Chapter 26
Da safe bayan Sadeeq ya tashi a bacci yaje ɗakin mama ya gaishe da ita, bayan sun gaisa ya tashi zai fita ta ce " babana zo ka zauna muyi magana."
Zama ya yi ya ce " toh mama."
" Dama haɗa lefe ne, ina kaje ka samu antyn ku kuyi magana ka bata kuɗi ta je Dubai ta haɗa duk abinda ake buƙata kaga bamu da isashen lokaci."
Jinjina kai ya yi ya ce " toh mama in shaa Allah kafin na fita zan tsaya muyi magana in shaa Allah."
" Toh shikenan, Allah ya yi maka albarka."
" Ameen."
Bayan ya fito daga part ɗin mama ya wuce na aunty.
A parlour ya sameta tana yiwa Nafeesarh tsifa.
Gaishe ta ya yi,bayan ta amsa ya ce " yanzu aunty wannan ƙatuwar kike yi wa tsifa."
Murmushi ta yi ta ce " ya zanyi doctor ta saka ni a gaba."
Murmushin shima ya yi ya ce " dama mama ce ta ce nazo muyi magana akan zuwa haɗa lefe."
Tsayawa ta yi tsifar da take yi ta ce " mun fara magana da ita jiya akan maganar."
" Ta ce tunda ina da visa sai kawai a siya ticket zuwa jibi sai na tafi kar lokaci ya ƙure."
Jinjina kai ya yi ya ce " toh shikena,Allah ya nuna mana jibin,yanzu zan tura maki 10 million idan da buƙatar ƙari sai muyi waya idan kinje."
Miƙewa ya yi ya ce " ni zan ɗan fita sai na dawo."
Nafeesarh ce ta ce " yaya a dawo lafiya."
Ya ce " Allah ya sa."
Aunty ma ta ce " toh doctor Allah ya tsare."
Ya ce " ameen."
Bayan sun gama jajen rayuwa mom ke faɗa ma mamy an kawo kudin auren Jaiyana kuma har an sa sati biyu.
Da farin ciki ta ce " masha Allah, Allah ya nuna mana lokacin ai kamar yau ne."
Mom ta ce " dama akan maganar kayan da za'a siya, ina ganin kawai muyi order su ba sai munje da kanmu ba."
" Da na ce sai mu shirya muje ko Turkey ko Dubai, amma kuma yanzu akwai abubuwan da suke buƙatar nayi su a nan."
" Ai ina ganin muyi order kawai,tunda duk ɗaya ne,muyi order ɗin kawai zai fi." Mamy ta faɗa.
" Nima kuma kinga ga yarinyar dake gidana be kamata a ce na kama hanya na tafi wani wurin ba."
" Yarinyar na buƙatar wanda zai yi guiding ɗin ta a wannan halin da take ciki,kuma nima kinga ban san wanda zai yi wa nawa ʼyaʼyan ba."
" Haka ne kam Allah ya ƙara shirya mana zuri'a."
Mamy ta ce " Ameen."
Tunda ya shiga ɗaki yake ta kai da kawowa gaba ɗaya duniyar ta yi masa duhu.
Ƙwaƙwalwarshi ta tsaya gaba ɗaya ta dena aiki, ya ma rasa wani irin tunani zai yi.
Kallon kanshi ya yi a madubi sai kuma ya ji muryar Safiyyah a cikin kanshi tana maimaita yadda aka yi ta aure shi.
Hannunshi yasa ya daki madubin ya tarwatse, jini ne ya fara ɗisa daga jikin hannunshi.
Da sauri Zannur dake compound ɗin gidan yana ta kai kawo ya yi hanyar ɗakin da HAYDAR yake ciki saboda yana da tabbacin wani abun HAYDAR ya fasa.
HAYDAR mutum ne me hankali da nutsuwa amma duk lokacin da ranshi ya ɓaci toh wannan nutsuwar tana barin gangar jikinshi.
Bubbuga ƙofar Zannur yake yi yana kiran sunan HAYDAR amma be amsa ba.
Cigaba da bugawa ya yi amma bai buɗe ba, tunawa ya yi yana da key ɗin ɗakin HAYDAR shima a nashi ɗakin.
Ɗakinshi da ke gefen na HAYDAR ya shiga yana addu'ar Allah yasa ya cire key ɗin daga jikin ƙofar bayan ya rufe.
Bayan ya ɗakko key ɗin yana saka shi kuma ya buɗe.
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya tura ƙofar ya shiga.
A jikin madubi ya ganshi a tsaye ga hannunshi yana ta ɗigar da jini.
Toilet ya shiga ya ɗakko first aid box ya dawo ya kama shi ya zaunar da shi a gefen gadon.
Sai da ya fara yi masa dressing sannan ya ɗago ya kalleshi ya ce " HAYDAR are you out of mind?, kana son ka illata kanka saboda abinda ya riga ya faru kuma bamu da ikon hana faruwar shi ko goge shi a babin rayuwarmu?."
" Meyasa a duk lokacin da ranka ya ɓaci kake rasa nutsuwarka?"
" Ya kamata ka koyi sarrafa ɓacin ranka."
Faɗa yake yi masa amma ba tare da ya ɗaga masa murya ba.
Don yasan yana ɗaga masa murya yadda ranshi yake a ɓace toh tabbas a kanshi zai sauke duk wani fushi da ɓacin ransa.
Ɗago jajayen idanunshi da suka rine ya yi ya kalli Zannur ya ce " how do you expect me to react Zannur bayan kai da kunnenka kaji irin abubuwan da suka rinƙa faruwa da ni."
" Ko kana tsammanin bayan duk abubuwan da suka faru nayi dariya na nuna kamar komai ma bai faru ba?"
Girgiza kai ya yi ya ce " ba haka nake nufi ba, kawai dai bai kamata ka hukunta kanka da laifin da ba kai ka aikata ba."
" Tabbas an cutar da rayuwarka amma ba haka ya kamata ka ɗauki mataki ba."
" Duk abinda ya faru ya riga ya faru, ya kamata ka manta da duk wani abu da ya faru,let's bygone be bygone."
" Safiyyah ta yi laifi,amma ita ma ba da son ranta ta aikata abinda ta aikata ba."
" Ya kamata ka yafe mata ka kuma manta abinda ta yi maka."
Wani banzan kallo HAYDAR ya yi wa Zannur ya warce hannunshi da yake ƙoƙarin ɗaura mashi bandage.
Ya ce " kar ka ƙara kira man sunanta a nan,idan ba haka ba zan yi maka abinda baka taɓa tunani ba."
" kuma ma dai ina tunanin ka samu matsala a ƙwaƙwalwarka Usman, tunda har kake tunanin na ƙyale yarinyar nan ta tafi scot free.?"
" Amma idan ka ce haka ma baka yi man adalci ba."
Hannunshi Zannur ya kama ya ce " haba HAYDAR kai kake yi man nasiha a ko yaushe kana faɗa man muhimmancin haƙuri."
" Duk lokacin da zaka buɗi baki kayi magana haka ka ke cewa Inna Allāha ma'a aṣ-ṣābirīn meyasa kai baka son kasancewa cikin su ne?"
" Ko dama iya a baki ne maganar ta ka bata kai har zuciya ba?"
" Idan da gaske kake toh yau nima zan yi maka tuni duk da nasan ka sani."
" HAYDAR a matsayina na ɗan uwanka kuma abokinka, ka yi haƙuri ka yafe ma Safiyyah Allah yana tare da masu haƙuri."
" Duk wanda kaga ya yi nasara toh tabbas ya yi haƙuri, ban taɓa jin labarin wanda aka ce bai yi haƙuri ba kuma ya yi nasara."
" Don haka ina me baka shawara da kayi haƙuri, nasan tabbas zaka ga amfanin hakan."
Maganganun Zannur ne suka fara tasiri a cikin zuciyarshi,kuma baya da niyyar fasa abinda yaso ya yi don haka ya miƙe ya shiga toilet ya barshi a nan.
Girgiza kai Zannur ya yi saboda ya fahimci abinda hakan ke nufi.
Safiyyah dake zaune a ɗakin da aka bata tana karanta Al'qur'ani ta ji wayarta na ringing da har ba zata ɗauka ba bayan ta ga me kiran sai kuma ta ɗaga.
Daga ɗaya ɓangaren Shema'u ta ce " ƙawata ya kike,kwana da yawa."
Safiyyah da kamar jira take ta ce "Allah ya ki yaye na zama ƙawarki,ki je can ki nemi ƙawarki amma ba niba."
" Na yi nadamar saninki a cikin rayuwata, saninki bai amfaneni da komai ba sai taɓewa,ki je na barki da me fitowar rana da faɗuwarta."
Daga cikin wayar Shema'u ta fashe da dariya ta ce " na yi baƙin ciki da kika shiryu tun yanzu."
" Ina da saƙo wurin mahaifiyarki,ki faɗa mata ba komai ake gani a yi magana ba."
" Yanzu gashi iya yinta ya janyo ɓacin ta ki rayuwar."
" Na saka ki a duhu ko?"
" Toh bari na baki ɗan taƙaitattacen labarin dalilin da ya sa na shigo cikin rayuwarki."
" Wata rana ina zaune a cikin mota muna jin daɗi tare da saurayina,motar da muke ciki sai girgizawa take yi."
" Duk wanda ya zo wucewa sai dai ya ce Allah ya shirya ya wuce,amma ita kuma ta tsaya ta ƙwanƙwasa mana ƙofa."
" A yanayin da muke na sauke glass ƙasa, bayan da taga yanayin da muke ta kau da idonta daga kallon mu."
" Wa'azi ta yi mana me shiga jiki,amma idan ya shiga ta kunnen dama sai ya fita ta kunnen hagu."
" Wannan dalilin ya sa na yi bincike na gane wacece ita har na fahimci ta fi son ki kaf cikin ʼyayanta."
" Ni kuma na ɗauki alƙawarin sai na ɓata maki taki rayuwar kema."
" Kamar yadda ta ke kallon mu a matsayin watsatsu."
" Kema sai kin zama haka."
" Wannan ne dalilin da yasa na fara bibiyarki a makaranta har na samu chance ɗin da zan gabatar da aiki na ba tare da na sha wahala ba."
" Amma duk da haka na yi takaici da kika shiryu tun yanzu, saboda na so ace kin yi zina da aurenki, don shi kaɗai ne zai sa naji na samu sukuni daga abinda mahaifiyarki ta yi man."
" Saboda ni duk wanda zai yi man nasiha toh tabbas babban maƙiyi na ne shi."
Tana gama faɗin haka ta kashe wayarta.
Wani sabon kukan Safiyyah ta fashe da shi tana ƙara da na sanin rayuwarta.