JA DA BAYA...

Mafari

by @meelahbazata978

JA DA BAYA....
Bookk 1
Page 1✍️
Meelah bazata 

Bismillahirrahmanirrahim
Kallo ɗaya za ka yi wa fuskar kamilallen mutumin ka san cewa yana cikin tsananin tashin hankali. Aruɗe yake sosai da sosai duk da AC ɗin da yake amfani a kayataccen falon da za mu iya kira aljannar duniya. Amma kallo ɗaya za ka san yana cikin taraddadi. Safa da marwa kaɗai yake yi a cikin falon, yayin da a gefe guda wata mata ce tana kuka kamar ranta zai fita Kai daganin fuskarta kasan tana cikin damuwa Mai tsanani kuka take tana
Faɗin,nashiga uku Alhaji, ina cikin tashin hankali. Ya Allah ka dube mu, Allah ka taimake mu. Me yasamu yaron nan?"abbansu shiyasa tun da fari na guji wasu abubuwan dasuke faruwa Amma kake Kara karfafa masa gwiwa yanzu ga abinda yasake faru da wanne zamuji ga mazaje abinda ya faru dashi ,kawai se ta fashe da kuka da alama ta Tina Wani abu Mai zafi arayuwarta
Yayin da shi kuma yake faɗin, "Haba Hajiya, ya za ki faɗi haka? Ke kanki kin san masu farautar yaron nan suna da yawa. Kwanaki a cikin gidan nan aka saka masa guba. Saboda haka ki yi haƙuri, mu jira mu ga abin da zai faru."fuskarsa dauke da damuwa Mai tsanani yake magana Gefe guda kuwa tsohuwa ce ke ta sharbar kuka tana ihu tana cewa,
"Shikenan an kashe min jika. Jikan da bai ji ba bai gani ba. Yaron nan yana ganin jarabawa."
Faɗi take,
"Muhammadu, mu tafi mu kai report gurin 'yan sanda."Kai sekace ba jami'i gaba daya ka kasa daukar Wani mataki
Ya ce,
"Hajiya innah, da boyayyiyar number aka kira ni, sannan shi kuma number dinsa ba ta shiga. Na kira Mahmud, ya ce min bai gan shi ba."
Ana haka wani mutum ya shigo falon shima hankali tashe yana faɗin,
"Yaya, ka ƙaryata ni. Ka ce min abin da aka kira ni aka ce min ba haka ba ne. Yaya, kar ka gaya min cewa Zakina ya mutu. Yaya, don Allah kar ka ce min Bobo ya mutu. Yaya, zuciyata za ta iya bugawa."
Kawai sai ya fashe da matsanancin kuka.
Yayinta ita ma tsohuwar ta ƙara faɗin,
"Wayyo! Shikenan."
Kamar an tsikari matar ta tashi da sauri. Tashinta ya yi daidai da shigowar Abu biyu: shigowarsa da kuma shigowar saƙo.
Na farko shi ne shigowarsa ɗakin cikin izza. Ya Allah! Me zan iya cewa? Wani irin tsayayyen mutum ne mai cike da izza a ƙirar jiki. Amma fuskarsa ba ta fito ba saboda akwai face mask a fuskarsa, sannan P-cap ce a kansa idanunsa sanye da bakin glass ya Allah bansan tayadda zan kwatanta muku Shiba Amma abu daya Dana shaida anan shine farine har Yana daukar ido atare duk sukai kansa da gudu kowa na kokarin gasgata abinda idonsa yagani inda wannan mutumin yarigasu karasawa ya rungumesa Yana fadin bobona ykk Zaki ba abinda yasameka ko,kallon mutumin yayi Yana girgiza Kai da alama DAI bayason magana Dan tun shigowarsa bece komaiba,Kuma basu fasa tambayarsa da alamar gajiyawa yace Abbie ba abinda yasamenifa,sannan yakarasa wajan mahifiyarsa ya rumgumeta Yana girgiza mata Kai saurin goge hawayen idonta tayi tana Kara kankamesa ajikinta kuka sukaji anfashe dashi wannan tsohuwarce ke fadin shikenan dayake ni baya Sona ko kallo ban isheshiba ta iyayensa kawai yake kallonta kawai yayi Yana murmushi inda ummee tace yashiga yaje yai wanka yafito Abbah ne yabude sakon da aka tura masa inda abinda sakon ya kunsa shine yakukaga wannan salon sharar fage kawai aka fara ko wasan baa faraba

 " Ya kukaga wannan salon sharar fagen✍️, ko wasan ba'a fara
1.Waye hakikanin Bobo/Zakina?* Me yasa ake farautar rayuwarsa😳shin  wayasaka  masa guba?
2.  *Waye ya turo sakon?* 
3.  *Me yasa bai so ya yi magana ba tun da ya shigo?* Wane irin rauni yake ɓoyewa?

Kai wannan book dinfa ya wuce duk yadda kuke zato 😂