11
Chapter.11
Tsaye ya ke a bakin window office ɗinsa ya harɗe hannayensa biyu a baya ya zubawa farfajiyar company ido, lokaci zuwa lokaci ya ke cire hannu yana zuƙan tsinken sigari da ke tsakanin yatsun hannunsa na hagu. Fuskarsa dai kadaran kadaham baka gane yanayen da ya ke ciki, a hankali a ka yi knocking ya bada izinin shiga, cikin sanyi jiki saurayin da aƙalla ba zai haura shekara ashirin da takwas ba ya ja ya tsaya bayan ya rufe ƙofa, hannu ya sa ya soma sosa kyarsa cikin tsoro da fargaban hukuncin da zai hau kansa a yau na kofsawa boss na sa aiki da ya yi a jiya bayan irin gargadinsa da ya yi a kan haka.
Bai juyon ba yana fuskantar windown ya ƙira sunansa a kaushashe cikin muryar da babu wasa cikin ta. "Sam." cikin inda inda ya ce. "S..sir." gabaki ɗaya ya sadakar yau ko ya rasa aikinsa da ya yi shekara da shekaru yana yi ko kuma a kwace salary na wannan wata idan bai yi sa'a ma harda watan gaba za'a cire, dan haka cikin muryar da ta bayyana tsantsan sarewarsa ya ce. "sorry sir, dan Allah ka yi min rai ka gafarce ni, I did exactly what you said sir. Amma ban san ya a ka yi we miss the numbers." Ya ƙare cikin karyewar muryar jikinsa sai rawa ya ke, jira kawai ya ke ji irin punishment ɗinsa a wannan karon dan wannan shiru da Sir ya yi akwai abin da ya ke ƙullawa wanda kuma k'arshen sa ba zai mishi kyau ba.
Sai dai ga ɗumbin mamakinsa sai ya ji ya ce. "aiki ya yi kyau, an samu abin da a ke so har ma ya gauta." Cikin rashin fahimtar abin da ya ke nufi ya ce. "Sir?" A hankali slowing kamar baya so Zaid ya juyo ya fuskance shi, tare da takowa gabansa ya bubbuga kafaɗarsar ya ce. "You have done a great job." Daga haka ya koma kan kujera ya zauna cikin harɗe ƙafa ya ɗaura ɗaya kan ɗaya, tapping deskt ya ke a hankali kamar Wanda ke bin baitin waƙa da gani ya na cikin nishaɗi. "Fad'i dukkan abin da kake so zan mallaka maka, gida, motar, ko ƙarin albashi?" just mentioned it.
Baki sangame Sam ke kallonsa dan har yanzu fa shi bai gama fahimtar ina Ogansa ya dosa ba, shi da ya zo amsan punishment d'in lalata aikin da ya basa bisa kuskuren ɗaya da suka yi shi ne shi kuma ya na fadin wata magana ta daban da bai san ina ta dosa ba. To kodai Sir ya bugu ne da bai san me ya ke fad'i ba ko kuma wanasa kawai ya ke dan ya ga reaction na sa?
Jin ya yi shiru bai magana ba ya sa Zaid gyaran murya. "Ka yi shiru ko duk ba su maka ba?" Then name it fad'i me kake so?" Da jin haka cikin rawar murya da tsoro da mamakin da bai gama sakinsa ba ya ce. "Sir duk abin ka ga ya dace kawai bani da zaɓi ai ni." Sai kuma ya sosa kai. "Amma motar ma ta yi Sir." Ya faɗa cikin farin cikin da ya soma debansa, gaba ɗaya sai ya manta ma da wani abu tsoro da ya shigo da shi sai farin ciki da zumuɗin da ya maye gurbin haka.
Shi dai bai san ya a ka yi hakan ta kasance ba, a iya sanin sa dai sun kofsa aiki amma tunda shi Oga bai gane ba ai shi kenan tun da an samu abin da a ke so is a win for him. Dan ba zai yi saken da har wannan damar ta kwace masa ba. Ya a ka yi, me a ka yi aiki ya cika bai sani ba amma dole ya yi anfani da wannan damar shima ya tatsi abin da zai tatsa koda za ta b'ace a gaba ya kasance ya more wani abun shima.
Zaid ya bud'e locker da ke k'asan desk dinsa ya fito da rapan kud'i y'an dubu duba guda uku ya jefa masa, da sauri Sam ya saka hannu ya cabke su cikin washe baki ya ke godiya.
Ya sake miƙa masa mukullin sabuwar motarsa da Nazli ta siya masa wacce ko sati ba ta yi a hannunsa ba duka duka hawansa cikin ta bai wuce sau biyu ba. "Na baka ita halal malak sai yadda ka yi da ita, dama ni can motar ba wani yimin ta yi ba." Ya fad'a cikin gatsine, Sam kuwa baki har kunne, ya rasa da wani baki ma zai yi godiya. Motar da a kan idonsa a ka siya da milyoyin kuɗaɗe dan kawai a faranta masa ya ji dad'i, amma shine ya ke wani faɗin bata masa ba? Lallai a bar masu kud'i da kuɗinsu, yo shi ai gaba ta kaisa.
Cikin wannan yanayen a ka turo ƙofar office a ka shigo ba tare da knocking bare sallama, Neesah ce. Sanyi take cikin wasu matsatsun riga da skirt yan kanti da suka bayana ilahriin surarar jikinta, ɗan jim tai ta tsaya tana kallonsu daya bayan ɗaya sai kuma cikin yauƙi da karairaya ta nufi Zaid da shima na sa idanu na kanta tun da ta shiga.
Ta rumgume shi tare da sakar masa pick a lips kana ta d'ago ta kalle Sam da ko a jikinsa yana ta juya mukullin motar yana sake warge baki don farin ciki domin kasantuwarsu a haka ba sabon ganinsa bane.
"Sam." Sai kuma ta yi murmushi irin wanda ke nuna tana cikin tsantsan farin ciki nan, ta maida kallon ta ga kuɗi da mukul motar da ke hannunsa ta sake sakin wani murmushi ta ce. "Gaskiya you've done a great job, ya kamata nima na ba ka tukwici aikin da ka yi." Daga haka ta saka hannu cikin jakar hannunta ta fito da kuɗaɗe ta basa. Sam dai baki har kunne, ya rasa ma ta ina zai fara.
Iya sanin sa dai bai cika aiki kamar yadda suke iƙirari, don mistakes d'in numbers ɗaki ya yi maimakon ya shiga ɗaki na 136 Wanda shi ne dakin da Nazli take ciki sai ya shiga daki na 139. Sai bayan da suka gama aika aika shi da abokinsa suka ga fa ashe sun yi ɓatan hanyar, to amma abun tambayar a nan shi ne, idan su da a a ka bawa aikin kwangilar basu yi ba wa to wa ya yi? Wannan tambaya ce da ba shi da amsar ta, dan haka sharewa ya yi kawai ya barwa Allah sani maida hankali kan damin kudin dake hanunsa sai juyawa yake yana farin ciki.
Wuri Neesah ta samu ta zauna kusa da Zaid da har yanzu bai dena zugan sigari ba, ido ta ɗan zura masa ta ɗaura hannu kan ƙirjinsa da ke cikin riga tana shafawa a hanakli. "Baby na yi missing na ka sosai fa, kai kuma na ga kamar ba ka yi farin cikin gani na ba. Why?" Bai bata amsa ba sai idanunsa da ya lumshe kamar me tunanin, dan janyewa ta yi daga jikinsa ta yi masa ƙuri da idanu cikin karantan yanayensa.
"Ohh! Don't tell me you are still mourning your divorce?" You're still mourning your darling ex wife ko?" Sai kuma kamar wacce a ka kunnawa wuta ta miƙe tsaye a zafafe take fadin.
"kar ka ce min har ɗan zaman da kuka yi ka fara sonta?" Look Zaid don't try me, wallahi don't dare me ka san ni kuma ka san what am capable of doing. Har ni za ka ci amanata?" Ta nuna kanta. "To wallahi koda da danshin sonta ne a zuciyarka to ka gaggauta cire shi if not...ta ja maganar ta ja kwafa ta sungumi jakarata ta juya cikin fushi za ta bar office ɗin ya riƙo hannunta da sauri cikin ƙarfin nama ya jawota ta faɗa kansa.
Wani ɗan iskan murmushi ya sakar mata ya soma shafa gashin dokin da ke kanta ya ce. "Daɗi na dake yawan hawa kamar yeast sam baki da hakuri, kema kin san ba wacce na ke so sama da ke, and zan iya yin komai don na faranta miki kuma kin shaida. kamar yadda na amince ga buƙatar ki a kan auren nan tun farko duk da ni ban so ba amma saboda son da na ke miki da umarnin Mami na aminci. I did everything that you asked of me ba tare da ƙi ko jayayya ba don ina tsoron ki ba sai dan soyayyar da na ke miki. Remember, ina zaman zamana kika same ni da wannan kuɗiri na ku kuma na bada goyon baya so why are you paranoid know kuma?" Ko ba ki yarda da ni ba ne?"
Ta ɗan ja ajiyar zuciya ta sauke jin bayanensa, duk da ba wai ta gamsu dare bisa dare bane amma sai ta ture komai gefe tunawa fa da yanzu Nazli bata cikin rayuwarsu balle ta damu ta shiga fargaba, Mommy ta riga da ta yi magninta. "Hmm to ni ina na sani abu zuciya, kuma ba dole ka sa na yi tunanin haka ba tun jiya da wannan abun ya faru na ke ta ƙiran ka amma ba ka ɗaga ba. Abun da ba ka taɓa min ba, zargin da na ke kuma ai kai ka bada hanya shi ya sa na na matsa a ka canja plan daga na farko zuwa wannan dan na lura idan ba i yi haka ba to tsam sai ka fada sonta ka bata mana aiki karshe an yi ba a yi ba." Ta faɗa cikin sake nazartar yanayensa amma bata ga wata alama da ta nuna yana son Nazli ba, hakan sai ya ƙara bata nutsuwa har ta saki ranta.
Ya shafa fuskarta zuwa lips ɗinta kana a hankali ya ce. "Am sorry baby, but kema kin san she's not my speke i love dem sultry." Ya faɗi hakan cikin kanne mata ido irin dai na shegun mayaudara, saboda dadin kalamansa ta manna kiss goshi da kumatu. Fahimtar kallon da ya ke mata ya sa ta miƙe ta nufi ƙofa ta saka key ta kana ta koma ta soma rage suturar jikinta ta faɗa kansa, cikin kwarewa da iya bariki ta soma cire boton din rigarsa a hankali suka soma shafar juna cikin shauƙin gangar shaiɗan da ke bugawa masu, suka lula wata duniya ta daban wacce babu komai cikinta sai tarin zunubai da tsinuwar mala'iku. Sun biyewa jin daɗi na kalilin lokaci suka aikata saɓon da Allah na fushi da wanda suke aikatawa, yadda suka zage wajan farantawa juna da kuma shaidan kai ka san ba yau suka fara sun saba da abun su bayan a fage.
******
Dad zaune ya ke a office ɗinsa ya harde hannayensa biyu ya tallafi kansa da ya ke jin kamar ba na sa, ji ya ke kamar yana cikin wata duniya ta daban ba ta mutane ba. Jinsa ya ke kamar yana saman ruwa yana tafi, gaba daya abun duniya ya bi ya ishe shi, tun da wannan abun ya faru ya karo Nazlinsa a gidan bai sake samun nutsuwa zuci, tunani, fargaba da tsoro ne sun dabaibaye shi. Gashi kuma duk yadda ya yi ƙoƙari kan haka sai abu ya faskara, domin da ya yi yunƙurin neman ta sai ya ji kamar a na basa umarnin ya aje komai, abun ba iya nan ya tsaya ba, don da zarar ya furta sunata sai ya ji moƙoshinsa ya riƙe tam kamar wanda a ke shaƙawa wuya. Shaƙace bata wasa ba don har dagana shi take da yin suma banda wasu abubuwa mara dadi da ke faruwa dashi, ji ya ke kamar zuciya ce kadai na sa amma kwakwalwa da ganganr jiki ba na sa bane dan sai ya yi abu bai san ya yi ba kamar wanda a ke dannawa remote ya yi abu.
Bayan nema da ya yi mata a lokacin da driver sa ya kawo masa labarin fashin da a ka yi masu a hanya suka tafi da ita, sai da ya faɗi saboda mugun hawa da jininsa ya yi. Idan hankalinsa ya yi dubu to ya tashi, hakan ne ya sa bai ko tsaya an sallame shi daga asibiti ba ya koma gida inda ya bada police report kan nemo ta. Saboda damuwa bawan Allah bai ci bai sha idan ka gansa sai ya yi mugun baka tausayi, sai dai abun mamaki duk wannan damuwar da kuma irin sintiri da ya ke cikin station ba dare ba rana, haka kurum ya tshi rana ɗaya ya janye report da ya yi na nemata. Duk yadda ƴan sanda suka kai ga son sanin dalilin janyewarsa duk da ƙoƙarinsu na ganin sun samu inda take, ya hana. Sai bayan da a ka yi hakan ya zo ya soma tunanin ya a ka yi?
~~~~~
Gaskiya ne Aminiya kina cin duniyar ki da tsinke, yanzu dai hankali ya kwanta sai da yadda kika yi da Muktar kuma." Faɗin Hajiya Ruky mahaifiyar Zaid, suna zaune ne cikin sabon gidan da ta saka Daddy ya siya mata, wanda za'a iya masa laƙabi da aljanar duniya dan ba abun da ya risa domin har ya kusa ƙeta na su da suke ciki. "Ke dai bari kawai duniya sabuwa sai yanzu na ke jina a raye, ba tare da na tashi a kulli yumin ina ganin shegiyar yarinyar nan na numfashi ba. Jina na ke sakayo." Mommy ta yi maganar cikin kai glass cup baki tana sipping ɗin orange juice a hankali. "Aikuwa dai na ga alama, ko daga annurin fuskarki ya nuna haka. Yanzu da komai ya daidaita,ya batun auren yaran nan yaci a ce an yi an gama dan na gaji da kallonsu a haka." "Uhmmm." Mom ta sauke ajiyar zuciya. "Kin san Allah, tun da na ke tsawun rayuwata ban taɓa ganin mutum mai taurin kai da kwarjinin mutumin nan, duk iya makirci da aikin da na ke kansa tsoron taransa da ko wacce magana magana na ke, musamman da ya kasance kan batun auren nan. Dan wallahi karki ga wai ina faɗa ya ke aiwatarwa yana komai ne da bai shafi tsinanniyar yarinyar can. Na rufe masa baki ne da riƙe hannunsa daga yin wani yunƙuri da zai saka ya gane ina da saka hannu cikin ɓatan ta. Amma duk wani abu da kika san ya shafe ta komin ƙanƙantarsa bai wasa da shi, na rasa gane wani irin asiri Ishiraqa tawa masa kan yarinyar kafin tafiyarta ba. Yadda kika san zuiya haka take a wajen ta, kina dai ganin yadda ya koma kamar maraya kamar matar da miji ya mutu ya barta da tarin 'ya'ya ba ta da wanj dogoro. Yaushe kike tunanin zai same sa da wannan batun? Barshi kawai idan komai ya lafa na san yanda zan ɓullo masa, amma yanzu dai kam a ɗan jikirta bai wuce ita Neesah ta gama karatunta tun da saura ƴan watanni ne kawai. Kuma gaggauwar me muke bayan yara na son juna ai komai ya zo gidan sauke, da ba don wannan plan ɗin ai yanzu ya ci ace suna tare cikin inuwar aure."