tsaya gaba d'aya ta kasa shiga ciki don bata san me za ta cewa Nazli ba.
Mom.
Ta sauke nannauyan numfashi ta nemi wuri kusa da Nazli ta zauna, a hankali ta mike hannu ta dafa Nazli da ita ma idanunta na kanta tun shigowar ta cikin palon, yanayen ta kad'ai ya tabbatar ma da Nazli lallai bata yi nasara ba ta tabbata dai Dad ya dena sonta, baya son ganin ta ya tsane ta. Tunanin haka ba k'aramin karya mata zuciya ya yi kwalla suka cika mata ido. "Mom please can someone tell me me ke faruwa?" Me ya same Nazli kuma ya na ganku a haka?" Cewar Neesah da ta kosa ta ji abin da ke faruwa, mom ta kawar da kai gefe ba tare da ta ba Neesah amsa ba ta ce. "Abban ku ya d'au fushi matuk'a duk yadda na yi da shi na fahimtar da shi illar rashin dacewar abun da yake k'ok'arin yi ya ki saurarona, har yanzu yana kan dokin fushi amma na tabbata da ya sauk'a komai zai gyaru kalaman da ya yi ba su kai zuciya ba dan haka karki kullace shi. Ta shafa kan Nazli cikin kulawa. "Yanzu abin da zai faru ki bar gidan na kwana biyu da ya huce shi da kansa zai nemi ki mu basa speace na d'an wani lokaci ni da kaina zan zo na dauke ki." Duk cikin kwantar da murya da lallashi Mom ke maganar, ita kanta daurewa kawai take amma Allah kad'ai ya san abin da ke zuciyarta dauriya ce kawai take tana magana amma ba wai ita kanta bata fushi da Nazli kan abin da ta aikata amma ganin 'yarta cikin wannan halin ba k'aramin damuwa ta shiga ba.
Zuwa lokacin Neesah ta soma fahimtar gadar zaren sai dai abin bata fahimta ba shi ne batun ta na Nazli barin gida, amma sai ta ce. "Mom ina kuma ta za ta tafi?" Dama tana da inda ya wuce nan da gidan mijinta me?" Ne fa ban gane ba ku min bayani yadda zan fahimta mana." Mom ta harare ta ce. "Yanzu daga ina kike?" "Mom ba fa inda na je, ba wani nisa na yi ba na je party ne da muka had'a ni da hawayena." Ta fad'a cikin had'a fuskar. "Beside ba wanda ya bani amsar tambayar da na yi me ke faruwa." Ba tare da Mom ta bi ta kanta ba ta kama hannun Nazli suka nufi sashen ta, da kanta ta had'a mata kaya kala uku da dan abun da ba'a rasa ba cikin jaka ta rufe.
Ta kalli inda Nazli ke zaune ta ce, ki duba idan da abun da ban saka ba ki saka." "Uhm." Ta ce, ta bud'e akwatin da ta shigo da su d'azu ta fito da AtM na ta saka a handbag na ta kana ta d'aura gyale a kanta suka fita.
A palo suka tadda Neesah da Nadiya ta gama labarta mata abin da ya faru, suna tsaka da barin palon Neesah ta ce. "To yanzu ina za ki tafi kuma babu waya a hannunki idan muna son magana da ke fa?" Sai a lokacin Mom ma ta tuna da babu waya a hannun Nazli to ya za su yi magana? Kamar Nazli ba za ta ce komai ba sai ta ce. "Don't worry da inda zan tafi, ko gidansu Elharm ne zan tafi zuwa hucewar Daddy na dawo, waya kuma i will buy on my way beside ina da numbern ku a kaina so wannan ba damuwa ba ce." "No darling ba za'a yi haka ba, bari ma ki ga." nan Mom ta cire nata SIM dake wayarta ta matsa wurin wayar Nazli da ta yi kaca kaca ta d'auki SIM card na ta ta saka a wayarta kana ta mike mata da fadin. "Kin ga yanzu hankalina zai fi kwancewa, duk yadda a ke ciki ki kira ni ji ko?" "Okay Mom."
Har mota suka raka ta, koda ta zo shiga saida ta rumgume su d'aya bayan d'aya. Ta kalli Nadiya ta ce. "Nadiya ki shirya da driver ya kai ni zai zo daukan ki zuwa gida, ki gaishe min da Mama nima idan na samu dama zan shigo duba su." Nadiya ta kad'a mata kai cikin kuka ji take kamar rabuwar kenan ba za su sake haduwa ba, duk abin dake wakana a idon Dad dake sama yana kallo cikin d'acin rai ta ta window d'akinsa. Ji yake kamar ya je ya tsaida ita ya hana ta tafiyar amma saboda taurin zuciya ya rik'e kansa duk da yadda zuciyarsa je zal-zalarsa kan hakan amma tafi ta'alka da gwara ya nuna mata kuskuren ta nan gaba ba za ta kuma ba. Da sauri ya saki labulen wajan ya matsa gefe ganin ta d'aga kai tana kallon saitin window na sa da hope din ganinsa koda daga nesa ne ko za ta ji sauki a ranta.
Ba don ta so ba ta shiga motar driver ya tada motar suka bar farfajiyar gidan haka take d'aga masu hannu suma suna d'aga mata hannu har suka bar compound d'in gidan mai gadi ya rufe gate. Wani irin kuka ne ya zo mata, me ya sa take jin ta rabu da su kenan ba za ta sake ganinsu ba? Driver ne ya katse ta hanyar cewa. "Uhm Hajiya sai hakuri fa kukun nan ai sai ya sakar miki zazzabi, ban dai san me ke faruwa amma na san komai na duniya mai wuce ne idan ka yi hakuri Ka rik'e Allah to wata ran sai labari." Ta kad'a masa tare goge haywayenta ta ce. Na gode Sahle." "Ba komai Hajiya yewa kai ne." ta masa kwatancen gidansu Elharm kawarta suka kama hanya.