Shafi na bakwai
YARIMA BAHJAT 🌏
Na
Harira Salihu Isah
(Uwar Batoorl)
SHAFI NA BAKWAI
⭐️
Bayan Zainaba mai tsohon ciki da mijinta, mutane biyar kawai aka sake fillewa kai, domin su ma sun ƙi maimaita kalaman wannan dogarin, wanda duk wanda imani ya ratsa, ya kwana ya hantse a Addinin musulunci to ya san ridda ake nufi suyi ƙarfi da yaji.
Sauran gungun bayin kaf sun maimaita kalaman dogarin, sun kuma sha giyar kamar yadda Sarki Dungu ya umurta, sannan sun amshi cross, bayan an kammala duk wannan, Sarki Dungu ya sake miƙewa ya musu maraba ta musamman, tunda sun bi addinin aminci, sannan ya shaida musu suyi komai ba komai, su dai tabbatar sun tabbata a kan Addinin kiristanci, ya kuma rufe maganarsa da yi musu fatan su nishaɗantu da hidimar bikin da za'a gabatar a kwanakin.
"Maa!"
Wani matashin yaro ɗan kimanin shekaru goma sha ya ƙira sunan matar da ke riƙe da kafaɗunsa.
"Na'am yaron Maa."
Matar ta amsa, tana mai ƙoƙarin haɗiye hawayen da take yi a zuci, na abinda ya gama faruwa a filin, domin zuwa yanzu an sallami kowa, an wuce da bayi, su kuma kowa zai koma inda ya fito, in gida in wajan sana'a.
Yaron fari ne tas, kyakkyawa, duk da kasancewarsa yaro amma kana ganinsa ka san za'a yi ingarman matashi idan ya girma, ga wani gashi da ke tare a kansa mai sulɓi da tsayi, wanda mahaifiyarsa da yake ƙira da Maa ta tufke masa da roberband a tsakiyar kansa, sai yayi wani kyau na musamman.
"Maa, kema kuka kike a ɓoye ko?"
Yaron ya tambaya yana zubawa mahaifiyar tasa fararen grey idanuwansa, da suka kaɗa da alamar tausayin abinda ya gama gudana a filin masarautar, hatta Iris nasa da suke grey sai da suka nuna alamar damuwar da yake ciki.
"Kar ka ce komai TJ, mu tafi ko."
Maa ta faɗa gami da riƙe hannunsa suka nufi gidansu.
"Subha..nallah!"
Maa ta ƙarasa sauran kalmar a can cikin zuciyarta, a lokaci guda kuma ta saka hannuwanta tana rufe idanuwan TJ, saboda mummunan ganin da tayi, bayan sun shawo kwanar da za ta sada su, da layin da gidansu yake.
Sai dai toshewa TJ idanuwa da tayi bai hana shi sanin me ke faruwa ba, saboda kafun ta gani ya riga ta gani, wannan wani abu ne da tun bai fahimta ba har ya fahimce shi, sau tari ko da rana tsaka idan yana tafiya makaranta ko yana dawowa, haka yake ganin mace da namiji rungume da juna suna wasu abubuwan da bai san ya zai ƙira su ba, ya dai gane kiss shan baki, amma ɗaya abinda suke yi bai gane ba, da fari ya so tambayar Maa ko menene hakan, amma da ya fahimci Maa ba ta son yana ganin kalar abun sai bai tambayeta ba.
"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, astagfirullah Ya Rabbi, Allah ka tsare mu ka tsare mana imaninmu a rayuwa cikin waɗannan bahagwayen jama'a, Allah ka tsare mini Tijjani ka taya mana da tarbiyar shi, Ubangiji duk tsanani da lalacewa da taɓewan mutanen masarautar nan, Allah ma hanamu shiga sahunsu, ka kuma cigaba da rufa mana asiri har zuwa lokacin da su ma za su fahimci hanyar gaskiya kuma madaidaiciya."
Maa ta dire addu'ar da take yi a zuci, tana share wani siririn ƙwalla da ya zubo mata cikin ciwon kalar rayuwar jama'ar masarautar, wanda take tsoron ko a mafarki tilon ɗanta TIJJANI da suke ƙira da TJ saboda basaja, ya ce zai ji sha'awar aikatawa, dalilin da ya sa ko abokai basu barshi yayi ba, haka ma karatun da suke na Nasara(boko), saboda Baa na shi ya matsa shiyasa ta yarda ya saka shi, amma a gida daga ita har Baa na shi suna koya masa komai na Addini, suna kuma jan kunnensa akan ko a wasa kar ya yadda ya nunawa wani Addini na daban suke yi saɓanin wanda Sarki Dungu ya wajabta a masarautar.
Masarautar Buzjar wata iriyar masarauta ce, da duk wani aiki na assha ba komai bane a wajansu, idan Sarki Dungu ya ce Addinin kiristanci suke bi ta kan yi mamaki, domin duk da ba ta da wani ilimi ko sani sosai a kan Addinin, amma tana ji daga malamansu masu son gaskiya, suna ba da tabbacin abubuwa da dama sun haramta a Addinin kiristanci, sai dai su a nan sun halatta komai ne, shan giya, zina, caca, kisa, komai na alfasha ba komai bane a wajansu, ire-irensu a ko wace kalar Addnini kuwa, su suke ɓatawa Addini suna da kamala, a ɗauka haka yake kuma kowa haka yake, alhalin ɗaiɗaiku ne kawai suke haka.....
"Har kun dawo?"
Wani dattijo ya jeho musu tambayar, yana mai kau da idanuwansa a kan gyaran ƙwarya da yake yi, wadda ta kasance sana'ar shi, wato gyartai, shi ɗin ƙwararre ne kuma wanda kaf a masarautar ake ji da ƙwaryoyin da yake gyarawa ko sayarwa, saboda yadda suke kwankwaɗar giya kamar ruwa, sai ya zamana sana'ar ƙwarya na ɗaya daga cikin sana'o'in da ke cin kasuwa sosai a masarautar.
Maganar dattijon ne ya katse zancen zucin Maa, hakan ya sa ta sauƙe nauyayyar numfashi, gami da kallon mijin nata, wanda cikin idanuwanta kawai ya gani, ya tabbatar da tayi kuka, sababben aikinta a kaf tsawon shekarun, tun ranar da suka tsinci kansu a wannan masarautar.
"Baa!"
TJ ya ƙira sunan mahaifinsa ya na mai ƙarisawa wajansa ya zauna daga gefensa.
"Na'am TJ, har kun dawo?"
Baa ya tambaya.
"Mun dawo Baa, yau ma an kashe mutane a cikin bayin da aka kawo baƙi, har da wata mai ciki babba."
"Allah ya gafarta musu, Allah ya ji ƙan su ya musu rahama, Allah ya sa sun huta, Allah ya sa can ya fiye musu nan, kar ka saka damuwar komai a ranka, komai yayi farko zai yi ƙarshe, kuma dama duk mai rai mamaci ne, kamar yadda komai yake rubutacce tun ran gini tun ran zane, bawa ba ya wuce ajalinsa."
Baa yayi maganar da sanyin murya, kuma ƙasa-ƙasa sosai, domin gudun kar iska ma ya ɗauki sautin maganar ya kai ga wasu.
"Haka ne Baa, in sha Allah can ya fi musu nan, ka ga dama Maa ta sha bani tarihi da karatu a kan ire-iren haka, kamar dai labarin Ashabul Uƙudud, mutanen da su ma aka musu irin haka, wanda yayi ridda a bar shi, wanda ya ƙi a jefa shi a wuta, a lokacin har aka samu jaririn da yayi magana a kan shaida lallai-lallai Allah ɗaya ne ba shi da abokin tarayya......"
TJ ya kai wa Baa ɗinsa tarihin har ma da na Fir'auna da mutanensa.
Cikin jin daɗi, alfahari da kuma godiya ga Allah, Baa ya jinjinawa TJ kai, sannan ya cigaba da taya Baa aikin ƙwaryar da yake yi.
Maa da ta jima da shigewa gida, ko da ta shiga kasa yin ko wani aiki tayi, kukan da ta kasa samun sararin yi ɗazu a filin taron, shi ta zage tana yi iya ƙarfinta, gaba ɗaya kisar mata mai tsohon cikin ya tsaya mata a ƙahon zuciya, tana jin da tana da hali da ta kawo sauyi a masarautar, akwai buƙatar a bawa kowa damar yin Addinin da yake so, kamar yadda aka bar kowa yayi abinda yake so, kai kamata yayi ma a ce an tsaurara ne a kan kar kowa ya aikata abinda yake so, a saka doka a kuma bi, a hana zinace-zinace da sauransu.
"Ya Allah!"
Ta faɗa da sautin kuka tana ɗaga hannayenta sama.
"Ubangiji ga amanar da ka damƙa mana, ƴaƴa amana ne a wajan iyaye, Ubangiji ka tsare mana Tijjani!"
Ta ƙarishe tana sake rushewa da kuka.
"Amin Ya Rabbi, in sha Allah Tijjani ba zai bar turbar da muke ta gaskiya ba."
Faɗin Baa, wanda shigowarsa cikin gidan kenan, ya baro TJ da ayyukan ya shigo domin duba matarsa, sanin kuka za ta tayi har ciwo ya rufeta, kuma kamar yadda ya tsammani kukan ya samu tana yi, da yake dai sanin hali ya fi sanin kama.
"Baa!"
Ta ƙira sunansa kamar yadda TJ ke ƙiransa, idanuwanta cike da tsantsar rauni, damuwa da kuma ƙunci.
"Komai lokacine Maa Tijjani, ki bar wa lokaci komai, Allah zai bamu mafita a komai, kuma in sha Allahu muna da babban sakamako na lada a wajan mahaliccinmu, mun sadaukar da komai ne saboda wannan amana da Allah ya bamu na ɗan mu, in sha Allahu za mu girbi alkairin da ke bayan hakan."
Faɗin Baa yana rungume Maa, zuciyarsa na motsawa cikin karaya shi ma, wani irin rayuwa suke fiskanta da a baya ko a mafarki ba su taɓa hasaso yin sa ba, amma komai sanadine da dalili, ya na musu fatan wadatuwa da alkairin bayan komai.
MASARAUTAR ANFA
⭐️
Ko da Yarima Muhjan da dogarawa suka yi nisa da tafiya, maimakon tunkarar fada, sai gani dogarawan suka yi Yarima Muhjan ya ja tunga ya tsaya.
"Takawarka lafiya Yarima, Allah ya ja da kwananka magajin adalin Sarki, dama da hauni lafiya maida garin wani kango.."
Dogarawan da Fulani Samira ta haɗa shi da su, suka dinga masa kirari ganin ya dakata da tafiya, a zatonsu ko ba lafiya ba.
"Kunga ku juya abinku, ni sashin Fulani Babba zan je."
Yarima Muhjan ya faɗa fiska a daƙune kamar ƙaramin yaro ɗan shekara biyu.
"Gaba Salamun baya salamun Yarimanmu, magaji magajin Sarki, gatan Anfa, taƙaman Amfa, Allah ya ja da kwananka, muna mai ba da haƙuri domin Fulani ta ce kai tsaye fada za mu rakaka."
Faɗin wani dogari.
Ɓata rai Yarima Muhjan yayi, sannan ya ce, "Sai ku je ai, ni kun ga tafiyata."
Ba tare da yayi wata-wata ba ya kwasa a guje sai sashin Fulani Hajara.
Dogarawan suman tsaye suka yi, duk suka yi ƙasa da kan su sun kasa cewa komai, balle batun rufa masa baya.
"Amma kun san idan Fulani ta ji ba fada muka raka shi ba akwai matsala?"
Ɗaya daga cikin dogarawan yayi magana a sigar tambaya.
"Ba ma za ta sani ba, dan haka mu kama gabanmu, wannan sakalallen ɗan nata ma wahalar da kanta take ina zai iya sarauta, yaro shakara goma amma yana abu kamar wanda aka haifa jiya."
Wani daga cikin dogaran ya kuma faɗa, a haka suka ta mita ƙasa-ƙasa har kowa ya kama gabansa, domin ba za su wahalar da kansu ba.
..Yarima Muhjan bai dakata da gudu ba sai a palourn Fulani Hajara, duk kuma inda ya ratso sai dai bayi da hadimai suke kaucewa suna bashi hanya, sanin wannan kaɗan ne daga cikin aikinsa.
"Subahanallah! Yarima lafiya?"
Fulani Hajara ta tambaya cikin kulawa, ta ɗauka ko biyosa aka yi a guje.
"Fulani ina Daleesha?"
Yarima Muhjan ya tambaya ba tare da ya tsaya gaishe da Fulani Hajara ba, balle amsa tambayar da ta masa.
"Yanzu ba jimawa suka fice."
Faɗin Fulani Hajara.
"Yauwa ga Mamanta ma."
Yarima Muhjan ya faɗa idanuwansa a kan Ummin Daleesha, wacce shigowarta kenan.
"Maman Daleesha ina Daleesha take?"
Ya tambaya.
"Rankashidaɗe tana wajan Babanta."
Ummin Daleesha ta faɗa cikin ba shi girman shi na Yarima magajin Sarki.
"Abbi ko!"
Yarima Muhjan ya yi maganar ya na mai sake ficewa a guje, bai ja birki ba sai a gaban Daleesha da Abbinta.
Daleesha na kallonsa ta ɗan yatsine fiska cikin manyance, kamar wata babbar budurwa.
"Dal!".
Ya ƙira sunanta a yanke, cikin nuna farincikinsa na ganinta, kamar wanda ya shekara ba su haɗu ba, bayan iya jiya ne kawai ba su haɗu ba, ko shekaran jiya kusan tare suka wuni.
"Ba fa ka gaishe da Abbina ba."
Daleesha ta faɗa tana harararsa.
Girgiza kai Abbi yayi yana kallonsu da murmushi saman fiskarsa, Daleesha rigima, Yarima Muhjan tsokana, idan suna tare duk da ya girme mata da shekaru biyar, amma idan tana masa wani abu kai ka ce ita ce Yayarsa, shi kuwa ko damuwa ba ya yi, damuwarsa kawai ita.
"Abbin Dal ina wuni?"
Faɗin Yarima Muhjan, har sannan da fara'a a saman fiskarsa.
"Lafiya lau Magaji, ka biyo mutuniyarka kenan?"
"Eh, Abbin Dal."
"Madalla Yarima, Allah ya muku albarka, ke kuma Daleesha ba na son tsiwa fa, mutum ya zo wajanki sannan kina masa tsiwa."
"Abbi to ai shi ne ba ya abu a nitse."
"Abbin Dal kar ka mata faɗa."
Abbi bai sake ce musu komai ba sai cigaba da yi musu karatun da yayi, dukansu suna amsawa, Yarima Muhjan na ta sakin murmushi saboda ganin Daleesha.
"Na faɗa maka ka dinga yin abu a nitse kai ne fa Sarkin gobe."
Daleesha ta faɗa ta na hararar Yarima Muhjan.
"Dal na faɗa miki ba na son mulki ni, kinga yanzu ma Fulani saka dogarai tayi su raka ni fada, amma na gudo wajanki saboda ba na son zuwa."
Yarima Muhjan ya faɗa cikin yaranta da rashin wayo, har yana dariya.
"Kuma fa sai ka mulki masarautar nan, da ma Fulaninka ta bar wahala domin kai ne za ka zama Sarki, ai shi Yayanka ɗan Fulani Babba yayi gaba."
Daleesha ta faɗa.
Ɓata fiska Yarima Muhjan yayi kamar ƙaramin yaro, "Ni fa ba zan yi mulki ba, kibar maganar nan."
Haka suka wuni suna hirarsu ta shirme, lokacin sallah da yayi a tare suka yi sallan, suka kuma ci abinci tare kamar Yaya da ƙanwa.
Yarima Muhjan shi ne bai bar wajan Daleesha ba sai Yamma, daga wajanta ya wuce fada ya sa dogarawa su raka shi sashin Fulani Samira, wai domin ta ga alama daga Fada yake kar ta masa faɗa, ba ya son faɗanta tsorata shi take yi.
FULANI SAMIRA
A gaban wani kwari ta bayyana, sai dai ta juya ta bai wa kwarin baya, domin ƙa'ida ne na boka Tungu na kan kwari, ba za ka kallesa ba, da bai za ka iso gare shi kuma a haka za ku gama magana la tafi, idan ka kuskura kayi ido biyu da shi haukacewa za kayi.
"Tsafi ya baka sa'a, Tungu-Tungu mugun tari, Tungu-Tungu na kan kwari, ka kar maza uwayensu sun barka dan dole, Tungu-Tungu..."
"Ba wanda ya tsaface miki Ɗa, kuma hawansa kan kujerar Anfa tabbatacce ne, dan haka ki kwantar da hankalinki tamkar tsumma a randa."
Wani baƙiƙƙirin ɗin, mummunan jibgegen mutum yayi maganar, idanuwansa ƙur a waje guda ko ƙifta su ba ya yi.
Wani nauyayyar numfashi Fulani Samira ta sauƙe, sannan cikin damuwa ta ce, "Ina so na sake haihuwa, ina so na haihu."
"Ba zai yiwu ba!"
Tungu na kan kwari ya faɗa mata hakan kai tsaye.
"Amma.."
Cikin sauri ya dakatar da ita ta hanyar cewa.
"Yana daga cikin sharruɗana da kika sani tun kafun zuwanki nan, iya dama uku nake bayarwa a yi magana a kai, bayan haka ba musu ba neman ƙarin bayani, ki tafi, idan kin sake dawowa kya faɗi ko ma menene."
Tungu na kan kwari yayi maganar da wani amon sauti mara daɗi.
Fulani Samira daga tsayen tana ɗangale da ƙafa guda, ta shanye idanuwanta ta muma shiga karanto wasu kalmomin surƙulle.
"Mtsw!"
Fulani Samira taja guntun tsaki, lokacin da ta zauna a bakin gadonta, gaba ɗaya kanta a cunkushe yake, Tungu na kan kwari gaba ɗaya birkitaccen mutum ne kuma ruɗaɗɗe, mai ruɗa mutum.
Ji take kamar dai ta kai wa La'anannen dattijon ziyara, amma dai bari ta sake komawa wajan Tungu, idan ba ta samu abinda take so ba sai ta sauya tasha, dama ai da tsohon zuma ake magani.
***Masu daraja HABIBTIES, idan baku mance ba tun a farkon labari, na shaida muku wannan tafiya ta daban ce, kuma a cike take da ruɗaɗɗun lamura rikitattu, waɗanda duk yadda za ka dubesu a taƙaice ba za ka taɓa hangar ƙarshen su ba, kai ba ma za ka banbance zare da abawa ba, sai ka je har ƙarshen labarin, ku dai ku bi Uwar Batoorl ƙafa da ƙafa don ta warware muku abubuwan da ba ku gane ba, kuke kuma tambayar zuƙatanku, ina mai farin cikin sanar muku da mun kusa fara shafukan kuɗi, kuma tun daga sannan za ku fara samun amsoshin tambayoyinku***
Follow my page's
●WATTPAD
@Uwarbatoorl96
●AREWABOOKS.
@Uwarbatoorl96
●TIKTOK
@Uwarbatoorl96