YARIMA BAHJAT

Shafi na biyar

by @uwarbatoorl96

YARIMA BAHJAT 🌏

Na

Harira Salihu Isah

(Uwar Batoorl)

SHAFI NA BIYAR

⭐️

"Ka ga kaɗan daga cikin halayenka, yanzu da ka shigo wa ka miƙa wa gaisuwa, tsakanin ni uwarka da kuma Yayanka? Madaki ka cire zuciyarka a kan kujerar nan ta Jarmai ce da yardar Allah."

"Shikkenan Mama, naji na haƙura, Allah ya bawa Jarmai ɗin, ai ni da shi ɗin duk ɗaya ne, idan ya samu kamar nine na samu, tunda kai da kaya duk mallakar wuya ne."

Madaki ya faɗa cikin sallamawa, tunda ko shi ya san kyawawan halayyar ɗan uwansa ya cancanci mulkin, duk da dai lamarinsa akwai sokanci.

"Ya dai fi ka sallama ka kuma taya mu wannan yaƙin."

Faɗin Jaruma Ƴarbaraya.

"To matsalar dai ɗaya ce wannan tsohon indai yana numfashi, da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa."

Faɗin Madaki.

"Ni kuma bana jin ta ta shi tunda cewa yayi sai yana numfashi, hakan na nufin idan ba ya numfashi ko kusa da masarauta daga hadimar har abun cikinta ba su isa zuwa ba, kai idan kuma mace ta haifa maji ma gani yadda zai ba mace sarauta, ko ma dai menene sai idan da numfashin nasa."

Jaruma Ƴarbaraya ta ƙarishe maganar tana sakin wani makirin murmushi, domin a wajanta wannan labarin ƙanzon kurege ne, ai sai ma abun cikin ya zo duniya balle ayi batun ba shi sarauta....

Tim! Ƙarar faɗuwan Jarmai ya katse maganarta.

"Jarmai!!"

Duk su biyun suka haɗa baki wajan ƙiran sunansa ganin ya yanke jiki ya faɗi lokaci guda, kusan a tare suka yi kansa.

Jarmai wanda tun shigowan Madaki ƙaninsa, ya ja bakinsa yayi shiru, tunda ya san a wannan maganar furar shi da tasu ba ta damu, yana zaune yana jin maganganunsu, jin kalaman ƙarshe na Madaki ya saka kanshi ya sara, hakan ya sa ya yunƙura ya miƙe, da nufin ya yiwa Mama Ƴarbaraya sallama ya fice, sai dai bai ankare ba jiri ya ɗibesa sai ƙasa.

"Jarma!"

Jaruma Ƴarbaraya ta ƙira sunansa cikin kulawa da tsantsar nuna ƙauna.

"Na'am Mama"

Ya amsa a sanyaye.

"Me ke damunka?"

Ta tambaya.

"Ba komai Mama, kawai ciwon kai naji yanzunnan sai kuma jiri ya ɗibe ni, amma da sauƙi."

Jaruma Ƴarbaraya aika Madaki tayi ya kawo wa Jarmai magani, ko da ya sha maganin a nan sashinta ta ce ta kwanta ya huta, bai musa mata ya kwanta kansa a saman ƙafafuwanta, saboda haka kawai yake jin wani iri, kewar mahaifiyartasa yake jin yana tsarga masa, kalar kewar da ke hauhawa ciwon kansa, da bugun zuciyarsa.

"Mama ki dage har Jarmai ya samu kujerar, ni kuma na masa Waziri, kinga ko irin haka ta sake faruwa ni zan wakilcesa, Allah kuma ya sa waccan algungumar Baiwar ta haifi mace, kai macen ma ta kasance matacciya, ko ma cikin ya zube, tunda tun a jiya batun zubar da jinin da tayi ya zagaye masarauta, kusan kowa ya sani, ni fa idan muka hau mulkin nan, sai nayi maganin munafukan masarautar nan, da masu gutsiri tsome masu yaɗa maganganu saboda tsabar munafurci."

Da ƴar murmushi Jaruma Ƴarbaraya ta amsawa Madaki, sai da suka ƙarisa maganarsu, ya yiwa ɗan uwansa fatan samun sauƙi, sannan ya fice.

Jaruma Ƴarbaraya na yunƙurin sauƙe kan Jarmai a jikinta, da nufin ta tashi, sai Jarmai ya dakatar da ita da hanyar ƙiran sunanta da muryarsa mai sanyi mara hayaniya.

"Mama."

"Na'am Jarmai, kan ne?"

Ta tambaya cikin kulawa.

"A'a, wata ƴar magana zan yi, fatan za ki fahimce ni ba za kiyi fushi ba, domin ina jin kamar wannan ce damata ta ƙarshe da zan samu na yi miki magana, banson haƙƙin rashin maganar, ko kuwa haƙƙin fushinki a kai na, saboda yadda nake jin yanayin kewarku ku duka ya wuce misali."

Jarmai ya ƙarishe maganar idanuwansa na cikowa da ƙwalla.

Cikin kulawa amma ba tare da wani tunani ba, Jaruma Ƴarbaraya ta ce, "Ni ba abinda zai sa nayi fushi da kai Jarma, dan haka ka faɗi koma menene ina jin ka, ba abinda zai faru sai alkairi."

"Mama dan Allah kar ku tsawwala a lamarin nan, naji zan amshi mulkin muddin Allah ya sa da rabona aka bani, zan amsa ko domin ke, Allah ya kuma taya ni riƙo, amma a yanzu kar ku matsawa lamura, kar ku shiga gonar Kaka, domin faɗa da aljani ba riba duk mun sani, shi zanen ƙaddara abu ne da yake tabbatacce tun kafun wanzuwarmu, da ace mutane za su bar wahalar da kansu, su miƙa lamuransu da komai ga Allah, su jira abinda lokaci zai zo da shi da zuƙata sun huta, domin babu wani abu da yake wanzuwa face tun-tuni a haka yake rubuce, Mama kar ku aikata abinda bai kamata ba, shi mahaƙurci mawadaci ne, kuma shi rabon kwaɗo ba ya hawa sama, kamar yadda duk zakarar da Allah ya nufa da cara sai yayi ko ana mari ana zuru...."

Cikin nitsuwa Jarmai yayi ƙoƙarin nusar da Jaruma Ƴarbaraya, sai dai har ya gama ba ta ce masa kanzil ba, asalima sauƙe kansa tayi saman ƙafafuwanta ta miƙe ta bar wajan.

A hankali hawayen da ke cike da kwarmar idanuwan Jarmai suka silalo, zuciyarsa na masa wani irin nauyi da kewar mahaifiyarsa, yana jin ba daɗi sosai a kan tashuwan da tayi ta tafi, sai dai yana fatan ya zame ba ɓata mata rai yayi ba.

A zuciya yayi mata addu'ar Allah ya fahimtar da ita, sannan a hankali ya lumshe ido ba jimawa kuma bacci yayi gaba da shi.

Wuni yayi a sashin mahaifiyartasa yana bacci, lokacin da ya tashi ficewa yayi bai tsaya nemanta ba, saboda ƙiraye-ƙirayen salla da ake yi.

***

"Abdi!"

Sarki Gamboji ya ƙira sunansa cikin zallan taƙaici da baƙin ciki.

"Na'am Baba."

Abdi ya amsa da sanyin murya cikin yin ƙas da kai.

"Ko da nayi magana na ce ina buƙatar shawarar wani ko wani ya kawo ra'ayinsa? Na yanke hukunci, hukuncin da ko ba na numfashi sai an zartar da shi dole idan lokaci yayi, ina sane da kaf sauran yaran naka ai, amma na ce wanda za'a haifa ne zai gaji kujerata, kai ka san dalilin da ya sa ban baka ba na ce sai yaranka?"

Sarki Gamboji ya dire maganar yana kan bin Abdi da kallon taƙaici, zuciyarsa na yi masa wani irin tuƙuƙi, a yadda yake ji idan ya kalli Abdi, to ba domin tsawon kwana da tausasar zuciyarsa da yake yi ba da ya jima da haɗiyar zuciya ya mutu, shiyasa ba zai taɓa yafewa wanda ya kassara masa rayuwar tilon ɗan sa ba, Abdi a dire yake ga mutum har mutum amma soko-soko gaɓo-gaɓo haka aka mayar da shi, sannan duk bincike da tsaface-tsaface na bokaye da dama da ya kai wa ziyara, ba'a samu hatsabibin da ya fito ya faɗa masa mahaluƙin da ya sabauta masa rayuwar ɗa ba,

Yaro an haife shi lafiya-lafiya Sadaukin gaske, amma tun daga lokacin da ya fara tasawa, ya fara maganar zai ba shi kujerarsa shikkenan lamarin Abdi ya fara lalacewa.

Abdi dai kansa na ƙasa bai ce kanzil ba, so yake kawai babansa ya fahimcesa ya bawa Jarmai karagarsa, tunda kowama ya shaida irin nitsuwa ta Jarmai da cancantarsa.

"Abdi, dalilin da yasa ban baka kujerata ba, dalilin ne zai hana ni bawa Jarmai, domin da kai da shi duk sammakal an gama da ku, kuma duk ranar da aka faɗa mini wanda ya aikata mini wannan aiki na loɓantar da kai, to ko a bangon duniya yake sai naje kuma na kashe shi da hannayena, tashi ka bani waje na gama magana, abinda Baiwa Kubura za ta haifa shi zai mulki Bahja, idan ka so bayan ta haihu sai a ɗaura muku aure ka cike ta huɗu da ita, tunda addinin da take bi bai lamunce a ɗaura aure da ciki ba."

Sarki Gamboji ya ƙarishe maganar yana tsuke yamutsatstsen fiskarsa, a sigar da ke nuni da ya gama magana bai son sake jin komai daga bakin Abdi.

Hakan ya sa Abdi ya miƙe ya fice kansa a ƙasa cikin rashin daɗin rai, amma dai ya bari idan an kwana biyu zai sake yiwa Sarki maganar Jarmai, zai dage har dai ya aminta, domin sosai Jarmai ya cancanci kujerar.

Sarki Gamboji cikin sabon taƙaicin yadda aka mayar masa da Abdi, ya miƙe ya ƙarisa can ƙuryar turakarsa, gaban wannan daskararren ruwan ya tsaya, ya kai hannu ya diɓo ya wanke fiskarsa, domin ya koma narkakken jini, sannan ya runtse idanuwa ya fara karanto kalmomin surƙulle, ba jimawa ya tsinci kansa a baƙin kogon dodongaji tsirara, kogo mai cike da duhu ta masifa.

Diƙis! Diƙis!! Sarki Gamboji ke tafiya a tuɓe, har ya ƙarasa inda hasken wutar dodongaji ya mamaye.

Kamar ko yaushe dodongaji na zaune saman iska shi da wutar gabansa, ƙafafuwansa a tanƙwashe kai ka ce taburma ya samu ya zauna ba a saman iska ba.

"Dodongaji na kan dutse, dodongaji na saman tsauni, dodongaji tsohon bamaguje, dodongaji...."

"Barka da zuwa Sarki Gamboji, barka da ziyarar ba zata, sai dai naji daɗin ziyarar taka, domin ko baka zo ba ina da shirin zuwa gareka ko kuwa na aika maka da saƙo."

Dodongaji ya faɗa yana rufe idanuwansa yana karanto wasu kalmomi marassa kan gado.

"Ka bar wahalar da kanka a game da Abdi, domin lamarinsa lamari ne da muka tsayar da magana tun da jimawa, ba wani boka ko matsafin da ya isa ya faɗa maka taƙamammen wanda yayi masa wannan aikin, abu mafi muhimmanci wanda ya kamata ka sani a yanzu shi ne jikanka Jarmai zai mutu, an bawa wasu baƙaƙen ifiritan aljanu jininsa..."

"Waye ya aikata wannan aikin?"

Sarki Gamboji ya tambaya da sauri yana katse dodongaji.

"Ba sanin wanda ya aikata bane abu mai muhimmanci, karya aikin da ifiritan aljanun za suyi shi ne abinda za mu damu da shi, domin shi yafi muhimmanci, ka san aikinka da ta zuri'arka kusan shi ne aikin da na bawa dukka rayuwata, to nasan wacce ta aikata, amma kai ka santa bai da wani amfani, musamman da ya kasance tayi sara ne a kan gaɓa, domin Jarmai mai ƙararran kwana ne, ajali ta rigaya da ta cin masa, shiyasa ma tun farko da nayi ƙoƙarin hana aljanun jininsa, na fahimci ba zai yiwu ba, domin lokacin mutuwarsa ta riga da tayi ne, dole sai ya mutu, ko su sha jininsa ko kar su sha, yanzu karya aikin ifiritan aljanun shi ne namu"

Dodongaji ya faɗa yana watsa wani gari a kusurwar kogon, ta ɓangaren da Sarki Gamboji ke tsaye, ba ɓata lokaci kuma Jarmai ya bayyana.

"A yanzu haka gangar jikinsa ne kawai ke a tare da ku, amma rayuwarsa ta ƙare tun wayewar garin yau."

Faɗin dodongaji yana nuna wa Sarki Gamboji yadda gangar jikin Jarmai ke komai cikin kasalar barin ruhi daga jikin.

Wani nauyayyan numfashi Sarki Gamboji ya sauƙe.

"Abdi ya mini maganarsa ɗazu, ashe ma ba mai tsawon kwana bane."

"Mamarsa ce ta saka Abdi yi maka magana, amma ita da kanta bata san cewa lagwadan leɓe kawai take ba."

"Wani aiki aka saka aljanun?"

Sarki Gamboji ya tambaya.

"A zahirin gaskiya halayyar Abdi daban na Jarmai daban, shi Abdi an mayar da shi maloho ne kawai, amma kuma shi Jarmai nitsuwa da hankali anjininsa suke, yaro ne na ƙwarai wanda da ace yana da nisan kwana, to zan so su gudanar da sha'anin mulki tare da Yarima Bahjat, amma kuma shi ba mai nisan kwana bane, dama miya mai daɗi ba ya gama tuwo, dalilin da yasa aka zaɓi ba da jininsa ma kenan, sannan akwai hasken addinin musulunci a tare da shi, addini ne na gaskiya mai tattare da haske da aminci, kuma addinine mai farin jini duk mun sani, tunda kawai mu mun zaɓi tabbata ne a kan addinin gargajiya ta iyaye da kakannunmu, amma addinin musulunci addini ne mai tattare da haske mara yankewa, wannan haske da sauran baiwa dake tattare da Jarmai da shi za'a yi aiki domin samarwa wani cikin jikokinka, wannan kujera ta mulkin Bahja, duk wanda aka yi wa wannan aikin kuma, tabbas tauraruwarsa za ta haskaka da taimakon hasken musulunci, kuma zai soyu a zuƙatan jama'a da taimakon tasirin addinin musulunci, hatta da kai sai ka so shi kuma ka ba shi kujerar ko baka shirya ba."

"Dodongaji kayi wani abu, lallai-lallai har a zuciyata Yarima mai zuwa nake son ya mulki Bahja, kai ka kawo shawarar a farko, amma a yanzu na fi ka son hakan ya tabbata."

Faɗin Sarki Gamboji

"Zan barsu suyi aikin, sai dai zan daƙushe da zarar sun kammala, ƙaiƙayi koma kan masheƙiya za'a musu, lamarinsu zai sake taɓarɓarewa, har ma wataƙila shi wanda ake son ya hau kujerar ya bi Jarmai inda ba'a dawowa, shi wannan haske da tasirin baiwar Jarmai kuma, za'a sake cusawa Yariman gobe."

"Na gode dodongaji, wuta ta baku sa'a"

Sarki Gamboji ya faɗa cikin jin daɗin matakin da dodongaji ya ɗauka.

"Za su ciyar da Baiwa Kubura wani magani, sai dai wannan maganin banda ikon ɓata shi, amma tunda na jima da haɗa abun cikin nata da badakiren Aljani ƙunƙur da tawagarsa, ina da yaƙinin za su kula da wannan, daga cikin ciki har Yarima ya fito za su kasance a tare da shi su ke bashi kariya, zan zuba ido, inda suka kasa na taimaka."

Faɗin dodongaji.

Sarki Gamboji bai da abun cewa sai numfashi da ya ja ya sauƙe, wato da gaske ya sake ruruta wutar lamarin tunda ya ajiyesu yayi wannan maganar, to waye? Wacece ke wannan aika-aikar?

Murmushi mara kyan gani dodongaji ya saki tare da cewa...

"Wannan ma kaɗan ne, tukunna ba'a yi komai ba Sarki Gamboji, na faɗa maka fiye da abu na ƙarshe mafi muni da zuciyarka za ta tunano maka, to za'a aikata shi a masarautarka, ka dai kasance a ankare, kuma daidai da iska idan ka shaƙeta bata nitsar da kai ba, to ka ƙaraso baƙar kogon dodongaji ba ɓata lokaci, domin ba'a bori da sanyin jiki.

BAYAN SHEKARA BIYAR (1911)

"Wai meyasa haƙata ta kasa cin ma ruwa ne har yanzu? Shekara ɗaiɗai har biyar amma komai ya kasa daidaita, shiru kakeji tamkar an shuka dusa, Yautai idan ba za ka iya ba zan bi wata hanyar, domin na kasa gane kalar aikinka, ni da mai asarar gishiri a dahuwar ƙaho ba mu da banbanci, tunda duk sammakal nama ya dahu romo ɗanye."

***

Follow my page's

●WATTPAD

@Uwarbatoorl96

●AREWABOOKS.

@Uwarbatoorl96

●TIKTOK

@Uwarbatoorl96

*