10
Chapter.10
Ta bude murfin mota za ta shiga kenan ta ji muryar Sahle da mechanic da suka zo tare, saboda dad'in ganin sa da ta yi har bata san sanda ta sauke wani gauran numfashi ba ta ce.
"Haba dai Sahle wannan dadewa haka wallahi har ka sa na soma tsorota na ce kodai wani abun ne ya same ka na ji shiru kai da ka ce nan da minti talatin za ka dawo." "Tuba na ke ranki ya dad'e mai gyaran ne babu a kusa, sai da na kira wannnan da ke duba motocin Alhaji ya zo, dalilin dad'ewar tawa kenan sai da na jira ya zo ya same ni muka zo." Fad'in Sahle tare da bud'e gaban motar machanic ya soma duba ta, nan da nan sai ya shawo matsalar motar ta tashi.
Sun yi sallama da shi a kan zai zo har gida ya amshi kudinsa, Sahle ya juya ga Nazli dake tsaye a waje ya ce. "Yanzu sai ina ranki ya dade?." A takaici ta ce. "Gida." Dan ta gaji da wannan walagigin nan na su da babu matsaya gwara ta koma can gida sai dai daddy ya kashe ta amma ba abun da zai sake fidda ita daga gidan Allah.
Suna cikin tafiya ta kasa hakuri ta ce. "Sahla ko za ka nema min abinci yunwa na ke ji." Ta gaban mirror ya dube ta ya ce. "Abinci?" Ai ina ga mun wuce restaurants a baya da kin yi magana tun dazu nan duk abincin ya ku bayi ne irin mu ba lallai ki iya celi ba, idan ki ka k'ara hakuri ma yanzu zamu isa gida ai."
"Ni dai a'a, kawai ka tsaida motar ka nema min abin da zan ci. Wanda ma ka ga yana zab'e ai wuri ya samu, yadda na ke jin kaina ba zan kai ba nan wallahi ko dusa ka saka min tsaf sai na tashe ta." Maganar ta ta so bashi dare amma sai ya maze ya ce.
"To me kike so wani irin abinci kike buk'ata?" Ya fad'a dai dai yana samun wuri a ta gefen titi ya yi parking yana mai jiran amsar ta.
"Ka ga can?" Ta ce tare da nuna masa saitin wata mata da ke suya a ta tsallake, ta d'aura. "Ban san ko me take dafawa ba amma na ji ina son ci ko menene." Juyawa ya yi ya kalleta da mamaki. "Amma da kin hakura minti 20 ma zai kai mu gida idan muka kara gudu."
Ta had'a fuska, da muryar da babu wasa ta ce. "Za ka siyan ne ko ko a'a?" Da sauri ya girgiza kai ya ce ki yi hakuri Allah ya huci zuciyar ki, yanzu kuwa za a kawo." Daga haka ya bud'e motar ya fita, inda ya barta a ciki tana kallon yadda mutane suka ma matar runfa kowa na jiran a saka masa na sa ya kama gabansa, abun da ya kwadaitar da ita kenan ta ji tana son ta d'and'ani koda me ne, dama ita Allah bai yi ta rena mutane bari abun hannunsu dan haka bata laifin cin abinci iri haka, a ganin ta abinci abinci ne da na mu da na su duka daya duk suna daya suke amsa wato abinci.
Ringing d'in wayarta da ta ji ne ya dawo da ita duniyar mu, a hankali ta jawo handbag na ta tana cikin k'ok'arin fidda wayar jakar ta fad'i sanadiyyar zubewar tarkacen da ke ciki. Ko kafin ta tattara ta yi picking wayar ta tsinke hakan ya sa ta maida ita cikin jaka ba tare da ta ga me k'iran ba, har ta zo zuge Zib ta hangi wannan bracelet na d'azu.
K'ura ma bracelet din ido ta yi emotion kala kala suke tashar mata, tun bata ga fuskarsa ba ta soma Jin tsanarta har kokon ranta dan komai da ke faruwa da ita a yanzu duk shi ne sila, ya raba ta mutuncinta, budurincin da ko shi wanda ke da iko kansa bai taba ba, ya raba ta iyayen ta ya raba ta da mijinta. Ya raba ta dukkan wani farin ciki na rayuwa, ya mata mummunan tabon da har ta mutu ba zai taba goguwa, ya bata mata suna. Komai shi ne, ita ko ya za ta taba yafe masa? Har abada ba za ta taba yafe masa ba, yadda ya jefa rayuwarta cikin tsaka me wuya sai ta masa ninkin banin nikin sa.
Sai dai fa duk wannan bai hana ta daure bracelet din cikin hanunta ta juya hannun bata san sanda murmushi ya subuce mata ba ganin yadda abun ya yi kyau a hannunta. "Who are you?" Ta furta kasa kasa. "Ka guji haduwa ta da kai dan sai ka yi dana sanin aikata min abin da ka yi, you will pay this, a heavy price at that." kiran da ya sake shiga wayarta ne ya sa ta jan karamin tsaki tana tunanin me kiran.
"Mom." Ta furta a kasalance. "Ohh! daughter kina ina ne haka gaba daya kin sa hankalina tashi tun dazu na ke faman kiran ki amma b ki yi picking ba, kodai da matsala ne ina ita Elherm din ki bani mu yi magana i need to know abin da ke faruwa. just tell me dear if you're not comfortable I can just....
"Mommyy! Ta ja sunan a gajiye jin sai rattabo da zance take ba gajiyawa, cikin rashin dadi Mom ta ce. "Sorry darling, am just worried sick about you dear ba burina na dame ki bane." Cikin sanyaye murya Nazli ta ce. "No ba haka bane, kawai am not well kaina na ciwo, beside bana wurin Elharm mun je bamu same su ba yanzu haka muna hanyar dawowa gida."
Ai ba shiri Mom ta mik'e tsaye daga zaunen da take idanunta a tsai tsai ta ce. "Wani gidan kuma kike shirin zuwa eyeh!?" Ba dai Nan gida ba." Ta fad'a cikin fitar hayyaci don Nazli ta kusa kunce mata lissafi da maganar dawowarta, zungurin da Neesah ta yi mata kafa ya sanya ta gane irin girman k'atobarar da ta yi.
Sai dai kancewar makiri ce wurin makirici sai yi saurin gyara kalamanta da fadin. "No dear, gidan babu dad'i ko kin dawo b'acen rai za ki tarar, Daddy ku har yanzu ya na dokin fushi bai sauko ba kin ga ma dawowa ta kenan daga dakinsa ammaba ki ji yadda muka yi ba abun dai babu dadin ji, karshi na fita da bacin rai. Zan juri komai amma banda ganin ki cikin damuwa Baby, wanda ke kanki ma ya ishe ki kar ki daurawa kanki ciwo da kananun shekarun ki, kaddara dai ta riga fata sai dai mu yi kokarin gyara gaba." Ta juya wayar kasa kasa take dura mata ashar tana fadin. 'Shegiya uwar na ci da jaraba.'
"Kina jina baby?" Yanzu dan kara hakuri mu basa space na dan lokaci zai sauko amma yanzu ganin ki zai fama masa da ciwo ya tuna abun da ya faru dan haka mu bashi sati haka sai ki dawo na san zuwa than ya sauko.
Nazli
Shiru Nazli ta yi tana sauraron ta cikin sanyi jiki, gaba d'aya jikinta ya sake yin La'asar da lamarin, sai ga sharr ta soma hawaye a hankali ta sa hannu ta goge fuskarta ta. "To Mom ina kuma kike son na tafi idan ban dawo gida ba ina da wani wuri da ya wuce nan din ne?" Sai dai na dawo ya sake korata amma ba inda zani idan bai son ganina ne sai ya maida ni Algeria kawai."
Wani bugu gaban Mom ya yi, ji wata magana, yarinyar nan dai ta zamar dashi burin ta kawai na ganin ta jagule mata lissafi. Ita da ke son ganin bayan ta take son raba ta da mijinta shine take wani kawo mata wani maganar Algeria? wannan shegun mutanen da da kyar ta iya jajib'eta daga k'asan su shi ne yanzu take ik'irarin komawa can? Anyi ba'a yi ba kenan ai, ina da alama sai ta tashi tsaye yau idan aikin da ta yi shekara da shekaru tana kinsib'awa ya warware a ita ce da hasara. Da kyar dai ta danne zuciyarta da ke faman tafarfasa ta ce.
"Hmm to yanzu kuna ina a daidai ina ne na zo na same ki?" Ta tambaya, d'aga kai Nazli ta yi ta kalli wurin da suke sai dai bata gane ina suke ba. Hakan ya sa ta bud'e baki da nufin cewa bata sani ba sai ga Sahle da Leda biyu a hannu ya shigo ya mika mata. A hanakli ta cire wayar daga kunnenta ta ce. "Wai a wace unguwa muke dai dai ina?" Ya fad'a mata zuciya d'aya ta sanar da Mom. "Okay daughter don't worry gani nan zuwa ki jira ni kin ji ko." "No, ki yi zaman ki Mom ba sai kin wahalar da kanki ba nan da 30 minutes zamu shigo."
Hararan wayar Mom ta yi bayan ta sauke. "Shegiya tsinanniya kawai, a zaton ki zuwa zan yi na same ki?" Hmm kina wasa yarinya." Ta yi saurin dealing number Goje da shi ya sanar da ita zuwan su gidan Elharm ba su tadda kowa ba sai mai gadi. Abun da ya sa ta k'ira Nazli kenan don son sanin inda take tunda bata can, a da ta hakura da kudirin ta a yanzu saboda wani dalili na ta, amma bayan maganar da suka yi a yanzu bata tunanin za ta sake b'ata lokaci ba tare da ta kawo k'arshen matsalar ba dan ta lura idan ta ce ta za ta yi sanya to kuwa shegiyar yarinyar nan mai kama da aljanu za ta kawo k'arshen wasan ta gashi tun ba'a je ko ina ba take son ruguje mata ginin da ta dade take ginawa.
~~~~~~~~
Nazli ta kalli Shale da ke miko mata leda ta karba tare da yi masa godiya, kana ta bud'e ta tsakura ta fara ci kamar bata so, gaba daya ranta a jagule ga wata sabuwar faduwar gaba da ta ke tun dazu.
Tana cikin tsaka da warwara har bata sand Sahle ya fita ya daura alwala ya shiga masallacin da ke wurina.
Ta tsoma hannunta daga abincin ta daure ta aje waje guda, ta sauke glass d'in motar ta yi can ta hangosa cikin jim'i suna sallar magrib.
Gyara zamanta ta yi cikin motar ta bud'e ruwan gora da ya hado mata ta sha kana ta yi zaman jiransa, ta nan ya dawo ya tada motar, babu Wanda ya ce da kowa komai suka soma tafiya.
A kuma lokacin a ka barke da ruwa mai k'arfin gaske, suna tafiya har sun d'an yi nisa suka hau titi da babu mutane illa tsurarin motoci da ke wucewa.
ji kake tass? Sai kuma siii tayar motar ta fashe, a tare suka furta subhanal Allah." Ba shiri ya tsaida motar, kana cikin ruwan nan ya fito domin duba tyre motar ba zato ko tsammani ya ji an saita masa wuka a dai dai cikinsa, kana cikin bada umarni a ka ce. "Tashi!, tashi dan iska." Cikin tsoro ya ce. "M..me ..me kuke so?"
Saboda a tunanin sa ba zai wuce yan daban yaran nan da ke fitowa cikin dare su tsaida motoci suna fashi ba, sai dai ga mamakinsa an ce. "Bude motar." Cikin taurin kai irin na sa ya ce. "ba zan bud'e ba, ku fad'i abun da kuke buk'ata." Bai yi aune ba ya ji an dungure masa kya tare da sakar masa wata azababbiyar rankwashi a kai tare da saita da bindiga. "Za ka yi abun da muka saka ka ne ko za ka tsaya yin ja yayya?"
Wani daga cikin y'an fashin ne wanda suke ce masa Habu ya matsa kusa da motar ya sunkuya ya leka cikin motar kana ya d'ago ya ce. "Ke fito nan?"
Ai ba shiri Nazli da ko ina na jikinta sai rawa ya ke ba abun da take sai salati ta bud'e murfin motar jiki na rawa ta fita kamar dama umarnin su take jira. Shale da har yanzu ba'a d'aga masa wuka daga ciki bane ya kalle ta cikin tausayawa kamar ya ce ta koma amma babu hali, dan wadan nan mutane daga gani babu tsoron Allah a zukatan su yanzu in ya ce zai yi gardama da su to ko second d'aya ba zai dauke su su aika sa lahira dan ya lura ba su da imani.
Wani irin karkarcewa Habu ya yi ya kunna tourch din hannumsa ya hasken Nazli tare da mai k'are mata kallo, d'an gaba ya yi kamar zai rumgume ta cikin layi irin na su na y'an maye ya ce. "Ehh yaah ne, Oga kai ka ga wata Haja a nan yaushe a ka bar matan hurul'aini suna fita ne?" Wannan kai kana gani ka san satar hanya ta yi ta fito amma ba yadda za'a yi a ce akwai masu kyau irin haka wannan ko India albarka." Sai kuma ya yi baya luu ya dawo gaba. "Shi kenan na yi mata, Allah ne ya dubi zuciyar Mamanmu da irin addu'ar ta gare ni kan shirye ni ya bani mata ya gari ta gyara ni." Tsake Goje ya yi ya ce. "matsala ta da kai mayen mata ne wallahi baka. gani ka kylae,to ba dai wannan ba kwalelenka don ta fi karfin ka kuma ba abin da ya kawo mu ba kenan."
Wize ya d'aura da. "Aiko dan dole ma ya had'e maitarsa, don wannan tafi karfinka idan ma ba tsautsaye ba kai ka isa ma ka hada hanya da kalan wannan?" Kar ka tsaya a iya matsayin ka."
Wani kallo Habu ya yi masa ya ce. "Ai ba tun yau na san kai d'an bak'in ciki ne wallahi , Allah ne ya kawo lokacin shiriye ta ya kawo min mata, ashe fa shi ya sa duk matan da Babar mu ta kawo min na guduwa ashe hurul'aini na hanya ba za su iya kishi da ita ba, to daga yau na shiryu sunana ya tashi daga Dan jagaliya ya koma Malam abubakar."
Ya fad'a hakan tare da yo kan Nazli gadan gadan zai rumgumeta ta yi saurin ja da baya cikin tsoro.
Babban cikin su wato Goje ya ce. "Kai dan kaza kazan Baban ka wa kake jira ya gyara tyer motar?" Ya fad'a tare da sakar ma Shale driver wani rankwashin a ka, ganin ya ki motsawa daga inda yake ne ya saka shi saka masa k'afa ya kayar da shi k'asa, daga nan suka had'e masa sai jibgar sa suke kamar sun samu kayan wanke, a hankali Nazli ta soma ja da baya ganin hankulan su baya kanta ya sa ta juya ta arce a nakare. Juyowar da Habu zai yi ya ga wayam babu hurul'aini dinsa, ai da k'arfi ya saka ihu ya tare da mara mata baya abin da ya jawo hankalin wizi da Goje kansa, shi ma wizi bai tsaya b'ata lokaci ba ya mara masu baya inda Goje ke fadin. "Kar ku bari ta tsare maku wallahi idan ba haka to dukkan mu sunan mu matattu."
ya kalli driver ya basa kutufa a ciki kana ya jawo sa kamar kayan wanke ya saka sa dan dole ya canza tyer motar.
Kasancewar dare ne kuma har zuwa lokacin ba'a dena ruwan sama ba, sai ya kasance ba su wani sha wahala wajen cabketa ba, saboda Nazli gudun take kamar bata yi abun ka ga wanda bai sama ba, balle su katte gudu ba wani abu bane a wajen su.
Ganin fizge fisgen da take ya sa wizi d'auke ta da wasu zafafan marukan ya na fadin. "Ai yau yadda kika sa mu gudu nan babu shiri sai kin yabawa aya zakinta." Nan ya kuma sake dauke ta da wasu marukan da suka sa ta gigicewa, ganin za ta ba su wahala ya sabata a kafada suka dawo. Bai yi wata wata ba ya wulla ta cikin motar ya rufe, kana sauran ma suka shiga, bayan dukan da suka ma Sahle suka barsa nan yashe a k'asa suka bar wajen da Nazli a mortar.
Sai fisge fisge take tana yakushinsu sai k'ok'arin bud'e murfin motar take, da k'arfi Wizi da dama shi babu wasa cikin lamarin sa ya daure mata hannaye tare da rufe mata baki da kyalle. Direct hanyar fita daga gari suka nufa, sun yi tafiya mai tsawu kafin suka tsaya a wani wuri da yake kamar dokar daji, babu kowa a wajen sai kukun tsuntsaye da kwadi dake tashi.
Gaba d'aya suka sauk'a suka bar illa Nazli cikin motar. "Yanzu ya za'a yi da ita ne Boss?" Habu ya yi tambayar, shima shugaba da bai san ya za'a yi ba ya fidda waya k'ira Mom da a wannan lokacin take tsaye kan Dad dake kwance yana baccin da kai da gani ka san ba na Allah bane, murmushi ta sake a lokacin da ta ga kiran Goje.
"Yaa Hajiya hajarki fa ta samu yanzu haka tana hannu sai yadda kika ce." Ta murmursa cikin dadin hakarta ta cimma ruwa ta ce. "Ina son ku kashe min ita, ku aika ta har lahira sannan ku tura min da shaidar aikinku don ina son na tabbatarwa da kaina ta mutu. Ina son ganin jinin IShIRAQA a wulakance." Daga haka ta sauke wayar cikin farin cikin samun nasara ta zubawa Dad da ke bacci bai san wainar da ake tauyawa ba, a hankali ta nufi cup shayin dake kan bedside table tare da murmushin keta tuna abin da ke cikin shayin da Daddy ya sha. Hannu ta sa a hankali ta shafa kansa kana cikin rada ta ce. "Good night, sweet dreams Ka yi bacci mai dad'i kafin gobe ka tashi ka tadda mummunan labarin da na tanadar maka a gobe." Daga haka ta sakar masa kiss a goshi kana ta fita tare da jawo masa da k'ofa ta rufe.
Goje na sauke wayar ya kalle yaransa ya fada masu umarnin Hajiya, ba tare da bata lokaci ba kuwa suka dauko fetir suka babbakawa motar wuta, Nazli tana ji tana gani suka kulle ta a ciki tare da bankawa motar wuta nan take kuwa wutar ta soma ci.