Shafi na shida
YARIMA BAHJAT 🌏
Na
Harira Salihu Isah
(Uwar Batoorl)
**DISCLAIMER: komai a wannan labari ƙirƙirarre ne, ban yi dan cin mutuncin wani ko wani Addini ba, ko wani mutum.**
**Ban yarda kuma a sauya mini labari ta ko wace siga ba, wanda ya aikata hakan hukuma za ta rabani da shi.***
SHAFI NA SHIDA
⭐️
"Mai takalmi, kar ki ce za ki kawo mini wargi a nan wajan, sanin kanki ne aiki na miki kuma ya ci, sai dai da yake gaba ma da gabanta shiyasa kike ganin haka...."
"Me ka mini Yautai?"
Jaruma maitakalmi ta jefa masa tambayar a ƙufule murya a sama.
Wani gurjejen dariyar da bai da alaƙa da nishaɗi, Yautai ya saki, da jajayen idanuwansa ya aikawa Jaruma maitakalmi wani banzan kallo.
"Tashi ki fice"
Ya faɗa a mugun tsawace, har sai da amon sautinsa ya zagaye dajin.
Yadda ƴan hanjin cikin Jaruma maitakalmi suka kaɗa, ya sa babu shiri ta miƙe, tana ƙoƙarin yin magana hatsabibi Yautai ya dakatar da ita a tsawace.
"Idan kika kuskura kika ce kanzil sai na mayar dake ganyen da zan ɗaura a ƙuguna, ki tashi ki fice na ce!"
Da wani gigitaccen tsawa ya ƙarishe maganar.
Jaruma maitakalmi tayi saurin runtse idanuwanta, gami da ɗaga hannayenta sama, a take kuwa guguwa yayi gaba da ita, da ya tashi maimakon ya direta sai jifa yayi da ita, har ta bugu da wani kututturen itace, ƴar ƙara ta saki gami da lallaɓawa ta daddafa ta miƙe tsaye, ta tsaya da niyar kakkaɓe jikinta, ta jiyo wani irin sauti da rugugi tamkar bishiyun dajin sun yo ayari za su far mata, ai a mugun guje ta ɗiba bata tsaya kakkaɓe jiki ba, balle kuma duba inda ta buge da kututturen itace.
"Hahahahahah! Hahahahaha! Hahahahaha!"
Sautin dariyar hatsabibi Yautai ke karaɗen dajin, a yayinda Jaruma maitakalmi ke gudun ceton ranta, domin wannan rugugi da ƙarar ba su daina binta a guje ba, dalilin da ya hanata furta ƙala balle tsayawa yin wani tunani.
***
Zaune take ta zuba tagumi kamar kullum, banda sharar hawaye ba abinda take yi, wani sababben aikinta a duk tsawon shekaru biyar ɗin nan, kuka dai shi ne aikinta, ta kasa sabawa da ƙaddarar da ta afka mata ta tsintar kanta a masarautar Bahja, masarautar da aka ɗauki ƙulle-ƙulle ba a bakin komai ba, a salwantar da rai a banza, gaba ɗaya ji take da ma mahaifanta ba su haifeta ba, da dai mummunar jarabawar da take ta fiskanta, tun daga ranar da tsautsayi ya saka ta a jerin bayin da Abdi zai kusanta, ba ta sake samun salamar rayuwa ba, kuma ta san da wuya ta samu ɗin har mutuwarta.
tunda abinda ta haifan ya mutu amma kuma har yanzu ba'a ƙyaleta ba, ba za'a barta taji da ciwo ɗaya ba, tayi ciki ba aure, ta haihu abin ya koma, sannan duk bayan haka a ɗaura mata aure da...
Motsin shigowarsa ɗakin shi ya katse zancen zucinta, sai dai kamar bata ji shi ba, domin ko ƙwaƙƙwaran motsi bata yi ba balle tayi yunƙurin yin magana ko tashuwa.
Cikin taku na nitsuwa da rashin hayaniya da kamewa, Abdi ya ƙarasa inda take zaune.
"Ba kya gajiya da kuka Jarumar Abdi, amaryar Abdi."
Ya faɗa yana haɗa jikinta da nashi.
Baiwa Kubura wacce tunda aka ɗaura mata aure da Abdi ta koma Jaruma maigoshi, ko mosti bata yi ba balle ta ce wani abu.
"Idan har rashin Yarima ne ya sa har yanzu kika kasa daina kuka, kike zama cikin damuwa, kuma kika ƙi bari a baki hadimai da za su ke ɗebe miki kewa, to kiyi haƙuri mu samu wani Yariman."
Da sauri Jaruma maigoshi ta ƙwace jikinta, da muryar kuka ta fara roƙon Abdi, guiwowinta a ƙasa kanta a duƙe hannayenta a haɗe.
"Dan Allah Takawa ka rabani da auren nan ba zan iya ba, bazan iya kishi da matanka ba, ni ba kowa bace face baiwa ƙasƙantacciya, dama ciki ne, kuma na haife shi alhamdulillahi ya zo ba rai kamar yadda ake so, dan Allah kar a sake gargara rayuwata, zama da aurenka tamkar gayyato mutuwa ce, domin bayan ɗan da aka raba ni da shi, ni za'a nemi rabawa da duniyar, dan Allah takawa!"
Jaruma Kubura ta ƙarishe maganar da wani irin karyayyen sauti, mai cike da ciwo da rauni, har ƙasan zuciyarta ba za ta iya ba, ba za ta taɓa iyawa ba.
⭐️
MASARAUTAR ANFA (1911).
"Zo nan ƴa ta."
Faɗin Fulani Hajara da kwantaccen murmushi a saman fiskarta, murmushin da kallo ɗaya za ka masa ka san na ƙarfin hali ne kawai.
Wata kyakkyawar yarinyar da ba ta gama cika shekaru biyar ba, ke tsaye ɗan nesa da Fulani Hajara, idanuwanta ƙur a kanta kamar ranar ta fara ganinta, duk ƙiran da Fulani Hajara ke mata da miƙa mata hannu ta ƙi zuwa gareta, wanda dama a duk tsawon shekarun da aka haifi yarinyar haka suke yi da Fulani, ita ba ta da sabo, ga shi Fulani Hajara kuma yarinyar ta shiga ranta sosai take ƙaunarta.
"Daleesha ba za ki je wajan Fulani Babba ba?"
Wata dattijuwar mata tayi magana wacce da alama ita ce mahaifiyar yarinyar da ta ƙira da Daleesha.
Guntun murmushin yaƙe Fulani Hajara ta kuma saki, sannan ta ce, "Daleesha dila sarkin wayo, ita fa bata yarda da kowa ba sai Mamanta."
Fulani Hajara ta dire maganar, wani abu na sokin zuciyarta, wani iri miki ta famo na shekaru goma sha, Mama, Uwa, wataƙila ita ba ta da rabon amsa wannan sunar.
A hankali ta sa hannu ta share hawayen da ya zubo mata.
"Kiyi haƙuri Rankishidaɗe, ƙuya irin na Daleesha na kasa gane masa, ke wuce ki je ko na zane ki."
Maman Daleesha ta ƙarishe maganar tana mai zarowa Daleesha idanuwa.
"A'a Karime, ƙyaleta kar ki saka ta kuka, kiyi aikinki, barta tayi wasanta mu ta kallon juna daga nesa, idan kuma Muhjan ya shigo wataƙila ta matso kusa da ni idan taga yayi hakan.."
Faɗin Fulani Hajara.
Sai da Maman Daleesha ta sake bai wa Fulani Hajara haƙuri, sannan ta juya ta cigaba da aikinta, a can cikin zuciyarta tausayin Fulani Hajara ne fall, duk da a bayan haihuwar Daleesha ne suka zo masarautar, amma ta samu labarin ɓatan dabon yaron Fulani Hajara, kuma tun daga ranar har zuwa yanzu mamaki bai saketa ba, ɗa ya ɓata uwarsa ko ganinsa ba tayi ba, to ta yaya? Kuma garin yaya? Ɗan mutum ba ɗan tsana ba.
Fulani Hajara idanuwanta a kan Daleesha, wacce ke wasanta kamar bata san da kowa a wajan ba.
Guntun murmushi Fulani Hajara ta saki, wanda ya zame mata jiki tun ranar da ta fara ɗaura idanuwanta a kan Daleesha, domin kafun zuwan ranar da ta fara ganin Daleesha ta mance yadda ake murmushi tunda ɗanta ya ɓace.
"Daleesha!"
Ta ƙira sunan a zuciyarta.
Juyowa Daleesha tayi ta zubawa Fulani Hajara madaidaitan idanuwanta, domin a kunnenta taji ƙiran sunanta da Fulani Hajara tayi.
"Ummi!"
Daleesha ta ƙira mahaifiyarta da zazzaƙar muryarta a shagwaɓe.
"Na'am Daleesha."
Mahaifiyarta ta amsa.
"Kai ni wajan Abbi."
Yarinyar ta faɗa a shagwaɓe.
"Dal...."
"A'a ɗauketa ki kaita, idan ya so sai ki dawo."
Faɗin Fulani Hajara da ta katse maganar da Maman Daleesha za tayi.
"To Rankishidaɗe."
Ta amsa, sannan ta ƙarisa wajan Daleesha, ta miƙa hannu za ta riƙeta, amma Daleesha ta ce sai dai a ɗauketa, a haka Umminta ta ɗauketa suka fice ba yadda ta iya, tunda ita da Abbin Daleeshan ne suka shagwaɓa ta.
"Ummi sunana akwai daɗi ko?"
Daleesha ta tambaya.
Guntun murmushi Ummi ta saki, gami da girgiza kai, sannan ta ce, "Eh Daleesha, sunanki akwai daɗi sosai, kuma yana da ma'ana."
"Shiyasa kullum sai Fulani Babba ta ƙira sunana a zuciyarta, bata san ina ji ba, tana son sunana ko Ummi?"
Daleesha ta sake jefawa Umminta tambaya, cikin sigar yaranta irin ta yara ƙananu masu wayo da kuma yawan magana.
"Ooh ni! Daleesha ya aka yi kika san tana ƙiran sunanki a zuciyarta? Ba na son yawan maganarkin nan fa ta shiririta."
Ummi ta faɗa cikin sigar faɗa a iya daidai shekarun Daleesha.
Tura baki Daleesha tayi, "Shiyasa ma na ce ki kaini wajan Abbi, shi idan na faɗa masa ai yana yarda, yanzu ma sirri za muyi da Abbina."
"To naji ƴar Abbi, Allah ya shiryeki."
Faɗin Ummi.
"Amin Ummina."
Daleesha ta amsa tana lafar da kanta a kafaɗar Umminta.
Murmushi Ummi ta saki, ƙaunar tilon ƴarta mace na sake mamaye zuciya da ruhinta, tana da yara maza har biyar, amma ba ta jin su a rai kamar Daleesha, Daleesha mai abun mamaki tun daga ranar da aka haifeta, domin ko zama Daleesha bata fara koya ba, kai tsaye rarrafe ta fara, watanninta bakwai tana tafiya ko ina da ƙafafuwanta, shekara ɗaya da watanni ta fara magana, haƙori kuwa cikin sauƙi ta yi su kamar wacce aka bawa sadakarsu, sam-sam ba ta da laulayi irin na sauran yayyunta, ko da ta kai shekaru uku kuma rass zaƙin muryarta ya fito idan tayi magana ka ce wani mai shekaru goman ne yayi, sam-sam babu tsami a maganarta, ga manyance ga ƙuya, bayan ita da Abbinta da kuma yayyunta ba ta zuwa wajan kowa, ko surutun nata ma iya su take yi wa, sai kuma Yarima Muhjan, ɗa ɗaya tilo ga Mai martaba Sarki Ahmad da Fulani Samira, muddin suka haɗu da Daleesha to magana take masa sosai, domin sa'i da lokaci yana shigowa sashin Fulani Babba, a nan suke haɗuwa har suka shaƙu, tunda daga ita har Daleeshan ba su taɓa taka sashin Fulani Samira ba.
"Ummi to me ma'anar sunana?"
Daleesha ta tambaya.
"Kinga aiki zan koma nayi, ki raba ni da surutunki Daleesha, je wajan Abbi ya faɗa miki."
Faɗin Umminta bayan ta sauƙar da ita.
"Sannu da aiki malam."
Faɗin Ummi ga dattijon da ke tsaye a gabansu, fiskarsa ɗauke da tattausan murmushi.
"Yauwa Ummin Daleesha, sannunki da naki aikin, ta taso ki ko?"
Ya tambaya.
"Kai da ka sani, wannan rigimammiyar yarinyar taka, ni dai na koma sai anjima"
Ummi ta faɗa gami da juyawa.
"Abbi."
Daleesha ta ƙira sunansa bayan da ya ɗaurata saman ƙafarsa.
"Na'am Daleen Abbi, ki taso Umminki ko?"
"To Abbi ai Fulani Babba ce sai take ta ƙiran sunana a zuciyarta bata san ina ji ba, kuma tana so naje wajanta, ni kuma tausayinta nake ji, idan naje zan yi kuka."
Murmushi Abbin Daleesha yayi, sanin wannan kaɗan ne daga cikin kalar manyancen Daleesha.
"Me ya faru kike tausayinta?"
Abbi ya tambaya.
"Abbi ai Yaronta ya ɓata, Umn! Abbi ka san me?"
"A'a."
Abbinta ya faɗa yana kallonta da mamaki da al'ajabi.
"Abbi ita ta ba da shi fa, Allah kar ka ce ƙarya ne Abbi."
Daleesha ta faɗa a hankali cikin raɗa kamar mai tsoron wani ya jiyo ta.
"Wa ya faɗa miki?"
Abbi ya tambaya da mamaki.
"Kaka mana, Abbi ba na baka labarin Kaka ba, idan ta zo fa har yawo take kai ni can wani gari kamar dai nan, sai dai mutanen can..."
"Ooh! Kaka ba, na tunata, to ya isa haka Daleeshan Abbi, ki rage yawan surutu kin ji autar Abbi, ba kyau yawan surutu, kinga masu iya magana fa suna cewa baki shi ke yanka wuya, duk da ba ki da wayo amma dai ki rage yawan surutu."
Faɗin Abbinta da yayi saurin katse ta.
"To na daina Abbi, amma Abbi tana son ta sake haihuwa, kuma wani abu aka mata shiyasa ba ta haihu ba, amma Abbi ka yarda na cire mata abun?"
Daleesha ta tambaya.
"Daleesha ina raba ki da kiwo kina faɗin kyalla ta haihu, Allah dai ya shirya mana ke ya tsare ki ya miki albarka."
Faɗin Abbi cikin damuwa, domin indai manyan maganganu ne daga bakin Daleesha ba yau ya fara ji ba, tunda ta fi yin zantukanta da shi fiye da Umminta, shi dai tsoronsa Allah tsoronsa kar a cutar masa da ƴa sanadiyar haka, duk da ma dai sauƙin abun ba da kowa take magana ba ga ƙuya, amma yana tsoron kar a cutar da ita, tunda ya fahimci baiwa ne ko wani abu daban a tattare da ita.
"Abbi kar na cire mata?"
Ta tambaya a marairaice da shagwaɓa.
"Abbi Kaka fa ta ce duk wanda ya taimaki wani zai samu lada, kuma zai shiga aljanna, kuma har Mamansa da Babansa za'a saka su a aljanna, Abbi ba ka so mu shiga aljanna? Abbi ka san me?"
"Daleesha ya isa haka, naji ki cire mata, amma ki bi a hankali bana so a cutar da ke..."
"Abbi ai babu abinda zai cutar da ni, saboda Kaka ta ce ni ƴar baiwa ce, ta ce ma akwai abinda zan yi na mamaki amma sai na girma..."
"Daleesha!"
Abbi ya katseta yana dafe kai.
"Ki cire mata, surutun ya isa haka, ki mini karatun da aka muku da safe a makaranta."
Murmushi mai kyau Daleesha black beauty ta saki, sannan ta gyara zama ta fara biyawa mahaifin nata karatun da aka musu, suratul buruj ne, kuma ta iya shi tas, haka Abbin nata ya shiga ɗora mata suran gaba, domin shi ma malami ne a masarautar, shi ne ma Ladan nasu.
FULANI SAMIRA
"Yarima Muhjan!"
Ta ƙira sunan tilon ɗanta mai shekaru goma, cikin tsantsar ƙauna da soyayya, domin kallonsa kawai idan tayi sai taji duk duniya an gama sallamarta, haihuwarsa ya fiye mata komai, musamman da ya kasance shi kaɗai wajan Sarki Ahmad kamar yadda ta so, tunda a tsawon shekarun kaf Fulani Hajara ba ta sake ko ɓatan wata ba, domin ba ta tsaya kallon ruwa ba balle kwaɗo ya mata ƙafa, tunda taga La'anannen dattijo ya tsaya yi mata wasan yara, tuni ta bar ayarinsa ta bi na wani Sarkin, ga shi kuwa kwalliya ta biya kuɗin sabulu, tunda buƙata ta biya, dama buƙatar maje Haji ai salla ne.
La'anannen dattijo ya ce tana haihuwa Fulani Hajara ma za ta haihu, amma shiru har yanzu tunda Boka Tungu na kan kwari ya mata aiki, to ai gaba ma da gabanta wai Kura ya hangi Zaki da Giwa.
"Na'am Fulani."
Yarima Muhjan ya amsa idanuwansa a kan mahaifiyarsa.
"Tashi ka shirya maza ka tafi fada wajan mai martaba, na sha faɗa maka kake zuwa ana sha'anin mulki da kai, domin a lokacin da ka tashi amsa komai ya zo maka da sauƙi, tunda ka saba zaman fada kana ganin komai."
Ɓata fiska Yarima Muhjan yayi kamar wani ɗan shekara biyu, "Fulani ni ba na so...."
"A kull naka!"
Fulani Samira tayi gaggawar katse abinda zai ce, tunda ta san labarin gizo bai wuce na ƙoƙi, waje guda kenan da suke samun damuwa da shi, duk sonda take masa ta fatattakesa ta ci masa mutunci ta kora shi fada, ai bai isa ya sakata yin aikin banza ba, batun ba ya son maganar mulki ma ai bai taso ba, dole ya mulki Anfa ko ya so ko ya ƙi, ko an so ko an ƙi kuwa.
Fiskarta ne ya tattare da ɓacin rai da fushi kamar ba ita ta gama yi masa murmushi cikin soyayya irin ta uwa ba.
"Yarima Muhjan, wannan ya zama lokaci na ƙarshe da za ka sake furta kalmar ba ka son sarauta, ko da kuwa a bayan idanuwana ne, idan ba haka ba zan yi mummunan saɓa maka, fatan ka ji ni da kyau ko?"
Fulani Samira ta dire maganar tana kama kunnenta, alamar yaji gargaɗinta da kyau.
"To Fulani"
Yarima Muhjan ya amsa yana daƙuna fiska.
Haka ta saka shi gaba sai da ya shirya cikin shiga ta alfarma, ya kuma ɗaura da alkyabba da rawaninsa kamar sai har ya zama Sarkin.
Sai da Fulani Samira ta tabbatar ta haɗa shi fa dogarawa su raka shi fada, sannan ta juya ta koma ɓangarenta ta na mita a zuciyarta.
"Idan ma wani ne ya shiga ya fita domin yayi maka farraƙu da kujerar nan, to kuwa yayi ƙarya ya kwana da yunwa, Ni Samira wargi ce daidai da ƙugun kowa, wanda bai shiga hanyata ba ma na murtsuke shi balle, wanda ya nemi shigar mini hanci da ƙudundune, ai kuwa sai na ga bayan ko ma waye ne."
Ta ƙarishe zancen zucinta daidai sadda ta sanya wani fari da jan ƙyalle a jikinta, baya ta baiwa bangon ɗakinta, ta ɗaga ƙafa guda kamar mai shirin yin wasan yara ta langa, ta sadda kanta ƙasa gami da shanye idanuwanta kamar mai shirin rufe su, ta fara karanto wasu kalmomin tsafi.
⭐️
MASARAUTAR BUZJAR (1911)
Wani babban fili ne ɗauke da dubban jama'a, idan ka gani ka ce kaf ma al'ummar masarautar ne a tare a wajan, to dai kusan hakan ne, sai dai kuma akwai ɗaiɗaikun da suke gidajensu, wajan sana'ar su, ko wajan ayyukansu, ba su samu halartar taron ba, bisa ra'ayin kan su, domin a masarautar kowa na da ƴanci da ra'ayinsa kansa na yin duk abinda ya so, illa abu ɗaya ne da babu mai wannan ƴancin aikatawa sai abinda Sarki ya yanke, wato Addini, hakan ya sa kaf masarautar addini guda suke bi, wato addinin Nasara(kiristanci).
Gungun mutane ne a tsakar filin, waɗanda dogarawan Sarki Dungu, suka yo fataucinsu, suka kuma kamo su suka taho da su a matsayin bayi.
A al'adar Sarki Dungu, duk lokacin da baƙi suka shigo masarautar, ko aka kamo bayi, ana tara kaf jama'ar masarautar, a kuma saka bayin a tsakiya, a sanar da su suna da damar yin komai amma banda yin wani Addini bayan kiristanci, to a wannan karon ma dalilin taron kenan, abinda Sarki Dungu ya miƙe domin sanar musu kenan.
"Ya ku baƙin bayin wannan masarauta tamu mai tarin albarka daga uba Yesu Almasihu, ni Dungu dungun Buzjar ina mai yi muku maraba da zuwa masarautar ƴanci, masarautar da za ku ji daɗin rayuwa a cikinta kamar ba bayi ba, domin kuna da damar yin komai da aikata komai da ranku yake so, ruhi mai tsarki ya lamunce muku, musamman da kuka shigo a sa'a, kasancewar muna hada-hadan naɗa magajina a kujerata, wato Yarima Dodo, dan haka ku kasance cikin walwala da aminci har a kammala taro, albarkar uwa, ɗa da ruhi mai tsarki ya kasance da ku..."
"Emen!"
Taron jama'ar suka haɗa baki wajan amsawa da amsakuwwa.
"Ku kasance a Addinin aminci da nasara, wato Addinin kiristanci."
Sarki Dungu ya kuma faɗa, ya na watsa idanuwansa ga gungun bayin, domin son ganin yanayin fuskokinsu.
Ya kuwa gani, domin ƙalilan daga cikinsu, cike da tashin hankali, mamaki da ƙyama duk a lokaci guda suka kai dubansu gare shi.
"Addini ɗaya muke gudanarwa a Buzjar, Addinin kiristanci, kuma dole duk mazaunin Buzjar yayi imani da Yesu Almasihu."
Sarki Dungu yayi maganar, a lokacin guda kuma fara'ar fiskarsa na ɗaukewa, sannan a take ya yiwa dogarawansa alama da ido, su kuma suka ɗauki haske, hakan ya sa suka yi wajan gungun bayin, suka umurcesu da su bi layi.
Da mamaki bayin suka yi layi kamar yadda aka buƙata.
"Duk wanda ya yarda yayi imani da Ruhi mai tsarki, zai sha wannan giyar, zai kuma amshi cross domin yin bauta daga ɗakinsa, wanda bai aminta ba kuma..."
Sarki Dungu yayi shiru bai ƙarisa ba.
"Ka maimaita abinda na ce."
Wani dogari ya faɗa ga dattijon farko da ke kan layi, fiskar nan a murtuƙe ba rahama balle alamun wasa.
Jinjina kai dattijon yayi, dogarin ya karanto masa ya maimaita cikin aminci, dama shi mabiyi addinin gargajiya ne, shiyasa dan ya koma kiristanci ba komai bane.
Giyar aka ba shi a ƙwarya ya kwankwaɗa, aka miƙa masa cross ya amsa cikin hanzari da ƙas da kai, sannan ya wuce zuwa inda za'a tara su, kafun a kai su masauƙinsu, wato sashinsu na bayi.
Mutane ɗaiɗai har goma aka yi haka da su, sai a kan ta sha ɗayar ce aka samu akasi, mace ce mai tsohon ciki ma kuwa, ta na tallafe da cikinta ta matso.
"Ki maimaita abinda na ce"
Dogarin ya faɗa a murtuƙe.
Girgiza kai matar ta fara idanuwanta na zubar da ƙwalla.
"Na yi Imani da Uwa, Ɗa da Rubi mai tsarki, cewa Yesu Almasihu shi ne..."
"A'a, a'a kar ku saka ni barin Addinina na gaskiya, Addinin musulunc....."
Tun kafun ta ƙarisa maganar, wani irin sauti ya ratsa, wanda kafun kowa ya farga sai kan matar aka gani a ƙasa, jini ya fara tsartuwa, gangar jikinta yayi gefe ya faɗi, har lokacin hannayenta dafe da tsohon cikinta.
"Zainabaaaaa!"
Wani magidanci ya ƙira sunanta da ƙarfi da muryar kuka, yayi kanta, sai dai kafun ya ƙarasa wajan gangar jikinta, shi ma ji Kake Fiyau! An raba kansa da gangar jikinsa, cikin tsantsar rashin imani balle tausayi.
"Duk wanda ba zai bi Addinin da muke bi ba, wannan shi ne hukuncinsa."
Faɗin wannan dogarin cikin muzurai hankali kwance, kamar ba mutane ya raba da rayukansu ba.
........
Follow my page's
●WATTPAD
@Uwarbatoorl96
●AREWABOOKS.
@Uwarbatoorl96
●TIKTOK
@Uwarbatoorl96