HAYAT NAZLI

9

by @maryamannour71


Chapter.9 

 

Suna isa ita ta fara sauƙa ta nufi gate ɗin gidan ta yi knocking, jim kaɗan sai ga mai gadi ya fito suka gaisa cikin mutuntawa. Kasancewar dama ya san ta tana zuwa gidan dan gidan ba sabon ta bane ya sa ya wayi fuskarta, sai dai abin da ya faɗa a gaba ne ya sa guiwowinta sake. Yanzu ya za ta yi kenan dama nan ɗin ne last hope na ta gashi kuma ta zo basa nan, bata son kuma ta nufi wani waje dan ba za ta so wasu daga waje su san abin ke faruwa ba, ita ma Elherm dan ta kasance ƙawa kuma aminiya ce da ba za ta yi gangancin zuwa nan ba. 

 

Ta sauke ajiyar zuciya ta nufi Sahle driver da ya fito da Jakarta ya nufe su ta ce. "No Sahle bar kayan nan, ka ga ma wai basa nan kwanansu biyu ma da barin gari." Tsaye ta yi kusa da motar tana tunanin abin yi, a hankali kamar bata so ta cire wayar da Mom ta bata kamar za ta ƙira ta sai kuma ta canza tunani ta yi dialling ɗin numbern Elharm wanda a ka yi rashin sa'a bai shiga. 

 

Rasa abun yi ta yi gashi dare na yi, ta ɗaga kai sama ganin yadda gari ya haɗe ya yi duhu alamun daukan ruwa a ko wani lokaci. 

 

Ta bud'e murfin motar ta shiga tare da ba driver umarnin su tafin ba tare da ta san ina suka nufa ba, adduar ta ɗaya Allah ya kawo mata mafita cikin sauƙe, ita ba dangin iya bare na Baba cikin garin. In fact babu wani d'an uwa na kusa da za ta iya zuwa gidansa ta zauna har tsawun lokacin da Dad zai sauko su sasanta ta koma gida, ba komai ne ya fad'o mata ba sai wani incident da ya faru da daɗewa tana ƙarama wanda yanzu take dana sanin sa. Da bata rufe ido ta watsa masu ƙasa a ido ba da yanzu tabbas da bata gayyara har haka ba, da wata ƙila duk wannan bak'in ciki da ke bibiyar ta bai faru ba. Ba tare da ta sani ba ta ji ɗumin hawaye na sauƙo mata, a hanakli ta saka hannu ta share fuskar ta. 

 

Ina ba za ta iya zuwa ta same su ba, to da wani idon ma za ta iya kallon su bayan rashin mutuncin da ta nuna masu a lokacin da suka so ta suka so dauƙan ta amma ta nuna masu ba su da ikon kan haka sai yanzu da ta gama caɓe mata? Ina ba za ta iya ba kamar yadda take da yaƙinin suma ba za su amshe tan ba, duk tsawun lokacin nan bata neme su ba bata tab'a jin tana son ganin su ko sha'awar rayuwa kusa da su sai yanzu da ta rasa muhalli, amma sai dai bata da laifi a kan haka don komai ya faru sune sila. 

 

Da sauri ba shiri ta dafa kujerar da ke gabanta wato me zaman banza jin yadda motar ta su ta yi gaba ta yi baya sai kuma suka tsaya cak alamun an samu matsala kenan, ta kalli driven ta ce. "Ya dai Sahle lafiya?" "Hajiya an samu matsala fa." "Matsala kuma?" Ba tare da ya bata amsa ba ya bud'e murfin motar ya fita cikin sauri ya zaga ya bud'e gaban motar yana dubawa. 

 

Dan ƙaramin tsake ta saki ta buɗe murfin motar ta fita ita ma, a hankali take k'are ma anguwar da suke kallo ganin babu mutane sosai cikinta sai ɗai-ɗaiku ne wanda ke wucewa. Rufe wajen ya yi ya kakkaɓe hannayensa ya ce. 

 

"Hajiya sai haƙuri fa engine ɗin motar ne ya samu matsala muna buk'atar mechanic." Wani kallo ta jefe sa da shi ta ce. "Dama ka san motar za ta ba mu matsala ka ɗauko ta bayan ga motoci birjik ka rasa wacce za ka ɗauka sai wannan gwangwan?" Yanzu ya kake son mu yi kenan kana gani dai dare na yi ga kuma weather da ya haɗe." "Allah ya huce zuciyarki ranki shi daɗe, amma ni kaina ban san hakan za ta faru ba." 

 

Saboda takaici uffan bata ta ce ba ta koma cikin motar ta zauna, daga wannan sai wannan yau dai tun da ta tashi ba abun da ya ke tafiyar mata dai dai komai sai lalacewa ya ke, gaba ɗaya komai ya ishe ta wallahi. 

 

Ɗan leƙawa ya yi ta window ya ce. "Hakuri Hajiya, bani minti 30 zan samu mai gyara yanzu zan dawo ba zan dau lokaci ba." Daga haka ya juya ya soma tafiya cikin sassarfa, a hanakli ta leƙa ta ce. "Sahle dan Allah karka daɗe ka ga dai inda na ke." Ta faɗa cikin yi masa nuni da yanayen anguwar. "In sha Allah Hajiya." 

 

~~~~~~~~ 

 

GIDAN DADDY 

 

Zaune suke a dinning kowa ya saka plate a gabansa suna tsakurin abincin kowa da abin da ke damunsa, kallo daya za ka ma Daddy da Mom ka san irin tashin hankali da ke bayyane kan fuskokin baren ma Dad da tun da ya zauna ya kurrwa wuri guda ido bai motsa ba damuwa ce fal ransa yana tunanin ko ina Nazlin sa take yanzu? Shin ko ta ce abincin ma? Gaba ɗaya tunda ta tafi ya kasa sukuni, Mom ta ɗaga kai ta kalle shi kamar za ta yi magana ta rabu da shi don har yanzu cike take da shi. 

 

Minti bayan minti ya ke kallan screen d'in wayarsa kamar wanda ke tsammanin ƙira daga wani, illai kuwa ba'a ɗau lokaci ba wayarsa ta hau ruri. Da sauri ya d'aga ba tare da faɗin komai ba ya tashi ya bar wajen, suka bi bayansa da kallo, Mom da Neesah suka haɗa ido inda Neesah ta ɗaga mata kafaɗa cikin rashin damuwa. Kasa yin hakuri Mom ta yi a tsanake ta miki ta mara masa baya. 

 

Dai dai sanda ya shiga ɗaki yana ƙoƙarin rufe ƙofa ta ji yana fadin. "Na'am P.A ina son komai ya kammala daga nan zuwa gobe ta koma can d'in ko hankalina zai fi kwanciya." Iya abin da ta ji kenan ya banko ƙofar, wani irin bugu gabanta ya yi, ba tare da ta tsaya ta sake jin komai ba ta koma ɗakinta ta soma safa da marwa cikin ɗakin yayinda tunanin ta na wani wajen. 

 

Sai da ta ƙiyyasta lokaci ta tabbatar sun gama magana P.A. ta danna masa kiran bugu biyu ya ɗaga kamar me jiran kiran na ta. 

 

Ba tare da bi ta kan gaisuwar da ya ke mata ba ta c. "Tell me, me kuma wannan mutumin ke Shirin yi yanzu?" P.A. ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Koda ba ki kira ba ina da niyyan haka, shiri ya ke ya fidda ta kasar waje karatu kamar yadda tun da can ya so kika hana, yana son ta koma can har zuwa sanda za ta kammala ta amshi ragamar ayyuka da kuma sabon company da ya siya kwanaki wanda a ka yi gwanjinsa bayan ya saka ma'akata da kayan aiki a ciki." 

 

Wani malolon abu ta ji ya tsaya mata a makoshi dan bakin ciki, ta yi huce tare da jan kwana ta ce. "Ban gane company da ya siya ba?" Wanne a ciki kenen?" Ba ka ce da sunan babbar ƴarsa ya siya ba, to ya a ka yi ya zama na ta yanzu kuma?" "Eh hakane na yi kuskuren fahimta ne amma da karamar a ka yi komai." 

 

"Ni Mukhtar zai yi wa haka?" Bayan mallaka mata komai na sa bai ishe sa ba wannan company da na saka buri a kai shi ne ya ke shirin saka sunan ta a kai?" Ta ja mugun huce. Dole ne ma na dau mataki Allah. 

 

Ta ja kwafa. "Thanks na san me zanyi, idan na bar shegiyar yarinyar nan ta ja ragamar company nan to shegiyana ke ban haifu ba wallahi. " daga haka ta katse ƙiran ba tare ta jira ya faɗa mata sauran maganar da ya san ko bata haukata ba ta sai ta zautar da ita. 

 

sai huce take kamar wata zakanya idon ta ya yi jaa gaba d'aya duk wani annurin fuskarta ya kau sai ta canza daga wannan Mom mai sanyi da kulawa ta koma wata ta daban. 

 

A hanakli ta furta. "inaa! ba zai yu ba, ba zan tsaya ina kallo ranar da nake buri da son gani ta zo na kusa cimma burina komai ya ruguje ina kallo ban dauki matakin da ya kamata ba. Yadda na sha wahala kan zuwan wannan ranar ba zan bar ko wace k'ofar da za ta tarwatsa min aiki ba, zan iya yin komai dan gujewa hakan, wanda kuma ya ce zai shiga tsakani na da buri na to ban damu na aikasa har lahira ba." Ta saki wani irirn makirin murmushi tuna ta samu makirin matsalarta Nan take. 

 

turo ƙofar a ka yi a ka shigo mata daki ne ya sanya cikin sauri ta waiwaya, Neesah ta shiga kan stool din mirror ta zauna tana facing din Mamanta ta ta zuba mata ido kamar ta yi magana sai kuma ta girgiza ta mike za ta bar dakin Mom ta dakatar da ita hanyar fadin. 

 

" Ke me ya sa ba ki da hakuri ne me kike jira na baka na zuba, eh?" Na faɗa miki ki kwantar da hankali ki sha hurimin yarinya kamar kin samu Zaid, ita wancan shegiya kazar mayun kuma ta tafi kenan ba dawowa kamar yadda duk Wanda ya mutu baya dawowa ita hakan ce, ki dai kawai nemi wuri ki zauna sannan ki zuba ido ki ga aiki da cikawa. yadda na saka Uban ya kore ta daga gidan nan to ta tafi kenan har abada ke kadai ce yarsa, matuƙar ina raye to wallahi tallahi ba zan taɓa barin jinin IShIRAQA ya huta ba. Yadda ta shiga tsakanina da farin ciki na ta rabani ni da Muktar to na yi alƙwarin sai na tarwatse farin cikin wani na kusa da ita. Yadda bakin cikina ya yi silan barin ta duniya ta haka shegiyar ƴar ta za ta bi sawun ta." 

 

Ta yi wani huce cikin tsantsan tsanar da ta yi wa matar ta ce. "Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba'a je ba Ishiraqa, na ɗauka da na rabi ki da Muktar da kuma ƴar mafi soyuwa a gareki to na ci galaba a kanki amma sai ga shi yarki na son fin ƙarfina tana son shiga cikin hurumin da ba na ta bane, ta mallake min miji ba abin da ya ke ji ko gani fashe ita. Komai ya samu Nazli, ya tashi Nazli, ya zauna Nazli, ya kwanta bacci Nazli ya tashi Nazli. Duk wannan bai ishe shi yana cuku cukun danka mata komai na sa alhalin ni da 'yata komai ya samu sai ita? . 

 

Ga dukkan alamu lokaci ya yi da zan aiwatar da ɗayan plan ɗinmu duk da ban so haka da sauri ba amma ya zama dole na kawo ƙarshen wutar da ke son shiga gona ta. dan na lura idan na ce zan bi a sannu to kuwa wankin hula ne zai kaini dare, ta yi fuskar tausaye ta ce. "Dole ne na kawo ƙarshen ki Nazli duk da ban so hakan ba a yanzu, amma ya kika iya ƙaddarar ki ta zo haka iyayen ki sun casa miki ba yanda kika iya." 

 

A hankali Neesah ta ta saki handle din Koda ta koma ta zauna kan gado ta soma magana tare da kallon ta Mom ta ce. "Me za ki ma ta?" "Ke dai na ki ba kallo bane?" Ai kawai ki zuba ido ki ga yadda komai zai wakana, ba burin ki Zaid ba to kwantar da hankalinki kamar kun yi aure kun zauna ne." 

 

Daga haka ta nufi madubin ɗakin ta ja stool ta zauna kana ta fidda wayarta ta yi dailing din wata number, ringing biyu a ka ɗaga kamar dama kiran ake jira. "Goje, kana ina ne da akwai aikin da zaku min." Dan shiru ta yi alamun tana sauraran me ake fadi ta dayan bangaren ta ce. "Yauwa a yau ɗin nan na ke son aikin ba gobe ba, dan idan na tsaya gobe lokaci zai ƙure min, zan tura maka hoto da da kuma address din wanda za ku min aikai akansa." 

 

Daga haka ta sauƙe wayar ta kalli Neesah da har yanzu ta kasa gane abin da mahaifiyarta ta ke shirin yi ta ce. "At least ki faɗa min abin da kika shirin yi mana." ba tare da ta bi ta kanta ba ta tura masu hoton Nazli da kuma adress din gidan Elherm kana ta sauke ajiyar zuciya finally za ta kawo ƙarshen matsalar ta. 

 

~~~~~~~ 

 

Tsaye take a bayan motar ta tallafi kanta da take jin kamar zai rabi gida biyu da hannayenta ta zubawa hanyar da ya bi da kallo, duk minti sai ta ɗago kai ta duba ko ya dawo amma shiru kake ji kamar an aika bawa garin su. Shi da ya ce minti 30 zai dawo gashi har ya haura awa ɗaya babu dalilinsa, gaba ɗaya ta galabaita ta fita hayyacinta, wani irin ciwon kai ne ke damunta ga kuma yunwar da ta yi ma hanjinta mugun kamo, ba abin da take da buri a yanzu irin ta ganta a gida ta sauke nauyin da marar ta ke mata. Uwa uba ga jirin da ke ɗawainiyya da ita har bibbiyu take gani. 

 

Zuwa lokacin dare ya yi rana ta sauka dan muru ya shigo, sai a lokacin ma ta tuna ashe ko sallan la'asar bata yi ba gashi yanzu a na neman magrib. Kamar an ce ta ɗago kai sama ta hangi wani babban hotel da ke ɗan nisa da ita, ba tare da ɓata lokaci ba ta buɗe murfin motar ta dauki hand bag ta kulle motar kana ta nufi wajen niyyarta ko kwana ne ta yi in ya so gobe ta san na yi dan a yadda take nan bata tunanin za ta iya sake minti 1 ɗaya ne a gurin nan ba tare da ta samu miƙar da haƙarƙarinta ta huta ta ci abinci ta magani ba. 

 

Tafiya take amma sai layi take kamar za ta faɗi saboda rashin karfin jiki abun da bai wuce ya ɗauke ta minti 5 ta isa ba gashi ta bata sama da minti 15 a hanya. 

 

Hamdallah ta yi a lokacin da isa harabar wajen cikin son ta isa ta ƙara sauri ta shiga ta samu receptionist suka gaisa, kana ta mata bayanin kalan ɗakin da take so tare da abubuwan buƙata da za'a tura mata, ta fidda ATM card ta ba receptionist dake wajen tana jiran ta cire kuɗin su bata mukullin ɗaki ta shiga dan tsauwar nan ma ba ƙaramin dauriya take ba, maimakon ta ga matar ta cire kuɗin sai ta ga ta miƙa mata ATM ɗin ta na girgiza kai. "Am sorry ma'am, but ATM na ki bai aiki." Cikin rashin fahimta ta dube ta ta ce. "Kamar ya bai aiki abun da ko jiya ma na yi anfani da shi na cire kudin ne ya za ki ce bai yi." "Sorry ma! Amma abin da ya nuna mana kenan." Cewar receptionist cikin girmamawa, mamaki ne ya cika Nazli, amma bata ce komai ta cire mata ɗayan da bata cika anfani da shi ba kusan every month Dad ke saka mata kudi a ciki sai dai bata cika taba su ba. 

 

"Take this." Sai dai me, shima hakan ce take is freez, Nazli sai dai ta fidda gaba ɗaya ATM ɗin ta guda uku duk matsalar ɗaya ce sun tsaya basa aiki. Saboda mamaki ta kasa magana, sai ta a je a kan daga machine din su ne, amma tana gani mutane na zuwa suna sakawa babu matsala hakan sai ya jega ta tunanin me ya sa same na ta. 

 

Manager da suka ƙira ne ya duba matsalar ya ce. "we're extreamly sorry Ma'am, amma matsalar daga card ɗinki ne, mostly ana samun wananna matsalar ne idan a ka yi frozen din account dinka, wato a tsayar da account din daga yin aiki babu damar anfani da shi ko kuɗinka a ciki to haka zai nuna, but the easier way da za ki matsalar to ina ga zai fi idan kika tuntubar Bank din kika anfani da su za su yi solving matsalar." 

 

Sororo ta yi tana kallansa jin kalamansa, ba kuma komai ne ya faɗo mata a rai sai Dad tunda shi ke tura mata kudi kuma shi kadai ke da damar yin haka." Ba tare da ko ta bi ta kan Manager da ke rattabo bayani ba ta juya ta bar wurin. 

 

A hankali ta ke tafiya sam bata sanin inda take jefa ƙafarta, tunani kawai take yadda rayuwa ta yi juyan waina da ita, jiya warhaka tana cikin gidanta, gidan auren ta tare da mijinta cikin farin ciki, amma yau kuma gata a gantale a titi bata san inda ta nufa ba, lallai rayuwa bata da tabbas duk wanda ya ce zai dau rayuwa da zafi to zai kone. 

 

Waɗan da kake tunanin su za su tsaya maka a lokacin kake da matuƙa buƙatarsu sai ya zama su ne masu guje maka masu juya maka baya. 

 

Karar da ta ji daga saka shi ya sa ta dawowa hayyacinta, saboda yadda ta ruɗe bata san ta ina ƙarar ke nufo ta ba ya sa kawai ta sallama ta zauna a nan ƙasan wajen ta ɗaura hannayen ta biyu a ka tare da runtse idanu, jira kawai ta ji daga ina za'a hankaɗe ta a yi sama da ita kurm, amma maimakon hakan sai ta ji ƙiii! aka ja birki motor na gab da kafafunta. 

 

Jin shirun ya yi yawa ne ya sa ta soma buɗe idanuta a hankalin kamar mai tsoron buɗe su, wani irin gauran mumfashi ta saki a ganin tsayuwar motor, a daddafe ta mike tsaye ta soma tattara kayan jakarta da ya watse ba tare ta ko bi ta kan mai motar ba. 

 

Buɗe motar a ka yi, kana cikin zafin nama wanda ya fita ya jawo ta jikinsa ganin yadda ta tsaya a kan hanya, haɗadɗen sauri ne da a ƙalla ba zai haura shekara 25 ba, fari ne dogo mai matsakaicin kyawu, sanyi ya ke cikin wando jeans da jar tshirt, fuskarsa sanyi da farin glashi. A hankali ta dago suka zubawa juna ido tare da yabon ƙyawun juna a zuci, a hankali cikin ɗadɗaɗan muryarsa ya ce. "Hope kina lafiya ba abin da ya same ki?" Ta kaɗa kai a hankali cikin son janye hannunta daga riƙon da ya yi mata, lura da hakan da ya yi ne ya sa shi saurin sakin ta ya koma baya ganin yadda jikinsu ke gogan na juna. 

 

cikin tsadadɗiyar motar ko, wani hansome guy ne zaune cikin back site ɗin motar, fuskarsa sanyi da facemask da kuma baƙin taburin da suka kara kawata yar karamar fuskar ta shi, gabansa laptop ne yana aikin sarrafata cikin gwanancewa, jin shiru wanda ya fitan bai dawo ba ya sa a hankali ya daga kai kamar baya so, a sa'ilin da ka soma wani irin isaka mai ƙarfin haske da ya sa mayafin kanta zamewa, wannan lallausan gashi nan na ta mai tsaye da sheki ya bayyana iska na kada sa, abin da ya jawo hankalinsa kenan da son ganin me fuskar, kasancewar ta ɗan ba motar baya hakan ya sa ba'a hangen fuskarta da kyau, sosai ya ƙura mata ido yana kallan yadda take faman kama mayafin iska na kuma janye sa.  

 

a slow motion ta juya ta kalli bangaren mortar yayin da take ji a jikinta kamar da me kallonta, sai kasancewar motar mai bakin glass ce ya sa baka hangen na ciki. Yana ganin yanda ta murmursa tanawa wannan saurayin magana ga dukan alamu magana ya fada mata wacce ta sa ta dauriya. 

 

Dan miƙe wuya ya yi tare da dan yin ƙasa da glasses din idanun sa da ke farare masu daukan hankali da ban nutsuwa ga me kallonsu, kwayar idonsa take baki irin sosai din nan sai hakan ya kara kawata idanuwan, ga kuma zara zara gashin idanun da ke mike abun ban kyau, ka daga ganin su ka san za'a zubda kyau a wurin, duk da fuskar na cikin masks bai hana ka fahimci kalar kasumbar da ya ke da a fusk.  

 

A hankali ya koma ya jingina ba tare da ya kau da  lulu eyes dinsa daga kansu ba, bai jin me suke cewa amma ga dukkan alamu hakuri ya ke bata, yana kallo saurayin ya tsuguna ya taya ta hada kayanta ya mike mata jakarta. Daidai lokacin da ta sakar masa da wannan lallausan murmushi na ta. Dum! Gaban sa ya fadi, da sauri ya kau da kai yana mai furta sunayen Allah sarkaka, bai san dalili ba amma ki ya yi kawai murmushin na fadar masa da zuciya. 

 

Yana cikin wannan yanaye da ya kasa fasara shi saurayin bude murfin motar ya shiga, sai a sannan ya daga kai ya kalli bangaren da take tsaye amma ya ga wayam bata wurin. Haka kawai sai ya tsinci kansa cikin rashin dadin bacewar ta har hakan ya bayyana a fuskarta. 

 

"Sorry man don't be mad, na duba na ga  ko ta ji ciwo ne and thank God she's fine." Bai kalle sa ba ya daga masa yatsun sa biyu kawai ya maida kansa ga aikin da yake cikin laptop din sai hankalinsa kasa nutsuwa ya yi, sanin me ya ke nufi ya sa na gaban ya ce. "Dan Allah yanzu da gaskiye za ka bar ƙasar bayan kasheɗi da warning ɗin PAPA?" 

 

A hankali cikin husky voice ya ƙira sunan sa. "Faisal." Da sauri wanda a ka ƙira da sunan Faisal ya ɗaga hannu sama alamun surender. "Sorry guy man, amma fa ka sani duk gudun ka za ka dawo ne ka fuskanci hukuci dan wannan karon ka ɗauko da zafi." 

 

Ajiyar zuciya ya sauke tare da rufe laptop ɗin dake cinyarsa tare runtsa idanu yana sauke ajiyar zuciya a jajjere ya duba agogon hannunsa ganin lokacin tashin jirginsa ya kusa. Ya ja tsakii hankali ya motsa laɓɓansa ya ce. "15 minutes to go." Da jin haka Faisal ya yi saurin tada motar suka bar wurin....