RIGAR ARO

17

by @pherty001




Nan masu camera kowa ya dauki position ɗin sa suka cigaba da haskawa, Nurayyah ta cire glass ɗin idanun ta taqi cire facemask Shima glass din ta cire shi dan girmama principal ɗin saboda a shekarunsa ya haife ta, tace "Malam abinda ya kawo mu, muna so mu san yaran da kuke tunani karatun su zai iya tsayawa a matakin primary kawai saboda rashin gata ko talaucin iyayensu, babban burin tafiyarmu shine mu tabbatar da cewa yara sun sami ilimi, we are here to take full financial responsibility for their future education, so iya waɗanda zasu je secondary school kawai Kuma ake tunanin iyayen su ba zasu iya providing ba." Principal da sauran malamai suka yi murmushin farinciki kafin yace " godiya muke Hajiya, ashe da sauran masu kishin talakawa a garin nan, gaskiya ba qaramin taimako bane sannan kuma ba qaramin tunani aka yi ba tabbas Al'Qaseem Binnani zai kawo mana canji a siyasar sa, muna da tarin yara masu kwakwalwa sosai waɗanda muke kyautata zaton idan suka gama primary karatun su zai tsaya saboda iyayensu ba suda qarfin aljihu ", Nurayyah ta jinjina kanta tana qara kallon malaman kafin tace "kuje classes din ku duba yaran sai ku bayar da list mu gansu"
nan take principal da sauran malamai suka ji dadi har da tabi, aka zabi malamansa da zasu je, babu jimawa sai gasu sun dawo dauke da list din sunayen, Nurayyah ta karbi takardar ta duba sai da gabanta ya fadi saboda kudin sun yi yawa sosai, cikin basarwa kada su fahimce ta, ta mika ta ga ɗaya daga cikin jami'an tsoronta the lead security guard, ya karɓa da sauri yana kallon ta, cikin izza da wata irin qasaita tace "Tura kuɗin da suke bukata a asusun bakin principal, insha Allah zan sake dawowa na bincika, make sure you take a very clear picture of the name list a cikin wayarka, bana son in dawo  na tarar  an cire sunan wani yaro maras karfi an musanya da waɗanda suna iya affording shiga school ɗin.", principal yace " insha Allah hakan bazai faru ba Hajiya, zaa masu adalci iya wadanda ke cikin wannan list zaa dauki nauyin karatun su, Allah ya saka da khairan ".  Sanda suka fito daga office ɗin  aka soma zagaya wa da ita tana duba school ɗin, ya soma yi mata korafe-korafe akan taimakon gwamnati da suke nema ta gyara classes cos idan damina yazo yara basu karatu yanda ya dace sama yana yoyon ruwan sama, sai rashin isassun kujerun zama da desk, da littafan karatu da gwamnati ta saba bayarwa ga yara kyauta wannan karon ba'a aiko ba da sauran su, kuma nan take Nurayyah ta amsa qorafin su tayi masu alqawari sune na farko da zaa waiwaya idan har Binnani yaci zabe ita da kanta zata zo tayi masu gyaran, cikin farinciki principal da malamai suka soma yi mata godiya, masu camera sai haskawa suke lokacin da ta harɗe hannuwanta alamar roqo gare su akan su zabi Al'Qaseem Binnani, sanda zata tafi har wurin motocin ta suka rakata ta bayar da umarni kudin da tazo dasu cikin envelope a bawa principal da malamansa, nan fa wata godiya aka fara mata suna faɗin "Sai Binnani".
*
Asokoro District Millennium City, 

Wani ƙaton mansion ne babba, ginin gidan ya kasance modern architectural masterpiece, duk yanda naso rubuta labarin tsaruwar mansion ɗin zai wuce tunanin ku, abu daya dake burge ni da gidan yanda yake da tsaro da securities, (special elite security guards).
Can na hango Al'Qaseem Binnani  a private backyard ɗin sa zaune a saman wata hadaddiyar kujera akan babban balcony dake saman hawa na biyu na ɓangarensa, Binnani yana sanye da farar shadda mai laushi da tasha ɗinkin hannu na sarauta, shekarunsa sa 40 a duniya, shekrun da suka nuna asali cika da kamalar sa, yana da wani irin kwarjini dake ratsa kowacce zuciya shiyasa duk inda yaje ko ya shiga yara da manya sai Binnani, shine kaɗai iyayen sa suka haifa, mahaifin sa bai jima da rasuwa ba duk bai fi 3yrs ba, yana zaune tare da mahaifiyarsa a mansion ɗin, mutum ne mai sauqin kai bashi da girman kai ko kaɗan, wani lokacin idan yana tare da ma'aikatan sa suna dariya da raha bazaka taba tunanin zai iya ba, da yawa masu aikin gidan Simple Man suke kiran sa a boye, yana da kyawawan hali kuma yana kyautata masu haka yana kyautatawa na waje bama su kaɗai ba, matansa da yawa sun sami aiki qarqashin sa shiyasa ba zasu taba manta alherin sa ba, har ana kyautata zaton shine zai lashe takarar gwamna da ake gab da yi yanxu.
Zaune yake yana duba wata jarida sanda guard din sa ya shigo cikin girmamawa bayan yayi sallama Binnani ya amsa, yaje kusa dashi tare da miqa masa iPad din hannunsa, Binnani bai karɓa ba sai ya dago daga kallon jarida yana kallon guard din, yace "menene wannan? Cikin girmamawa guard din yace " qarya take da sunan ka a gari, shine ake haska live" Binnani ya maida kallon sa ga iPad din kafin ya saka hannu ya karɓa yana kallonta sanda ake mata qorafi abubuwan da makarantar take buqata kuma ana nuna komai da gaske, abinda ya daure masa kai yanda tayi masu alqawarin zata gyara komai tayi providing duk abinda suke so da zarar Binnani yaci zabe, kamar bai ji da kyau ba sanda ta kira kanta Matar Binnani, "matan Binnani har guda nawa ne" yayi tambayar yana kallon guard din cikin tuhuma, guard din bai amsa ba Binnani ya maida kallon sa ga iPad din da gaske kuma school ɗin na buqatar gyara daga yanda yaga ana nuna komai, hankali da tunanin sa bai taba bashi hakan ba, wai yaje primary school yayi gyara, ya yatsina fuska duk da ta rufe fuskarta da facemask hakan bai sa ya gane qaramar yarinya bace daga murya da idanun ta, bai gama kallo ba saboda takaici ya miqa wa guard din iPad yana faɗin "And who is she?"




End of free pages.....