NANNY(MAI RENO)

6

by @jamilaumarjanafty

*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Na*

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty)*


*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*

*Sanyi flusher!* 
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. 
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*

*Tightening set na hade mace ta  dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.

*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*

*Muna da gimbiyar zabuwa  da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.

       *BABI NA SHIDDA*

Har ya isa Office fuskarshi ba annuri, har suka gama sallamar baƙinsu waɗanda abokan harkarsu ne daga Lagos, office d'in Ishaq suka wuce suna cigaba da tattauna abunda ya shafi kasuwancinsu, suna shiga Tahir ya nufi ɗan ƙaramin fridge d'in dake Office d'in ya buɗe ya ɗauko musu ruwa guda ɗaya bayan ya ɗauko wasu ƙananan kofuna guda biyu kai tsaye bisa kujeran dake fuskartar wacce Ishaq ya zauna shima ya zauna ya ajiye kofunan bisa teburin dake gabansa batare da yace komai ba ya tsiyayama Ishaq ya miƙa mai ya karɓa da murmushi kafin yace "Thanks."

Bai yi magana ba illah murmusawa kawai da yayi kafin shima ya tsiyayama kanshi ya kafa kai yana sha, dukkansu atare ko wannen su ya ajiye kofin ruwan kuma suka sakarma juna murmushi alokaci ɗaya, ajiyar zuciya Tahir ya sauke yana wani lumshe ido kansa ya jingina jikin kujera yana ƙara takure fuska kafin ya sanya hannu yana taɓa naman goshinsa daya tattare, Ishaq na lura dashi ganin yadda yake yamutsa fuskane yasa ya gane akwai matsala sosai.

Gyara zama yayi kafin yace "Uhm..Tahir meke damunka ne..? Tun shigowarka Company na lura baka cikin walwalarka..?" Bai ɗago ba illah sauke hannunshi dayayi yana ƙara lumshe dara daran idanuwansa har Ishaq ya fidda rai da zai yi magana sai chan yaji ya furta.."Kai ma da neman magana kake, a duk duniya ni Tahir ina da wata damuwa ne bayan damuwar Farida..? Bani da ita komai na duniyar nan na mallakeshi Ishaq sa'ar mace tagari ne kaɗai banyi ba, shi kaɗai ne matsalata a yanzu da damuwata Ishaq..wallahi halin Farida ya isheni, na kai maƙura..."

Ishaq ya saki ajiyar zuciya kafin yace "Nasani Tahir buh ya maganar da mukayi dakai last week da kaje Ɗanbatta baka ƙara ma Goggo Abu maganar auren naka bane..?" Sai lokacin Tahir ya miƙe daga kishingiɗan dayayi yana faɗin "Hmmm bari kawai Ishaq, narasa me Farida tama Goggo Abu da take gudun ɓacin ranta, amma ni take ƙoƙarin danne min hakki wallahi ko wannan zuwan taƙi kuma tace zata saɓamin in na sake na tunkari Hakimi da maganar, wai zata ƙara ma Farida magana in sunyi waya.." Tsaki Ishaq yaja kafin yace "Wallahi baji zatayi ba, ai da tana jin magana dataji tasu Alhaji, gaskiya in na samu lokaci zanje ƙauye nama Goggon bayanin za'a cutar dakai kuma Farida bata da asara." Murmushin dayafi kuka ciwo Tahir yayi kafin yace "Kadama ka wahalar da kanka Ishaq, domin Goggo bazata taɓa sauraranka ba daga ƙarshema zatace haɗa baki mukayi na turo mata kai. Kawai nidai yanzu na cire lamarin Farida araina ina ta addu'a amma tabbas Ishaq na kai maƙura nifa mutum ne mai lafiya ba dutse ba ina buƙatar macen da zan dinga samun natsuwa awajenta.." Saurarawa yayi yana maida numfashi cike da ɓacin rai kafin ya cigaba da faɗin "Ko bama haka ba Ishaq ina buƙatar macen da zata kula dani nima, taji dani nima ina so naga ana bani girma amatsayina na namiji, yanzu ka duba kagani Ishaq rainin da Farida tamin har yakai ta tafi tsawon kwana biyar bata agida, amma jiya data dawo basai ta nemeni ba..? Toh sai ma kallon rainin data bini dashi da ƙyar ta iya cemin ina kwana, fisabillahi wannan wace irin rayuwa ce? Duk haƙurinka sai an ƙureka.." Ya faɗa yana dafe kanshi. Ishaq dake kallonsa cike da tausayinshi tsam ya miƙe ya zagayo gabanshi yasaka hannu ya dafa kafaɗarsa yana faɗin "Is Ok...Ya isa haka Tahir maganar duk bashi da amafani tunda ba ji zatayi ba, ni narasa wane irin taurin kai ne Farida ke dashi ko Aliya fa tayi tayi da ita amma ƙarshenta ma yanzu sama sama take mata magana bazata chanza ba, haƙuri zaka ƙara da kuma tausan Goggo Abu har ta amince maka ka sanar da Hakimi kana buƙatar ƙara aure..."

Tahir baiyi magana ba illah sauke ƙananun ajiyar zuciya dayakeyi kafin ya miƙe yana sauke jannun Ishaq dake kafaɗars bai bari sun haɗa ido ba sai ma ƙoƙarin duba agogon hannunshi da yayi lokaci ɗaya yana faɗin "Ishaq zamu makara fa, muyi alwala mu isa masallaci.." Ya faɗa yana kama hanyar ficewa, ajiyar zuciya Ishaq ya sauke kafin yace "Ok..." Daidai lokacin da Tahir ya fice daga Office d'in shima bai zauna ba wayarsa ya ɗauka ya tura cikin aljihu yabi bayan Tahir ɗin da sassarfa.

Farida ko tun bayan fitansu take zaune a falo tana latse latsen waya, sai da ta gaji taga dama kana ta tashi ta nufi dining tayi breakfast ta gama kenan sai ga iya ta fito ɗauke da Naila wacce ta tashi daga barci Iya tayi mata wanka ta saka mata wata riga doguwa bulawus mai kyau rigima takeji don yau ko madarar nata data dama mata bata sha ba, shine ta fito da ita zuwa wajen Farida karɓan ta tayi ta cilla ta sama alamar wasa duk yadda Naila keson wasa yau bata nuna ba don kuka ta saka mata tana binta da kallo, Farida ta kyaɓe fuska tana faɗin "Meya sameta ne Iya..? Baki bata madararta bane..?"

Iya tace "Na bata ta ƙi karɓa Hajiya gwada bata nono ƙila shi takema kewa.." Dariya Farida tayi tana shafa kumatun Naila tace "Wannan babbar yarinyar? Ai tayi girma da shan nono, kinga ina ɗaukanta ina haki shiyasa nake jinjina ma Mufeeda don tana ƙoƙarin ɗaukan Naila, tunda naga tafi sabawa da madararta na yayeta domin bazan iya ma tuna rabon da na bata nono ba gaskiya.."

Iya tayi galala da baki kafin tace "Haba Hajiya Naila fa yarinyace ƙarama har yanzu ko shekara bata rufe ba fa.? Gaskiya bai kyautu ki yayeta tun yanzu ba, don Allah ki barta ko wata sha takwas tayi in bazaki barta ta cike biyu ba..." Tun kafin Iya ta ƙarasa Farida ke jifanta da wani banzan kallo batayi magana ba sai da ta miƙe ta miƙama Iya Naila kafin ta ɗauki wayarta tana fadin "Iya ki kama bakinki, ina ruwanki da hukuncin dana yanke? Ai nima nasan ciwon kaina ko..? So plz ki tsaya iya matsayinki bana so kina shiga hurumin da banaki ba.."

Iya ta rausayar da kai tana ƙara riƙe Naila dake rigima tace "Allah ya baki haƙuri Hajiya.." Bata bi ta kanta ba ta haura sama ta amsa kira, da kallon kaiconki Iya ta bita kafin ta kaɗa kai ta koma ɗakin Mufeeda da Naila da ƙyar ta lallasheta ta sha madararta kuma ma harda rigimar bata ga Mufeeda ba goyata tayi kafin ta fito falo ta fara tsabataceshi, bata gama ba Naila tayi barci sai ta maidata ɗaki ta kwantar ita kuma tazo ta cigaba da aikinta lokaci bayan lokaci tana leƙa Naila acikin ranta kuma tana fatan Allah ya kawoma Alhaji mafita amma tabbas baiyi dacen abokiyar arziki ta gari ba duk da ba Alhaji ya kawota gidan ba amma kuma kyawawan halayyarshi da kyautatarwarshi garesu yasa take ganin girmanshi da darajanshi kuma take zaune dasu da zuciya ɗaya.

******

*BAYAN KWANA UKU*

Duk tsawon wannan kwanakin zaman doya da manja ke gudana tsakanin ma'auratan, shi Tahir ya riga daya fita sha'anin Farida sam domin yana ganin yana gaba da ita amma baida daraja da arzikin da Farida zata nemeshi, shiyasa yayi burus da ita dagashi sai 'ya'yanshi suke harkar rayuwarsu ko alama bai sakama ranshi yana da wata mata agidan, toh itama Farida bata damu dashi ba, hakan da yayi ma yayi mata daÉ—i domin batason fitinar Tahir sam gani take da zarar ta nemeshi fitinarshi zata tashi shiyasa ta shareshi a zuwan in ya gaji zai nemeta lokacin ya huce sai su daidaita.
  
Kwana biyu ne da dawowarta bata fita ba saboda gajiyar dake jikinta, ranar data kwana uku bata wuni a gida ba, baima san ta fita ba, sai da ya dawo gidan wajen 6 na yamma Iya ke sanar dashi Farida bata gida ƙoƙarin ɓoye damuwarsa yayi amma na yau kam Farida takaishi bango sosai. Garzali yaje ɗauko su Basma daga Islamiya sama ya haura ɗauke da Naila wacce ya amsheta hannu Iya har ya shiga wanka ya fito zuciyarsa tafasa take, koda ya fito Naila tayi barci dama ita rigimarta kaɗan ce dan dataji taushi da iska sai barci yana ƙoƙarin zura jallabiyarsa ne yaji ƙarar buɗe gate alamun Garzali ya dawo daga ɗauko su Mufeeda, carbinsa ya ɗauka ya fito kansa na ɗigar da ruwa kaɗan, dasu ya cikaro duk suka gaisheshi ya amsa fuskarsa ba walwala kafin ya kalli Bassam yana faɗin "Oya shiga ka fito mu tafi Masjid.." Kada kai yayi kafin ya shiga ɗakinsa agurguje Bassam ya ɗauro alwala ya fito Tahir ya kama hannunshi suka fice zuwa masallacin dake kusa dasu yayinda Mufeeda da Basma kowacce tayi ɗakinta domin ɗaura alwala tunda wasu masallatan ma sun riga sun tada Sallarsu.

A Æ™a'idar Tahir baya baro masallaci sai an idar da sallar Isha'i yau ma É—in hakane ta kasance riÆ™e da hannun Bassam kamar koda yaushe suka shigo gidan megadi na musu barka da zuwa basu kai ga isa Æ™ofar da zata sadasu da babban falon gidan ba horn d'in motar Farida yayi musu maraba da hanzari megadi ya wangale mata gate ta sako hancin motarta cikin gidan, cak Tahir ya tsaya ya waigo yana kallonta tana Æ™oÆ™arin faka motar a parking spaces, ta cikin motar itama take kallonsa ganin yadda yake mata wani kallo ne yasa tasha jinin jikinta sosai tana Æ™oÆ™arin fitowa daga motar ne nepa suka É—auke wuta wajen yayi duhu shi ya taimaketa don Tahir hannun Bassam yasaki yace mai ya shiga cikin gida shi kuma ya nufi wajen Garzali yana sanar dashi ya duba Genaretor É—in Allah yasa akwai diseal, lokacin ne Farida ta samu sa'a tayi wuf ta fada cikin falon, yana ganin haka shima ya juya ya take mata baya tana Æ™oÆ™arin haura steps d'in benen ne taji kakkausar muryanshi yana faÉ—in 

  

  "Da zinin wa kika fita Farida....?" Muryansa cike da amon sauti mai cike da tsantsar É“acin rai, rass gabanta ya faÉ—i sai ta kasa juyowa don muryansa kaÉ—ai ta isa ta bayyana mata yau Tahir ya gama haÆ™uri da ita, bata samu zarafin juyowa ba ya sake daka mata wata uwar tsawar data gigita ta, bama ita kaÉ—ai ba hatta su Basma da Bassam da Mufeeda da Iya dake É—akunansu sai da suka firgita suka fito falon da sauri daidai lokacin da aka kunna Genaretor haske ya gauaraye ko'ina.

"Nace da izinin wa kika fita Farida...? Saboda raini kina jina ina magana kina min banza..?" Ya faɗa yana tattare naman goshinsa saboda fushi, Farida ta juyo a hankali tana kallonshi tana kuma ƙoƙarin ɓoye razanarta haɗe fuska tayi kafin tace "Dama na saba tambayar izininka ne idan zan fita...? Na ɗauka nida kai mun wuce wannan ƙarnin..." Ta faɗa tana kaɗa key ɗin motar dake hannunta ba tare data jira komai ba ta kaɗa kai ta juya ta cigaba da taka steps d'in cikin halin ko in kula wani ɓacin rai mai zafi ya ziyarci zuciyar Tahir ko gani bayayi yayi kukan kura ya bi bayanta a harzuƙe kafin ma ta ankara ya cimmata sai ji tayi ya jawota baya da sauri ƙiiiiii.....kamar wata kayan wanki, bai direta ko'ina ba sai tsakiyar falon bayan ya ingizata baya tayi taga taga zata faɗi, ba domin Allah ya taimaketa ta daddage ta riƙe kujeran dake falon ba da sai ta faɗi ƙasa..

Cike da mamaki take binsa da kallo kafin ta buɗe baki tace "Tahir...Lafiyanka ƙalau kuwa..? Ta faɗa tana binsa da kallo ganin yanda yake huci bai bata amsa ba illah cewar daya ƙarayi "Nace da izinin ubanwa kika fita Farida...?" Baki buɗe take kallonshi kamar yadda Basma da Bassam suka zura musu ido, cike da wani yanayi hakama Mufeeda, Iya ce dake tsaye ranta duk ba daɗi tunda suke da Alhaji basu taɓa ganinshi cikin fushi hakaba tana ƙoƙarin isa gareshi Farida tace "Kace da izinin ubanwa na fita ko..? Toh da izinin ubana ko..." Ai bata ƙarasa ba taji Tas! Tas! Maruka biyu kyawawa Tahir ya wanke fuskar Farida dama da hauni lokaci ɗaya, kamar walƙiya taji marukan saboda azaba sai gata zaune daɓas da ɗuwawunta akasan cafet ɗin falon hannayenta dafe da kuncinta tana bin Tahir da kallo hawayenta na sauka kamar an buɗe famfo.

Ba Farida kaɗai ba hatta Basma da Bassam saboda razana sai da ya ƙanƙame Basma suna rawar jiki a tare lokaci ɗaya suka fashe da kuka, hakama Mufeeda da ta maƙale jikin ƙofa tana rawar jiki, Iya ko ƙirji ta dafe tana faɗin "Innalillahi Wa'inna Ilaihirraju'un...Alhaji mezan gani jaka..? Ashsha abu baiyi daɗi ba.." Ta fada cike da damuwa.

Ko sauraranta baiyi ba ya kalli Farida yana nuna ta da yatsa kafin ya fara faɗin "Wannan ne na farko kuma na ƙarshe... wallahi in kika ƙara fita bada izina na ba Farida daga ranar zaki tabbatar da babu wani amfanin da kike dashi a cikin rayuwar Tahir..." Ya faɗa cikin kakkausar murya, kuka Farida ta fashe dashi bilhaƙƙi da gaskiya kafin ta miƙe cikin kuka tana faɗin "And So What...Nima ai baka da wani amfani a wajena, waye kai awajen Farida? Ka sakeni in ka isa tunda bani da amfani juz Tahir ka sakeni ka gani in rayuwata zata yanke ko ta wulaƙanta daga yau ka sakeni don Allah..." Ta faɗa tana hargowa cikin kuka.

Basma ce ta saki ihu tana faɗin "No..Momy Daddy Stop plz..." Ta faɗa tana duƙawa haka shima Bassam yayi suna kuka suna faɗin "Plz Daddy Momy don Allah ku bari kuna sakamu muna jin ba daɗi..." Suna faɗa suna kuka, Mufeeda ma kukan take, da kallo Tahir ya bisu lokaci ɗaya kuma sai jikinsa yayi sanyi sosai idanuwansa sunyi jawur kai kawai ya kaɗa kafin ya wucesu da sauri ya haura sama cikin sassarfa, ganin haka yasa Farida tabi bayanshi da sauri tana kuka sai dai kafin ta ƙarasa ya shige bedroom ɗinsa ya banko ƙofa a ƙofar ɗakin ta tsaya tana kuka tana faɗin "In ya isa ya fito ya saketa dama ita tagaji da aurensa..." yana jinta ya mata banza kan gadonsa ya hau ya saka kanshi cikin gwiwoyinsa yana ƙoƙarin daidaita numfashinsa.

Basma da Bassam ko kuka suke sosai na ganin abunda ke faruwa tsakanin iyayensu wanda basu taÉ“a gani ba da Æ™yar Iya ta lallashesu kowanne ya nufi É—akinsa cikin damuwa, haka ma Mufeeda ta koma É—akinta ta faÉ—a bisa gado tana kuka, wanda tarasa dalilinshi, ranar dai gaba É—aya gidan ba wanda ya yi dinner haka kuma barci sai dai sama sama, daga Tahir É—in har Farida barci É“arawo ne ya É—aukesu balle su Basma da suka tashi fuskokinsu duk a kumbure saboda kuka. 


*HIJABS CORNER BY JANAFTY*

*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, É—inki cikin kwarewa da* *mabambanta design,  muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan É—aya ko sari.*
****, tuntuɓa ta wannan lambar*
*KADUNA/ZARIA*


*Janafty..*
*Aisha Alto.*