NANNY(MAI RENO)

4

by @jamilaumarjanafty

*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Na*

*AISHA ALTO*
*JAMILA UMAR(Janafty)*


*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*

*Sanyi flusher!* 
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. 
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*

*Tightening set na hade mace ta  dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.

*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*

*Muna da gimbiyar zabuwa  da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.


       *BABI NA HUDU*

  *MALLAM BELLO GURGUN DANBATTA* Sunan mahaifin Mufeeda wanda shima ya kasance haifaffan garin na Ɗanbatta ne gaba da baya, haka ma matarsa Inna Fulera itama haihuwan nan ce kuma tashin nan.

Sai dai kuma tun asali dukkansu biyun sun fito daga tsatson talakawa ne futuk marasa ƙarfi kuma dama auren zumunci ne tsakanin Bello da Fulera, bayan haka kuma dangin nasu basu da yawa saura sun mutu sauran kuma sun lula garuruwa neman kuɗi.

Bello gurgun Ɗanbatta ya samo asali ne da tun yana yaro ciwon daji yakamashi ahannu wanda yayi sanadiyar cire mai hannu guda ɗaya shikenan in za'a kirasa sai adinga mai in kiya da Bello gurgun Ɗanbatta, daga Malam Bello har Inna Fulera duka sun rasa iyayensu so suna zaune awani ƙuntataccen gidan ƙasa cikin matsi da wahalar rayuwa, dukkansu babu wanda yayi ilimin boko sai na allo shima ɗin sama sama don lokacin bawai sanin darajan abun sukayi ba, balle su damu dashi baida wata sana'a sai sana'ar noma kayan lambu kamarsu tumatur dasu kabeji da albasa, yana shiga cikin gari yana siyarwa da hannun nasa guda har su samu su rufama kansu asiri.

Sun shekara kusan goma da aure kafin Allah yabasu Mufeeda wanda bayan ita ta haifi 'yan biyu duka maza basu zo da rai ba daga lokacin kuma haihuwa ta tsayama Inna Fulera sai suka cigaba da rainon Mufeeda wacce suka ɗauki son duniya suka ɗora mata saboda ita kaɗai garesu itace 'yarsu kuma ahalinsu sannan abokiyar hirarsu shiyasa itama Mufeeda ta taso cikin so da ƙaunar duka iyayen nata guda biyu, duk da tazo ta iskesu cikin wahalan rayuwa amma suna iya bakin ƙoƙarinsu akanta don ita kanta Inna Fulera bata zauna ba tana saida dafaffen kabeji acikin gida ana zuwa siya ba laifi tunda tana da   tsabta...

Haka suka cigaba da gangara rayuwarsu da daɗi ko ba daɗi har lokacin da Mufeeda keda shekara goma sha uku a duniya ta girma duk wasu alamun budurci basu bayyanar mata ba sakamakon siririyace ita bata da jiki sosai, kwatsam suka tashi da wani rashi, rashi mai girma daya taɓa zuciyarsu wanda har yau suka kasa mantawa dashi na rasuwar Bello Gurgu sanadiyar faɗawa rafi ruwa ya cinyesa Inna Fulera da Mufeeda sunyi kuka kamar ransu zai fita, duk da a lokacin Mufeedan nada ƙarancin shekaru amma wannan rashin da sukayi ya tsaya mata sosai a cikin ranta. 

Ko takaba Inna Fulera bata fita ba suka fara shiga tasku da wahalar rayuwa na babu sai su kwana basu ci ba, abun na damunta duba da ƙarancin shekarun ita Mufeedan shiya sanya tana gama takaba labarin neman ma'aikata daga gidan Hakimi ya sameta inda Tahir ya bada cigiyar neman waɗanda zasu dingama iyayensa hidima yana biyansu duk wata Inna Fulera batayi ƙasa agwiwa ba ta isa gidan Hakimi gaban Goggo Abu sai dai koda taje an riga angama ɗaukan adadin ma'aikatan, nan Inna Fulera ta faɗi gaban Goggo Abu tana kuka tana roƙonta data rufa mata asiri ta taimaki rayuwarta data marainiyar Allah Mufeeda toh a lokacin sai taausayin ƙarancin shekarun Mufeeda ya ɗarsu a zuciyar Goggo Abu har yayi sanadiyar data ɗauki Inna Fulera amatsayin hadimarta amma in tagama da shashenta takan shiga madafi ta taimaka duk wata 15k Tahir ke biyansu dukkansu wanda cikin lokaci kaɗan ya taimaki rayuwar mutane dadama ciki harda Inna Fulera wanda cikin haka ne ta sanya Mufeeda a makarantar Primary Ɗanbatta tana zuwa idan ta taso sai ta biyo gidan Hakimi wajen Innarta taci abinci ta ƙoshi ba shashen datake zuwa sai shashen Goggo Abu ta zauna tayi shuru dake bata da yawan magana wani lokacin in Goggo Abu ta ganta sai Tahir ya faɗo mata acikin ranta tana tunanin shigen miskilancinsa amma in ta kalli yanayin Mufeeda sai taga ta shanyeshi haka kurum take jin tausayin yarinyar shiyasa take janta ajiki sosai.

Mufeeda bata da wata ƙawa agarin sai Lantana wacce maƙotansu ne itama Mamarta tana aiki agidan Hakimi ita kaɗai ce ƙawarta kuma gashi makarantarsu ɗaya kuma ajinsu ɗaya, shiyasa sai tasu tazo ɗaya kuma in sun tashi daga makaranta tare suke wutowa gidan Hakimi wajen iyayensu, Mufeeda bata da saurayi kamar na sauran 'yanmatan ƙauye ko nace bata bi ta kansu kwata kwata saboda ita bata son auren wurin da'ake musu mutum ɗaya ne take kulawa shima sai ya dameta Iliya mai rake, tun tana ƙaramarta yake bibiyarta abokin saurayin da Lantana zata aura ne Murtala shiyasa wani lokacin in sun biyo hanyar makarantar allo in Murtala yaja Lantana gefe itama sai Iliya ya jata duk dai bata sakarmai fuska bai damu ba saboda yaci ace ya saba da yanayin rayuwar Mufeeda.

  
   Inna Fulera bata rufe shekara da samun aiki agidan Hakimi ba Farida tazo garin inda ta samu Goggo da shawaran tana buƙatar a nema mata wata yar yarinya wacce zata tafi da ita amatsayin Nanny saboda kula da Naila sai su dinga biyanta duk wata suna aikoma da iyayenta tunda ta lura duk waɗanda Umma ke samo mata daga Kano ita basu mata, Goggo Abu na jin haka sai Mufeeda ta faɗo mata arai amma sai ta fara tunanin kamar ba zata iya ba, ilai ko Faridan na ganin Mufeedan tace ko itama aka bata ta isa, Goggo Abu bata yanke hukunci ba sai da ta nemi shawaran Hakimi da Innaro suka kuma bada goyon baya Duk Da Tahir ɗansu ne amma suna da kyakkyawan sheida akanshi shi da matarshi basu wulaƙanta mutane...

Cike da ƙwarin gwiwa Goggo Abu tasa aka mata kiran Inna Fulera ta labarta mata muradinta azahirin gaskiya taji firgicin maganar duba da Mufeedan kaɗai gareta kuma ta ƙwallafa rai da ita amma kuma Goggo Abu bazata nemi alfarma taƙi mata ba, bata da yarda zatayi ta amince amma zuciyarta ba daɗi duk da ko ta tabbatar Mufeeda zata samu ingantacciyar rayuwa agidan Tahir, amincewar Inna Fulera ya sanyayama Goggo Abu rai nan ta mata alƙawarin insha Allahu bazatayi nadama ba, Farida ta koma bayan ta bar sallahun Mufeeda ta shirya sati mai zuwa direba zai zo ya ɗauketa.

Inna Fulera data koma gida tayi kuka sosai kuma bata iya sanarma da Mufeeda ba, fahimtar haka yasa Goggo Abu ta saka Inna Fuleran ta turo mata Mufeedan ta sanar da ita, wayyo gwanin ban tausayi duk da ta kasance mai rauni wajen kazar kazar ɗin rayuwa amma kukanta ya kasa ɓoyuwa tana kiran ita bazata bar Innarta ba Goggo Abu ke ta lallashinta amma taƙi yin shiru ƙarshenta ma ta tashi da gudu ta fita sai gida chan taje ta sakama Inna Fulera kukan ba inda zata tafi ta barta, kwana tayi lallashinta da bata baki amma Mufeeda taƙi yarda.

Sati kuma na cika sai ga Tahir yazo garin Garzali ya kawoshi kuma shi Farida bata sanar dashi komai ba, Goggo Abu kuma tana ganin haka sai ta zata ya sani ne shine yazo tafiya da Mufeedan nan da nan tasa aka kiramata Inna Fulera tace tayi maza taje ta shiryo Mufeeda da kayanta ga Attahiru nan yazo tafiya da ita Kaduna, Allah sarki raba uwa da 'ya sai Allah da kuka da komai Inna Fulera ta kawo Mufeeda gidan Hakimi sai lokacin ma Tahir yasan da maganar bai wani damu ba sanin dama Farida bata ɗaukeshi bakin komai ba, abun kuma yayi mai daɗi ko banza yana daraja garin haihuwarsa haka Mufeeda ke kuka Inna Fulera nayi taƙi shiga mota ta ƙanƙameta Innarta tana wani kuka mai ban tausayi tare da ƙawarta Lantana, har sai da Hakimi yace a haƙura da tafiya da Mufeedan asamu wata saboda yadda daga Mufeedan har Inna Fuleran suka bashi tausayi haka shima Tahir wanda da kanshi yaje ya riƙo hannun Mufeeda yana kallonta ƙwarjininsa ya hanata yi mishi gardama gaban Inna Fulera ya duƙa yana ƙara jaddadamata insha Allahu zai kular mata da Mufeeda kamar 'yar da ya haifa kuma alƙawari ne yayi mata zai dinga kawo Mufeeda lokaci bayan lokaci tana zuwa ganinta, wannan kalaman nashi su suka sanyaya ran Inna Fulera da kanshi ya saka Mufeeda cikin mota da ƙullin kayanta wanda ƙwarjininsa da kimarsa yasa ta kasa mishi gardama amma har motarsu ta ɗaga daga ƙofar gidan Hakimi Mufeeda na kuka tana ɗagama Inna Fulera hannu itama tana kuka tana ɗagamata Iliya ma yana laɓe daga chan yana leƙen tafiyar Mufeedan sai da ya share ƙwallah saboda an rabashi da masoyiyarsa zuwa birni shima Murtalan Lantana ke gaya mai..

  Koda Farida taga Tahir da Mufeeda bata damu ba dama tunda yace yau zashi Ɗanbatta ta sani Goggo Abu zata bada Mufeeda azo mata da ita shiyasa bata damu ba, lokacin da Mufeeda ta tsinci kanta agidan Tahir ta sani ta shiga wata sabuwar rayuwa na bambamcin komai kama daga wayewa da garin ma gaba ɗaya, da farko bata iya sakin jiki ba duk da ko ɗakinta ita kaɗai Farida ta bata bayan ta miƙa mata amanar Naila wacce lokaci ɗaya yarinyar ta shiga ranta abunda ya ƙara sanyayamata rai shine yadda ko su Basma basu nuna mata bambamci duka ɗaya suke ga Iya itama tana mata kyakyawan mu'amala ta ɗauketa kamar 'yar data haifa da cikinta, balle Farida da bakomai take bama muhimmanci ba, kuma ance mai ɗa wawa balle data lura yadda Naila ke samun kulawa sosai wajen Mufeeda cikin lokaci kaɗan tayi kiɓa ta chanza shiyasa komai nata na ɗakin Mufeedan awajenta yake kwana in ba Tahir bane ya matsa ta ɗaukota nono kuma in tana nan ne take bata in ko bata nan sai dai ta wuni shan madaran ruwa.

Farida bata da matsala ta ɓangaren ƙyashi ko wulaƙanta mutane ta fito daga gidan arziki shiyasa Allah bai ɗora mata wannan ƙyashin ba, komai zatama Basma da Bassam sai ta haɗa da Mufeeda da Iya haka ma Tahir baya nuna bambamci akan komai abinci tare suke ci, tun Mufeeda na ɗari ɗari har ta saki jiki ta saba, kuma duk wata Tahir na turama Inna Fulera 20k da farko cewa tayi bazata karɓa ba yayi yawa sai da Goggo Abu ta matsa mata.
Watanta uku da zuwa Farida tabama Tahir shawaran asanya Mufeeda a makaranta nan da nan ko ya yarda da shawaranta shima abun na ranshi cikin sati ɗaya cike cikenta ya tabbata ta samu gurbin karatu a Model School Kaduna inda ta fara daga Js1 duk da tana Primary 4 ta tsaya lamarin dayama Mufeeda daɗi sai da tayi kuka da farko ta fara samun matsala ta ɓangaren wayewa da kuma turanci, sai kuma Tahir ya sama musu Lesson Teacher ita dasu Basma yana koya musu suma kuma suna ƙoƙarin koya mata abunda bata gane ba tunda suma Js1 ɗin suke sai dai su Commond School sukeyi sai an kaisu kana direba ya wuce da ita in ta tafi makaranta sai Iya ta karɓi kula da Naila wacce tasha kuka kafin ta saba da rashin Mufeeda kafin ta dawo makaranta ta gaji da kuka ta haƙura.

  Sai da suka samu hutun farko kana ta roƙi Tahir wanda take cema Daddy don amatsayin uba ta ɗaukesa zata je Ɗanbatta direba ya kaita ta kwana biyar ta dawo saboda Naila, zuwan daya yima Inna Fulera dad'i haka suka ƙanƙame juna Lantana da wasu mutanen gari basu iya gane Mufeeda ba saboda yarda ta zama 'yar gayu tayi kyau kamar ba ita ba, hakama Iliya daya ganta sai da hankalinshi ya tashi na ganin tabbas Mufeeda tafi ƙarfinsa koda ta koma bikin Lantana ya kusa, bata saran zuwa ba amma data roƙi Mami Farida ta roƙar mata Daddy sai gashi ya barta taje ta kwana ɗaya ta dawo zuwan daya sanya ta zama zara cikin wata saboda kyanta da kuma ilimi da wayewar data samu tare da cigaban rayuwa.

Matsalar Farida da Tahir ta fara girma tunda yanzu sai ta shafe wata da watanni bata bashi hakkinshi ba, kuma shi ba dutse bane yana buƙatar wajen ɗebe kewa da damuwa, amma sam Farida hakan baya gabanta in ya nemeta tayi ra'ayi to laba'asa ne da komai ya kammala shikenan ko ajikinta, abun na damunshi kullum cikin azumi yake gashi bata zama agida abun haushi yawon gidajen ƙawaye in Farida taji biki jikinta na rawa tun ada yana ɗauka yarinta ne in taƙara girma zata bari amma ina ko raguwa baiyi ba, su Abba ko ya gaya musu suka mata faɗa zata nuna taji amma kuma ta bayan kunnanta yake wucewa haka Goggo Abu wacce ke tausanshi kada ya sanarma Hakimi halin dayake ciki, maganar ƙarin aure kuma ba ra'ayinshi bane tunda shi mutum ne mara son hayaniya gashi kuma da haƙuri amma ƙanwarsa Ashe ce ta bashi shawaran ya ƙara aure ya bar Faridan ita taje chan ta ƙarata da halinta tun bai yarda da shawaranta ba har ya fara tunanin shine mafita toh Goggo Abu ce ta takamai burki sau uku kenan yana zuwar mata da maganar tana dakatar dashi, saboda dalilinta na kada azo ayi abunda zai lalata zumuncinsu, abun na damun Tahir amma haƙurinsa da kuma kawaicinsa yasa ba'a gane halin dayake ciki banda abokinshi kuma amininshi Ishaq.


Wannan kenan.


******

*Kano*

_Tarauni Gra_


 Ƙudundune take a cikin lallausan bargo tana sharar barcinta hankalinta kwance Umma ce ta shigo cikin bedroom ɗin tana bin Faridan da kallo lokaci ɗaya tana duba agogon bangon daya ƙawata bedroom d'in ƙarfe 12 daidai kai ta girgiza kafin ta ƙarasa kusa da Farida gefenta ta zauna tana ƙara gyara zaman doguwar rigar leshin dake jikinta matashiyar dattijuwa ce fara mai yalwar fara'a kallo ɗaya zaka mata ka fahimci hutu da jin daɗi sun zauna mata fuskarta kuwa ɗauke da kwalliyarta don Hajiya Aliya bata yarda da zama haka ko kuma girma ya cuceta ba a'a tafi kowa kula da mijinta da tattalinshi, inda ace Farida tana lura da yanayin rayuwar iyayen nata da har abada Tahir bai taɓa complain akanta ba.


 Bargon ta yaye kafin ta fara buga ƙafarta tana faɗin "Farida...Ke Farida..." Miƙa tayi tana wani ƙara narkewa bargon take ƙoƙarin ƙara ja, da sauri Umma ta fizge tana faɗin "Wai miye haka..? Tun jiya da kika iso kike kwance kina wannan barcin, bazaki tashi kiyi ƙoƙarin komawa gidanki ba baki tunanin wani hali mijinki ke ciki da 'ya'yanki balle ma ki riƙa tuna ƙaramarsu Naila mai shan nono..."

 Ta fada cikin damuwa, miƙa Farida tayi tana turo baki kafin ta miƙe da ƙyar tana gyara gashin kanta wanda duk ya baje saboda barci, fuska ta yamutsa kafin tace "Toh Umma me zai samesu..? Lafiyansu ƙalau su fa, Basma ba yara bane, Tahir ma haka Naila kuma Mufeeda na kula da ita, in ma ta tafi makaranta iya na gida zata kula da ita.." Ta faɗa tana zuro ƙafarta ƙasa, kallonta Umma tayi kafin ta dafa kafaɗarta tana faɗin "Toh naji tashi dai ki yi wanka ki shirya ki fito ki karya ki yi haraman tafiya kinji Faridata..?" Ta faɗa da sigar lallashi da lalama, miƙewa Farida tayi bayan ta zura wani takalmi mai taushi tace "Umma ina Abba..?

 Miƙewa itama tayi tana faɗin "Abbanki ya fita tun safe yana da baƙi, amma ya bar sallahu direba ya tuƙa ki zuwa Kaduna yace bayason kina doguwar tafiya ke kaɗai.." Murmushi ta saki kafin tace "Abbana kenan toh me zai sameni nifa ko achan Kaduna Tahir baya tuƙani duk inda zani da motata nake zuwa har Ɗanbatta in kinga direba ya tuƙamu tare ƙila tafiyar tazo ɗaya ne.." Murmushi Umma tayi kafin tace "Hakane, toh kindai ji sakonsa ko..? Toh kiyi maza ki shirya ki fito.." ta faɗa tana kama hanyar ficewa, ƙara tura baki Farida tayi kafin tace "Kai Umma sai wani koro na kikeyi.." Ta faɗa tana tura ƙofar toilet Umma bata ba zancenta muhimmamci ba tace "Eh saboda baki da gatan daya wuce gidan mijinki da 'ya'yanki.." Faridar na jinta daga bayi sai ma ta kyaɓe baki don ita basu dameta ba gani take da ƙafarsu da lafiyansu sai ta zauna ta ƙoƙarin ƙare rayuwarta akansu.


 Sai da Farida ta shafe wajen awa ɗaya kana ta fito daga cikin bedroom ɗinta na gidan iyayenta, sanye da wata irin shadda Gezner mai ruwan brown ɗinkin doguwar riga, sai ɗaurin Maryam Babangida data cukashi, fuskarta ba kwalliya amma kuma kallon farko zaka mata ka fahimci bata da wata damuwa, vail ne yafe akanta sai ƙaramar jakarta Umma ta tarar akan dining tana breakfast cikin yanga ta ƙarasa itama taja kujera ta zauna tea kad'ai tasha sai ferfesun kayan cikin ta miƙe tana share bakinta da tissue, kallonta Umma tayi kafin tace "Don Allah Farida ki dinga zama agidanki ba don niba sai don ki girmama darajan aure ki kuma girmama haƙurin mijinki akanki plz.."

 Rausayar dakai tayi kafin tace "Umma kenan Tahir ya gama shanye ku kuma, kamar yadda ya gama da iyayenshi, shikenan kuma ni ban san ciwon kaina ba Umma nafa girma nima daidai gwargwado na mallaki hankalin kaina ai nasan me nakeyi, bikin fa ƙanwar Beauty akayi fa Umma kuma kinsan yadda muke da Beauty tun muna makaranta, kawai shegen ƙorafin shi ne yayi yawa..." Ta faɗa tana ɓata fuska kafin ta wuce ta koma cikin bedroom ɗinta ta ɗauko ƙaramar trolley ɗinta ta fito tana faɗin "Umma zan tafi sai munyi waya.."

   Umma ta bita har waje inda direba ke jiranta trolley d'in direban ya karɓa ya saka cikin wata baƙar Venz ɗin Farida, kafin ya buɗe mata gidan baya sai da ta shiga kana ta leƙa tana fadin "Umma zan bashi kuɗi ya shiga motar haya in mun isa, ki gaida Abba..." Kai Umma ta gyada tana faɗin "Allah ya kiyaye hanya kar dai naji kin sake fita har zuwa nan da sati biyu Allah kuwa.." Dariya Farida ta saki har haƙorin Makkanta sai da ya bayyana kallonta Umma tayi kafin tace "Kinji ni ko baki ji ba..?"

 Kai ta gyaɗa kawai batayi magana ba amma acikin ranta tana tunanin irin shagalin da suke dashi ranar sati anan Kaduna, ƙanin Bilkisu zai yi aure dole suje su raƙashe, har motarsu ta fice daga haraban gidan Umma na ɗaga musu hannu ita kuma Farida sai ta ƙara gyara zama ta jingina kanta jikin kujera ta fito da wayarta ta fara latsawa tana sakin murmushi lokacin data shiga WattsApp, inda taga group ɗinsu na Classes Bbys na waɗanɗa sukayi makaranta tare ya cika da massagea tasan ƙila maganar yadda bikin ƙanin Bilkisu zai gudana ne jiki na rawa ta shiga ta fara bin Chat ɗin cike da farin ciki.


*HIJABS CORNER BY JANAFTY*

*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, ɗinki cikin kwarewa da* *mabambanta design,  muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan ɗaya ko sari.*
****, tuntuɓa ta wannan lambar*
*KADUNA/ZARIA*



*Aisha Alto*
*Janafty*