GADAR TSAUTSAYI

GADAR TSAUTSAYI 36

by @nusybee143

Page 36



Wani banzan kallo Shaheeda take aika masa daga inda take zaune, fuska a ɗaure, cikin fusata ta fara magana 

"A harkar business ka gan ni,ka yi business da ni,idan da ace zan yi karuwanci ba sai ka gaya min ko ka yaudare ni da wasu ƴan kuɗin ka ba,idan kuɗi ne ko ban siyar da ƙwaya ba ina da hanyar samunsu,don haka hattara!

Ka yi abin da ya kawo ka kawai,kaya ne kake so,idan ka shirya a shigo maka ko a fitar maka da kaya,idan ka kashe waccan mummunar aƙidar taka to Shaheeda tana maraba da kai"ta miƙe a fusace zata fita 

"A haba kyakykyawa!haba kyakykyawa!ya da haka ne?

Don Allah ki yi haƙuri,na rusa waccan maganar, na ɗauka ke ma ƴar hannu ce,amma yanzu na gane,zauna mu yi magana"tana daga tsaye ta ce"yi maganarka ina jin ka"ya marairaice ya ce"don Allah ki yi haƙuri ki zauna"babu musu ta zauna tana aika masa da wani mugun kallo 

Yana murmushi ya ce"haba kyakykyawa!don Allah ki saki fuskarki, wallahi ba kya yin kyau a haka,haba kyakykyawa "ɗan sakin fuskar ta yi,amma bata yi murmushi ba,ta sake faɗin"yi bayani,ina jin ka"babu musu ya fara bayani 

"Akwai kayana a Columbia,ina so su shigo Nigeria,kuma ke nake so ki shigo min da su, don Allah bana son a samu matsala "

Babu bata lokaci ta ce"consider it done in sha Allah, menene ƙimar kayan?

Kuma menene kasona na abin da zan samu?"

Alhaji ya ce"kayan sun kai ƙimar dala million hamsin,kuma kina da 5%"yatsina fuska ta yi tana yi masa kallon hadarin kaji,ta ce"albarka!"

"To kashi goma idan kin amince "miƙewa ta yi tsaye ta ce"idan ka shirya biyan kaso ashirin da biyar sai ka yi min magana "ta kama hanya don ficewa daga parlourn 

"A haba yarinya ki duba mana!

Kashi ashirin da biyar ai da yawa fa,ribar me zan samu kenan?"juyowa ta yi tana kallonsa ta ce"Ni baka duba tsananin kasadar da zan ɗauka ba?

Sai kai akan kuɗinka?to yadda kake son kuɗi haka na fito neman kuɗi,ya rage naka ka saki kuɗi ka samu kuɗi,ko ka riƙe kuɗi ka huta"ta juya hankali kwance zata fice daga parlourn 

"Na yarda,na yarda,haba ranki ya daɗe"babu ɓata lokaci ta juyo ta samu waje ta zauna tana fuskantar shi 

Da kanshi ya tsara mata yadda abubuwa za su tafi,kuma bata tafi ba sai da ya tura mata Miliyan ashirin na cin chewing gum

Bayan ta koma gida ta sanar da su Oga boss yadda suka yi,sun yi farin ciki sosai, Oga boss ya sake jaddada mata cewa ta kula, saboda irin su ba su da tabbas 

Alhaji Sa'idu wada da kanshi ya haɗa ta da mutanen da za su taimake ta,wasu daga cikinsu yan sanda ne,har ma da ma'aikatan hukumar DSS,daga kan state directors zuwa kan masu muƙamai, ba'a maganar ma'aikatan customs da immigration wadanda suka zama sune manyan yaranta wajen shigar da kayan

Cikin nasara kuma ba tare da ɓata lokaci na ta fara aiwatar da aikinta,sai dai kamar yadda Oga boss ya bata shawara ta sauya sunanta daga Fatima zuwa ROXY 

Banda waɗanda suka santa a baya,da waɗanda suke jikinta babu wanda ya san asalin sunanta,a tsawon shekara ɗaya da fara wannan sana'ar tata ta hadu da mutane da yawa,ciki har da babban yaronta David, wanda yake taimaka mata a kasuwancin nata

Ta koyi dabaru kala-kala na rayuwa da gujewa jami'an tsaro,bayan ta tabbatar ta tsaya da ƙafafunta har gida ta je ta sanar da Alhaji Sa'idu wada cewa ta gama yi masa aiki,itama yanzu ta kama gashin kanta 

Duk yadda ya so ta koma ta cigaba da yi masa aiki ta ƙi,hakan ya fusata Alhaji Sa'idu, babu ɓata lokaci ya bayar da hotonta a kama masa ita,don a lokacin ya kasa tantance wanne suna ne asalin sunanta 

Ɗaya daga cikin jami'ai, wanda ya kasance ita yake yiwa aiki ne ya kira ta ya sanar da ita,hakan ya sa ta yi murmushi,kuma ta ƙudurce a ranta dole ne ta sake shiri 

Shirin farko da ta fara yi shine gayawa duniya da take yi a sirrance cewa babu mai iya kama ta, saboda ta yi dukkan wasu dabaru don gujewa hakan,ta fara amfani da harufan NOCCM, waɗanda babu wani abu da suke nufi sai NO ONE CAN CATCH ME,kuma ta yi farin ciki ganin jami'an tsaro sun mayar da hankali don gane abin da haruffan suke nufi,ita kuma ta mayar da hankali don abin da yake gabanta

Daga nan barin ƙasar ta yi,ta koma Spain, inda ta cigaba da sana'arta cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba

Sai da ta shirya cif sannan ta dawo Nigeria,ta saka idanu sosai akan dukkan wani jami'in tsaro da zai fara bincikarta,daga an fara bincikarta zata saka a bincika mata wanene jami'in,zata shiga rayuwarsa ta yi masa barazana,da haka zai yar da case ɗin saboda tsoron abin da zai faru gare shi ko ga iyalinsa 

A ɗaya ɓangaren kuwa bata fasa saka idanu ga ɗanta ɗaya tilo ba,kuma bata fasa zuwa wajen kantamemen gate ɗin MALIYA ESTATE ba,wani lokacin idan ta ga fitowar Abba ko Ummeenta tana yin kuka sosai, tana tsananin son su,amma yanzu sun yi mata nisa 

Amma har zuwa yanzu zuciyarta baya karaya ba,kuma duk yadda take jin damuwa bata taɓa barin wani ya sani ko ya gane,ta cinye abarta ita kaɗai,sai idan abu ya dame ta ta sha kwayoyinta ta yi bacci 

Da haka CSO HAISAM ABDULMALIK MADAKA jami'in tsaro na hukumar DSS ya shiga rayuwarta ya fara farautarta,da farko bata ɗauki case ɗin sa da zafi ba,ta ɗauka shi ɗin gama garin jami'i ne kamar sauran jami'an tsaron da suke farautarta,sai da ta yi kyakkyawan bincike akansa ta gane yadda take hatsabibiya haka yake da hatsabibanci,har ma ya fi ta, hankalinta ya tashi,ta yi dukkan mai yiwuwa don ta guje masa,ta yi masa barazana da iyalinsa,ta yi masa da ranshi amma duka a banza,a ƙarshe sai da ya san yadda zai yi ya ga bayan aikinta da ta gina tsawon shekaru uku 

Wannan shine labarin FATIMA SHAHEEDA, wadda a yanzu take amsa sunan ROXY saboda yanayin aikinta ko sana'arta, abubuwan da suka faru da ita har ta tsinci kanta a cikin wannan halin 




💫


Shiru ya biyo baya na yan sakwanni,kan Haisam a ƙasa,gaba ɗaya jikinsa a mace, kafin a hankali ya ɗaga kai ya kalle ta,sassanyan murmushi ta sakar masa,ya ɗaga gira alamar ya dai?ta girgiza kai ba tare da ta yi magana ba,sun ƙara jan wasu seconds ɗin kafin ya ce"na san lokacin da na je kama ki a Spain akwai wanda ya sanar da ke batun tafiyar a tawagata, wanda shine yake ba ki bayanai akaina da yunƙurina,shin za ki iya gaya min wanene shi?"

Sauke numfashi ta yi tana kawar da kai gefe, kafin ta ce"I'm sorry to say,ba zan iya gaya maka sunansa ba, saboda bana son ya rasa aikinsa,idan haka ta faru kuma ban san wanne irin criminal gobe zata haifar ba,ka bar shi a yadda yake,duk bala'i bai isa ya fito ya yiwa ƙasa zagon ƙasa Kamar yadda na yi ba"

Haisam ya ce"babu abin da zai samu aikinsa,asalima manya ba za su ji ba, maganar tsakanin ni da shi ne kawai"

Shiru ta yi tana kallonshi,ya yi murmushi ya ce"nima ba ki yarda da ni ba ko?"girgiza kai ta yi ta ce"A'a, kawai ina so na tabbatar da gaskiyarka ne, kamar yadda na faɗa maka bana fatan wani ya rasa aikinsa ta dalilina

Amma zan gaya maka,ba kowa bane sai abokin aikinka Awwal!

Ya daɗe yana yi min aiki,in fact,yana daga cikin yaran da state director na Kano State ya saka don su rinƙa taimakona "

A razane Haisam yake kallonta, kafin da ƙyar ya furta"You mean? State director da haɗin bakinsa a wannan badaƙalar?"

Jinjina kai ta yi, sannan ta ce"akwai bakinsa, amma shima Alhaji Sa'idu wada yake yiwa aiki,kuma bijirewar da na yiwa Alhaji Sa'idu ita ce ta janyo ya kware min baya ya fara farautata"

Haisam ya jinjina kai ya ce "Wanene ya ba ki dabarun gujewa jami'an tsaro?"

Gyara zama ta yi tana ɗauke kanta,ta sauke numfashi ta ce"a duk lokacin da mutum yake ji ba zai iya aikata wani abu ba to bai same shi ba, ballantana ni da duk lokacin da na saka a raina zan yi abu to sai na yi shi

Kar ka manta nice na rainawa iyayena hankali,na auri wani ba tare da saninsu ba,na bi shi muka bar ƙasar baki ɗaya ba su sani ba,har yanzu a makaranta mataki na biyu nake,amma na yi abin da dubban masu Masters ba su yi ba da nasu,a taƙaice dai,duk wani abu da mutum ya saka kanshi to tabbas sai ya iya

Ni yanzu na san na gama tunda kuka kawo ni nan,mafi ƙarancin abin da zan iya fuskanta a kotu shine hukuncin ɗaurin rai da rai, saboda na san laifina babban laifi ne,abu ɗaya ne damuwata a rayuwa,shine ɗana mubarak"ta ɗago duk da babu alamun damuwa a fuskarta,amma ya gani a cikin idanunta,ta ce"a karo na biyu ina sake roƙonka,a wanne hali Mubarak yake ciki?

Kar ka manta na haife shi a maraya, wanda yake cikin ganiyar rashin gata,nima na yi masa laifi, saboda zaɓar duniya na watsar da shi na kama rayuwata,bai san daɗin iyayensa ba,bai san wani daɗi na rayuwa ba, musamman duba ga inda ya taso 

Zan so a ce nan gaba ya samu farin ciki kamar kowa,ya samu ingantacciyar rayuwa, sannan kuma ya yi min addu'a "

Haisam ya yi murmushi ya ce"a matsayinki na wa zai yi miki addu'a?"

Ta kalle shi sosai tana ɗan murmushi ta ce"a ƙalla in samu darajar ɗaukar ciki da haihuwa mana officer "

Yana kallonta ya ce"ke mahaifiyarsa ce tabbas,ban isa na ce ba kya son shi ba, saboda na san ƙarya nake yi,amma meyasa za ki watsar da rayuwar tilon ɗanki ki kama rayuwar da kike so?

Na san dai babu jin haushin mahaifinsa a tare da ke, musamman da kika fuskanci laifinki ne "

Girgiza kai ta yi,ta ce"na kasa jurar hakan ne,matsayin Mubarak na ɗan Arnold, kamar yadda na gaya maka a baya idan na kalle shi ina tuna cewa Arnold ya yaudare ni,na aure shi na rabu da iyayena,amma shi ya watsa min ƙasa a idanu,ya tozarta ni,a ƙarshe a dalilin sa na shiga wannan rayuwar da nake ciki

Larurar Mubarak da ya gado daga wajen dangin babansa ta sake dasa min wani ciwo,hakan ya sa na zaɓi na nisance shi, gudun kar na illata shi akan laifin da ba nashi ba,kar na zalunce shi "

Haisam ya ce"ai kin gama zaluntar shi Shaheeda!

Tunda kika kasa zaɓa masa uba na gari, gashi a ƙarshe rayuwarsa ta koma wani sashen dabam na wahalhalu, meyasa kika yi hakan?"

"Wannan ƙaddarata ce da ban isa na tsallake ta ba a rayuwa,da a ce kowanne bawa shine yake tsarawa kanshi rayuwa da na tsarawa kaina yan'uwa daga mahaifiyata, waɗanda za su damu da ni ko da a ce ita mahaifiyar tawa bata kula ni ba,da ban tsarawa kaina soyayya irin wadda zata makantar da ni daga hangen abin da zai je ya dawo ba,da ban tsarawa kaina lalacewar rayuwata saboda abin duniya ba


A tsawon shekaru uku da na kasance a wannan halin sam bana cikin farin ciki,ko babu komai tsinuwar al'umma aba ce mai tasiri ga rayuwar mutum"ta ɗaga kai tana kallonsa, kafin ta ce"Ni yanzu abu ɗaya nake fata idan zai samu,a yanke min hukuncin kisa kawai,ina fatan hakan ya zama kaffarata "kukan da take riƙe da shi ya kubce mata

Miƙewa ya yi cikin jarumta jin zata karya masa zuciya,ya fara magana cikin kwantar da murya"ranar Monday za'a shiga da ke court,gobe idan Allah ya kai mu za mu zo da lawyer ɗin ki,in sha Allah komai zai zo da sauƙi,ina fatan don Allah kar ki yi mata taurin kai "a hankali ta jinjina kai, kafin ta ce"na yi maka wata tambaya amma har yanzu ba ka ba ni amsar da ta gamsar da ni ba

A karo na biyu ina roƙon ka ba ni amsa don Allah "

Kallonta yake yi ya ce"wacce tambaya ce?"

Sauke numfashi ta yi,ta ce"ɗana Mubarak,yana ina?

Sannan kuma a wanne hali yake ciki don Allah?"






#Nusy_bee