Yarima Amir

Chapter 1

by @rashmarraka940

YARIMA AMIR

      By

Rashma
   
             *Gargaɗi.*
  Ban yarda wata ko wani ya sauya min labari ba ta ko wace siga banyarda ba.

    

   بسم الله الرحمن الرحيم

🆓p 1 

      Babban masallacin juma'a cike yake da jama'a manya mutane  da sarakuna daban_daban gaba ɗaya masallaci ya ɗauki shiru bakajin komai sai sautin muryar  malam Sagir yana huɗuba cike da kamala da harshe mai sauƙi yake huɗubar har ya kammala aka tada sallah bayan angama sallar juma'a aka fara shirin ɗaurin auren da ya tara wasu daga cikin mutanen inda malam Sagir ya ɗaura auren Amar da amaryarsa Ayra ya rage ɗaurin aure ɗaya wanda dangin amaryar ne basu ƙara so ba  haka aka zauna jiransu gashi  ana ta kiransu basu ɗaukar waya hakan ya matuƙar ɓata ran mai martaba amma kamilalliyar fuskar sa ta ɓoye hakan inda a ɗayan gefe da angwayen suke zaune fuskar Amir ta nuna ɓacin rai ƙarara dama shi baya iya ɓoye fushin sa hannu Amar ya ɗora akan nasa sun shafe kusan awa ɗaya ana zaman jiransu har mutane sun fara watsewa waɗanda suke da uzuri  sai ga ɗan aike daga gidan su amarya wai suyi haƙuri sun fasa wannan karon kam sarki ya nuna ɓacin ransa ƙarara malam Sagir yana ganin haka yace "ranka ya daɗe zan bawa Amir ƴata idan yana buƙata."

        Lumshe idanu sarki ya yi dan yasan tabbas sunyi hakan ne dan su muzanta shi su kunyata shi ga baƙin da ya gayyato waɗan da sunzo daga garuruwa da dama harda waɗanda suka zo daga ƙasar waje be iya magana ba sai jijina masa kai da ya yi Galadima ne ya yi malam Sagir bayanin abinda sarki yake nufi da gyaɗa kansa a take aka ɗaura auren Amir da Hafsatu manga, fisge hannun sa ya yi daga riƙon da Amar ya masa ya miƙe ya bar masallacin a fusace da ido sarki ya bishi da shi dan ya karanto damuwa sosai a fuskar ɗan nasa kuma wanda ya fiso a duk cikin ƴaƴan sa amma yana jin ciwon hallayar sa gashi dai duk yafi yaran sa kyau d ƙwar jini da cikar haiba amma munanan halayen sa duk yasa ya tsane shi numfashi ya sauke dan shi kansa yana jin tausayin ɗan nasa, a guje ya figi mota  ko takan fadawan sa baibi ba suma suna ganin yanayin sa suka kame kansu sosai yake gudu akan titi dan shi yama rasa ina zaije yaji sanyi a ransa gefen hanya ya samu ya tsaya ya kifa kansa akan sitiyarin motar yana tuna maganganu da sukeyi tsakanin sa da abar son sa da tsara yanayin zamansu "kasan Allah my prince na fika buƙatar injini kusa da kai."

    "To me kika tanada min a daren farkon mu?"

    "Ai a daren ba'a magana dan zan shayar dakai ne zumar da baka taɓa sha ba."

   Dariya ya yi "kice ranar zan kwana noma kenan."

    "Aikam dai idan ma bakada ƙarfi ka nemi magani dan sai naga iya jarumtarka."

    Rumtse idanunsa ya yi akan azabar sara masa da kansa ya yi a fili yana cewa "me yasa Raudah zatayi min haka saida ta bari zuciyata ta mutu akanta sannan itama zata juya min baya  me yasa mata basuda amana ne ni tawa ƙaddara kenan bazan taɓa samun macen da nake so ba kenan   me ƴar gidan malam ta sani na rayuwa bayan ta  yi ta zumbula min hijabi..........."

    Ƙarar wayarsa ne ta dawo dashi daga duniyar tunani da lula sweet mom ya gani ɗagawa yayi kafin ya yi magana ta ce "duk inda kake kazo ina son ganinka."

    Be iya mata magana ba sai kansa da ya gyaɗa sauke wayar ya yi ya duba time ya ga lokaci yaja sosai dan har an kusa magariba baisan ya daɗe sosai a nan ba tada motar ya yi yafara tafiya cikin minti talatin ya isa masarautar su mai cike da tarihi da ƙayatuwa a kullum cikin gyaran ta ke tundaga get ɗin farko ake gaida shi amma ko kallo basu isheshi ba gurin ajiye motoci ya ajiye motar sa sannan ya fito yana riƙe da wayar sa da makullin motar sa ɓangaren momyn sa ya nufa duk da yaji ana kiran sallah a masallaci masarautar can ƙasa ya yi sallama Amar ne zaune yasha adon shi daka gani kaga sabon ango  yana ganin sa ya tashi ya rungume sa yana cewa "Rabin jiki gaba ɗaya inata neman ka banganka ba kuma ina ta kiranka baka ɗagawa."

     Bai tanka masa ba sai kallon Momy da ya yi "ku tafi masallaci ga acan ana tada sallah idan kundawo zamuyi magana."

   Juyawa kawai ya yi ya tafi da kallo ta bishi dan tasan yanzu kam sun ƙara sa kashe masa farin ciki da walwala da yakeyi a kullum..........

****  ****  **** ****  ****  **** 

      Da fara'a Malam Sagir ya shigo gidan sa babban gida ne dan iya ƙeruwa ya ƙeru, ma aikatan gidan duk sun lura da yau malam yana cikin farin ciki Babban falon sa ya shiga mai cike da kayan more rayuwa yana zama matan sa suka fara shigowa suna gaida shi harda yaran   amaryar sa ya kalla ya ce "Nafisa  ina Hafsa ne ban ganta ba?"

    Cike da ladabi ta ce "ranka ya daɗe taje wankin kai ne amma nayi waya da ita tace ta kusa dawowa."

    "To badamuwa." Kallon Amatullah ya yi da take zaune kusa da shi "kije ɓangaren yayun ku kice musu suzo ina kiransu......."

   Bai gama rufe baki ba sai ga zaratan maza su biyar sun shigo saida suka gaida shi sannan babban cikin su ya ce "Baba naji abinda ya faru a masallaci kana ganin ba'ayi kuskure ba yaron Hausa tarbiyya ko kaɗan."

    Tsuke fuska Malam ya yi "kanada hujjar abinda akace yana aikatawa ne a kullum ina hanaku shaidar zur amma kamar bakusan hukunci mai shaidar zur ba."

    "Assalamu alaikum."
Wata siririyar murya mai kamada sarewa ta rangaɗa sallama sanye take da dogon hijabin ta har ƙasa sai siririn glass dake akan fuskar ta "wa, alaikumussalam Hafsatu na kin dawo?"

    Kusa da shi ta zauna ta yaye ƙaton hijabin ta "eh Babana na kaina na dawo anyi juma'a lafiya?"

     "Lafiya lau Alhmdulillah."

    Kallon yayun ta ta yi taga babu wanda ya kulata sai kallon ta da sukeyi dariya ta yi "oh ni manga hala na canza muku ne kuketa kallo na haka?

    Kafin su bata amsa Baba ya yi gyaran murya "Hafsa meye matsayi na a gurin ki."

   Take gaban ta ya faɗi dan jin yanayin da ya yi magana kallon a ta yi taga ba alamar wasa wasu yawu ta haɗiye sannan ta ce "kai mahaifina ne wanda nake ji dashi sosai."

    Kuɗi ya ciro ya ɗora mata akan hannu ta da kallo ta bishi "Alhmdulillah Hafsa wannan sadakin ki ne a yau na ɗaura miki aure."

   Ƙwalla ce ta cika mata idanu "to Baba nagode Allah ya ƙara girma ya bani ikon maka biyayya."

   Murmushi ya yi yaɗora hannu sa akan ta "Ubangiji ya miki Albarka yabaki ƴaƴa nagari masu albarka ba gaba ɗaya ɗakin da amin suka amsa miƙewa ta yi ta ajiye kuɗin a gurin da ta tashi "baki tambaye ni waye mijin naki ba."

   Yaƙe ta yi dan tana gab da fashewa da kuka "to Baba waye ?"

    "YARIMA AMIR NE."

     ***