YARIMA BAHJAT

Shafi na huɗu

by @uwarbatoorl96

YARIMA BAHJAT 🌏

Na

Harira Salihu Isah

(Uwar Batoorl)

SHAFI NA HUƊU

⭐️

Jakadiya da mamakin maganar Jaruma Argiji ya rufeta, bai sake ta ba sai lokacin da guguwan ya dakata, cike da jin haushi ta saki ƙwafa gami da samun waje ta rakuɓe tana jiran dawowar Jaruma Argiji.

"Yautai ba baƙona bane, duk abinda za ki zanta da shi tamkar majiƙi haka zai zayyane mini na gani, ki gama ki dawo ina zaman jiranki, aikin banza gwalo a duhu...."

Haka Jakadiya tayi ta mita a zuciyarta har tsawon lokaci, saboda taji haushin barinta da Jaruma Argiji tayi, ta so ganin ƙwaƙwaf, amma Jaruma Argiji ta kwafsa mata, banbancinsu da Jaruma maitakalmi kenan.

Jakadiya na zaune shiru har zuwa sanda wani guguwan, ya sake turnuƙe wajan, ba jimawa kuma ya lafa, Jaruma Argiji ta bayyana.

"Takawarki lafiya uwargijiyata, sannunki da fitowa Jarumar Bahja, Jarumar Abdi kuma Jarumar mu, aljanna mai masoya da yawa, ina gwanar wata ga tawa,..!"

"Ki adana wannan zaƙin bakin naki mu tafi, ba na son gari ya waye mini ba'a ɗakina ba"

Jaruma Argiji ta faɗa gami da jan guntun tsaki suka kama hanya, suna tafe a hanya shiru kowa da abinda yake saƙawa a zuciya, sai dai duk akan abinda Jaruma Argiji tayi da hatsabibi Yautai ne.

Ita Jakadiya haushinta a kan barinta da Jaruma Argiji tayi ne, yayinda ita kuma Jaruma Argiji abinda suka zanta ne ke mata kai kawo a zuciya yana amsakuwwa.

"Hmn!"

Jaruma Argiji ta sauƙe ɓoyayyen numfashi, saboda abinda suka ƙarisa tattaunawa da hatsabibi Yautai da ya tsaya mata a rai har sannan, da taje da Jakadiya da kashinta ya bushe, tunda ras ta fahimci jirwaye ya mata mai kama da wanka.

Su ne basu isa masarauta ba sai da alfijir ya ƙeto, tun daga cikin masarautar suka raba hanya, Jakadiya tayi hanyar da zai sadata da sashinsu na bayi, Jaruma Argiji kuma cikin ɓadda kama ta wuce sashinta.

Wani nauyayyan numfashi ta sauƙe lokacin da ta shigo ɗakinta, ɓoyo mai kyau ta yiwa maganin da hatsabibi Yautai ya bata, sannan ta wuce makewayi, ba jimawa ta fito tabi lafiyar gadonta mai zubin sarauta, ta kwanta, zuciyarta fal saƙe-saƙen abubuwa da dama.

JARUMA ƳARBARAYA

Amaryar Abdi kenan, matarsa ta uku, matashiya ce amma cike take da tsantsar wayo, kirsa da kisisina, Abdi na ji da ita sosai kuma ba ya iya ɓoye son da yake mata.

Tunda suka dawo daga wannan zaman da aka yi, ba ta tsaya ɓata lokaci a kan komai ba, sallamar yaranta tayi ba tare da ta ce musu komai ba, asalima duƙufa tayi a kan yin abubuwan da suka kamata, saboda ita ce da kwanan turakar Abdi a ranar.

Sai da dogarawa suka yi mata iso sannan ta shiga, tana tafe cikin yauƙi tana tashin ƙamshi.

Daga murmushin da Abdi ya fara tarbanta da shi, ta tabbatar da kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

"Jarumina barka da hutawa."

Jaruma Ƴarbaraya ta faɗa tana kama hannun Abdi da ya miƙa mata.

"Jarumar Abdi, sannu da shigowa."

Abdi ya faɗa da muryarsa mai matuƙar sanyi da rashin hayaniya.

"Naji daɗin ganinki tun yanzu, fatan lafiya kika wuni ba komai?"

Abdi ya tambaya cikin kulawa.

Cikin salo Jaruma Argiji ta amsa, yanayin da ya sa Abdi miƙa mata kansa gaba ɗaya.

"Jarumina tabbas maganar Baba ta ɗazu tana kan daidai, domin gwanda a samu magaji tsakanin yara ƙananan ko kuma abinda za'a haifa, su waɗannan manyan sun haɗa hannkulansu da tuwo sun cinye, dan haka nima ina tare da Baba."

Jaruma Ƴarbaraya tayi maganar tana mai gyara kwanciyarta a jikin Abdi.

"Wannan haka ne Jarumata, su Yarima su Sardauna su Chiroma kaf yadda suke tafiyar da lamuransu a masarautar nan, shi yasa Baba ya yanke wannan hukuncin, amma tabbas zan tuntuɓe shi, ko da ba abinda za'a haifa ba, ai ga su Jarma, su ma za'a iya ba su sarautar"

Abdi ya faɗa da yanayinsa na rashin hayaniya, kuma har zuciyarsa zai so a bawa jinin Jaruma Ƴarbaraya sarauta, domin son da yake mata ita da ƴaƴanta na daban ne.

Cikin hillata da tsananin sanin ta kan kirsa, Jaruma Ƴarbaraya ta zuge Abdi a fakaice, har ma yayi mata alƙawarin yin magana da Sarki Gamboji a kan su Jarma, waɗanda suka kasance ƴaƴanta.

"In kana da kyau ka ƙara da wanka"

Jaruma Ƴarbaraya ta faɗa a zuciyarta, a fili kuwa wani murmushi ta saki na hararo cin nasara, saboda rayuwar duniya ƴar siyasa ce, a buga nan a buga can, ko da asiri sai an haɗa da kirsa da sauransu.

Tana jin sauƙan numfashin Abdi alamar yayi bacci, ta miƙe ta wuce makewayi, ba jimawa ta fito ta koma ta kwanta.

***

Hannu na rawa Uwar tuwo ta miƙa ta amshi ƙullin da Jaruma Argiji ke miƙa mata.

"Idan aka samu akasi ko wani kure to ki kuka da kanki Uwar Tuwo, domin a kan wannan aiki ina iya ɓatar da ke da duk zuri'arki, haka ma idan kika bari ƙwabarki tayi ruwa, ko kuwa kika yi shuka a kan idon makorwa, to kul! A hir naki, kar naji kar kuma naga kin ambaci sunana, dole ke za ki kwashi romon kuskurenki, dan haka ki iya takunki, ki iya hannunki, ki kuma kula da kyau, saɓanin haka komai ya biyo baya ke kika jiyo."

Jaruma Argiji ta ƙarishe maganar tana aikawa Uwar tuwo mugun kallo, saboda ganin yadda jikinta ke rawa kamar wacce aka damƙa wa garwashi, ba ƙarya tana gudun Uwar tuwo ta kawo mata tangarɗa a aikinta, amma kuma zuciyarta ba ta tunano mata wata daban da za ta bawa aikin ba, sai Uwar tuwo, domin kawai tana aiki ne da Jakadiya, ba wai dan ta yarda da ita ba, ai kalarka kalar kayanka, daga shegen kauɗi da zaƙin baki irin na Jakadiya ka san za tayi gutsiri tsome....

Jiki na rawa Uwar tuwo ta miƙe tsaye ta fice, bayan Jaruma Argiji ta sake yi mata gargaɗi.

Wani nauyayyan numfashi Jaruma Argiji ta saki, tana jin ta gama da kaso talatin cikin ɗari, na ayyukan da Hatsabibi Yautai ya bata, wanda hakan ke nufin ta haye wani siraɗin, tunda a yadda ta fahimta, shi Yautai ba iya sunan wanda aka kai wajansa ke cikin haɗari ba, har kai da ka kai sunan kana cikin haɗari, haihuwar guzuma kenan, ƴa kwance uwa kwance.

....

«"Sirri! Sirri na ɗaya daga cikin amanar da mu bokaye muke da ita, dan haka kada ki wani tashi hankalinki, Yautai ba zai bankaɗa labulen sirrinki ba, asalima zan miki aikin da asirinki zai ta zama a rufe har zuwa lokacin da ya dace, dalilin da yasa na ce lokacin da ya dace, saboda ki sani duk nisan jifa ƙasa zai dawo, dole akwai ranar ƙin dillanci, amma a yanzu kam ki kwantar da hankalinki tamkar kina jirgin sama mai ya ƙare, Yautai ya rufa miki wannan sirrin, Hahahaha!"»

Cikin hanzari Jaruma Argiji ta sa hannayenta ta toshe kunnuwanta, domin yadda kalaman hatsabibi Yautai na daren jiya suka tariyo kansu a kunnuwanta, haka sautin ƙaƙƙarfan dariyarsa ta ƙeta, ji take tamkar a lokacin sautin ke ƙaraɗe kunnuwanta, sautin dariyar da sautin kukan ya fi sa daɗin sauraro.

Toshe kunnen Jaruma Argiji bai mata amfani ba, domin zuciyarta bata sarara ba wajan tariyar sauran kalaman Yautai.

«"tarawa da ɗan ki Yarima na nufin macewar Baiwa Kubura da abin cikinta, domin aljanun da za suyi aiki da abinda kuka fitar a jikinku, cikin gaggawa za su zuƙe jininsu, idan na ce miki a yanzu haka aljanu na ƙwalamar jinin abinda ke cikin baiwar kar ki sha mamaki, domin akwai wani al'amari babba a tattare da cikin idan aka haife shi."

"Sadaukar da jinin ɗan kishiyarki ta uku na nufin cin galaba a kan kowa ba iya Baiwa Kubura da abun cikinta ba, hatta da jariri sabon haihuwa a masarautarku zai goyi bayan ɗanki Yarima ya mulki masarautar Bahja."

"Tarawarki da aljanu na tsawon wata guda na nufin, a cikin wannan kwanakin za'a ɓatar da baiwar, sannan ɗanki zai hau karagar mulkin."»

Ɗiff! Kalaman hatsabibi Yautai suka dakata da tusa kansu a tunaninta da zuciyarta.

Wani nauyayyan numfashi ta kuma ja sannan ta sauƙe, tana girgiza kai ta fara magana a fili.

"Zan iya yin komai, amma banda tarayya da Yarima, kamar yadda ko karan hauka ne ya cije ni ba zan iya bari aljanu su kassarani tun burina bai cika ba, hmn! Jaruma Ƴarbaraya aiki ya biyo ta kanki, ki shirya makokin ɗan tsakon da kike wani feleƙe a kansa, da son nuna cewa yana daidai da yaran da suka kwana suka hantse a gidan Abdi, za ki ɗanɗani zafin mutuwa Ƴarbaraya, ga ni ga ɗan ki Jarmai...."

Cikin firgici Jaruma Argiji ta dakata da maganarta, saboda muryar Yautai da ta tsinkaya bagatatan daga sama yana magana cikin wannan dariyar tasa mara daɗin sauraro.

"Ina son mutane irinki, ina matuƙar son aiki da mutane irinki Jaruma Argiji, hahahahahahaha! Kin yi kyan kai, dan haka kin gama naki, a duk zaɓukan da na baki, zaɓa ne kawai naki, gabatar da ayyukan na ifiritan baƙaƙen aljanu ne, hahahahahaha!"

Shiru ne ya ratsa ɗakin, bayan da sautin dariyar Yautai ya ɗauke, sai lokacin Jaruma Argiji ta samu damar fara waige-waige a ɗakin, ko za ta ga wata alama ta wanzuwar hatsabibi Yautai, amma ba komai.

Cikin ɗari-ɗari Jaruma Argiji ta miƙe ta fice a ɗakin.

***

"Barka da safiya Mama."

Faɗin wani baƙi kyakkyawa kuma nitsattsen matashi cikin girmamawa da nuna tsantsar ladabi.

"Barka dai Jarmai, ya kuka tashi? Ya ƙannenka?"

"Duk muna lafiya Mama."

"Fatan ka je ka miƙa gaisuwa a fada?"

Jaruma Ƴarbaraya ta tambaya, idanuwanta a kan nitsattsen ɗanta, kuma mafi soyuwa a zuciyarta, ɗan da a kansa ta tabbata wannan kalma ta bakin tukunya mai fidda farin tuwo, domin sam-sam bai kwaso ko da abu ɗaya a halayyanta ba, halayyansa na nitsuwa da rashin son hayaniya ya fi kala da halayyar Abdi, shiyasa za ta iya aikata komai domin ganin ya samu wannan kujerar.

"Na je Mama, mun gaisa da kaka har da Baba, har ma dai Baba ya mini wata magana, amma na ba shi haƙuri, domin a ganina da ni da su Yaya Yarima, da abinda za'a haifa a gaba duk ɗaya ne, abinda yafi muhimmanci shi ne muyi fatan Allah ya damƙa mulkin a hannun wanda ya kamata, kuma ma dai ni banason harkokin mulkin nan...."

"Jarmai!!"

"Wallahi idan ba ya so ni ina so Mama!"

Kusan a tare ƙiran sunansa da Jaruma Ƴarbaraya tayi, da maganar ƙaninsa Madaki, suka katse maganar da yake yi, wanda hakan ya saka shi jan bakinsa yayi shiru, ya kuma yi ƙasa da kansa.

Wani mugun kallo Jaruma Ƴarbaraya ta aikawa Madaki, ta buɗe baki da niyar rufe Jarmai da faɗa, sai madaki ya katse ta.

"Dan Allah Mama ki ƙyalesa tunda ba ya so, ba ga ni ba, sai ki ƙwatar mini kujerar na hau, domin wallahi tsohon nan zai aikata aiwatar da abinda ya ce, kinga kuwa gida bai ƙoshi ba ai ba'a kai wa dawa ba, idan Jarma ba ya so, ni Madaki ina so, da dai a bawa su Yaya Yarima ko abinda ƙasƙantacciyar baiwar can za ta haifa mulkin Bahja, ai gwanda kiyi gwagwarmaya ni na hau Mama."

"Madaki zan kwashe maka albarka, ka fita idona, da Jarma nake magana ba kai ba, yanzu kai a kalaman bakinka har kana lissafa kanka a cikin masu hawa wannan karaga? Ko ka manta cewa duk abinda kuka faɗa na aibata Sarki tamkar a kunnensa yake? To duk cikin ku banga wanda ya cancanci mulkin nan ba sai Jarma, domin kaf ya fi ku nitsuwa, shi ya biyo halin Babanku sak."

"Ya dai biyo sokancin babanmu."

Madaki ya faɗa a maƙoshinsa.

A fili kuma ya ce, "Haka dai kike gani Mama, amma fa sai an gwada a kan san na ƙwarai, tunda ba ya so kar ki masa dole, ni ɗin dai a bani a ga kamun ludayina."

"Jarmai!!"

Duk su biyun suka haɗa baki wajan ƙiran sunansa da ƙarfi, saboda ganin ya yanke jiki ya faɗi lokaci ɗaya.

****

Follow my page's

●WATTPAD

@Uwarbatoorl96

●AREWABOOKS.

@Uwarbatoorl96

●TIKTOK

@Uwarbatoorl96

*