G_D - 19
Har ta isa gida bata juyo ba, jikinta da zuciyarta ba su daina rawa ba, tunanin me zata fadawa Umma Hindu ma be ko zo mata ba, domin yau ta ga abun da ya fi fadan Umma Hindu, ta shiga gidan a firgice jikinta nata rawa hannunta a wuyanta, kowa yana tambayar lafiya amman bata iya bada alamar komai ba, idonta sun fito alamar a tsora ce take.
"Allah kadai ya san me yarinyar nan ta gani, kullum sai yamma kike turata, yin kara, kuma kin san fitar rana tsaka ko magariba bata da kyau"
Mutanen gidan suka rufe Umma Hindu da fada, Batula dai bata iya yima kowa bayanin komai ba, har lokacin a firgice take, ga wani azababen zafi da take jin makoshinta na yi, bakinta ma ciwo yake. Haka ta kwana bata fadawa kowa abin da ya faru ba, duk kuwa da irin tambayar da ake mata, sai dai tunani be barta ta runtsa ba, waye wannan mutumen? Wata kila likita ne domin be yi mata kama da aljannu ba, amman taya ya san idan an taba gurin zata iya magana? Shi ne abun da yayi ta mata yawo akai, kuma ta gagara samun gansashiyar amsar da zata kama, wata kila dan ba ta taba gwada yin magana ba ne, ta kai hannunta ta rike makoshin ta fara yunkurin yin magana amman abun ya ci tura, kamar ba ita ce tadun ta iya furta sunanta ba.
Sai ta samu kanta da murmushi da hawaye a lokaci daya, ko a iya yau ta mutu zata mutu da wannan farincikin na jin sautin muryarta da ta yi. Sai kusa asuba bachi ya dauke ta domin ta raya daren da kokarin gwada yin magana, sai dai kuma hakarta bata cin ma ruwa ba, har bachin ya sace ta.
Bata yi bachin minti talati ba ta farka da wuri kamar yadda ta saba, ta hau surfen da ta saba, tana surfen tana tunanin muryarta, idan ta daka ta daka sai ta taba wuyanta ta gwada yin magana amman maganar bata fita. Haka dai ta yi ta yi har ta gama surfin ta wanke, ta dauka ta fita ta siyar da katsarin sannan ta dawo da kudin ta shiga dakin Umma Hindu, ta same ta zaune rike da wani kudin tana kirgawa Batula ta saka hannu biyu tana kai kasa cike da ladabi ta mika mata kudin hannunta. Ta karba ta kirga.
"Karki yi nisa, kina gama karyawa ki zuba ruwa ki yi wanka ki saka tufafinki mai kyau, ki tafi gidansu Ramatu ki zauna can mun yi magana da ita zata kai ki gurin da take kai mutane aiki, kin ga dai ni ai na yi girma da zuwa, duk da dai wasu suna zuwa, amman tace an fi son yara, idan kika tafi zamu samu mu tara kudin aurenki idan Allah ya kawo miji, kuma wasu hidindimun za su rage mana, amman ban ce ki fadawa kowa inda zaki ba"
Batula ta kalleta idonta na cika da hawaye.
"Mi? Kukan zaki fara na munafurci? Har sai an gane Baba Auta ya saka baki? Na rantse kika hana wannan tafiyar na lahira sai ya fiki jindadi a gidan nan, jiya da aka ce za a saka ki boko kina murna ke anamimiya, amman yau da yake ni zaki yi ma wahala kin fara kuka ko? Hakan nan kawai sai a saka ki boko ba zaki zauna a gida ki amfana min komai ba? Ba ke kika kashe min aure ba? Sauran kuma idan kika tafi can din ki yi abun da zai saka a dawo da ke, ai na san halinki, in ci ubanki kuma Wallahi"
Ta saka hannayenta ta share hawayen da suka zubo mota tana jin kamar an raba duniyarta gida biyu, saboda bakinciki miyasa Umma Hindu bata duba mata? Miyasa ita ba a damuwa da matsalarta? Ba a tambayar shawararta? Ba a neman yarda? Karatun da Turaki yace zai maidata ya tashi kenan? Yanzu kuma zata tafi wani gurin ta yi zaman bauta? Gashi bata isa ta fadawa kowa matsalarta.
Ta fito daga dakin tana kokarin tare kukanta gudun kar aga hawaye a idonta a fahimci damuwarta, ta shiga bangaren Baba Auta ta gaishe shi, sai ya sanar mata daga yau ba zata sake zuwa daji ko gona dibar kara ba ya hana hakan domin an fada masa abun da ya faru jiya, daman tun da ya dawo aka fada masa ya kira Umma Hindu ya ce daga yau kar ta sake aika Batula yin kara a daji, ta rika siya a cikin kudin sana'ar da suke, idan kuma ba haka ba sai dai a daina sana'ar gaba daya, Umma Hindu ta yi bakinciki sosai amman bata nuna ba, saboda ta san abun da ta shirya tun a satin da yawu, gashi kuma an yi daidai da faruwar wannan abun.
"Ai ba zan sake zuwa ba Baba, Umma Hindu birni zata tura ni gurin aiki, ina ma ace ka sani ka hana wannan tafiyar, ni ban taba zuwa ko'ina ba, kuma ban san su waye ba, ban san ko za su karbe ni ba"
Ta fada a ranta a zahiri kuma kanta na tana share hawaye.
"Ki yi hakuri kinji, jarrabawa ce, da Allah ya so da ya raya iyayenki kin tashi a hannunsu, amman sai kika tashi hannun macen da yayanta ma ba su jidadinta ba balle wani, amman wata rana sai labari, wahala bata taba dawwama ba, Allah zai kawo miki dauki domin iyayenki mutanen kirki ne, musamman mahaifiyarki mace ce mai hakuri mai kawar da kai, ta yi hakuri da yan'uwanta sosai lokacin da take raye, haka take kamar ke, ba ki rage komai daga kamaninta ba, iyayenki sun sha wahala kamin su same ki Batula, barinta hudu sai ake cikin ya tsaya, babu jnda mahaifinki be yi neman magani ba, ace iska ne, ace asiri ne, haka dai har Allah yasa aka dace, da aka samu cikinki iyayenki kamar su zuba ruwa a kasa su sha, balle kuma da kika zo duniya, duk abun da mahaifinki ya mallaka a ranar sai da ya kyautar da shi, gashi mahaifiyarki ta wahala gurin haihuwarki, saboda mu nan mutanen karkara babu ruwanmu da zuwa asibiti, amman dai an yi nasara tun da kin zo duniya, sai dai kuma ko suna ba su kai ga rada miki ba, suka bar duniya, ashe Allah be nufi su ga wannan farincikin da suke ta daukin da nema ba, Allah be nufi a rayu a tare ba, ke ma Allah be nufi ki gansu ba"
Baba Auta ya kai hannu ya shafa kan Batula, sai ta kwantar da kanta jikin cinyarsa tana hawaye, da kewar iyayen da bata san ya fuskarsu take ba, ina ma ace sun rayu da ita, shi ne abun da take ta rayawa a ranta, da Allah kadai ya san irin gata da jindadin da zata samu, wata kila da sun haifa mata kanen ma, amman yanzu ita kadai take rayuwa.
"Ki yi hakuri, Allah ya musu rahama ke kuma Allah ya raya ki, ya shirya ki ya kula da ke"
Ta dago ta share hawayenta, ta kama hannu Baba Auta daya ta saka hannu biyu ta rike, domin bata da tabbacin ko zata dawo ta same shi a raye, tsoho ne sosai da shi kadai ya rage a cikin kakaninta, tana son ta tambaye shi abubuwa da yawa game da Mamanta ko Babanta amman bata da bakin tambaya.
"Batula fito ga abincin ki ci"
Ta zabura da sauri ta share hawayenta ta fita, Dumamen tuwo ne Umma Hindu ta zuba mata mai yawa, ta zauna amman ta kasa cin ko loma ɗaya, saboda tunanin abun da Baba Auta ya fada mata, ko ya masu iyaye suke ji? Ko ya masu kanne da yayyen suke ji? Kamun da aka bata ma kasa sha ta yi, sai ta aje ta shiga bandakin da rabin gini ne, idan mutum ya mike tsaye za a iya hango shi ta yi wanka ta fito, ta shiga dakin Umma Hindu ta nufi bankon kayanta ta dauko kayanta na sallah ta saka ta saka har da hijab, tun da aka kwaso su tare da kayan Umma Hindu bata saka ba sai yau.
Ta fito ta aje ta tsaya, tana ta kallon gidan da mutanen cikinsa, tana jin kamar ace wani ya iya karantar damuwarta ya hana ta tafiya, amman babu wanda ya lura da hakan har Umma Hindu ta kama hannunta suka fita tare. Ba su yi nisa da tafiyar ba, suka isa gidan Baba Ramatu Umma Hindu ta shiga da sallama tana rike da hannun Batula.
"Haba kin taushe hannu Wallahi, ina ta son na aika kuma ina tsoro tun da kin ce baki son a gane, ga shi idan rana ta yi babu dadi tafiya ba kusa ba"
"Gata nan ai, kin san halin yar taki ta son jiki"
Ta warware zanenta ta dauko yan canji ta mikawa Baba Ramatu.
"Ga wannan ku kara ku hau mota"
"Tohm kin dai gargade ta ko?, kar taje ta yi abun assha, kin san idan yaro yayi ba daidai ba mu ake kira kuma mu ake hukuntawa, ni kuma ke zan rike"
"Na gargadeta, ai duk ta kuskura ta yi abun da zai saka a dawo da ita garin nan ba wai ta zo ganin gida ba, Wallahi sai na kusa kasheta"
"Yauwa yayi ni ma zan kara ja mata kunne, su biyu ne zan tafi da su daga iya sai Talatu, akwai wanda tace tana son a kawo mata tsohuwa mai kula mata da gida, dayar kuma tace a kawo mata yarinya mai raino"
"Ba matsala, Allah ya tsare ya kai lafiya, Batula dan Allah ki kama kanki ki zauna lafiya, mu samu dan abun da za samu kamin lokaci da kure"
Umma Hindu ta karasa tana kallon Batula, sai Batula ta kama hannun Umma Hindu ta rike tana hawaye tana girgiza mata kai, domin bata son zuwan. Umma Hindu ta fisge hannunta.
"Kina dalla can, idan kin je ki dawo fitsarariya ba ke kika kashe min auren ba, kina kallon yadda muke fadi tashi a nan, abun da zamu ci ma sai mun wahala, can kuwa raino ne kawai zaki yi a ba mu kudi, kuma mai yawa"
"Ke Hindu tun can ya kamata ki mata wannan bayanin, kin ga dai ba zan tafi da ita birni tana ta wannan kukan ace satota na yi ba"
Umma Hindu ta kalli Batula rai a bace.
"Batula, karki fusata ni kin ga yadda na shirya ayi tafiyar nan dake idan aka samu matsala sai raina kanki, ki bar ganin mutanen gida na tare miki, Wallahi idan na tashi gana miki azaba babu wanda ma zai sani, kila ma na kashe ki, dan haka ki yi shiru ki bita ku tafi kuma idan kun tafi ki zauna lafiya, kar a dawo min da ke ko a kawo min kararki"
Tana maganar tana jan kunnenta, Batula ta daga kai da sauri ta share hawayenta, zuciyarta na kuna, amman a haka ta shaye ta zauna a tsakar gidan har sai da Baba Ramatu ta fito suka ta biyawa Talatu suka kama hanya. Hankalin Batula be tashi ba sai da suka shiga mota suka kama hanyar fita daga kauye, bakinciki ya samu guri can can can kasan zuciyarta kusa da gurbataccen jini ya zauna.
Motsin kirki bata yi ba har suka fito cikin garin su iso Dange, a tashar Dange local Government suka hau motar sokoto.
Na Batula ido ne kawai, idan aka ce ta fito ta fito idan aka ce shiga ta shiga, tana zaune motar tana kallon titi da motoci har aka iso rawun mai ruwa ta sokoto.
"Fito"
Baba Ramatu ta fada, sai ta saka kafarta waje ta fito wani yanayin da iska mai dadi na ratsa hancinta ta shaki iskar cikin garin Sokoto mai ni'ima, Sakkwato Birnin Shehu, Madogarar ilimi da addini, Mazaunin malamai da masu hikima, Tutar Daular Usmaniyya, Ƙasar da tarihi ya kafa tubalinta da imani, Gidan mutunci, haƙuri da karamci, garin da ba sokoto ba dajin Allah na Shehu dan gaskiya aka yi mu.
Ta sauke ajiyar zuciya a hankali, ai yanayin kamshin garin ma dabam yake, Garin Shehu Usmanu ɗan Fodiyo! Garin Sarki Muhammadu Bello! Da Muhammadu Macciɗo! Mai Ƙofar Rini da Ƙofar Marke, Mai Ƙofar Kade da Ƙofar Kware,
Mai Ƙofar Dundaye, da Ƙofar Taramniya, Mai Ƙofar Aliyu Jodi da Ƙofar Atiku.
Masu babur suka zagaye motocin dake ake ta sauke fasinjoji, daman haka garin sokoto yake indai ka sauka a rawun mai ruwa masu achaba gasu nan birjin sai ka zaba, Batula na ta kallon yadda aka kawata garin sokoto, har aka yi cininin abun hawa bata sani ba, sai jin ta yi ance ta hau. Mashin ɗaya suka hau ita da Baba Talatu, Baba Ramatu kuma ta hau wani achaban suka kama hanya, ita dai tana tsakiya iskar na kau mata karo ta kowane gefe.
Sun yi tafiya mai nisa, suna ta ratsa unguwanin har suka iso inda za su sauka, a unguwar da bata san ina ba ne balle gidan da za su je.
Baba Talatu ce ta sallami mai masu mashinan sannan ta karawa Batula da wani gargadin domin ta lura tun da duka sauko kan mashin din a firgice take, sai da ta tabbatar kowa ya natsu sannan ta kwankwasa kofar katon gidan da zai yi gidan wani mai kudin uku. Ta sake kwankwasawa har sau uku sannan mai gadin ya leko ta karamar kusurwa ya leko ya koma, ya bude karamar kofar.
"Hajiya Ramatu sannu da zuwa"
Ta washe hakora tana jindadin yadda ya fadi sunan nata a gabansu Batula, daman abun da mutunen karkara ya fi so kamar a karrama shi.
"Bello, ya gidan ya Hajiya Allah yasa dai tana nan"
"Walle kin zo a sa'a Hajiya kam tana ciki yau bata tai ko'ina ba"
"tohm Alhamdulillah"
Ya kauce mata ta shiga ciki tana amsa gaisuwar da sai a yanzu yake mika mata.
"Walle lahiya lumui Bello, mun iskeku lahiya dai ko?"
Ta wuce cikin gidan Baba Talatu na binta a baya, Batula kuma tana can baya sosai yawu kamar za su zubo tsabar kallo da kauyanci, a take zuciyarta ta fara raya mata masu wannan katon gidan suna da yan kan kai ko kuma suna da alaka da mai yankan kan, domin arziki na halak ba zai baka wannan dukiyar ba a karamun tunaninta. Bata an karo ta kawo bakin entrance din gidan ba har sai da ta ji ta yi tuntube zata fadi kasa.
"Mtssssss, ka ga matsalar yan kauye tun yanzu kin kara sai da halin ko?"
Batula na jin haka sai ta natsu tana watching steps dinta ta taka one after the other ta haura ta isa inda Baba Ramatu take tsaye tana kwankwasa kofa. Idan ta buga sai ta ja baya ta tsaya sai an dauki lokaci sannan ta buga, can dai da ta ga alamar ba bude kofar za'ayi ba sai ta ciro wayarta a jaka keypad ta latsa ta latso ta nemo number ta kira. Cikin daga murya ta mika gaisuwa ta sanar cewar suna bakin kofa.
"Tohm Tohm Hajiya, Allah yasa dai ban tashe ki bachi ba"
Ba a amsa mata ba, aka kashe wayar, a hakan ma sai da suka kusan kara kwashe minti talati a tsaye sannan aka bude kofar falon. Ita ta fara wucewa gaba ta shiga sannan Baba Talatu Batula ce ta karshe, tsoro duk ya gama mamayeta, domin bata taba mafarkin zuwa a gidan da be kai wannan ba balle ma wannan din, sai ga shi kuma a zahiri ba a mafarki ba.
Sanyi ac ya raba musu lale marhabun, daman sun debo rana da zafin mota, ba Batula ba har uwar tafiyar a kasa ta zube balle kuma su da suka yi rakiya, Batula ta dukunkune guri daya can raben kujera tana kallon katon plasma da bata taba ganin irinsa ba, mutanen ciki kamar za su fito waje tsabar girma, ga muryar tv ma a home-theater suke fito abun da bata san miye ba, amman dai muryar ta cika dakin, ga wani tile mai sulɓi da ya cika ko'ina na falon da a ganinta za a iya ɗaki uku a ciki.
Nan sun sha zama har suka raina kansu sannan matar gidan ta fito cikin da izza da gadara, tana tafe dankwalinta a hannu shaddar madam getzner dake jikinta sai motsi take, ta zauna a kujera iska babu yabo babu fallasa. Baba Ramatu ta fara zuba banbandanci.
"Barka da fitowa Hajiya, hajaji kayan Allah, Sa'adatu sa'ar mata, gidan da ba sa'a ba sa'a, yaro ko baka son sa'a kana son Sa'a, sa'ar mata Sa'adatu, Allah yasa dai ba bachi na tashe ki ba"
Sai a lokacin ta dan yi murmushi kadan tana wani dauke ido.
"Ramatu, an samu shigowa, aa ni ba bachi nake ba, ai idan ina bachi ba a tashina sai na farka"
"Haka ai shi ne daidai Hajiya Sa'adatu, talaka ma ya wuta balle mai shi"
Ta sake yin murmushin kasaita, ta kalli Batula da Baba Talatu.
"Su kuma wadanan fa.? Sarkin kwashe kwashe ina kika kwaso su"
Baba Ramatu ta kyakyale da dariya ta nuna Batula...
"Kin ga wacan tohm ga mu mun zo fa, sai da na zaba, na zabo na duba na dubo sannan na dauko miki wannan, bata da matsala ko kadan, kuma marainiya ce ba uwa ba uba, kuma bata da matsala ko kadan, ga aiki kamar jaka bata gajiya"
Adda Sa'adatu ta kalli Batula da kyau.
"Okay, an mata bayanin abun da zata yi ko? Dan bana son kananan magana"
"An fada mata komai Hajiya, ta sani"
"Tohm kuma a gargade ta bana son shishhigi ko shiga abun da babu ruwanta, dan kar ta yi min ba daidai ba, ta duban tana marainiya zan kyaleta, ba ruwana da wannan gurin maraici dabam gurin hukunci dabam"
Batula na jin haka yan hanjin cikinta suka kada, ta kara raina kanta daman ta ga kalar matar ba kanwar lasa bace, bata yi ma zaton gidan za a barta ba.
"Bata da wannan, yarinya ce mai natsuwa Hajiya, ai na san yadda kike ba zan kawo miki gaibu ba"
"Yayi kyau, an fadawa iyayenta albashinta ko?"
"Eh an musu bayanin komai, ita uwar rikon tata, dan bata da iyaye a raye ai"
"Ai duk daya ne, ni ma ai marainiyarce, tun da mahaifiyata ta rasu"
"Allah yayi mata rahama Hajiya, Allahu Akbar"
"Ameen"
Ta amsa kamar an mata dole, sannan ta mike tsaye.
"Bari na kira na saka Safiya ta kawo muku abinci, amman dan Allah aci a can waje Baranda kar a bata min falo"
"Tohm Hajiya Tohm tohm ai ba zamu ma ci a nan ba, wannan falo mai uwar dukiya ina zamu bata shi"
Baba Ramatu ta amsa, Baba Talatu sai kallon ikon Allah take tana hamdala da ba ita za a aje gurin ba, domin alamu ya nuna kamar matar gidan bata san darajar dan'adam ba.
Batula na rabe tana ta sharar hawaye, ta fara kewar gida, kamar yadda ta fara hararo irin rayuwar da zata yi a gidan, idan har aka tafi aka barta.